Showing 21001 words to 21816 words out of 21816 words

Chapter 8 - WANI AUREN BOOK COMPLETE BY SADIYA ABDULL.txt

Anti Kursum ya fi yin daɗi?"

Da mamaki Yusra take kallonsu, ta ja abincin ta yi cokali ɗaya ta ji babu wata matsala, ta ce"Ita na Anti Kursum ba irin wannan ba ne?"

Afna ta ce"Nata ya fi daɗi, kuma da wuri take gama yi mana, ta ba mu a baki".

Yusra kanta ya kulle tana kallon abincin ta ce"Mene ne bambancinsu?"

"Yara ma suka gane ballantana ke? Haba Yusra yanzu za ki ce duk tsawon lokacin nan ba ki gane canjin ɗanɗanon abinci da aka samu ba a gidan nan sanadin Kursum?" Sadiq ya faɗa wanda ba su san da shigowarsa ba

Cak ta tsaya tana kallonsa da auna maganganunsa, ya ce"Wannan ba wani abun mamaki ba ne, kin san an ce dama kowa da irin hannunsa, ni ɗakko min abincina na koma, yunwa ce ta dawo da ni, Kursum kafin sha biyu take kai min abincina har na saba da ci da wuri, ke kuwa sai ƙarfe biyu, duk yunwa ta gama cinye mutum".

Ai Yusra ji ta yi kamar an zare mata laka saboda tsananin mamaki, ba ta gama tsinkewa ba sai da ta ga ya shiga kitchen ya ɗakko abincin ya zauna zai fara ci, ta tashi ta je ta tankwaɓe cokalin hannunsa abincin da ya ɗibo ya zube, ya ɗago yana yi mata kallon mamaki, ta ce"Abincin da babu daɗi za ka ci? Ai sai ka jira Kursum ɗin ta dafa maka! Wai da gaske ni kake faɗawa wata ta fi ni iya girki?"

Sadiq ya ce"Yaushe kika ji na ce haka? Don na ce an samu canjin ɗanɗano ba shi yake nufin nata ya fi daɗi ba, shekararmu nawa da nake ina cin abincinki? Idan ba ya yi mini daɗi za a kai wannan ranar ban faɗa ba? Inda kin zauna kina sauke hakkin gidanki ta ya ma Kursum ta kai na ci abincinta?" Ya faɗi hakan, don kuwa bai ga abin da zai sa ya yi sake Kursum ta bar gidan nan ba, don ko ta fannin girki kaɗai an samu ci gaba, shayi ma wannan idan ta dafa sai ya ji bambanci da na Yusra.

Ta ɗan ji dama-dama a zuciyarta ta ce"Amma ai ka ce ita da wuri take kai maka abinci, mai yasa za ka yabeta?"

Ya ce"Dole fa idan an yi min na faɗa, kullum ba kya kai min abinci sai kun gama ci ke da yara, ita kuwa kafin sha biyu ta gama ta kawo min".

"Hmm!" Ta sauke ajiyar zuciya, sannan ta ɗakko masa wani cokali ta koma ɗakinta ta zauna ta yi shiru, ba don tana son Kursum ba da babu abin da zai hana ta canzo wata, don ta san mijinta ba akan komai yake mayar da hankali ba, tun da ya fara wannan ƙananun maganganun akwai dalili, amma koma mene ne ta saka a ranta za ta fara kula.

Daddare yana falo yana chart da Ummu, wacce take ta ce masa ya je ya kwanta yau Anti tana gida, shi kuma sun ɗakko maganar da ba ya so a katse, kwatsam sai ji ya yi an warce wayar hannunsa, ya ɗaga kai ya kalli Yusra wacce bai ji ko motsin fitowarta ba, da sauri ya kai hannu zai warce wayar ta riƙe ta ƙam cikin hargagi take cewa"Sadiq wace ce Ummu? Wace mai tsautsayin ce ta shigo mini rayuwata!? Sadiq!"

Ransa a ɓace ya ce"Malama ba ni wayata".

Tana huci tare da zazzare ido ta ce"Ba zan bayar ba!".

Ya ruƙo ta, sai ga su suna kokowa har ya ƙwace wayarsa ya shige ɗaki, ya barta durƙushe a falo tana kuka. Zama ya yi a bakin gado ya dafe kansa, yana tunanin bai kyauta mata ba, sai dai wata zuciyar tana faɗa masa hakan ba komai ba ne, tun da ba haramun ya aikata ba, shi kam a yadda yake jin Ummu a cikin zuciyarsa babu me iya raba shi da ita, kuma ya ma saka a ransa ya zama dole ya nunawa Yusra ba yana ƙin kula mata ba ne saboda tsoron kishinta ko kuma ba shi da niyyar ƙarin auren ba, saboda haka dole a cikin satin nan ya san wace ce Ummunsa, kuma su daina wasan ɓuyan nan su fuskanci juna, kowa ya san the game is over.

To fa! Kuna tunanin idan Sadiq ya san wace ce ɓoyayyiyar masoyiyarsa zai ci gaba da sonta? Sannan ya Yusra za ta yi idan auren ya tabbata?

Ga dai Ali nan an tarfa shi a cikin gidan Hajiya, yana da hanyar fita? Ƙwan da Hajiya ta kai gidan Ali idan ya fashe ya za a kwashe tsakanin Ali da Maryam?

Halima ta dawo, yaya alaƙar Zainab da Haruna za ta kasance? Shin dabarar da ta ce ta samu za ta kai musu kuwa?

LAST FREE PAGES! ƳAR'UWA KI SIYA KI KARANTA CIKIN AMINCI, YANZU AKA FARA TAFIYAR

LITTAFIN WANI AUREN NA KUƊI NE A KAN NAIRA 300 KACAL!

8028966015
Sadiya Abdulrazaƙ
Opay bank

KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN
08028966015/09060689001
KO KATIN AIRTEL NA 300 ƳAN NIGER ZA KU TURO 300F AIRTEL

6
7
8

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login