Showing 18001 words to 21000 words out of 21816 words

Chapter 7 - WANI AUREN BOOK COMPLETE BY SADIYA ABDULL.txt

akwai lokacin da ta yi kwana uku ba ta tura masa saƙo ba, duk ya kasa sukuni, motsi kaɗan ya duba wayarsa, ranar na ukn sai ya kirata a waya, sosai ta nuna farincikinta, kuma ta faɗa masa ba ta da lafiya ne, jiya aka sallamo ta daga asibiti, kamar wasa tun daga ranar suka fara yin waya da yarinyar da ta ce sunanta Ummu, ta iya kalamai masu tsayawa a rai, sosai yake mamakin kansa, don bayan Yusra bai yi tunanin zai sake iya soyayya da wata ba, sai ga shi cikin sauƙi ya faɗa soyayya da wacce bai santa ba, kuma ko hotonta za ta turo masa sai dai ta rufe fuskarta, to shi ma a yanzu bai shiryawa wani auren ba, shi yasa ya bar ta a je a hakan, amma yarinyar ta yi masa har zuciyarsa, sosai suke waya musamman ranar da Yusra take aikin kwana.

LITTAFIN WANI AUREN NA KUƊI NE A KAN NAIRA 300 KACAL!

2526907490
Aisha Abdulrazaƙ
Zenith bank

KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN
08028966015
KO KATIN Airtel NA 300 ƳAN NIGER ZA KU TURO 300F AIRTEL.
[7/30, 5:34 AM] Sadiya Abdulrazak: *WANI AUREN*


BY
SADIYA ABDULRAZAƘ


FIRST CLASS WRITERS


PAGE 8

Follow the AUTAR MANYA CHANNEL channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VakTcGc5Ejy40GSTWA0h

*BOJUWA HERBAL'S & SCENTS*
*Suna kawo Saiwowin sanyi da suke dagargaza sanyin mara da na jijiya.*
*Haka nan akwai dafaffen maganin ga wanda tafi son ready made.*
*Haka nan suna kawo Saiwowi daban daban daga Chad da Sudan, kuma marasa illah*
*Saiwowin tsumi*
*Saiwowin dahuwar kaza/tattabaru*
*Saiwowin matsi gangariya*
*Original gadalin mata*
*Ƴaƴan gadali na asali*
*Original gumba*
*Tsumin Saiwowi*
*Tsumin kwakwa da Dabino*
*Igiyar alkairi*
*Zumar goran tula*
*Hakkin daka na musamman na asali*
*Bayan haka suna dafa kazar amare da masu jego da ma uwayen gida*.
*Akwai bridal package*
*Mai jego package*
*Ƴar gata package*.
*Dukkan kayan kuma available ne for pickup or immediate delivery.*
*A Kano nake amma kuma nationwide delivery ne*
*Ku tuntubi Surayya Halin yau a wannan lambar dan samun naku cikin musulmin farashi*
*08032773332*
*Serious buyers pls*
*Iyah Basiru na gaisuwa*😅

GIDAN HARUNA

Ƙiri-ƙiri Haruna ya ƙi cewa Halima ta dawo, duk da ta faɗa masa jikin da sauƙi sosai, ita kuma mahaifiyarta tausayinta take ji, shi yasa ta ƙyale ta ta dinga hutawa, Halima har mamaki take yi yadda kullum idan zai zo ganinta sai ya taho da leda sannan ya ba ta kuɗin kashewa, sosai hakan ya yi mata daɗi, ta fara tunanin mijinta ya fara samu sosai a kasuwa, amma ta saka a ranta duk da haka ba za ta dakatar da sana'arta ba, za ta ci gaba da yi don a taru a rufawa juna asiri.

Bayan kwana uku suka shirya da Zainab, har ma suka shirya yau ma za su haɗu a ɗakinsa, don haka da daddare ƙarfe ɗaya Zainab ta tashi saɗaf-saɗaf, ta shige ɗakinsa, ta saka sakata, suka fara sha'aninsu, bai fi minti goma da shigarta ba Baaba ta tashi don yin fitsari, ta ji ɗakin a buɗe duk da ta san da kanta ta saka sakata, kuma Zainab ba ta tashi fitsarin dare, sai ta yi tunanin ko yau ta tashi ne tana banɗaki, ganin butarsu a yadda ta ajiyeta ma bai sa ta yi wani tunanin ba, ta ɗauka ta je ƙofar banɗaki ta tsaya tana jiran fitowarta, jin shiru ba ta da niyyar fitowa ya sa ta cewa"Da mutum?" Ta ji shiru, ta bubbuga ƙofar nan ma shiru, sai ta leƙa a hankali tana haskawa ta ga wayam babu kowa, ƙirjinta ya bada sautin rass ta fara tunanin ina Zainab za ta tafi cikin daren nan? Ta shiga ta yi fitsarinta, ta yi zaure ta ga ƙofar gida a rufe tsaf, gabanta sai faɗuwa yake yi, ta dawo ta shiga ɗaki wai ta ƙara dubawa ko idonta ne ya nuna mata Zainab ba ta nan, amma ganin ko bargo babu a kan shimfiɗar ballantana a yi tunanin ta lafe a ciki ya sa ta saddaƙar wani abu ya samu jikarta, tuni ta fara hawaye, zuciyarta tana bugawa.

Kamar ta tashi Haruna ta faɗa masa halin da take ciki, sai kuma ta fasa, don tana tunanin samari ne suka hure mata kunne ta gudu bariki, sai ta miƙe zumbur ta shiga ɗaki ta duba kayan sakawar Zainab, ta gansu tsaf babu alamar an ɗauki wani abun, har hijjabin da ta yi sallar isha'i ma yana nan a inda ta bar shi, Baaba ta dawo tsakar gida ta zauna a kujera tana matsar ƙwalla.

A firgice ta ɗago jin an buɗe ɗakin Halima, ta miƙe tsaye don ta samu damar da za ta faɗawa Haruna, ya je ya dubo ko ba ta yi nisa ba ya faffalla mata mari ya dawo da ita, sai dai ta yi turus ganin mace ce ta fito, cikin sakan ɗaya ta yi tunanin ko Halima ta dawo tana bacci? Amma ganin wacce ta fito ɗin ta doshi ɗakinta gadan-gadan ya sa ta yi saurin kunna fitarta hannunta na rawa.

A firgice Zainab ta juyo ganin an haskata, ƙirjinta ya buga da ƙarfi ganin Baaba ce a tsaye. Baaba kuwa sakin fitilar ta yi, ta dafe ƙirji, cikin razani ta ce"Zainab! Me kika yi a ɗakin Halima?"

Cikin inda-inda ta ce"Caji na saka fa Baaba".

Baaba ta ce"Bantan ubanki ke da cajin" Sai ta ƙaraso ta rufe ta da duka, kafin ta saketa ta fashe da kuka, ta shige ɗaki. Ita ma Zainab ɗin shigowa ta yi, ta zauna rakuɓe a gefe tana hawayen nadama, can Baaba ta ce"Zainab yanzu shahararki a iskanci ta kai har da na gida? Har cikin gida, da mijin maƙociyarmu? Innalillahi wa inna ilaihi raji'un!".

Zainab tana kuka ta ce"Ki yi haƙuri Baaba, wallahi iya yau ne kawai, kuma mun yi na farko mun yi na ƙarshe".

Baaba ta ce"Amma wannan yaron an yi ɗan banza, Allah sarki Halima ashe ba ta yi dacen miji ba, kaico! Da halinku ke da shi ɗin, sai Allah Ya sakawa Halima".

Sai kuma ta tashi, ta je ta fara ƙwanƙwasa ɗakin Haruna, don Zainab tana fita ya saka sakata, ya yi lakur saboda yana jiyo tattaunawarsu sama-sama, gabansa ya faɗi da ƙarfi da ya ji ana buga ƙofar, kamar kar ya buɗe sai kuma ya daure zuciyarsa ya buɗe, cikin karaya ya ce"Baaba ce da daren nan?"

Baaba ta ce"Haruna ka ji tsoron Allah! Ka sani akwai mutuwa, akwai hisabi, sannan zina bashi ce, kuma duk wanda yake cin amanar aure ba zai yi kyakkyawan ƙarshe ba in sha Allah!".

Cikin ƙarfin hali ya ce"Mene ne ya faru ne Baaba?"

A fusace ta ce"Uwarka ce ta faru da ubanka! Me ya kawo Zainab ɗakinka da daren nan?"

Ya ce"Wai Zainab? Wallahi zuwa ta yi, ta ce min wayarta babu kuɗi, na kira mata Halima za ta tambaye ta wani abu, akan sana'ar da take taya ta".

Baaba ta ce"Ita kuma ta ce caji ta saka, babu komai Haruna duniya ce ta fi bagaruwa iya jima! Idan ni da Halima muna da hakki akan cutarwar da kuke yi mana Allah Ya saka mana tun a duniya".

Daga haka ta shige ɗakinta, ta bar shi riƙe da ƙofa, jiki a mace kamar kazar da ta taka wuƙa ya dawo ya zauna a kujera yana dafe kansa, ya jima a haka sannan ya tashi ya saka sakata ya koma ya kwanta.

Washegari safe Zainab ta tashi ta shiga harkokin wainarta kamar ba a yi komai ba, saɓanin Haruna da ya kasa fitowa sai da suka yi chart ta faɗa masa babu komai ya maze kawai, kuma haɗuwa yanzu ma suka fara, ta samo musu wata dabara, wannan ne ya ba shi ƙwarin gwiwa ya saki jikinsa, har ya fice daga gidan.

Ita kuwa Baaba ƙarfe goma na safe ta shirya ta tafi gidan su Halima, suka gaisa ta cewa babarta ta zo tafiya da Halima ne, Umma tana murmushi ta ce"Ai Baaba gani na yi har yanzu bai ce ta koma ba, shi yasa na barta ta ƙara hutawa".

Baaba ta ce"Haba ƴar nan, ku kuma ai ya kamata ku gane kara ce yake yi, sai ka ce laulayin kanta ne farau? Kuma fa ƴata Halima ai jaruma ce, ni dai yau da ita zan koma gidan nan Allah kuwa".

Umma ta ce"To kin ji dai Halima, sai ki tashi ki shirya, bari na je kasuwa na yi miki ƴar siyayya, idan na dawo sai ki bi Baaba ku tafi, ka samu mai kula da lamarinka ma ai abun murna ne, mun gode Baaba".

Bayan ta tafi kasuwa suka dinga fira da Halima tana ta jaddada mata ta riƙe mijinta, ta dinga saka ido sosai a kan shi saboda ƴan matan zamani ba su da kirki, a haka har Umma ta dawo, Baaba ta saka ta a gaba suka koma.

Ita kanta Baaba sai da ta yi mamakin yadda Zainab ta nuna ko a jikinta, ita ta gyara mata ɗakinta fess tana ta yi mata sannu. Haruna bai san da dawowarta ba, da yake akwai mukulli a hannunta, sai dawowa ya yi ya tarar da ita, ya ɗan ji daɗi saboda dama yana shakkar dabarar Zainab duk da shi ma ya san ba abu ba ne mai sauƙi yadda ya saba da ita su rabu lokaci ɗaya, amma tun da Baaba ta san komai ya zama dole su canza taku idan ma za a kuma ɗin, da wannan ya saki jiki da Halima har suka taɓa fira kafin ta yi bacci.

GIDAN ALI

A cikin satin Ali ya zowa da Maryam sabon labari, na cewar wani kamfani a can Enugu zai ɗauke su aiki na sati ɗaya, kullum dubu goma, kuma su ne za su yi musu kuɗin mota,masauki da abinci bakiɗaya, ganin ta ɓata rai ya sa shi tausasa murya ya ce"Maryam don Allah idan na zo mana da abun alkhairi ki daina gwasale ni, ki dinga yin fatan alkhairi kawai, kwana bakwai fa kacal za mu yi, dubu saba'in ina laifi? Ba sai na yi miki kayan sallah a ciki ba?"

Ta ce"Ni fa ba aikin ne ba na so ba, garin ya yi nisa, kuma har kwana bakwai".

Ya ce"To ai haƙuri za ki yi, wanda ya tashi nema ai ba ya duba nisa Maryam, ni ma zan yi kewarki kuma na akwai masu tafiya su yi wata bakwai, ko shekara bakwai, to ina laifi don na yi kwana bakwai?"

Ta ce"Haka ne, shi kenan Allah Ya kai ka lafiya, ya dawo mini da kai lafiya, Allah Ya ba da abin da aka je nema".

Ya ce"Amin mace ta gari, ko kefa! Amma da kin tsaya kina wani tantama? Gobe da yamma za mu tafi, saboda haka yau kam duk rowarki sai kin bar min daren nan duka, kya dinga tunawa da ni ko?"

Ta ce"Kai ai aikinka kenan, na rasa me kake ji, ni dama tun can babu wannan abun a aure da na ji daɗina" Ta juya kai gefe

Ya ce"Maryam kenan, ke dai na rasa irin tunaninki wallahi, nan gaba za ki saba dai, ina ga sai kin haihu ko?" Ba ta ce komai ba, ta tashi ta kwashe kwanukan da suka ci abinci. Kafin ya shigo ɗaki ta yi luf kamar mai bacci, saboda fargabar furucinsa ta kasa baccin ma, ya yi abin da zai yi ya kwanta, yana kai hannu jikinta, ta ce"Na fa fara bacci, ga ciwon kai".

Ya matsa gefe, don dama ba wai buƙatarta yake yi ba, kawai dai don ta sake yarda da tafiyar tashi ce, shi da zai je ya ɓarje guminsa a gidan Hajiya har ya tsaya ana kace-nace da shi? Daga haka ya juya ya fara baccinsa hankali kwance, har zumuɗin zuwan goben yake yi.

Washegari bai fita aiki ba, da kanta ta haɗa masa kaya a jaka, har ta ce ya siyo fulawa ta yi masa cincin ya ce a'a ta bar shi, tun da kanta yana ciwo, tun azhar Hajiya ta yi masa tex ɗin tana ta jira, ya ce mata sai da yamma, ana idar da sallar la'asar ya ɗauki jaka yana yi wa Maryam marayan kallo saboda yaudara, sai ya ga ta tashi ta saka hijjabi, ya ce"A ina zuwa kuma?"

Ta ce"Ai ya kamata na raka ka tasha ko?"

Ya ce"Haba Maryam wace tasha kuma? Mu da za mu haɗa da yawanmu a ƙasan layi sannan mu ɗunguma zuwa tasha, kuma tsakani da Allah sai a ce ni ne kaɗai matata ta rako ni?"

Ta ce"To mene ne idan ma an faɗa?"

Ya ce"A'a wallahi ni dai ina kishin a gane mini kyakkyawar matata, duk sallamar da za mu yi mu yi ta a iya zaure, kwana bakwai ne fa, kamar yau ne, yi haƙuri kin ji?"

Haka dai ya lallaɓata ya tafi, bai samu nutsuwa ba sai da ya gan shi a gidan Hajiya, sosai take farin ciki da zuwansa, jinta take tamkar wacce ta yi sabon aure, ɗakin mijinta ta buɗe ta kai kayansa ciki, ta faɗa masa nan ne masaukinsa, tun kafin ya zo ta sallami ƴar aikinta, ta ce mata tafiya za ta yi, sai bayan sati ɗaya idan ta dawo za ta neme ta, saboda haka da kanta ta yi masa girki sakwara da haɗaɗɗiyar miyar da ta zuba yajin maza a ciki ta yi lafiyayyen kunun aya shi ma ta watsa masa ƙwayoyi, Aliyyu ya kwashi abinci ya yi wanka, suka fara shagalinsu, bayan ya kashe wayarsa.

Bai kunnata ba sai washegari shi ma sai azhar, don sosai ya kwashi ramuwar bacci da safe, ya kira Maryam suka gaisa yake faɗa mata yanzun nan suka sauka, ta ce"Alhamdulillah! Tafiya ta yi kyau, ina ta tunani wayarka na kikkira a kashe ashe sai yanzu kuka je, amma dai da nisa".

Ya ce"Ke dai bari Love, kwana muka yi a hanya, ana sharara gudu, sai yanzu muka isa".

Ta ce"Ma sha Allah! Da daddare za mu yi chart".

Hajiya dake zaune tana jin duk wayar tasu, ta kaɗa masa ɗan yatsa alamar a'a, tana maƙe kafaɗa kamar yarinya. Ya ce"Ai Maryam chart dai yau ba zai yiwu ba, jiya fa ban yi bacci ba, yanzu caji zan bada wayata, a kaimu mu ga yanayin aikin, sai mu ci abinci a kaimu masauki, kin ga ina yin wanka sai bacci, tun da gobe sassafe za mu tafi wurin aikin".

Cike da tausayawa ta ce"To Allah Ya tsare ku, Ya ba da sa'a Love ka kula da kanka sosai don Allah, ban da kai wa dare a waje ka ga dai ba ka san kowa ba".

Ya ce"Haba ina ma na ga wannan damar? Mu da za mu wuni aiki, ai ina dawowa sai bacci, ke ma sai dai ki yi haƙuri ba za mu dinga doguwar waya ba".

Daga haka suka yi sallama, ya kalli Hajiya yana washe baki, ta juya kai ta ce"Ina kishi da wannan matar taka gaskiya".

Ya ce"A haba Hajiya, ai kin wuce ki yi kishi da Maryam".

Ta ce"Ba ni labarinta, tana sonka sosai ko?"

Kamar ta yi masa allurar tonon silili haka ya ɓarke ya fara ba ta labarin Maryam, hatta gidan iyayenta da yadda suka fara soyayya zuwa aurensu, da sana'ar da take yi, duk sai da ya faɗa mata, sannan daga baya ta nemi sanin unguwar da yake haya, ya kwatanta mata tsaf.

Haka rayuwa take gudana tsakanin Hajiya da Aliyyunta, suna ɓarje soyayya, Ali sai dai a ci a sha a kwanta a yi bacci, daga shi sai gajeren wando za ka gan shi a falo yana kallon TV, AC tana ratsa shi, ya shiga kitchen ya yi ciye-ciyensa son ransa, kullum ya ji alert ɗin dubu goma.

Kwanansa biyar a gidan, Hajiya ta ce masa za ta je unguwa, tun da ya zo bai ga ta fita ba sai yau, tana yin baƙi, idan za su zo sai dai ta ya shige ɗakinsa ya yi kwanciyarsa. Kai tsaye Hajiya ta bi kwatancen da ya yi mata, ta je har gidan Maryam, a buɗe ta tarar da gidan, ta yi sallama ta shiga, ta tarar da mata guda biyu suna fira, wanda kwarjinin Hajiyar ya sa suka yi zaton wata babbar baƙuwa ta yi, suka yi wa Maryam sallama suka tafi, Maryam ta tashi tana yi mata sannu da zuwa, Hajiya ta ja kujera ƴar tsuguno ta zauna ta ce"Yawwa Maryam, dama kitso na zo ko zan samu?"

Ta ce"Za ki samu, bari na ɗakko tabarma". Ta shiga ɗaki, Hajiya ta bi bayanta da wulaƙantaccen kallo, ta fito ta shimfiɗa hannunta riƙe da kibiya ta ce"Bisimillah".

Hajiya ta zauna a tabarma, Maryam ta fara yi mata kitso, tana ji ta ɗakko wayarta ta yi kira, ta ji tana cewa"Ali na samu gidan Maryam ɗin, ga shi nan ma har ta fara yi mini kitson". Can kuma ta ce"A babu komai wallahi, tana da kirki, bari dai idan na zo gidan ma yi magana".

Maryam ta ɗan yi mamaki jin irin sunan mijinta kuma da alama mai sunan ne ya kwatanta mata har ta zo kitson, ba ta kawo komai ba har ta gama yi mata, Hajiya ta ɗauki dubu biyu ta bata, Maryam ta ce"Ai baiwar Allah bai kai haka ba, ungo kuɗinki har dubu biyu?"

Hajiya ta ce"Haba ai yiwa kaine, ke da Ali ai duk ɗaya kuke a wajena".

Cak Maryam ta tsaya ta ce"Wai wane Alin?"

Ta ce"Ba sunan mijinki Ali ba, wanda ya yi miki ƙaryar ya tafi Enugu aikin kamfani? To idan ya dawo ki faɗa masa Hajiya Zuwaira tana gaishe shi".

Daga haka ta fice tana murmushi, ta bar Maryam wacce mamaki ya daskarar da ita.

Shi kuwa Ali yana falo ya yi ɗai-ɗai yana kallo a TV, lokaci-lokaci yana damƙar dambun nama yana ci, ya ga an buɗe ƙofa, da sauri ya miƙe tsaye ganin wani mutumi ne ya shigo ba Hajiya ba, kallon-kallo suka shiga yi da mutum, kafin Ali ya kwasa a guje ya yi hanyar ɗakinsa, mutumin ya bi sa ya guje yana cewa"Waye kai!?" Ali ya murɗa key zuciyarsa tana bugawa da mugun ƙarfi, ga shi ya bar wayarsa a falo.

GIDAN SADIQ

Yau ta kasance Asabar Yusra tana gida, don haka Kursum ba za ta zo ba, bayan ta gama duk ayyukan gida ta kwanta tana bacci, har ta makara sai da aka fara kiraye-kirayen sallah ta farka, ta fito ta ɗora girki, tana gamawa ta zubawa yara, suna yin cokali ɗaya suka kalli juna, Afna ta ce"Ni dai Momy na ƙoshi"

Fanan kuma ta ce"Momy me yasa abincin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login