Showing 6001 words to 9000 words out of 45050 words
Chapter 3 - Kulsum Part 1 Complete Hausa Novel By Sumayya Takori.txt
doctor din su. Bala ma yamai godiya sannan ya wuce.
Doctor malik ya kira mummy yamata bayanin komai, tace tabbas yar'ta ce dan dama tun wajen kwana biyu daya wuce akaje dauko ta daga makaranta, amma sukaji shiru basu iso gida ba, an duba hanya an gano motarsu tayi hatsari ta kone sai gawan mutum biyu akone kawai aka gani, kuma ance mana tare suke da kawarta daga makaranta, doctor yace kawar ce ta rasu da driver kenan, dan yanxu haka sumy na nan kuma jikinta yayi sauki sai dan ciwon da baza'a rasa ba, tayi mai godiya sosai tace zata turo baba shehu yaxo ya dawo da sumy gida..
Kursum ta tashi sai dai ba ihu yanxu sai kuka kawai take, doctor ya shigo yana gayamata ai kawarta da sukai accident tare ta rasu dan haka yanxu ta shirya kanta dan kanin mamanta yazo daukanta suje gida, ya dauko wallet da pictures din yabata hade da jakan gabadaya sannan ya bata magunguna wanda zata sha, yace sumy ki tabata kinsha maganin nan saboda your body is still weak, tace to nagode sosai doctor, Kursum kam hankalinta duk ya tashi shikenan sumy ta rasu yanxu ya zata yi , gashi kuma ana tunanin itace sumy alhalin kuma sumy ce ta rasu ba kursum ba, amma kuma dole ne ta tsaya a matsayin itace sumy kodan ta samo wa hanifa gata da yancin ta.
Ta fito ta iske baba shehu na jiran ta, dukda batasan shi ba saida tace kawu ina wuni, ya bita da kallon banza sannan ya amsa a kwasale yayi gaba abunshi tana binshi a abaya, a zuciyan ta tace tab wato family dinnan babu sauki, lailai zata daura damara dasu dan kuwa baza tai tolerating ko wana nonsense ba.
Suna isa gidan yayi parking mota suka fito, masha Allahu kawai take fada dan kuwa bata taba ganin katon gida mai kyau kaman wannan ba, wani tausayin sumy taji, Allah yaji kanki kawata kuma insha Allahu hanifa sai ta samu gatan xaman gidan nan Daram. ...
Hajiya da xee suna zaune a parlour suna jiran isowan su sumy, baba shehu yafara turo kofa sai kursum abaya, tana karasowa cikin palon xee da mum suka tashi tsaye afirgice suna kallon ta.......
Nima afirgice nayar da biron rubutuna dan na tsorata da yanayin mom, ita da bata gani miyasata firgita haka..😳😳
*Xarah Bêê*
*Dedicated to Bady social*
~Luv u all~😘😘😘
[10/14, 8:12 PM] Badee Social: 🌺🌺🌺KURSUM🌺🌺🌺
🌺🌺 By ~Xarah Bêê
Page 3⃣6⃣ ~ 4⃣0⃣✨
Kursum ta dukusa har kasa ta gaishe su, hajiya kam hankalinta bai tare da ita, mamaki kawai take yadda sumy ta zama kekkyawan budurwa dan koda tasan ta abaya ba wani kyau garetaba sai fari kawai .......abangaren xee kuwa faduwan gabanta sai karuwa yake, yaudai duk takama da kyawuta taga Wace ta fita kyau da komai, wani irin tsanar kursum taji azuciyanta. .......😡😡
Hajiya amsa adakile, ta kwallawa samira kira, taxo da sauri tana gani hajiya, tace kikai sumy can gidan baya kusa da dakin masu aiki sai ta zabi dakin data ke so, samira tace toh.
Kursum da haushi hajiya ya isheta ta, ta karaso cikin palon ta xauna tace tunda gidan ubana ne babu wanda ya isa yasani xama dakin masu aiki, dan haka nima a main house zan zauna, ta tambayi samira ina dakuna suke da kuma wana dakine yafi kyau da girma a gidan, tace antee dakuna asama suke kuma dakin daddy yafi kyau da girma tunda ya rasu babu wanda ya shiga, kursum ta mike tsaye ta karewa hajiya da xee kallon sannan tace samira kaini dakin daddy dan yanxu yaxama nawa in ga wanda ya isa ya hanani...😕
Hajiya kaman tafasa ihu 😫😫 dan takaici, lailai yarinyan nan wato ba kyau kadai takara ba harda baki tayi, yazama dole insa mata ido saboda.....
Da daddare Abba da umma ke zauna a parlour sai hira suke suna darawa, umma tace gaskia yakama in leka hajiya mun dade bamu haduba aiki yamin yawa.
Abba ya kalleta yace wai ke bana hanaki shiga harkar hadiza ba, kinsan sarai banason matan nan saboda Sam bata da mutunci, kowa yasan itace sanadiya mutuwan mijinta , umma tace haba alhaji ya za ai kace haka, lokacin mijinta ne yayi....... bata ida magana na ba yazid ya shigo da sallaman sa, sanye yake da uniform dinsa na pilot wanda ya kara fito da ainuhin kyau shi, ya fada kan kujera yana wai na gaji, umma ta kalle shi tace my son hope dai you are okay, banason ganinka da stress , Abba yayi tsaki yace wlh maryam ke kike kara sangarta yaron nan, idan baije aiki ba so kike yana xaman gida ko me, shida wataran zaiyi aure ya kula da iyalansa......yauwa nama tuna shehu yazo min da batun diyar shi Zainab dinnan kwana kin baya, kun dade kuna soyyaya amma baka ma xancen aurenta kuma ma dai at your age ya kamata ace kafara tunanin fara iyali.
Yazid ya tamke fuska, yace gaskia abba ni ban shirya aure ba dukda inason xee, koda zanyi aure sai nan da shekera daya, ya tashi a fusace ya wuce dakin shi.
Abba ya kalli umma yace kinga halin son dinki ko , tace karka takura mai tunda yace ba yanxu ba, ni xee dince ma banaso ya aure Sam bata da kamun kai, yace to ina ruwanki bashi ya gani yanaso ba kuma ni banga rashin kumun kan taba, babanta abokina ne kuma yana da kirki sosai,
umma dai shiru tayi bata ce komai.
***************************
Bayan kwana biyu jikin kursum ya warware ta samu sauki sosai tayi fresh ta kara kyau, sai dai zaman kadaice da take babu mai shiga harkanta a gidan sai samira kawai dan ita ke kawo mata abinci har daki, tayi tsaki ta kwallawa samira kira,
taxo da saurin ta tace antee kina bukatan wani abu ne, kursum tace babu komai tambayan ki zanyi wai babu masu shigowa gidan nan ne, naga tunda na zo banji an shigo ba, gida sai kace kurkuku......samira ta gyara zama tace antee ai indai gidan nan ne ana wata biyu babu wanda ya shigo, yaya yazid kadai ke xuwa wataran umman shi takan zo wajan hajiya dan kawarta ce sosai,
kursum ta nisa tace Waye kuma yaya yazid wajan wa yake zuwa, samira tace ai saurayin antee Zee ne kuma suna son junan su sosai bare ma antee zee tana iya mutuwa akanshi,
kursum ta bata rai tace tashi ki fita ban tambayi ki wannan ba, sumsum ta tashi ta fice da saurinta......ita ko wani farin ciki taji ta maimaita sunan yaya yazid, gaskia sunan ya mata dadi. .. 😀😀
Da yamma barrister shu'aibu yazo har gidan ya damkawa kursum takardun gidan da komai data mallaka amatsayin itace sumy, sannan yace mata ta shirya gobe zata fara aiki acompany din babanta amatsayin managing director, tamai godiya sosai ya masu sallama ya fice.
Hajiya dake gefe sai hararan kursum take ta eye glass dinta (oho dai batasan kina yiba)......😜😜😜
Baba shehu ma ya cika yayi fam 😜😜😜, ya kalli kursum yace yanxu sumy abunda ya kamata shine kibarmin komai a hannun na tunda na dade in charge, xan naima maki admission ki shiga university tunda iya kacinki secondary skull kuma baki da experience na managing babban company,
kursum shiru kawai tayi batace komai ba ta haura sama abunta. ....
Baba shehu yayi murmushin samun nasara da alaman yarinyar ta yadda da Zancen shi....😀😀
Washe gari da safe kursum ta shirya cikin hadadden pink and white suit mai shegen kyau na kardashian collection tayi rolling kanta da karamin pink veil mai kyau, ta dauki handbag karamin mai kyan gaske mai tambari versace tarike a hannu, tabi stairs tana sauka atsanake hankalinta kwance, ji tayi an bangajeta har tana naima fadowa kasa, tana daga kai tayi ido hudu da xee, da ganinta kasan she is high danko kayan jikinta bana kirki bane,
xee tace ke dabbar ina ce ko bakiga ina hawowa bane, banza bakauya taja tsaki ta wuce,
kursum kasa cewa komai tayi ta wuce abunta tana mamakin hali irin na xee ta tabbata daga club take kuma till dawn tayi, dan samira ta taba gayamata xee bata fiya kwana agida ba, bata da aiki sai clubbing, kuma baba shehu da hajiya suna sane amma babu mai kwabarta....
Allah ya shiryeta kawai tace ta karasa waje ta shiga hadaddeyar motar ta kirar 2016 Buick Cascada..........driver yaja ta sai company.
Babban Company ne mai huge twenty-story office building, all curved glass and steel, an architect's utilitarian fantasy, with Tanimu bawa oil & investment written discreetly in steel over the glass front doors.
Tana shiga officials din suka karaso suna gaishe ta tare da mata congrat as the new MD , ta amsa da fara'arta tana masu godiya, Mr dabo ya karaso gabanta yace madam am your PA let me excort u to ur office,
ta bishi har office din amma sai tayi mamakin 😳😳 ganin office karami kaman gidan kaji, ta juyo tace Mr dabo how comes ina MD zaa bani karamin office haka, yace madam kiyi hakuri ba laifin mu bane, kawunki yace abaki nan tunda ba wani sanin kan aikin kikayi ba,
kursum tace lailai ma baba shehu wato itace ta dace danan, aikuwa zanyi maganin shi.... ..tace Mr dabo kaini office din baba shehu yace toh...
Suna shiga taga office dinshi tankameme kaman aljarnar duniya komai na office din ya burgeta tace Mr dabo nan nake so as my office ka kwashe tarkacen kawo ka canza mai wani office sannan kuma ka kawo min file din ko wana employee zan fara aiki na, yace to angama madam Ya fice. ...
Kursum zauna kan office chair tana swivel din kanta, sumy kawai take tunanin, Allah sarki kawata da yanxu kice anan bani ba, Allah yaji kanki insha Allahu zan rike maki hanifa tamkar nina haifeta...
Banko wan kofan da akayi ne ya firgita ta, baba shehu ne fuskar nan tamke, babu annuri ko kadan, yace "I won't let you disrespect me, I've been working day, noon, and night for this company, busting my hump since before you were born." who are you to throw me out of my office?
Kursum ta mike tsaye ta karemai kallon sannan tace, the early bird doesn't always catch the worm, Warming a seat in this company doesn't mean you're working,
baba shehu daya gama kulewa ya nunata da yatsa yace, how dare you, you snot-nosed brat!
Kinsan dawa kike magana kuwa, ta kara kare mai kallo tace, I dare because I'm the heir to my father's company. From now on, I'm going to monitor the performance of every employee; including you. No, not including, but beginning with you. If you don't like it, the door is wide open enough. Understand? or should I draw you a picture?"
Baba shehu kasa cewa komai Cox kalamanta ba karamin girgiza shi yayi ba, sai yanxu ya tabbatar kawar da yarinyan nan will not b easy, amma dole ne ya naima mafita kafin taza ma doom dinshi🙆🏿
Hmmmm
*Xarah Bêê*
*Dedicated to Bady social*
~Luv u all~😘😘😘
[10/14, 8:12 PM] Badee Social: 🌺🌺🌺 KURSUM🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺 By ~Xarah B
Page 4⃣1⃣ ~ 4⃣5⃣
Zaune yake a office dinsa yana waya da xee tana ta zuba mai shagwaba kaman tana gabanshi, ta turo baki tace baby kace zaka zo Jiya baka zo ba I couldn't sleep Cox I was thinking of u kuma your fone was off, ta kara shagwabe fuska, yace am sorry dear I was kinda busy ne xanzo anjima, kar kiyi fushi kinsan I love you alot..........Abba ne ya shigo office din yasamu kujera ya zauna jiran ya gama wayan, yazid yace baby xan kiraki later, tace toh my love, kisses & hugs dear 💋💋......
Abba yace miye amfanin love dinnan da bai da future, ance kayi aure kace you are not ready, kudai yaran zamani halinku sai ku, yayi murmushi yace abba abar xancen auran nan plz, nace muku am not ready, abba yace kai ka sani yanxu dai ga document din shares din mu na Tanimu bawa oil & investment company, Ina so gobe ka kaiwa new MD na company din tasa hannu, ya dire mai document din ya fice abunshi , yazid ya bude yana dubawa yace abba kenan wato dan aikin nan ma bazai tura wani ba dole dai ni zai aika........😡😡😡
Hajiya ce zaune a falo rike da sandar ta, tasha bakin glass dinta, tunanin kawai take yadda za ta fidda sumy daga gidan dan Sam bata yarda da ita ba, tana suspecting akwai abunda take boye masu, tasha leka dan karamin ramin dake jikin kofan dakin ta, ta ganta rike da wani hoto tana kuka tana cewa ki yafeni hakan da nayi shine kadai mafita, hajiya ta tashi da saurin ta haura sama, ita dai tana son sanin wana mafita sumy take nufi, ta bude dakin kursum ta shiga ta fara bude bude da binciken amma bata ga komai ba, side drawer na gadon taxo budewo ta ji muryan samira abakin kofa tana cewa Antee kin dawo ne, da sauri ta maida glass dinta ta fito daga dakin, samira tace hajiya kece aciki ashe, ko kallonta bata yi ba ta bi gefe ta wuce tana dafa bango dan karta fadi........
Samira mamaki ne ya cika ta, matar da bata gani miye na shiga dakin daba nata ba kuma da alama ma bincike take, ikon Allah kenan.....😳😳😳
Kursum zaune a office tana hada files waje daya dan yamma tayi zata wuce gida, ta kira Mr dabo tace mai ya kwashe duka files din ta gama dubasu sannan tamai sallama ta wuce parking lot tasamu driver na jiranta a mota, ta shiga ya ja....🚗🚗
Sun hau kan babban titi driver ya hango hold up sosai, babu alaman motoci na motsi, yace madam hold up dinnan yayi yawa amma akwai wani one way gaba kadan, bari inbi damu tanan, kursum tace toh duk yadda kayi ta cigaba da kallon sabuwar wayar da ta siya dazu kirar iphone 3G king's Button...
Daidai lokacin da driver ya danno kan motar, dai dai lokacin da shima ya karyo kwana sai ji kake kiiiiiiiiiii........ko wannan su yaja birki, kiris ya rage suyi accident..🙆🙆🙆🙆
Sanye yake da uniform dinsa na pilot yasha kyau da alama shima daga aiki yake ya fito fuska tamke, tun kafin ya karaso driver ya fito da sauri yazo yana bashi hakuri, amma ina shi kam baisan hakuri ba sai zazzaga masifa yake yace kai wawan ina ne, koka taba ganin inda akabi one way, hanyar da ake fita shine kake shirin shiga tunda baka da hankali, driver dai sa hakuri yake bashi....🙏🏻🙏🏻
Tana daga mota take jin hayaniyan su, wato driver na bashi hakuri shi ko guy din kara harzuka yake, lailai ko zata yi maganin shi, ta bude kofar motar ta fito da tafiyar ta mai daukan hankali ta karaso ta bayan shi tace Mr man ko Kaine devil himself sai haka, ana baka hakuri kana kara harzuka, toh karka hakura idan titin taka ce sai mu gani, taja uban tsaki, ya juyo a fusace fuskan nan ba annuri, ya kare mata kallo tas yace ni kike gayawa wai maganar banza , ita ko hankalinta bai ma jikinta dan ba karamin tsorata tayi ba, tabbas babu tantama wannan shine wanda sumy ta aura ya yaudare ta ya gudu, sau daya ta taba ganin shi amma bazata taba manta wa da fuskan shi ba, ba shiri ta saita kanta, ta wurga mai harara tace kwarai kuwa dakai nake kai din banza Waye kai da bazaka hakura ba, Driver mu tafi plz karya hakura din yana iya kwana anan tunda hanyar tasa ce, ta juya ta barshi nan tsaya yana mamaki karfin hali irin nata, lailai ko sai ya koyawa mata hankali, ya ga ubanwa ya tsaya mata da har ta isa ta gayamai magana, yayi kwafa yaja motar sa yabar wajen.
Suna cikin mota tana tunani iri iri, gaskia dole ta naimo Mr devil kodan ta koyamai hankali, wato hankalin shi kwance har wani kyau yakara, kibiyar tsanar shi ce ta soki zuciyar ta, tayi murmushin mugunta afili tace count down to my revenge has ended, it's time for pay back Mr devil......👹👹
Driver yace madam mun iso fah naga kinata magana ke ka dai, tace ahh ba komai barin sauka saika gyara parking, yace toh.
Ta turo kofar parlour da sallaman ta, hajiya da xee na zaune ko kallo bata ishe su ba, tana gaishe su ko amsawa basuyi ba suka bita da harara, ta haura sama abunta....🏃🏻🏃🏻
Xee da taci uban kwalliya da wasu matsasu kayan dake jikinta, ta kalli hajiya tace ni wlh na tsani yarinyan nan ga shegen kyau kamar aljana, ni wataran kina min kama da ita ma, hajiya taja tsaki tace ke daina hadani da mayya ni kaina na fiki tsanar ta, na gayamaki tsinto ta Alhaji yayi a titi, ko jini ban hada da ita ba........zata kara magana hajiya ta tsayar da ita, tace surutun ki ya isheni haka, ba kince saurayin ki zai zo ba, toh sai kiyi zaman jiran shi ai, nikam na tafi daki......xee tace haba hajiya ki tsaya ku gaisa mana, tace nikam bacci zanyi ta haura sama abunta.
Tun komawar shi gida, sallah kawai ya iya gabatarwa, ya rasa inda zaisa kanshi yaji dadi, abunda ya faru dazu gani yake tamkar a mafarki, wai yau shine little witch (sunan daya laka mata ) tama rashin M, lailai ko saiya making life dinta miserable sai tayi dana sanin cin zarafi da ta mai, wani irin tsanar ta yake ji, ya mike ya naushi bango a fili yace Game on little witch..........😡😡😡
Hmmmm tashin hankali🙆🙆🙆🙆
Masu karatu muje xuwa.....