Showing 3001 words to 6000 words out of 26566 words

Chapter 2 - Miftahuzzarbil Book 1 Complete By Abdulaziz Sani Madakin Gini.txt

dole ne nayi kuskure na halaka."
Na juya ga mahaifina Shaubatul Azman ina mai zub da hawaye nace,"Ya kai Abbana kayi sani cewa anan ne zanyi bankwana da kai ina mai yi muku fatan nasara,ni kam tawa ta kare."
Shaubatul Azman ya rungume ni muka fashe da kuka a tare.A lokacin ne jarumi Miqdad ya janyeni daga jikin Shaubatul Azman ya jani gefe guda muka fuskanci juna muna tsaye daf da daf.Miqdad ya kuramin idanu yace,"Yake Suhaila ina so ki dubi cikin idanu na da kyau ki gayamin abinda kika gani a cikinsu."
Na dubi idanun da kyau.Sannan nace,"Naga kauna da yarda a cikinsu."
Miqdad yayi murmushi yace,"Kin amince dani akan bazan cutar dake ba?"
Nace na amince.
"Abinda nake so dake shine ki ayyana a ranki cewa zamu samu nasarar shallake wannan kogin na darma bisa son cikar burin dake zuqatan mu.Zaki hau kan kafaduna ynx ki zauna kina mai rufe idanun ki.Ni kuma zan haye dake izuwa karshen wannan kogi na darma.Lallai kada ki kuskura kisa tsoro a zuciyarki,ko kuma ki bude idanun ki yayin da muka tsallake wannnan kogi na darma,domin yin haka zai janyo halakar mune."
Koda Miqdad ya gama wannan jawabi sai ya dubi Shaubatul Azman ya ce,"ya shugabana shin zaka iya kiyasta yawan sandunan karfen nan da suke jere a layi daga farkon kogin nan zuwa karshen sa?"
Shaubatul Azman ya dubi sandunan ya gansu reras ba adadi iya hangen sa.Ya kada kai yace,"Ba zan iya ba."
Miqdad ya kama kafadunsa yace,"ya shugabana na san cewa kai namiji ne mai dakawa maza gumba a hannu,ina son ka tuno da irin gwagwarmayar daka sha a rayuwar ka,ka dauka a ranka tamkar ynx kake yinta.Abinda nake so dakai ka biyoni a baya kana mai runtse idanun ka kuma kayi amfani da Kunnenka sosai wajen jin sautin inda na dora sawuna.In dai kayi haka albarkacin abin bauta zamu shallake wannan kogi na darma."
Miqdad na gama fadin haka ya tsuguna a gabana ya umarce ni da na hau kan kafadarsa.Cikin kwarin zuciya da aminci na hau kan kafadar tasa na zauna.Sannan na maida littafin nan cikin rigata na ajiye.Ba tare da fargabar komai ba jarumi Miqdad ya nufi kogin darma gadan gadan Shaubatul Azman na biye damu.Koda muka zo daf da kogin sai Miqdad ya kurawa sandunan ciki idanu tsawon lokaci yana nazarin tazarar dake tsakanin kowanne.Sannan ya kiyasta iya adadin su a zuciyarsa.Kawai saiya rufe idanun sa.Sannan ya umarce mu damu rufe idanuwan mu ni da mahaifina Shaubatul Azman.Take muka bi umarnin sa,kuma ya fara hawa kan sandunan yana tafiya a nutse kamar akan turba yake.
Shaubatul Azman kuwa ya biyo bayansa duk inda Miqdad ya dauke sawunsa sai Shaubatul Azman yasa nasa a wajen.A haka dae muka yi ta tafiyar har ya rage saura taku biyu kacal mu haure kogon darmar.Anan ne Shaubatul Azman yayi kuskure maimakon yasa kafarsa akan sanda ta uku saiya dora akan ta biyu.A lokacin kuwa mu muna kan sanda ta karshe.Sa'adda Shaubatul Azman yayi kuskuren tuni kunnen Miqdad ya kai masa saqon kuskuren.Har Shaubatul Azman yayi kasa zai fada cikin kogin na darma sai jarumi Miqdad yayi sauri cikin zafin nama ya durqusa ya cafo shi da hannu daya.Sannan ya miqe tsaye a haka ruqe da shi,kuma ba tare da ya bude idanun sa ba ya daka tsalle ya dirga can gaba kan turba.
Muna dirga muka bude idanun mu cikin tsananin mamakin juriya da bajintar jarumi Miqdad.Nan take naji son jarumi Miqdad ya shiga cikin zuciya ta ya mamaye ta gaba daya.Ban san sa'adda na daka tsalle na rungume shi ba ina farin ciki.Shima Shaubatul Azman sai ya taho garemu ya rungume mu gaba daya.Shaubatul Azman ya dubi Jarumi Miqdad yace da shi,
"Ya kai wannan gwarzon sadauki ina son ka gaya mini abubuwan da kake son na saka maka da su idan har munyi nasarar fita daga cikin kogon nan."
Koda jin wannan batu sai jarumi Miqdad yayi murmushi yace,"ya shugabana kayi sani cewa bana buqatar komai face abu guda kuma ba zan sanar da kai shi ba har sai mun tsira."
Shaubatul Azman yayi murmushi yace,"to shikenan muje zuwa."
Nan dai muka qara nausawa cikin kogon muka bi wata hanya daban mai surquqi.Wannan hanya bata da duhu,kuma ta cikin wani kwararo ake bi wanda ba dama mutum ya wuce a tsaye saidai ya sunkuya.
Miqdad ya wuce gaba ina biye da shi.Sannan sarki Shaubatul Azman.Sai da muka sake yin tafiyar rabin sa'a sannan muka iso maqura ashe akan wani kogon dutse muke,wanda qarqashin sa wata masifaffiyar gagarumar wuta ke ci.Babu yadda za'a yi mutum ya wuce face yabi ta cikin wutar.Daga inda muke zuwa qarshen wutar yake ya kai kamu dari biyar.Nan fa muka tsaya muka yi duru-duru.Daga can sai muka hango alamun rigunan dakarun Ashikatul Ashiriya a cikin wutar basu gama cinyewa ba, kuma ga su nan birjik babu adadi.Al'amarin daya dugunzuma hankalin mu kenan.Na dubi jarumi Miqdad nace,"ya kai Miqdad ta ya ya zamu iya haure wutar nan?"
Miqdad yace,"ina littafin nan yake?"
Take na sake zura hannu cikin aljihun rigata na dauko,Miqdad ya kar6a ya bude shafin da wutar take ya karanto jawabi kamar haka:
"Ya kai bakon wannan kogo kayi sani cewa ba zaka iya haure wutar nan ba face ta saman gininta.Za kaga wadansu karafa a manne jikin ginin sama farare da baqaqe a cakude.Lallai fararen zaka rinqa kamawa kana tafiya.Ma'ana kafafunka na reto a kas,kuma idanun ka a rufe.Idan ka kuskura kayi kuskure ka kama bakin qarfe, karfen zai tumbuko daga cikin gini ka fado qasa cikin wutar nan ka kone."

MU HADU A PART C DON JIN CIGABAN KAYATACCEN LABARI...
Najibullah Muhammad**MIFTAHUZZARBIL**
LITTAFI NA BIYU💯🙏
PART C🗡️🗡️
AUTHOR: ABDUL'AZIZ SANI MADAKIN GINI 🤴
TYPING: AHMAD MUNNIR.
POSTING: NAJIBULLAH MUHAMMAD ❤️

MARUBUCIN YACI GABA DA CEWA...

Koda Miqdad ya gama karanta wannan jawabi sai na tsuguna qasa cikin karayar zuciya na dago kai na dube shi nace,"zai fi kyau ku bar ni anan don dole ne ma nayi kuskure.Dubi fa yadda dubunnan karafan nan suke a cakude farare da baqaqe.Kuma koma banyi kuskure ba ai kafin mutum yakai karshe saiya gaji da tafiyar a haka ya fado."
Miqdad ya tsuguna a gabana yace,"ya ke suhaila kiyi sani cewa ba zan iya tafiya ba na barki.Idan kuwa za ki hallaka a cikin kogon nan zan so mu halaka tare.Ni na san cewa dani da mahaifin ki zamu iya ketare wannan wuta albarkacin abin bautar mu.Tun da kin tsorata ni zan tsallakar dake ta hanyar ki rungume ni a kirji kuma ki daure jikin ki da nawa.Idan har zaki fado cikin wutar nan saidai mu fado tare."
Koda gama fadin haka saina dube shi nace,"haba ya ma za ai mu tsira da wannan dabarar? Ka tuna fa cewa nauyin jikin ka ma kadai zai gundureka ballantana ka kara da nawa nauyin."
Miqdad yace,"karki damu ina son ki yarda da ni kisa a ranki lallai zan iya."
Nayi shiru ina mai nuna alamun rashin gamsuwa,yayin da mahaifina Shaubatul Azman ya fuskanci haka sai shima ya durqusa a gabana ya kama kafaduna.Sannan yace,"yake 'ya ta ki saki jikinki ki tuna irin hadarin da ke can baya na kogin darma,amma saida Miqdad ya hayar dake.Tabbas na san zai iya kubutar dake."
Wannan jawabi ne yasa jikina yayi sanyi na aminta.Kawai sai na yarda na rungume Miqdad shi kuma Shaubatul Azman sai ya kwance rawanin sa ya daure jikina dana Miqdad tamau.Koda yin hakan sai ya dubi Miqdad yayi murmushi,sannan yace,"idan har ka tserar da rayuwar 'ya ta daga wannan hadari ka biya sadakin aurenta."
Cikin tsananin mamaki da farin ciki na dubi Shaubatul Azman na kama dariya,shima sai ya kama dariyar.Miqdad yayi murmushi yace,"ai kuwa zan nemo wannan sadaki ta kowane hali iyakar qoqarina."
Nan take jarumi Miqdad ya runtse idanun sa sannan ya daka tsalle sama ya kamo fararen qarafa biyu.Sannan ya cigaba da tafiya a sama yana kama karafan dake gaba.Sai da Shaubatul Azman ya lura da yadda jarumi Miqdad ke sauya hannayensa wajen kamo karafan.Sannan shima yayi koyi da shi.Idan muka yi tafiya mai dan tsawo saiya tsaya ya huta,sannan ya cigaba da tafiyar.Babu abinda ya bani mamaki face yadda ya jure nauyina da kuma gajiyar.Saida muka isa daf da karshen wutar nan sai rawanin dani a jikin Miqdad ya kwance.Ai kuwa saina su6uto na yi yo kasa.Cikin zafin nama na ruqo kafafun Miqdad sai gashi ina reto a sama kamar zan fado.
Nan fa na rikice na dunga kwala ihu.Miqdad ya daka min tsawa yace,"ki nutsu ko na karkada kafafuna ki fada cikin wutar."
Da jin wannan batu sai na yi tsit.Miqdad yace,"haba gimbiya 'yar sarakai wadda ta gaji zuciyar maza.Ki cigaba da kama kafafuna kina hawowa sama ni kuma zan taimaka miki na dawo dake kan kirjina.Idan kika yi haka zan gamsu cewa kema kina son ki ceci kanki,kuma kin cika mace mai zuciyar maza."
Koda jin haka saina ji wani sabon qarfi ya shige ni gami da kwarin gwiwa.Nan take na cigaba da hawa kan kafafun nasa duk da cewar shima reto yake a sama.Saida na kai iya kugunsa sannan yasa hannu daya ya dagoni sama ya dorani a kirjinsa ni kuwa na qara maqalqale shi.Duk wannan abu dake faruwa idanun mu a rufe suke kuma sarki Shaubatul Azman bai qaraso inda muke ba.Nan da nan muka dirga a karshen wutar bisa turba.Koda Miqdad ya ga cewa har ynx Shaubatul Azman na can baya sai ya sake tsalle ya ruqo karafan nan na sama ya koma da baya cikin sauri kamar dama can ya laqanci tafiya a wajen yasa Shaubatul Azman a kirjinsa kamar yadda yayi mini ya taho da shi da sauri suka riskeni.A wannan lokaci ne na jinjinawa Miqdad na dube shi nace da shi,"hakika ka cika gwarzon jarumi mai matuqar sadaukan taka da juriya."
Miqdad yayi murmushi sannan ya kama hannuna ya jani da gudu muka kara nausawa cikin kogon Shaubatul Azman na biye da mu.
Haka dai muka cigaba da riskar abubuwan hadari iri-iri har kala goma a tsawon kwana biyu.Kuma cikin sa'a duk muka tsallake su dayan mu bai halaka ba.Amma fa munga gawarwakin fadawan Ashikatul Ashiriya da yawa ba adadi.Ba zato ba tsammani sai muka tsinci kanmu a wata makekiyar fada wacce ta cika ta batse da dukiya ninkin baninkin dukiyar da muka gani a farkon shigowa wannan kogo na Baitul Husuk.Ni kam babu abinda ya fi bani mamaki face girman kogon domin har ynx a wani bangare dabam muke bamu shiga wasu wuraren ba.Har na kutsa kai zan shiga cikin dukiyar nan sai Miqdad yayi sauri ya ruqo hannuna kuma yayi wa Shaubatul Azman nuni da cewar duk muyi shiru mu daina motsi.Cikin sanda jarumi Miqdad ya nufi cikin wasu tukwane marasa adadi wadanda a cike suke taf da sulallan zinare.Miqdad ya zare takobin sa ya soka cikin sulallan.Kawai sai muka ji ihu daga cikin tukunyar.Miqdad na zare takobin saiga jini a jikin ta.

Nan da nan dakarun Ashikatul Ashiriya suka rinqa fitowa daga cikin tukwanen sulallan suka afka mana.Ashe tuntuni sunji motsin tahowar mu shi yasa suka yi lam6o.Nan fa wuri ya hargitse sarki Shaubatul Azman kuwa ya kaiwa Miqdad dauki aka fara azababben yaki.Ni kaina mayakiya na zama a wannan lokacin na dunga sara da suka saiga shi kuwa ina zubar da maza dama na dade da koyon yaki a wajen jarumi Haiman amma ban taba jarraba jarumtata sai a sannan.Muna cikin tsakiyar artabu da wadannan tsirarun dakarun ne na hango Ashikatul Ashiriya a can sama cikin wani daki tana karanta wadansu dalasimai na tsafi.Ai kuwa fara karatun nata ke da wuya sai wani irin haske mai tsananin qarfi ya haskake wajen da ake yaki gaba daya.Take kowa ya qame aka zama kamar gumaka ni kadai ce ban komai ba.
Ashikatul Ashiriya ta kyalkyale da dariyar qeta ta juyo ta dubi inda muke kawai sai ta hango ni a tsaye na ruqe quguna da hannu biyu ina kallonta.Cikin tsananin mamaki ta dube ni ta daka min tsawa tace,"ya akai ke baki qame ba?"
Maimakon na bata amsar tambayar saina zaro littafin nan na sirrin arzikin Kisra daga cikin rigata na nuna mata ina mai murmushi nace,"ya ke wannan sarauniya kiyi sani cewa indai ina tare da wannan littafi babu wani sihiri na cikin kogon nan da zaiyi tasiri a kaina."
Yayin da Ashikatul Ashiriya ta ji haka saita fashe da kuka sannan ta dube ni tace,"yake 'ya ta ashe kin manta da duk irin son dana nuna Miki a rayuwa.Ki tuna cewa nonona kika sha kika girma har kika kawo iyanzu.Na kasance a cikin tsananin qaunar ki tun daga quruciyar ki don haka har abada ba zan cutar da ke ba.Ina mai roqonki daki kawo mini wannan littafin yanzu nayi alqawari ba zan cutar da ke ba kuma zan cigaba da riqeki a matsayin'yar cikina."
Koda Ashikatul Ashiriya ta zo nan a zancenta sai na kyalkyale da dariya nace,"haba sarauniyar yaudara kiyi sani cewa na sanki na san halinki,idan kika qi abu har abada baza ki so shi ba,kuma nima kin koya mini wannan hali.Na rantse da son da nake wa mahaifina yanzu haka na tabbatar da cewa yaudara ta kike so kiyi in baki wannan littafi don ki halakar dani,kuma ki sami damar fita daga cikin kogon nan don haka ba zan ba ki ba.Ina tabbatar miki da cewa ajalinki na cikin kogon nan."
Koda jin wannan batu sai sarauniya Ashikatul Ashiriya ta zare takobin ta ta rugo gareni tana qaraji da nufin ta sare ni.Nima saina ruga gareta muka hadu a tsakiya muka fara dauki ba dadi.Nan fa muka rinqa kaiwa juna sara da suka.Hannuna guda na ruqe da takobi,dayan kuma na ruqe da wannan littafi na Mabudin arzikin Kisra.Bisa mamaki saina ga ta quntata ni ta hanani sakat,domin ta fini kwarewa a iya sarrafa takobi nesa ba kusa ba.
Nan da nan ta rikirkita ni har ta sami nasarar yi mini yanka guda biyu.Daya a damtsen hannu,daya kuma a cinya.Al'amarin daya sa nayi ihu na fadi kasa ita kuwa saita matsoni tana kyalkyala dariya lokacin dana ke ja da baya.Ashikatul Ashiriya ta ce,"haba yarinya ai duk wanda ya riga ka kwana dole ne ya riga ka tashi.Na rantse da darajar karagata koda Haiman na kara ba zai samu nasara ba a kaina bare ke."
Ina cikin jan jiki da baya ne bayana ya tokare da bango babu damar gudu.Koda ganin haka sai Ashikatul Ashiriya ta qara bushewa da dariya tace,"yauwa yanxu kam na rutsa ki kuma cikin ruwan sanyi zan kashe ki na dauke wannan littafi."
Take ta daga takobin ta ta kawo mini sara da nufin ta tsarge ni biyu.Cikin zafin nama na kare saran da littafin nan na Mabudin arzikin Kisra.Ko da takobin ta sari littafin sai hasken nan mai qarfi ya sake baibaye kogon gaba daya.Take ruhin kowa ya dawo aka cigaba da yaki.Ashikatul Ashiriya tayi sauri ta ruga cikin dakin nan don ta karanta wadansu dalasimai na tsafi.Ai kuwa saina bita da gudu na sa kafata na harde ta ta fadi qasa takobin ta ta su6uce daga hannun ta.Kawai saina daka tsalle na dira a kanta muka cigaba da kokawa mu murgina nan,mu hautsina can.
Nan fa ta samu ta hau ruwan cikina ta rinqa naushina a fuska ta hada mini jini hanci da baki,sai dana suma.Sannan ta dagani kuma ta cire littafin nan daga hannuna.Cikin sauri ta rinqa bude shafukan littafin harta zo kan shafin karshe inda aka yi bayanin yadda za'a bude wata kofa ta fita daga cikin kogon da kuma yadda za'a qone kogon gaba daya.Ashikatul Ashiriya ta karanta wadansu kalmomin tsafi saiga wadansu raquma da alfadarai sama da guda dubu dari uku sun bayyana.Bayyanar su keda wuya sai dukiyar nan ta cikin tukwane ta dora kanta a kansu.Ashikatul Ashiriya ta sake karanta wadansu kalmomin sai wata katuwar kofa ta bayyana ta bude kanta.Cikin sauri Ashikatul Ashiriya ta kada raquman nan da alfadaran suka fara fita wajen Kogon Baitul Husuk dauke da dukiyar.Ita ma saita ruga da gudu izuwa kofar don ta fice.Har yanzu ana ta fafata yaki da su jarumi Miqdad sai ragargazar maza yake baima lura da abinda ya faru gare ni ba,bare ya hango Ashikatul Ashiriya wacce ta nufi kofar fita da gudu.
A dai dai wannan lokaci ne na farfado daga dogon suman dana yi,kuma a sannan ne Ashikatul Ashiriya ta isa bakin kofa.Tana zuwa tayi arba da jarumi Haiman tsaye a gabanta ruqe da zabgegiyar wuqa.Cikin tsananin tsoro da fargaba ta ja da baya tana mai nuna shi da dan yatsanta wanda ke karkarwa tace,
"Ashe ba kai na kashe ba tun gabanin shigowar mu cikin kogon nan?"
Jarumi Haiman yace,"kwarai kuwa ni kika kashe amma ban mutu ba,kece dai za ki mutu yanzu."

MU HADU PART D DON JIN CIGABAN WANNAN KAYATACCIYAR HIKAYAR.**MIFTAHUZZARBIL**
LITTAFI NA BIYU.
PART D ❤️❤️
NA ABDUL'AZIZ SANI MADAKIN GINI 🤴
TYPING AHMAD MUNNIR ☺️
POSTING NAJIBULLAH MUHAMMAD ❤️

MARUBUCIN YACI GABA DA CEWA...
Cikin zafin nama Ashikatul Ashiriya ta yunqura ta zare wata qaramar wuqa daga qugunta ta kai masa sura a kirji.Haiman ya goce wuqar ta soki iska.Kafin ta sake wani yunqurin tuni ya kir6a mata tasa wuqar a kirji.Wuqar ta nutse a cikin kirjin nata ta fadi qasa jini na 6ul6ulowa tana kakarin mutuwa,har ynx bata saki wuqar dake hannun ta ba.Haiman ya sunkuya a kanta yace,"wannan shine sakamakon 'yar uwar data nemi hallaka dan uwanta saboda mulki da dukiya."
Kafin Haiman ya gama rufe bakinsa Ashikatul Ashiriya ta luma masa wuqar nan dake hannun ta a maqoshin sa,take ya fadi qasa matacce.A lokacin ne na qaraso wajen na fusge littafin nan daga hannun ta kuma na doki hannun ta mai ruqe da wuqa da qafata.Wuqar tayi can gefe guda.Ashikatul Ashiriya tayi dariyar qarshe tace,"yake 'ya ta kiyi sani cewa ban mutu raguwa ba,jaruma ce ni wadda na kashe daya daga cikin manyan jaruman duniya wato dan uwana Haiman.Kiyi sani cewa ga dukiyar nan bisa raquma da alfadarai duk taki ce ke kadai,amma ki sani kema ba zaki gama rayuwar ki ba ta duniya sai qunci da bakin ciki sun riske ki.Tuni na gama shirya hakan cikin sihirin tsafi.Da wannan kalma nake miki bankwana a ci duniya da tsinke lafiya."
Ashikatul Ashiriya na gama fadin haka idanun ta suka qafe komai nata ya daina motsi.A dai dai wannan lokaci ne jarumi Miqdad da sarki Shaubatul Azman suka gama karkashe sauran dakarun Ashikatul Ashiriya.Sannan suka taho gareni.Koda jarumi Miqdad yaga gawar Haiman kusa da gawar sarauniya saiya durqusa ya dago da gawar Haiman ya rungume ta.Sannan ya fashe da kuka yana mai cewa,
"Shi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login