Showing 3001 words to 6000 words out of 18821 words
Chapter 2 - Dakarun Musulunci Book 1 By Abdulaziz Sani M Gini.txt
a duniya, kawai sai yayi tsaki ya juya ya tafi ga adokinsa ya Kamashi ya hau ya sukqaneshi a guje.
* * * * * *
Da magriba yarima uzaifat ya shiga cikin gidan sarautar ya nufi bangaren mahaifiyarsa gimbiya shulaifa. Dashigarsa cikin tura karta sai ya isketa a zaune ta idar da sallah taba nafila.
Cikin biyayya uzaifat ya sani wuri ya zana a gefe daya. Koda ta idar da sallah ta juyi sai tayi arba da raunin dake jikin hannun uzaifat. Nan taje hankalinta ya tashi, ta mike tsaye ta karaso gareshi ta rike kafadunsa tace, yaya akayi kajika wannan raunin? Ai wannan ma da gani saranka akayi da takobi?.
Ya yin da uzaifat yaji wannan tambayar sai ya yi murmushi yace, karki damu ya ummina, wannan ba komai bane, kin san muna fita hoton yaki ni da dakaruna, to a can ne na sami wannan raunin.
Shulaifa tayi ajiyar zuciya tace, Haba dana yau kwana nawa kuna fita wannan horon? Me yasa tsawon kwanankin nan bakayi wannan raunin ba sai yau? Na san irin jarumtakarka duk garin nan mutum dayane za ka kafsa dashi har ya sani nasarar yi maka rauni.
Koda jin wannan batu sai jikin uzaifat yaya sanyi, ya tabbatar da cewa ta gano cewa ukashat ne yayi masa wannan rauni.
Cikin alamun damuwa ya dubeta yace yake ummina kiyi sani cewa shima wanda yayi min wannan rauni nima haka nayi masa. Na rokeki dan girman Allah kibar wannan zance a tsakanin mu, domin idan maganar taje ga kunnen sarki gurina zai wargatse zai iya fasa gasar da yasa mana tsakanina da dan uwana.
Sa'adda shulaifa taji haka sai itama jikinta yayi sanyi tace, shikenan na bar Maganar. Yanzu wane irin ci gaba ka samu a bangaren horon daku ke yi kai Dakarunka?.
Uzaifat yace Alhamdulillahi muna samun ci gaba sosai. Yake ummina abin danake so shine, ki cigaba da yin min addu'a bisa nasara da nake nema a wannan ganin dazamu yi da birnin shumbul.
Shulaifa tace, kullum a cikin yi maka addu'a nake, kuma da izinin Allah zaka sami wannan nasara, domin alherine a zuciyarka ba sharru ba. Ina tabbatar maka da cewa bazan daina yi maka addu'a ba daga yau har izuwa ranar da zaka tafi wannan yaki.
Nasihata a gareka itace, ka rike abu uku, in dai kana rike da su dukabinda daka sa a gabanka zakayi nasara.
Wadannan abubuwa guda uku ba komai bane face duk abinda zaka fadi ka tabbatar cewar ka fadi gaskiya, idan aka baka Amana ka riketa, kuma idan ka dauki alkawari ka tabbatar cewar ka cikashi, indai ka kiyaye wadannan abubuwan uku to tabbas makiya bazasu ga bayanka ba.
Lokacin da shulaifa tazo nan a zancenta sai yarima uzaifat ya jinjina kai yace, Insha Allahu kuwa zan kiyaye wadannan abubuwa uku. Nan take yayi mata sallama ya fita daga cikin turakar.
* * * * * *
Al'amarin yarima ukashat kuwa, lokacin da ya shiga turakar mahaifiyarsa muzaira taga wannan rauni na hannunsa sai hankalinta ya dugunzuma, ta dubeshi tace, ya kau dana, yaya akayi ka sami wannan rauni?.
Ukashat ya kashe labarin duk abinda ya faru tsakanisa da dan uwansa uzaifat ya shaida mata.
Koda jin haka sai ranta ya baci, kishi ya turnuketa ta sunkui da kanta kasa ta shiga tunani mai zurfi. Daga can sai ta dago kai ta dubeshi tace, yaki dana kayi sani cewa a duniya bani da wani buri wanda yafi naga ka gaji mahaifinka, wato ya zamana cewa kaine ka hau karagar mulkinsa. A shirye nake na fansar da raina don cika wannan buri, kuma duk abinda baka zato zan iya yi don samun biyan bukata. A yanzu haka akwai kulle kullen da nake yi akan hakan.
Yayin da yarima ukashat yaji wannan batu sai ya cika da murna. Daga can kuma sai ya dubeta cikin damuwa yace, yake ummina kiyi sani cewa ni a ganina da ni da dan uwana uzaifat babu wanda zaici wannan gasa da yashirya mana domin naje wajen malamai sama da guda bakwai sunyi istihara akan hakan. Abinda suke gaya min shine zamuje wannan yaki, kuma zamu sha bakar wahala, da kyar ma zamu tsira da rayuwar mu. Yanzu wane matakin kike ganin ya kamata mu dauka akan wannan al'amarin?.
Yayin da muzaira taji wannan batu sai ta bushe da dariya sannan tace, yaro man kaza, hakika ba ka san rana ba sai ka shigeta, ka nake tukunna. Ai na gaya maka cewa tuni na yi kulle kullena don haka ka Kwanar da hankalika, duk wuya duk rintsi komai gumu kai ne zaka gaji sarki. Abinda malamanka suka gaya maka gaskiya ne, zaku sha bakar wahala a wannan yaki, amma ina tabbatar maka da cewa kai bazaka mutuba. Abinda nake so da kai shine, duk umarnin da na baka kabishi kada ka kuskara ka kereshi indai kayi hakan zamu cika burinmu.
Mahaifinku yace a gobe ne zai yi bayanin yadda tafi wannan yaki da yadda zaku gabatar da yakin, kuma a goben ne zakuyi shiri ku tunkari birnin shumbul. Kafin ku tafi ne idan zamu yi bankwana zan gaya maka umarnin da zaka bi.
Cikin mamaki ukashat ya dubi muzaira yace, wai shin ya ke ummina wane irin kulle kulle kika yine akan wannan bukata tamu?
Muzaira tayi murmushi tace, lokacin sanjnka bai yiba, idan yayi lallai zaka fahimaci komai bayan an kammala wanan yaki.
Ukashat ya matsawa muzaira akan sai ta gaya masa irin shirin da tayi, ita kuwa taki. A karshe dole ya hakura ya tashi ya tafi izuwa bangaren da turakarsa take.
A daren wannan rana sarki uwaisul karni a dakin muzaira zai kwana, amma a ka'ida kullum sai ya shiga dakin wadda bata da kwanan sa ya tambayeta ko tana da wata matsala kafin yaje daya dakin ya kwanta. Bisa wanann al'ada sarki uwaisul karni ya shiga dakin shulaifa inda ya isketa a zaune tayi tagumi kuma ta zurfafa a cikin tunani.
Koda Yau sallama sai ga amsa, kuma ta mike da sauri ta taho gareshi ta tsaya daf dashi a bakin kofa suka fuskanci juna ya yin da fuskarta ke nuna alamun tsoro da damuwa karara. Kafin ma ya budi baki ya tambayeta abinda ke damunta sai ta fashe da kuka, al'amarin da ya dugunzuma hankalinsa kenan ya dubeta yace, yake matata ina dalilin wanann kuka naki?
Maimakon ta bashi amsa sai ya rungumeshi ta sake fashewa da sabon kuka. Da kyar ya rarrasheta tayi shiru , sannan ya cire ji
kinsa daga cikin nata ya rike kafadunta yace, yanzu idan baki gaya min abinda ke damunki ba to wa zaki dayawa.
Cikin sanyin murya shulaifa tace, yakai mijina kayi sani cewa jiya da daddare nayi wani mafarki mai ban tsoro wanda ya tsaya min a zuciya har izuwa daren yau ya hanani sukuni, domin a jiya yadda naga rana haka naga dare.
A cikin mafarkin an nuna mini cewar ka shiga cikin wank irin mugun hali, wato rayuwar ka na tsakanin mutuwa da jinya.
Sannan kuma an nuna mini yarima uzaifat a cikin tsakanin halin shan wuya tamkar shima zai rasa rayuwarsa.
Tun da na farka daga barci sakamakon wanann mugun mafarki da tsakar dare sai nayi ta addu'o'i har gari ya waye ban rintsa ba.
Ya kai mijina ka sani cewa mafi akasarin mafarkina yana zama gaskiya, bisa wanann daliline na shiga mugun tashin hankali. Shima baka tsammanin cewa wannan yaki da su uzaifat zasu tafi yana da nasaba da wanann mafarkin nawa?
Sa'adda shulaifa ta zo nan a zanceta sai sarki uwaisul karni yayi murmushi a gareta yace, yaje matata kiyi Sani cewa dukkan wani mahaluki rayuwar sa ta kasance rubutaccen al'amari tun kafin ya zo duniya, saboda haka abinda nake so dake shine ki kwantar da hankalin ki kuma ki ci gaba da tayamu da addu'a bisa aikin alherin da muka sa a gabanmu. Ni yanzu tsufa ya riskeni, fatan kawai shine na cika da imani.
Shulaifa ta dago kai ta dubi uwaisul karni a lokacin da hawaye ke sartu bisa kumatunta tace, ya kai mijina, to wai shin me yasa tun tuni baka zabi halifanka ba a tsakanin uzaifat da ukashat har zaka sanya wanann gasa a tsakaninsu mai tsananin hadaki? Kai da kanka ka yaki kasar shumbul yafi sau a kirga baka taba samun nasara akan su ba. Ta yaya kake tsammanin cewa 'ya 'yanka zasu iya samun nasara?.
Koda jin wannan tambaya sai sarki uwaisul karni ya sunkui da kansa kasa yayi shiru baice komai ba. Daga can saiya dago kai ya dubeta, bisa mamaki sai taga hawaye na zuba a idanunsa. Al'amarin daya mutukar bata mamaki kenan ta dubshe cikin mutukar damuwa tace, ka gafarceni ya kai mijina idan wannan tambayar da nayi maka ta Sosa naka zuciya.
Sarki uwaisul karni yasa hannu ya share hawayen sa, Sanna yace,yake matata kiyi sani cewa tambayar ki bata bata min rai ba face ta tuno min da qani kuskure da na tafka guda daya sa'adda na gaji ubana akan wanann karagar mulki, sa'adda nake da shekara talatin da Shifa a duniya.
Ina so ki saurari labarin da zam baki da kyau domin ki fahimci kuskuren da nayi rauywata da kuma illar da kuskuren ya haifar a garenj wanda gashi har na mutu bazan iya magance matsalar ba face 'ya'yana sunci birnin shumbul da yaki.
Nan zamu dakata sai mun hadu lokaci na gaba. Ina muku fatan alkhairi.
Naku a kullum da ko yaushe UMAR FAROUQ ZANGO.
[26/01, 12:14 pm] Umar Farouq: DAKARUN MUSULUNCI
LITTAFI NA DAYA:- 1C
MARUBUCI:- ABDUL AZIZ SANI MADAKIN GINI
TYPING:- UMAR FAROUQ ZANGO.
MARUBUCIN YACI GABA DA CEWA:-
Kimanin shekaru dari da ashirin baya, mahiafina sarki Hurusul karni ya kasance shahararren a wannan nahiya, babu wani sarki mai daukakarsa da karfin mulkinsa faceahaifin sarki sharan na birnin shumbul wato sarki Nukaib.
Duk da cewa mahaifina musulmine shi kuma sarki Nukaib kafirine ma'abocin bautar gunki, akwai kyakkyawar alaka a tsakaninsu, ba don komai ba sai domin tun suna yara kanana iyayensu suka kaisu wata makaranta ta koyon yaki a birnin rum.
A can suka hadu kuma suka zamo abokai. Sai da suka shekara tara a wannan makaranta sannan suka rabuwa kowannensu ya koma kasarsa. A wannan zama da sukayi ne na tsawon shekaru tara a wannan makaranta yasa suka shaku ainun har sukayi alkaqarin cewa zasu tabbatar da abotarsu har abada kuma zasu tabbatar da zaman lafiya a tsakanin kasashen gajiyar duk da cewa a wannan lokaci ma duk shekara sai anyi yaki a tsakanin kasashen masu kuma duk Sa'adda akayi yakin RAGAS akeyi.
Mahaifina sarki Hurusul karni da mahaifin sarki Nukaib basu san cewa 'ya'yansu sun hadu a wannan makaranta ba har suka shaku da juna, kuma basu san wannan alkawari da suka daukarwa juna ba.
A wannan shekara da su sarki Hurusul karni suka kammala wannan makaranta ne yaki ya taso, kuma sai aka sami akasi cewa Hurusul karni shine zai jagoranci mayakan birnin Darul Husuf, shikuma Naukib shine zai jagiranci mayakan kasar Shumbul.
A wanna lokaci duk iyayensu sun tsufa ainun baza su iya fita yaki ba, suna kwance a cikin ciwon ajali, kuma kowannensu burinsa shine yaga kafin ya mutu yaci wannan yaki.
A lokacin malamai sun tabbatarwa da kakana cewa wannan ciwo nasa bana tashi bane, lallai shine ajalinsa. Shima sarki Nukaib bokayensa sun tabbatar masa da cewa mutuwa zaiyi. Bisa wanann daliki ne kowannensu ya gaba da dansa kafin ya fita yakin.
Suka roki 'ya'yan masu akan duk yadda za suyi su tabbatar da cewa sunci wanann yaki.
Sarki Hurusul karni da sarki Nukaib suka yiwa iyayensu alkawarin cewa wanann karon kk dukkannin mayakansu zasu kare sai sun Karar da abokan gaba.
Babban kuskuren da Hurusul karni da Nukaib sukayi shine, har suka rabuwa a makaranta babu wanda gadan sunan garin kowa, asalima basu san cewa a nahiya daya suke ba, kuma duk shekara kasashen su ma yakar juna.
Lokacin da rundunar biyu ta baiyyana a filin daga ya zamana cewa Hurusul karni ma jagirantar mutanen Darul Husuf, shu kuma Naukib na jagorantar mutanen shumbul sai aka sami duk su biyun sunyi wata irin shiga ta rufe fuskokinsu, don haka babu wanda ya shaida kowa. Tazarar dake tsakanin rundunar biyu ta kai zira'i dari, don haka daga nesa ake kallon kallo. Kowanne zuciyarsa cike da mugun nufi. Ba tare da bata lokaci ba sarki Nukaib ya daga takobinsa sama yayi wa jama'arsa inkiya a afkawa abokan gaba. Ai kuwa duk sai suka zare takubbansu suka sakarwa dawakansu linzami suka nufi inda rundunar su Hurusul karni suke.
Koda aka hangosu sai shima Hurusul karni ya baiwa nasa jama'ar umarni suka sukwano da gudu suna kabbara, takobin kowa a sama, wato arna na ihu musulmai na kabbara.
Yayin da aka hadu a tsakiya sai wuri ya yamutse da kuwwar mazaje, Karar karafa da haniniyra dawakai ta yawaita, aka garkame da azababben yaki ya zamana cewa duk indasu sarki Nukaib da suka sa gaba sai dai kaga musulmai na zubewa kasa suna shahada. Haka shima sarki Hurusul karni duk inda ya durfafa sai da kaga arba na zubewa kasa matattu.
Yayain da shugabannin biyu suka ga suna yiwa junan mummanar barna sai suka yi kokari suka tari juna suna masu warewa gefe guda suka bar jama'arsu suna masu ci gaba da kafsawa.
Wohoho! Hakika masu iya magana sunyi gaskiya da suka ce fadan manya babu mai shiga, idan kuwa mutum ya shiga zaiyi nadama.
Nan zamu dakata sai Allah ya kara hadamu a wani lokacin nan gaba.
Ina godiya bisa nuna soyayyarku gareni.
Ina muku fatan alkhairi, naku a kullum da ko da yaushe, UMAR FAROUQ ZANGO
[26/01, 8:16 pm] Umar Farouq: DAKARUN MUSULUNCI
LITTAFI NA DAYA 1C. ( !! )
MARUBUCI:- ABDUL AZIZ SANI MADAKIN GINI
TYPING:- UMAR FAROUQ ZANGO.
MARUBUCIN yakara da:-
Lokacin da sarki Nukaib da sarki Hurusul karni suka ware gefe daya suka fara fafata yaki sai da suka shafe sa'a guda cur! Suna kaiwa juna sara da suka akan dawakai, amma dayansu bai sami nasarar koda lakutar jikin daya ba. Al'amarin da ya basu mamaki kenan, kuma ya fusata su. Bisa dole sai suka sauko daga kan dawakan nasu suka fara sabon yaki a kasa. Nan ma sai da suka sake shafe wata sa'a guda babu wanda ya sami nasara komai. Babban abinda da ya daure musu kai shi ne, karfi yazo daya, kuma dabatun yakinsu iri dayane. Nan kowannensu ya fusata ainun ya kara zage dantse suka ci gaba da fafatawa da dukkanin karfin su. A lokacin ne kowa ya sami nasarar yankar kowa.
Sarki Nukaib ya yanki Hurusul karni a kafada, shi kuma ya yankeshi a cinya. Lokacin guda kowannensu ya dafe raunin sa gami da gyara tsayuwa.
Kamar hadin baki sai kowannensu ya yagi rigar jikinsa ya daure raunin jikinsa, sannan suka sake kacamewa da sabon azababben yaki. Wannan karon sai da suka shafe sa'a uku cur!.
Suna fafatawa amma dayansu bai gajiya ba, kuma basu fasa fi gaba da yakin ba.
Ganin yadda suke wannan mugun artabune duk jama'ar tasu suka tsaya da yakin suka Kewaye su suna kallonsu, don aga wanda zai samu nasara akan wani.
Hakika a wannan rana an ga jaruma
taka da sadaukantaka gami da juriya irin wadanda ba'ataba gani ba a tarihin jaruman nahiyar gaba daya.
Bayan jaruman biyu sun shafe sa'a uku ne suna wannan artabu, sannan suka fara samun nasarar ci gaba da yiwa juna rauni, har ta kai cewa kowannensu ya sami rauni goma sha uku a jikinsa, ya zamana cewa dukkanin su jikinsu yayi fata fata da jini har jiri na dibarsu, amma an rasa wanda zai je kasa. Kuma wani babban abin mamaki shine, a lokaci guda suke yiwa juna rauni, wato da zarar daya ya sami nasara akan dayan sai shima dayan ya sami nasara. Kai tun suna tsaye sai da suka durkushe kasa amma basu fasa kaiwa juna hadi ba. Abu dai har ta kai cewa makaman hannunsu sun lalace sun zubar da su suka kacame da kokawa, a hakan ne kowanne su rawaninsa ya tube fuskokinsu suka baiyana a fili. Koda suka yi arba da fuskokin juna sai suka kame kamar humaka suka kurawa juna ido cikin tsakanin takaici da nadama, daga can kuma sai aka ga sun fashe da kuka, suka rungume juna. Al'amarin da yayi mutukar baiwa kowa mamaki a wajen kenan, jikin jama'ar yayi sanyi aka kara marmatsowa kusa da su. Sarkin Naukib ya dubi Hurusul karni a lokacin da hawaye ke zuba a idanunsa yace, ya kai abokina ya ya akayi muka yi wannan babban kuskure, yanzu Ashe da kai nake yin wanann yakin ban saniba?.
Cikin matukar karfin hali Hurusul karni ya share nasa hawayen sannan ya kara kankame Nukaib a kirjinsa yace, Hakika munyi babban kuskure da har muka rabu a makaranta bamu sanar da junanmu ainahin kasashenmu ba.
Tabbas rashin sani yafi dare duhu, yanzu gashi abune mawuyaci mu rayu bare mu kawo karshen wannan yaki a tsakanin alummarmu, alhalin tun a baya munyi alkawarin tabbata da zaman lafiya a nahiyoyinmu gami da tsayar da yake yake a duk Sa'adda muka zamo shugabanni. Yanzu gashi mun kawo matsayin shugabancin amma kuna burinmu ya yanke anan.
Sa'adda sarki Hurusul karni yazo dai dai man a jawabinsa sai shima sarki Nukaib ya sake kankameshi a kirjinsa duk su biyun suka sake fashewa da kuka, sannan Nukaib yace, ya kai abokina kayi sami cewa duk da cewa mutuwa zamuyi a yanzu ina matakur Farin ciki da zan mutu ina kan kirjinka, domin a ko