Showing 12001 words to 15000 words out of 18821 words

Chapter 5 - Dakarun Musulunci Book 1 By Abdulaziz Sani M Gini.txt

kafin ya dawo sarki ya mutu, kin ga kenan dana ya zama sarki, Darul Husuf ta zama tamu. Idan babu sarki babu uzaifat ta ya ya zakiji dadin rayuwa da mu?
Lallai a sannane zaki ga wulakanci da tozarci irin wanda baki taba gani ba a rayuwarki. Ko magen gidan sarautarmu sai ta fiki jin daraja.
Lokacin da muzaira tazo nan a zancenta sai kawai raga shulaifa ta dubeta tayi murmushi tace, ka jahila wadda bata san fari da baki ba!

Shin kin matane cewa RAI DA MUTUWA duk a hannun Allah suke? Ina mai tabbatar miki da cewar gubar da ki kabawa sarki yaci bata isa ta kasheshi ba face idan kwanan sa ya kare.
Haka kuma duk irin gumun da za'ayi a filin yaki bai zama dole dana ya hallaka ba, zai iya tsira da rayuwar sa tinda Allah ne mai kashe wa da rayawa ba mutum mai najasa ba.
Furucin karshe da zan miki shine, kiji tsoran karshen rayuwarki, domin duk wanda ya shika sharri dole ya girbi sharri.
Koda gama fadin haka sai shulaifa ta juya ta nufi gidan sarautar tabar muzaira a tsaye tana kyalkyala dariya, domin ta tabbatar da cewa babu abinda zai han hakant ya cimma ruwa.
Wannan shine abinda ya faru a birnin Darul Husuf bayan yarima uzaifat da yarima ukashat sun tafi yaki tare da DAKARUN MUSULUNCI rukuni biyu.

Masha Allah nan zamu tsaya sai Allah ya kaimu gobe zamu ci gaba.
Bayan haka ina mai baku hakuri bisa rashin sakar littafin sau biyu a yini daya, hakan ya farune saboda wasu dalilai amma Insha Allahu zanyi kokari naga na saita ta yadda zai cigaba da zuwan muku yadda aka fara da farko na nagode da nuna kauna da goyon bayanku gareni.
Naku a kullum da ko da yaushe UMAR FAROUQ ZANGO. Na barku lafiya
[30/01, 11:04 am] Umar Farouq: DAKARUN MUSULUNCI LITTAFI NA 1
MARUBUCI:- ABDUL AZIZ SANI MADAKIN GINI
TYPING:- UMAR FAROUQ ZANGO

Lokacin da rundunar DAKARUN MUSULUNCI rukuni biyu ta dau hanya sai suka wanzu suna ta tafiya ba tare da sassauci ba har sai da rana ta fadi. Babu abinda ke tsai dasu face sallah da cin abincin rana da sukeyi sau daya.
Sa'adda rana ta fadi sai suka yada zango a cikin wani daji mai yawan sarkakiya, duhuwa da dogayen bishiyoyi.
Shi dai wannan daji yana da mutukar kwarjini da ban tsoro, domin sai da kowa ya sha jinin jikinsa. Tabbas ba za a rasa mugayen abubuwa ba a cikin wannan daji fiye da shekaru arba'in baya fatake ma basa yarda su yada zango a bakin wannan daji, amma yau sai gashi DAKARUN MUSULUNCI sun tsaya a wannan waje. Watakila ko don sun ga yawansu ne ko kuma don sun yarda da Kansu ne? Amma a zihir dosowar magriba ce ta sa suka yada zango a wajen domin su gabatar da sallar magriba.
Nan take salahuddeen da Abul shaja'a suka baiwa dakarun su umarnin a sassabe ciyayi masu tsawo, sannan a kunna fitilun itace kuma a kafa tantuna. Nan da nan kuwa aka cika wannan umarni, cikin kankanin lokaci. Bayan an tabbatar da cewa babu wani mugun abu a kusa sai aka tayarda sallar magriba. Da aka idar aka shafa addu'a sai aka shiga kokarin cin abincin dare.
A wannan lokaci ne Abul shaja'a da yarima uzaifat suka shiga cikin tanti suka zauna aka kawo musu nasu abincin. Koda uzaifat yayi loma daya sai ya kasa ci gaba da cin abincin, ya sunkui da kansa kasa ya shiga tunani.
Cikin alamun damuwa Abu shaja'a ya dafa kafadar uzaifat yace, ya Shugabana lafiya, tunanin me kakeyi haka?
Uzaifat yayi gyaran murya yace, ya kai Abul shaja'a kayi sani cewa ina cikin tsananin damuwa bisa halin da na baro mahaifina a ciki na rashin lafiya, har ina jin kamar na koma da baya a sirrance na shiga har cikin turakar sa na ganshi.
Koda jin haka sai Abul shaja'a yace, haba ya shugabana ai tunda sarki ya kafa dokar cewa kada dayan ku ya sake ya shiga cikin turakar sa face da izininsa ai bai kamata ka karya dokarsa ba, tunda ka kasance mai biyayya a gareshi tun daga kuruciyarka kawo izuwa girmanka.

Ina son kasani cewa sarki na da babbar hujja wadda tasa ya kafa wannan doka babu mamaki idan ka karya dokar ka wargatsa masa wank shiri nasa.
Sa'adda uzaifat yaji wannan batu sai idanunsa suka ciko da kwalla, ya ce,
Wane shiri ne ga mutumin da ke kwance cikin jinyar ajali? Ya kai Abul shaja'a kayi sani cewa ban sa ran sarki zai kara kwana bakwai a duniya.
Cikin mamaki Abul shaja'a ya dubi shi yace ya ya akayi kasan haka?
Take hawaye ya zubowa uzaifat yace, ya kai Abul shaja'a ka sani cewa mahaifiyata tayi mafarki an ciyar da sarki guba tun data bani wannan labari sai nayi istihara aka nuna min abinda ta gani. Abinciken da nayi wajen likitoci sun tabbatar min da cewa in dai mutum yaci guba a cikin abinci abune mawuyaci ya wuce kwana bakwai a duniya.
Abul shaja'a ya kawo gwauron numfashi ya ajiye, sannan ya dubi uzaifat cikin matukar mamaki yace, wane ne ya baiwa sarki guba yaci.

Uzaifat yace, a gaskiya bazan iya cewa komai ba sai dai mu jira izuwa lokacin da asirinsa zai tonu.
Wai shin yanzu tafiyar kwana nawa zamuyi mu isa filin daga inda za'a kafsa wannan yaki tsakanin mu da mutanen birnin shumbul?
Abul shaja'a yace, a Kalla sai munyi tafiyar kwana goma sha biyar sannan zamu isa. Ya kai yarima ka sani cewa karo da mayakan birnin shumbul ba karamin aiki bane, domin duk sa'adda muka gwabza yaki dasu muna shan tsananin wuya...
In ba domin karfin addu'a ba zasu iya samun nasara akanmu.
Tabbas a wannan karonina shakkar gamuwarmu da mutanen birnin shumbul saboda matsala biyu.
Matsala ta farko itace, babu gwarzon mayakin mu wanda yafi kowa jarumataka a Darul Husuf, wato sarki da kansa. Matsala ta biyu itace, wannan karon adadin mayakan da muka fito da su rundunar ka data ukashat gaba daya basu fi rabin rundunar da muka saba fitowa da su ba a duk sa'adda zamu yi yaki da birnin shumbul.


Alhamdulillahi zamu tsaya anan sai Allah ya kaimu anjima zamu ci gaba.
[30/01, 8:04 pm] Umar Farouq: DAKARUN MUSULUNCI
LITTAFI NA DAYA 1
MARUBUCI:- ABDUL AZIZ SANI MADAKIN GINI
TYPING:- UMAR FAROUQ ZANGO

Uzaifat ya dubi Abul shaja'a yace, wai shin wace irin sadaukantaka sarki ke da ita ne? Kasan cewa ban taba ganin yakinsa ba.
Abul shaja'a ya jinjina kai yace, ai ni a rayuwata ban taba ganin sadauki mai zafin nama da jarumataka ba kamar Mahaifinku face mai bakaken kaya na birnin shumbul, wanda a ko yaushe suke RAGAS!
Cikin mamaki uzaifat yace, to wai shin shi Wannna mai bakaken kaya wane ne shi, menene matsayinsa a birnin shumbul?
Abul shaja'a yace, yau shekara takwas kenan da fara fitowar mai bakaken kaya filin yaki, babu wanda ya taba ganin fuskar sa kuma baya daya daga cikin manyan mayakan kasar. Ina tabbatar maka da cewa koda kai da ukashat zaku taru akan mai bakaken kaya bazaku iya hallakashiba, saboda yana da mutukar karfin damtse na gaban kwatance.
Uzaifat ya sunkui da kansa kasa yace, ai kuwa ko zan hallaka zai natari wannan mai bakaken kaya koda zan halaka.
Haka dai uzaifat d Abul shaja'a suka ci gaba da hira har lokacin sallar isha yayi, suka fito daga tantin suka iske tuni su ukashat sunyi alwala.

Koda aka zo za a tayar da sallah sai ukashat yayi sauri ya shige gaba da nufin yayi limanci alhalin ko a gida uzaifat ne yaci gaba da limanci a lokacin da sarki ya sami lalurar rashin lafiya.
Koda salahuddeen yaga ukashat ya wuce gaba zai yi limanci sai ya matsa daf dashi yace, ya shugabana sarki fa ya nada uzaifat a matsayin limaminmu na sallah a cikin wannan tafiya.
Koda jin wannan batu sai ukashat ya dakaw salahuddeen harara yace, nan ba gida bane, don haka da ni da uzaifat anan kowa sarki ne.
Koda gama fadin haka sai ukashat ya juyo ya dubi mai tayar da ikama yace da shi Bismillah, nan take kuwa aka tada sallah.
Ko kadan uzaifat bai nuna wata damuwa ba. Bayan an idar da sallar sai uzaifat yaje ga ukashat yace, ya kai dan uwana ka sani cewa yana da kyau mu zauna ni da kai mu tattauna akan yadda zamu bullowa mai bakaken kaya na birnin shumbul, domin na sami labarin cewa ni da kaima bazamu iya da shiba.

Haka kuma yana da kyau mu tattauna akan yadda zamu bullowa tsarin yakin, domin adadin da abokan gaba ya ninka mu sau biyu ko ma fiye da haka.
Yayin da ukashat yaji wannan batu sai ya yi irin murmushin mugunta da ya saba yi, sannan yace.
Ya kai dan uwana shin ka manta ne cewa wannan yaki da muka fito gasane a tsakanina ni da kai? Ya za'ayi mu hada kai wajen neman nasara? Ai sai dai kowa tasa ta fishsheshi!
Ka sank cewa a halin yanzu duk sa'adda na dubi fuskarka sai naga kamar bakin kumurci nake kallo.
Nifa ban daukeka a matsayin dan uwa ba face makiyi wanda ke kokarin dakusar min da burin rayuwa.
Ni yanzu abin da nake so da kai shine, ka manta da cewa akwai wata nasaba ta jini tsakanina da kai, idan ma kana ganin zaka iya Kawar da ni ka jarraba, domin rayuwata hadarice ga taka.

Koda ukashat yazo nan a zancensa sai uzaifat yace, subahanallahi! Yanzu matsayin da ka daukeni kenan?
To in dk saboda ka mallaki karagar mahaifinmu ne ka tsaneni har kake son Kawar da ni daga yau na janye wannan gasa na bar maka.
Na yarda ka zamo sarki Darul Husuf!
Koda jin haka sai ukashat yayi tsaki yace, ai bakin alkalami ya bushe tunda ka Riga ma amsa cewa zaka yi wannan gasa a gaban sarki. Inda bakason muyi gaba da tun sa sannan zaka janye ka bar min.
Daga yau ina mai shawartarka da ka fita daga harkata, idan da hali ma ka daina yi min magana.
Bazai ga Uzaifat yace, wa'iyazubillahi! Ai a matsayina na musulmi haramun ne na daina maka magana. Ya ya kake zance kamar wNj jahili?
Ukashat yace, ai ni akan wannan sarautar na makance, kuma na kurmance. Gaba daya tinanina ya gushe, babu komai a gabana face nasara ta kowanne hali.

Koda jin wannan batu sai uzaifat ya gyada kai yace, ai kuwa sai dai nace Allah ya shirye ka.
Ukashat yayi tsaki a karo na biyu ya tafi ya bar uzaifat a tsaye yana binsa da kallo kawai cikin mamaki, domin bai taba zaton zai ji kalaman da yayi ba daga bakinsa.
Lokacin da uzaifat ya koma cikin tantinsa ya kwanta don yayi bacci sai ya kasa saboda tunani da mamakin kalmonin da dan uwansa ukashat ya gaya masa a yau.
Yana cikin wannan haline Abul shaja'a ya shigo cikin tantin. Koda yaga uzaifat a cikin wannan hali sai ya zauna kusa da shi yayi gyaran murya, hankalin uzaifat ya dawo jikinsa.
Abul shaja'a ya sake dubansa cikin mamaki yace dashi.
Ya shugabana me kuka tattauna ne da dan uwanka ukashat? Ga dukkan alamu abin da ya hanaka bacci kenan.
Koda jin wannan batu sai uzaifat ya kurawa Abul shaja'a idanu na dan wani lokaci, daga bisani ya kau da kai gefe yace.

Tsakanin dan uwa sirrine, bazan iya gayawa kowa ba.
Koda jin haka sai Abul shaja'a yayi shiru bai kara cewa komai ba. Kawai sai ya koma kan shimfidarsa ya kwanta.
Uzaifat ya juyo ya dubeshi yace, yaya ka tsara harkar tsaro anan?
Abul shaja'a yace, rabin dakarunmu ne zasu yi bacci, rabi suyi gadi.
Muzaira Uzaifat yace, da kyau, kayi tsari mai kyau.
Daga nan duk su biyun suka yi shiru basu kara cewa komai ba har bacci ya kwashesu basu sani ba.
Asuba na yi dai dai lokacin sallah sai Abul shaja'a ya farka.
Koda ya bude idanunsa yaga uzaiu bai farka ba sai ya mike da hanzari ya fita wajen tantin.
Koda fitowa sai yaga babu dakarun ukashat ko mutum daya daga cikin masu aikin tsaro.

Nan take hankalin Abul shaja'a ya dugunzuma, yakoma cikin tantin nasu da gudu a dimauce ya taso uzaifat.
Koda suka fito daga cikin tantin sai suka shiga duba cikin tantuna.
Bisa mamaki sai suka ga babu kowa a cikin tantunan. Hatta tantin yarima kuwa.
A dimauce suka duba sawu lo zasu ga sawun 'yan uwansu ko wani wuri suka tafi amma ko alamar sawunsu basu gani ba.
Al'amarin daya jefasu cikin tsananin mamaki kenan, hankalinsu ya kara dugunzuma ainun, suka tsaya suna tunanin mafita.
Daga can sai uzaifat ya dubi Abul shaja'a yace, mu fara gabatar neman 'yan uwanmu.
Ba tare da bata lokaci ba kuwa suka yi alwala sukayi sallah, sannan suka roki Allah akan ya baiyanar musu da 'yan uwasu.
Nan take suka nufi inda aka daure dawakai bisa mamaki kuwa sai suka iske dawakan rututu a daure kamar yadda aka barsu jiya, Ma'ana ko guda daya ba a daukaba.

Cikin hanzari suka kama dawakansu suka zaburesu izuwa cikin dajin suna tafiya a hankali suna waige waige ko zasu ga alamar inda 'yan uwansu suke.
Abu kamar wasa sai da suka shafe sa'a uku suna yawo a cikin dajin basu ga duriyar abokan tafiyar su ba.
Babban abin da yafi tayar musu da hankali shine, yayin sa suka kara nutsawa a cikin dajin suna shiga cikin muguwar sarkakiya don ratsawa, kwatsam! Sai suka ji sun fada cikin wani irin mugun tabo. Kafin suyi wani yunkuri tuni tabon yarike dawakansu suka kasa gaba ko baya, sannan kuma dawakan na nutsawa kasa.
Uzaifat da Abul shaja'a suka daga kai sama suka yi nazarin wajen gaba daya, suka ga ba zasu iya yin tsalle ba daga kan dawakan nasu subar harabar da tabon yake, domin tabon ya mamaye ko ina, gabas da yamma, kudu da arewa.
Koda suka fuskanci hakan sai hankalinsu ya kara dugunzuma ainun, domin sun tabbatar da cewa in ba wani ikon Allah ba babu yadda za suyi su tsira da rayuwarsu.

Babban tashin hankalin shine , tuni tabon ya shanye gangar jikin dawakan nasu, yazo musu iya wuya.
Cikin karayar zuciya Abul shaja'a ya dubi uzaifat yace, ya shugabana bamu da abinyi face mu fara shahada, domin tabbas mutuwa za muyi a cikin wannan tabon, domin ban ga yadda zamu iya kubutar da kanmu ba.
Koda jin wannan batu sai uzaifat ya dakawa Abul shaja'a tsawa yace, akul ka kara irin wannan furuci, domin dukkan mai rai baya cire tsammanin rahamar Allah a irin yanayin da ya tsinci kansa.
Koda gama wannan jawabi sai uzaifat ya fada karanto wata addu'a bisa neman taimakon ubangiji.
Haja dai wannan tabo ya ci gaba da shanye jikin su uzaifat har ya zamana cewa gangar jikinsu ta nutse a ciki, ya kawo musu iya habarsu.
Har a sannan uzaifat bai cire tsammanin samun taimakon Allah ba, kuma bai fasa yin addu'a ba.
Shi kuwa Abul shaja'a ban da Kalmar shahada babu abinda yake yi.

Ba zato ba tsammani sai suka hango wani mutum daga can saman wani tsauni mai tsawon gaske bisa dole ya taho izuwa karshen tsaunin.
Mutumin na sanye da bakaken kaya, fuskar sa ma a rufe take ruf cikin hanzari mutumin ya sauko daga kan dokinsa ya debo wasu dogayen igiyoyi guda biyu yayi musu zarge, sannan ya jeho su kasa daga saman tsaunin.
A lokaci guda igiyoyin suka fada kawunan su uzaifat da Abul shaja'a, sukayi musu kawanya a wuyansu.
Kawai sai mutumin yaja igiyoyin. Sai gashi yana janyosu daga cikin tabon, amma saboda igiyoyin sun shake wuyan su nan da nan suka fita haiyacinsu. Kafin ya gama fito da su daga cikin tabon duk su biyun sun suma.
Koda mutumin yaga ya samu nasarar janyosu izuwa gareshi jikin tsaunin da yake kai saiya dauko battar ruwa ya budeta ya sako ruwan daga sama ya zuba a kansu.
Faruwar Hakan ke da wuya sai uzaifat da Abul shaja'a suka farfado suna taron wahala a matukar galabaice.

Alhamdulillahi nan zamu dakata sai Allah ya kaimu gobe Insha Allahu zamu dora daga inda muka tsaya.
DAKARUN MUSULUNCI
LITTAFI NA DAYA 1

MARUBUCI:- ABDUL AZIZ SANI MADAKIN GINI

TYPING:- UMAR FAROUQ ZANGO

Mai rubutun ya ci gaba da cewa,
Koda suka daga kai sukayi arba da Wannan mutum wanda ya ceci rayuwar su sai ya bude baki yace dasu, ku cire igiyoyin daga wuyanku ku rikesu, ni kuma zan taimaka muku na hawo da ku izuwa saman wannan tsauni inda nake.
Yayin da uzaifat da Abul shaja'a suka ji muryar wannan mutumi sai suka cika da tsananin mamaki, suka daga kai suna kallonsa a cikin rashin yarda.
Ba komaine ya janyo hakan ba face sunji muryar tasa ce irin ta mata mai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login