Showing 6001 words to 9000 words out of 18821 words
Chapter 3 - Dakarun Musulunci Book 1 By Abdulaziz Sani M Gini.txt
yaushe burin masoyi shine ya kasance tare da masoyinsa. In da ace ka kadai ne zaka tafi ka barni da tabbas sai bakin ciki ya sa na kashe kaina, domin kaine abokina na farko a duniya kuma kaine na karshe, domin tun da muka rabu ban sake yin wani abokin ba. Kayi sani cewa kaine mutumin da na shaku da shi ainun fiye da iyayena da suka haifeni, amma idan baka manta ba mun rabu a makaranta ba tare da sanin cewa zamu rabu ba, domin mahaifina ne yazo a rana daya ya daukeni daga makarantar saboda kawai ya sami labarin cewa ni da kai mun shaku ainun. Lokacin da muka isa gida sai ya rufeni da da matsanaicin fada yana mai cewa saboda me zan yi abota da ma'abocin addinin musulunci? A wannan lokaci yayi ta nuna min illolin jama'ar ku da addininku da irin gabar dake tsakanin mu da ku tun iyaye da kakanni. Nan dai kawai ina sauraronsa ne kawai amma ko kadan a zuciyata ban gamsu cewa ku mutanen banza bane domin a zaman da nayi da kai ban taba ganin mutum mai kyawun hali ba kamarka da sanin yakamata da kuma tausayi da taimako. Ya kai masoyina kayi sane cewa tun a bayan rabuwarmu nake ta bincike a sirrince domin na gano sunan kasarku na kawo maka ziyarar ba zato, amma sai na kasa samun wanda yasan a inda kake. Ni kam tuntuni na gamsu da addininku, don haka a yanzu take inason ka shigar dani cikin wannan addini mai albarka.
Koda jin wannan batun sai Hurusul karni ya cika da tsananin farin ciki. Na taje ya soma bi yawa sarki Nukaib Kalmar shahada. Allah sarki! Hakika idan mutum yana da rabo to fa komai rintsi sai rabonsa ya riskeshi. A dai dai lokacin da Hurusul karni ke biyawa Nukaib Kalmar shahada yana maimaitawa ne Allah ya karbi rayukansu a lokaci guda.
Koda gainin abinda ya faru sai gardama ta kare a tsakanin rundunar biyu. Mutanen Hurusul karni suka ce ai duka gawar biyu ta zama tasu tinda sarki Nukaib ya karbi musulunci. Su kuwa mutanen birnin shumbul suka ce A'a Sam Sam basu yarda ba, sia dai a basu gawar Nukaib su tafi da abarsu. Al'amarin da yajanyo akaci gaba da yaki kenan, yakin ya zamo mai tsananin gaske, jar sai da kowa ya mutuba wajen, mutum daya bai tsira da rayuwarsa ba bare a sami wanda zai kai labarin hakikanin abinda ya faru a filin yakin. Sai bayan kwana guda da faruwar yakin ne iyayen su sarki Hurusul karni suka yi shiri suka zo filin yakin saboda sun ji shiru babu wanda jama'arsa ta koma gida. Koda aka da iso filin yakin kowa yaga dukkanin mayakansa sun zama gawa, haka ma 'ya'yayensu sai suka cika da tsananin bakin ciki suka kama kuka kamar bazasu daina ba. Tsananin bakin cikin rashin yayan nasu ne ya hanasu yin wani sabon yakin a wajen, don haka kowa sai ya dauki gawar dansa yabtafi da ita izuwa kasarsa akan cewa daga baya za a sake yin sabon shirin yakin. A wanann lokaci ne sarki uwaisul karni bai fi shekara bakwai ba a duniya.
Alhamdulillahi nan zamu dakata sai Allah ya kaimu gobe zaku jimu da ci gaban wannan littafi.
Ina fatan yana nishadantar ku.
Ina muku fatan alkhairi
UMAR FAROUQ ZANGO.
[27/01, 11:57 am] Umar Farouq: DAKARUN MUSULUNCI
LITTAFI NA DAYA
MARUBUCI:- ABDUL AZIZ SANI MADAKIN GINI.
TYPING:- UMAR FAROUQ ZANGO.
YACI GABA DA CEWA:-
Lokacin da kakana ya dawo gida dauke dagawar mahaifina rungume a kirjinsa yana ta faman rusa kuka muna tsaye a harabar nan gidan ni da uwata muna ya wasan birin birin ta daure min fuskata da yanki. Koda uwata ta hango gawar mijinta a hannun ubansa sai ta tafka salati da karfi. Nan take zuciyarta ta buga ta sulale kasa matacciya. Cikin hanzari na cire yankim dake fuskata. Koda naga mahaifiyata a kasa ta zama gawa kuma naga mahaifina a kirjinsa kakana shima ya zama gawa sai na fada kan gawar uwata na fashe da matsanaicin kuka. Duk mutum mai imani dole ne ya tausaya min a wannan lokaci, domin bani da kowa face kakana. Kuma na shaku matuka da mahaifina domin a kullum shi ke koya mini yaki kafin su fita wannan yakin da aka kashe shi.
Lokacin dana fashe da matsanaicin kuka sai shima kakana ya kama mikan aka rasa wanda zai rarrashi wani a tsakanin mu. Sai da muka jima a hakan sannan ya ajiye gawar mahaifina yazo gareni ya kamani ya rungumeni a kirjinsa ya shiga karfafa min gwiwa yana cewa.
Ya kai jikana kayi sani cewa ni tsufa ya riskeni don haka a koda yaushe ta Allah zata iya kasancewa a kaina. Idan ka gajeni ka tabbata cewa ka ci gaba da yaki da birnin shumbul har sai izuwa ranar da ka rushe birnin su ka kashe dukkanin mazansu da matansu. Lallai inaso ka daukar min wannan alkawari.
Koda naji wannan batu sai na shiga rantsuwa da girman Allah ina mai cewa, ya kai kakana na dauki alkawari komai dadewa kamar yadda na ga gawar uwata da ubana yanzu sai naga gawar duk abinda ke da rai a cikin birnin shumbul kuma sai na naje birnin su. Idan kuwa abin ya gagareni ba zan mutuba face na dora 'ya'yana akan wannan turba.
Sa'adda sarki uwaisul karni yazo dai dai nan a labarinsa sai hawaye ya zubo masa ya dubi shulaifa yace, kinji asalin abinda ya haddasa yaki tsakanina da kasar shumbul kuma har kwanan gobe ina son na cika alkawarin da na daukarwa kakana duk da cewa na san kuskure be yin hakan tunda mahaifina da sarki Nukaib bai mutuba ba face sai da ya karbi musulunci.
Koda jin wannan batu sai shulaifa ta cika da tsananin mamaki tace, ya kai mijina lg akayi kasan cewa sarki Nukaib ya karbi musulunci alhalin kowa ya mutu a filin yakin ba a sami wanda ya kawo labarin abinda ya faru ba?.
Uwaisul karni yayi ajiyar zuciya sannan yace, yake matata hakika kinyi tambaya mai matukar mahinmmanci kuma mai Ma'ana. Ina son ki sani cewa bayan kimanin shekaru arbain da mutuwar mahaifina na tsinci wata wasika a cikin irin tufafinsa da na gada wadanda ban taba sauyawa ba. Wannan wasika na kunshe da wasiyya ce ta mahaifina a gareni. Ashe kafin ya mutu a wannan filin yaki ya sami damar rubuta wannan wasiya, domin ya kawo karshen yakin a tsakanin kasashen biyu. A cikin wasikar ne ya bukaci da nayi tallan addinin musulunci ga mutanen kasar shumbul, kuma a cikin wasikar ne yayi min bayanin dangantakarsa da sarki Nukaib bisa abotarsu a makaranta da kuma duk abinda ya faru a tsakaninsu a filin yaki. Lokacin da na gama kiranta wannan wasika sai na fashe da kuka domin bakin alkalami ya Riga da ya bushe babu abinda zan iya yi a kan al'amarin. Bazan iya tsaida yakin ba tsakanina da birnin shumbul saboda na rigaya na dauki alkawarin ci gaba da yaki ga kakana, kuma har a ranar da kakana zai mutum yana kan cinyata babu abinda yaje maimaita min face na cika alkawarin da ke tsakaninmu. Yake matata tabbas bazan taba janye wannan alkawari ba, don haka dolene naci gaba da karfafawa su uzaifat gwiwa akan wannan yaki kuma duk wanda ya sami nasarar cin birnin shumbul da yaki shinea zai gajeni. Wannan itace wasiyyatr da zan bari kuma ko a bayan raina da ita za'ayi amfani.
Koda gama wannan jawabi sai uwaisul karni yayiwa shulaifa sallama ya tafi izuwa dakin muzaira domin ya bata kwananta.
* * * * * *
Kashe gari bayan an yi kalacin safe sarki uwaisul karni ya tura aka kirawo yarima uzaifat da yarima ukashat suka gabata gareshi. Bayan sun durkusa a gabansa sun kwashi gaisuwa sai ya dube su a nutse yace yaku 'Ya'yana ina son nayi muku nasiha guda daya kafin nayi muku bayanin yadda zaku gabatar da wannan yaki da mutanen shumbul.
Nasihar da zan muku itace, duk abinda zaku yi kada kuyi gaggawa, domin ita gaggawa taba kai mutum izuwa ga nadama. Sannan kuma ku kasance masu bincike bisa duk al'amarin da yazo muku saboda bincike na iya haifar da fahimtar juna gami da samun zaman lafiya ba tare da kun aikata abin da zaizo ya dameku ba. Dan gane da batun yakin da zaku tafi, ina son kuyi shiri kowannenku ya jagoranci rundunar dakarunsa a lokacin guda ku tafi yakin inda aka saba fafatawa muda mutanen birnin shumbul a gobe. A yanzu zan yi muku kacici kacici domin fitar da rundunar da zata fara tarar abokan gaba.
Koda gama fadin haka sai sarki uwaisul karni ya sanya hannunsa a cikin aljihun rigarsa ya fiddo wadansu takardu dunkulallu biyu ya ajiye a gabansu yace kowannenku ya zabi takarda guda. Wanda ya dauki takardar da aka rubuta daya a cikinta dakarunsa ne zasu fara fita filin daga.
Koda jin wannan batu sai uzaifat da ukashat suka tsirawa takardun biyu idanu aka rasa wanda zai fara dauka. Sarki uwaisul karni ya daka musu tsawa yace, me kuke jirane.
Koda jin tsawar sai jikin su ya kama kyarma, cikin sauri uzaifat ya kai hannunsa ya dauki takardar dake gabansa sannan ukashat ya dauki dayar, sarki yace to ku warware takardun don muga abinda ke ciki. Ba tare da fargabar komai ba uzaifat yayi bisimillah ya bude tasa shi kuwa shi kuwa ukashat sai ya kama nuku nuku da kyar ya bude tasa.
Sarki uwaisul karni ya karbi ta uzaifat ya duba sai ga lamba biyu a rubuce, kawai sai ya nunawa ukashat yace, to kaine zaka fara tarar abokan gaba.
Nan take bakin ciki ya turnuke ukashat saboda shi a tunaninsa idan su uzaifat ne suka fara yin yakin nan da nan za a fara cin lagonsu uzaifat sai su kasa samun nasara inyaso daga baya sai su tsinci dami a kala.
Yayin da sarki uwaisul karni yaga alamun damuwa karara a fuskar ukashat sai ya dubeshi yace, ya kai dana kayi sani cewa komai na duniya rabone. Babu wanda ya isa ya hanaka samun nasara a wannan yaki idan kana da rabo, haka kuma babu wanda ya isa ya sa samu idan baka da rabo.
Koda sarki uwaisul karni ya zo nan a zancesa sai tari ya sarkeshi. Abu kamar wasa sai tarin yaki tsayawa, sai kuma ya fara aman jini. Nan da nan hankalin uzaifat da na ukashat ya dugunzuma suka dimauce. Cikin karaji uzaifat ya kwalawa wani hadimi kira wai shi amzabu. A guje Amazabu ya shigo cikin turakar, uzaifat ya umarci amzabu daya ruga gidan likitan sarki abu sharaz ya ki rashi yanzu yanzu. Koda jin wannan umarni sai amzabu ya sake juya wa wajen ya kama dokin ya haye ya zabureshi.
Jima kadan sai ga amzabu tare da abu sharaz sun shigo cikin turakar sarki. Da shigowar su abu sharaz ya ga halin da sarki ke ciki, a wannan lokaci sarki na numfashi sama sama kuma idanunsa sun kada sunyi jawur babu kyan gani, sai shima hankalinsa ya dugunzuma nan take ya bude jakarsa ya fiddo wadansu magunguna ya hadasu a cikin kofi sannan ya durawa sarki a baki.
Alhamdulillahi nan zamu dakata sai Allah ya kaimu lokaci na gaba zaku jimu da ci gaban wannan littafi.
[28/01, 8:25 pm] Umar Farouq: DAKARUN MUSULUNCI
Haryanzu muna cikin LITTAFI NA DAYA
MARUBUCI:- ABDUL AZIZ SANI MADAKIN GINI
TYPING:- UMAR FAROUQ ZANGO
Yaci gaba da cewa
Koda sarki uwaisul karni ya sha wannan maganin sai ya sake yin wani sabon kumallon mai dauke da wani irin bakin abu.
Likita abu sharaz yayi nazarin wannan bakin abu kuma sai yayi nazarin kumallon da sarki yayi sai kawai ya sunkui sa kai cikin takaici ya kwantar da sarki akan gadonsa ya lullubeshi da mayafi sabo da jikinsa na karkarwar dari.
Cikin dimauta uzaifat da ukashat suka dubi sharaz suka ce likita sarki zai sami lafiya ko?
Kafin abu sharaz ya budi baki ya basu amsa sai kawai sukaji sarki uwaisul karni yayi ajiyar zuciya yace, ku fita ku bamu wuri ni da abu sharaz zamuyi sirri.
Koda jin sarki yayi magana sai murna ta kama uzaifat da ukashat domin suna ganin cewa ya sami lafiya kenan. Ba tare da wata gardama ba uzaifat da ukashat suka mike suka fita daga cikin turakar.
Fitarsu ke da wuya sai sarki uwaisul karni Ya dubi Abu sharaz yace, tashi ka rufe kofa da tagogin dakin nan domin bana son kowa yaji abinda zamu zanta.
Cikin sauri Abu shares ya mike ya cika wannan umarni, sannan ya dawo kusa da sarki ya zauna daf da shi a gefen fadin suka kurawa juna idanu tsawon dakiku biyar dayansu baice uffan ba. Daga can sai sarki uwaisul karni ya yi kakin jini ya tofar sannan ya dubi Abu sharaz cikin alamun takaici da karayar zuciya yace, ya kai amintaccen likitana fada mini gaskiyar al'amari bisa abinda ka fahimta akan wannan rashin lafiya data sameni.
Sa'adda likita Abu sharaz yaji wannan batu sai yayi ajiyar numfashi a lokacin da idanunsa suka ciko da kwalla sannan yace, ya shugabana hakika a cikin abincin da kaci na karshe ko a yau ko ajiya an zuba guba a ciki. Tuni wannan guba ta gama zagaya jinin jikin ka. Maganin da na baka zai kwantar da gubarne kawai amma abune mawuyace ka hate illar wannan guba sai dai idan kana da sauran kwana a duniya.
Koda Abu sharaz yazo nan a zancensa sai ya ga hawaye ya zubo a idanun sarki uwaisul karni, al'amarin daya dugunzuma hankalinsa kenan, yayi na damar sanar dashi gaskiyar al'amarin.
Yayin da sarki uwaisul karni ya fahimci halin da Abu sharaz ya shiga sai ya dubeshi a nutse yace, yakai amintaccen likitana kayi sani cewa wannan hawaye nawa daka ga ya zuba ba na tsoro bane kuma bana takaici bane face na takaicin rashin daukar shawarar mahaifiyata, domin kuwa in da nayi amfani da shawararta da banshiga wannan hali da na shiga ba.
Tabbas yanzu na gano cewa ba wani bane ya zuba mini guba a abincina ba face muzaira mahaifiyar ukashat.
Tun kafin na auri muzaira mahaifiyata ta shawarceni akan kada na aureta domin bani take so ba, mulkin da nake ciki take sha'awa wannan lokacin soyayya tasa idanuna sun rufe bana ganin laifin muzaira ko kadan don haka sai naki amfani da shawarar mahaifiyata. Tabbas a yau na gane cewa duk wanda ya ketare maganar manya sai ya ga ba dai dai ba. Yanzu gashi muzaira ta nemi rayuwata saboda kawai ta mallaki mulkina. Ma'ana ta karbe karagata ta baiwa danta.ya kai amintaccen likitana yanzu a kiyasce kana ganin cewa tsawon wane lokayzan iya rayuwa tare da wannan guba da ke jikina?
Koda jin wannan tambaya sai tausayin sarki uwaisul karni ya turnukeshi har kwalla tazo masa yace, ya shugabana ka sani cewa mutuwa lokaci ce, indai lokacin yazo baza a kara ba, kuma ba za a rage ba. Amma a kiyasi irin namu ba likitoci indai mutum ya sha irin wannan guba da kasha duk irin taimakon daza a bashi ba zai wuce kwana bakwai a duniya ba.
Koda jin wannan batu sai fuskar sarki uwaisul karni ta fadada sa murmushi yace, Alhamdulillahi! Abinda na ke so da kai shine, ina so ka tafi izuwa gidan Malam abdulwahab ka gaya masa cewa ya tara sauran jama'ar sa su shiga halwa bisa rokawa kasata sarkin da zaifi zama alkhairi ga jama'ata bayan mutuwa ta. Wannan shine kadai sakon da nake son ka Isar min da shi, kuma a yanzu idan ka fita ka sanar da 'ya'yana su uzaifat cewa bana bukatar kowa ya kara shigowa cikin turakata, hatta iyayensu mata kuwa sai lokacin da na bukacesu da kaina.
Koda jin wannan batu sai likita abu sharaz ya dubi sarki uwaisul karni cikin mamaki yace, ya shugabana yanzu tun da kana da tabbacin cewa muzaira ce ta saka maka guba a cikin abincin ka me zai hana kayi mata hukunci.
Koda jin wannan tambaya sai sarki uwaisul karni yayi yake yace, ai baa fafe gora ranar tafiya, shi zunubi matane in dai ka daukeahi baka isa ka ajiye shi ba face asirinka ya tonu, domin sai nauyinsa yasa ka gajiya. Da sannu gaskiya zatayi halinta kowa ya ganta a fili karara. Yanzu na sallameka sai naje ka cika wannan umarni.
Yayain da sarki uwaisul karni yazo nan a zancensa sai likita abu sharaz ya mike tsaye cikin sanyin jiki ya fita daga turkar yana waigen sarki yana zubar da hawaye saboda tausayi da kuma sabonda sukayi tsawon shekara da shekaru.
Da fitowar abu sharaz daga turakar sarki sai ya iske uzaifat da ukashat a tsaitsaye a cikin alamun tashin hankali. Koda suka ga ya fito daga cikin turakar sarki uwaisul karni sai suka taho gareshi da sauri da nufin shi shiga cikin turakar.
Abu sharaz ya sha gabansu yace, sarki yace na gaya muku cewa daga yau kada kowa ya sake shiga cikin turkarsa face bawansa mai yi masa hidima a kullum har sai yabukaci ganinki.
Koda jin wannan batu sai su uzaifat suka cika da mamaki, kuma hankalin su ya dugunzuma ainun.
Nan dai abu sharaz ya tafi ya barsu a tsaye cikin mutukar damuwa da tunani. Bisa dole suma suka tafi suka bat kofar turakar sarki.
* * * * * *
Lokacin da ukashat ya koma turakar mahaifiyarsa muzaira ya sanar da ita duk abinda ya faru tskaninsu da sarki sai ta