Showing 3001 words to 6000 words out of 23330 words

Chapter 2 - Dakarun Musulunci Book 3 By Abdulaziz Sani M Gini.txt

ta san cewa ita da su Uzaifat sun tsira daga sharrin iyayenta domin basu isa su ketara wannan iyaka ba saboda haja dokar tsafin zurkas ta shirya masa shi da matarsa maziba, amma banda yayansa.
Idan kuwa har suka yi gangancin haura iyakar nan take jikinsu zai kama da wuta gaba daya ya babbake sai dai kashi yayi saura.
Rabin sa'a na cika sai hirama ta jiyo ihun uwar mayu da wadansu dai daikun yayanta daga can nesa.
Hirama ta tsaya cak! A inda take bata motsa ba bare tayi yunkurin komawa da baya don kai dauki, amma sai ta mike tsaye ta ci gaba da kallon hanya.
Jim kadan sai ga uwar mayu da ragowar yayanta su goma sha biyar kacal sun kasa uban tsere da zurkas da maziba. Uwar mayu da yayanta suna ihu suna waige.
A duk Sa'adda suka wai ga suka ga tazararsu da su maziba bata wuce taku uku ba.
A haka ne kuna maziba da zurkas suka ci gaba da cafke yayan uwar mayu suna tsintsinkasu tamkar suna kakkarya kara suna cinyewa danyi akan hanya ana cikin gudun.
Kaico! Nan fa uwar mayu taga inda aka fita maita domin maziba domin da mijinta zurkas suna cin naman yayanta ne da jini.
Kai hatta kashinsu basa zubarwa taunewa suke. Daga cikin yayan uwar mayun duk wanda ya waigo yaga ana walima da dan uwansa sai ka ga ya kara firgicewa kuma ya kara karfin gudunsa, amma duk ya zama a banza domin kuwa zurkas da maziba kure musu gudu suke yi sna cafkeau suna cinyewa.
Kafin akai iyakar dajin huzurul has tuni zurkas da maziysun cinye gaba daya yayan Uwar mayu saura daya JAL da ita kanta uwar mayun.
Koda uwar mayuda danta suka tsallaka karshen dajin suka dira a cikin dajin birnin shumbul suka fadi a gaban Hirama sai uwar mayu ta rungume dan ta ta fashe da matsanaicin kuka.
Ba shiri zurkas da maziba sukayi turjiya basu yarda kafarsu sun taka kasanr dajin birnin shumbul ba.
Nan fa aka fara kallon kallo tsakanin Hirama da su zurkas kallo na tsananin Kiyayya da takaici.
Cikin tsananin fushi da takaici fuskar sa ta kama yatsina kamar zata zazzago kasa yace, ya ke yata hakika kin ci amanarmu ni da mahaifiyar ki kuma in badon saarki tayi yawa ba da baki isa ki tsallake sharrinmu ba.
Ni yanzu abinda nake rokonki shine ki bamu wadannan biladama guda uku dake gabanki da kuma uwar mayu da danta guda daya wanda ya rage mu cinye su yanzu taje a gabanki idan kikayi haka kin wanke dukkan laifi ki a wajenmu kuma zamu yafe miki bisa alkawarin ba zamu cutar dake ba inyaso sai ki bimu mu koma gida.
Ina so ki fahimta cewa ba yar Adam bace ke ba dodo bace, kuma ba aljana bace.
Babu inda zakije ki yi rayuwa mai dadi a fadin duniyar nan face tare da mu, domin duk inda kikaji za'a kyamaceki a dinga tsoronki.
Koda zurkas yazo nan a zancensa sai hirama ta bushe da dariyar mugunta, lokaci guda kuna ta turbine fuska, a lokacin da hawaye ya zubo mata ta dubi zurkas tace, ya kai abbana ina son ka sani cewa an dade ana ruwa kasa na tsotsewa don haka ba zaku iya yaudarata ba da daina bakinku kai da uwata.
Na sanku kuma na san Ma'anar ko wanne motsi naku.
Na yarda na fuskanci kowanne irin yanayi da zan tsinci kaina a ciki.
Kalmata ta karshe a gareki itace karshen zalincinku ga sauran halittu yazo.
Ku saurari ranar da ajalinkh zai riskeni a cikin wannan dajin huzurul has. Wannan shine bankwana nawa a gareku.
Gama fadin hakan ke da wuya sai Uzaifat Lafirat da Abul shaja'a suka farka daga dogon barcin da sukeyi.
Cikin tsananin mamaki duk su ukun suka mike tsaye, suka kama kallon su zurkas da Hirama.
Nan take Lafirat ta gane abinda yafaru saboda haka sai ta dubi Hirama tace, ta yaya kika zabemu kika guji iyayenki har kika kubutar daga sharrinsu?
Koda jin wannan tambaya sai Hirama tayi murmushi tace, iyayena azzalumaine wadanda suka shafe daruruwan shekaru suna zalunci a doron kasa, ni kaina za su iya salwantar da rayuwata don kada na hanasu zaluncinsu.
Tuni na yanke kauna tsakanina da su bisa wannna daliline na yanke shawarar na kubutar da rayuwarku kuma na bimu izuwa inda zakuje domin naje na fara sabuwar rayuwa a wani bangare dabam.
Kafin Hirama ta gama rufe bakinta tuni maziba ta tsandara ihu sannan ta yunkura zata daka tsalle ta fada kanta sai zurkas yayi sauri ya riketa tamau da hannayensa biyu ya daka mata tsawa yace, baki da hankalina ko kuwa kin manta cewa idan ni ko ke dayansu ya shiga dajin gaba take zai hallaka?
Koda jin haka sai maziba ta fashe da kukan bakin ciki tace, yanzu ni menene amfanin wannan bakar haihuwa da mukayi?
Gwara ka kyakeni na kasheta koda kuwa nima zan hallaka.
Hawayen takaici ya zubowa zurkas yace, rabu da ita amma su abokan tafiyar ta idan sun isa su tako izuwa nan inda muke mana.
Koda jin haka sai Uzaifat ya fusata ya zare takobinsa zai afkawa su zurkas sai Lafirat tayi caraf! Ta rukoshi ta dawo da shi baya ta dubeshi tace, aikin dake gabanmu gagarumin akan wannan.
Kayi hakuri muje mu dawo babu mamaki ajalinsa a wuyanka zai rataya.
Gama fadin hakan ke da wuya sai Lafirat ta kama hannun Uzaifat ta jashi suka juya suka ci gaba da tafiya.
Abul shaja'a uwar mayu da danta guda daya da garage suka take musu baya.
Zurkas da maziba kuwa suka bisu da kallo kawai suna ciza yarda cikin tsananin takaici domin suna ji suna gani babu wata illah da zasu iya yi musu.
Ba tare da wai waye ko tsayawa ba su Uzaifat suka ci gaba da tafiya suka durfafi birnin shumbul kai tsaye.
Da yake Lafirat ce ta san hanya itace akan gaba.
************* *******
Najibullah Muhammad
************ **********

Koda ta ga su Uzaifat sun zare takubbansu suna waige waige da hange hange sai ta yi murmushi tace, ku kwantar da hankalinku ai muna da sauran daoguwar tafiya kafin mu isa birninmu, domin a kalla nan gaba sai mun tafiyar sa'a bakwai sannan zamu isa kofar birnin shumbul.
Kuma ina tabbatar muku da cewa daga nan har izuwa birnin shumbul ba zamu sake haduwa da wani mugun tarko na mahaifina ba face tsirarun yan fashi, muggan dabbobin daji da muggan aljanu.
Koda jin haka sai Uzaifat da Abul shaja'a suka fara mayar da takubbansu cikin kufe suka ci gaba da tafiya cikin kwanciyar hankali.
Haka dai suka wanzu suna ta keta daji har izuwa kusan sa'a uku, a sannane magriba ta kunno kai.
Koda Uzaifat ya ga magriba ta kusa sai ya dubi Abul shaja'a da uwar mayu tare da danta yace, ina ganin zaifi kyau mu yada zango tunda magriba ta kusa, in yazo bayan munyi sallar ishai kuma munck abinci sai mu ci gaba da tafiya.
Cikin hadin baki Abul shaja'a uwar da danta suka ce, lallai haka ya kamata ayi.
Ba tare da neman shawarar Lafirat da hirama ba aka tsai da tafiya, Uzaifat ya kafa tanti sannan yayi alwala.
Cikin sauri Abul shaja'a da uwar mayu suna sukayi alwala suka bishi yayi musu sallah.
A wannan lokaci Lafirat na zaune a gefe daya ta kurawa su Uzaifat idanu tana kallon Yadda suke yin ibadarsu, abin na birgeta tana ta murmushi.
Sa'adda Hirama taga yadda su Uzaifat suke wannan ibada sai ta cika da tsananin mamaki domin ita bata taba sanin cewa akwai wani ubangiji da ake bautawa ba face aljanu.
Hirama ta mike tsam daga inda take zaune ta koma daf da Lafirat ta zauna sannan ta dubeta tace, wadannan kuma wane irin sihiri ne su Uzaifat sukeyi?
Koda jin Wannan tambaya sai Lafirat tayi dariya sannan tace, ai wannan abinda kika ga suna yi ba sihiri bane, aikine na bauta ga ubangijin su, wato abin dogaronsu wanda ni kaina na aminta dashi kuma ako yaushe zan iya karbar wannan addinin nasu.
A Yanzu haka uwar mayu ma da kike gani ta karbi addinin nasu.
Cikin mamaki Hirama tace, to menene yaja hankalin uwar mayu ta karbi wannan addini alhalin bata sanshi ba bata san komai a kansa ba?
Lafirat tace, babu bukatar na baki amsar wannan tambaya domin ance gani ya kori ji. Lallai idan kina tare damu zaki ga amsar wannan tambaya da kika min da idanun ki.
Bayan su Uzaifat sun gabatar da sallar ishai sai aka ci abinci, sannan Uzaifat, Abul shaja'a da Lafirat sukayi shimfida kowanne ya kishingida domin ya huta.
Dama an kunna wuta a tsakiyarsu don jin dumi sakamakon sanyin da ke kadawa a cikin dajin, kuma sun yiwa wutar kawanya suna daf sa juna.
Duk Sa'adda Uzaifat ya dago kai ya sai ya hada ido da Lafirat, sai suyiwa junansu murmushi kawai kowa ya sunkui da kai.
Babu wanda ya lura da wannan hali da suke ciki face Hirama don haka sai tayi dariyar ciki kawai tayi shiru ba tace komai ba.
Ana cikin haka ne Hirama ta taso daga inda take zaune ta zo daf da Uzaifat lokacin da yadaga kansa sama yana kallon taurari, nan take ya shiga tunani mai zurfi sai ga hawaye na zubo masa.
Babu wanda ya lura da wannan sabon yanayi sa Uzaifat ya shiga face Hirama don haka sai ta dubeshi cikin mamaki tace, ya kai wannan jarumi mai kirar sadaukai Ina dalilin zubar wannan hawaye a idanunka?
Kodajin wannan tambaya sai Uzaifat yayi ajiyar zuciya yace, yake wannan ma'abociyar taimako a garemu kiyi sani cewa ba komai ne ya sani zubar da hawaye ba face tunowa da irin halin da dan uwana Ukashat ya jefa kansa a ciki na bijirewa ubanhijinmu, kuma ya hada kai da makiyanmu su sarki shaaran domin ya rushe birninmu saboda kwadayin duniya kawai.
Ashe dan uwa na iya barin dan uwansa na jini saboda abin duniya?
Sa'adda Uzaifat yazo nan a zancensa sai ya ga itama Hirama hawaye ya zubo mata.
Hirama ta dubi Uzaifat cikin yanayin ban tausayi tace, ni fa ma tuna cewa iyayena na bari da dan uwana saboda bambancin rarayinmu bisa mugayen dabiun da muka dade munyi wadanda na gabe cewa basu dace ba.
Koda jin haka sai Uzaifat yaji ya kamu da tsananin tausayinta don haka sai ya dubeta yace, ya ke hirama inayi miki fatan samun babban rabo na karbar addininmu domin da zarar ki karbeshi zaki sami nutsuwa da kwanciyar hankali kuma mune zamu maye miki gurbin iyayenki da dan uwanki da kika rasa. Saboda dukkanin musulmi na kwari yana kaunar dan uwansa musulmi kamar yadda yake kaunar kansa.
Kafin Hirama ta kara cewa wani abu sai kawai suka ga Lafirat ma ta so daga inda take kishingide ta dawo daf da Uzaifat ta zauna a gefen shimfidar sa sannan ta dubi hirama tace, ya ke wannan ma'abociyar kyautayi da taimako a garemu hakika na tausaya miki bisa yadda kika danne zuciyar ki kika sabawa kyayenki domin ki tserar sa rayuwa mu.
Amma ki sani cewa nice abar tausayi fiye da ke, domin ni na tsani iyayen nawa kamar yadda nasani mutuwa ta kuma bani da burin da yafi na ga na hallaka su da hannuna don kawar da bakin ciki da takaicin da suka dasa min a zuciyata.
Kafin wani a cikinsu ya kara cewa wani abu sai suka fara jiyo wani irin gurnani mai ban tsoro acikin duuwar dajin.
Ba shiri dukkanin su suka mike tsaye Uzaifat, Lafirat da Abul shaja'a suka zare takubbansu. Hirama da Uwar mayu suka gyara tsayuwa gami da bude hannayensu masu dauke da manyan yan yatsu da farata cako cako suna jiran ko takwana.
Ba zato ba tsammani sai ga wasu murguza murguzan kuraye masu tsananin kwarjini da ban tsoro sama da guda dubu sun firfito daga cikin duhuwar bishiyoyi da ciyayi suka yi musu kawanya kuma suka rinka matsowa a hankali.
A iya rayuwar Uzaifat da ta Abul shaja'a ko a labari basu taba jin irin wadannan kuraye ba. Uzaifat ya dubi Hirama da Uwar mayu yace me kuka sani dangane da wadannan kuraye.
Duk su biyun sai suka gyada kai alamar cewa basusan komai ba akansu. Uzaifa ya dubi Lafirat yace, ke kuma fa kin san wani abu akan wadannan kuraye?
Lafirat ta jinjina kai tace kwarai kuwa na sansu.
Wadannan kuraye tsafaffune kuma mahaifina ne yayi musu kiwo na musamman kuma ya tsafance su ya zamana cewa ya killacesu.
Nataba ji yace ba zai taba fito da su b sai ya gama fita yakin karshe tsakanin birninmu da birninku na darul husuf.
Duk yadda akayi mahaifina da dakarunsa suna nan Musa da inda muke.
Koda jin wannan batu sai uwar mayu da hirama suka firgita ainun domin su Kansu sun san masifar sarki sha'aran da matsayin sa a fagen yaki da yadda yake da karfi akan dukkanin halittun dake cikin dazuzzukan da suka kwaye kasasrsu.
Lokacin da Uzaifat da Abul shaja'a suka a saura kiris wadannan kuraye su cimmusu sai sukayi kabbara cikin hadin baki suka afkawa kurayen suka hausu da sara da suka, suma kurayen sai sukayi musu rubdugu.
Nan take wurin ya yamutse aka kacame da azababben yaki ya zamana cewa Uzaifat da Abul shaja'a sun fara samu nasara akan kurayen domin duk wacce suka sara ko suka soka sai dai kaga jikinta ya dare ko ya bule jini na zuba.
Amma a bangaren Lafirat da hirama da uwar mayu abin ba haka yake ba domin ko kadan sun a kasa cutar da kurayen saboda duk Sa'adda suka karci jikin kuraye ko suka saresu sai kaga ko kwarzanewa basa yi, suma kurayen sun kasa yiwa su Lafirat lahani da kaifin faratnsu da na hakoransu, amma kuma duk Sa'adda suka bangajesu sai kaga sun kaisu kas wani lokacin ma har turmushesu suke yi suna dudufniya a Kansu.
Lokacin da Uzaifat ya lura da halin da su Lafirat suka shiga sai ya daka tsalle daga inda yake yana mai kwalla kabbara da karfi fiye da ko yaushe ya tarwatsa kurayen yaci gaba da ragargazarsu, kafin a jima Uzaifat ya kashe sama da kuraye dari biyu.
Shikuwa Abul shaja'a ya kashe dari. Ganin wannan nasara da suke sanine itama uwar mayu tayi koyi da su ta rinka kwalla kabbara sai gashi tana guda cikin kurayen da tsinin faratan hannayenta suna zubewa kasa matattu.
Kafin kace wani abu itama ta kashe sama da guda hamsin.
Kwatsam ba zato ba tsammani sai sukaji an busa wani irin kaho mai karfin sauti wanda ya cika dajin gaba daya.
Dajin sautin kahon sai sauran suka daina gumurzun dasu suka ja da baya suka tsaya cak tamkar basu da rai a jikinsu.
Kawai sai su Uzaifat suka jiyo motsin sawayen dawakai a can samansu bisa wani dogon tsauni da yayiwa dajin gaba daya kawanya.
Koda su Uzaifat sukayi arba da rundunar mayakan birnin shumbul wadanda adadinsu ya wuce miliyan biyar. Sarki sha'aran, Ukashat da sazirat ne akan gaba bisa wadansu ingarmun dawakai sunyi gagarumar shigar yaki.
Nan taje aka fara kallon kallo tsakanin sarki sha'aran da su Uzaifat.
Sazirat da Lafirat suka fara hararar junansu, haja ma Uzaifat da Ukashat kowannesu zuciyarsa na tafarfasa kamar su ruga su afkawa juna.
Shi kuwa sarki sha'aran koda ya dubi au Uzaifat ya gansu yan kalilan sai ya bushe da dariyar mugunta.
Lokaci guda ya murtuke fuska tamkar an aiki masa da sakon mutuwa ya dubi Lafirat a fusace yace, kaiconki yata, hakika kin bani kunya kuma kin ci amanar kulawar da na vakj a matsayina na mahaifinki Tun kina jaririya.
Tabbas yanzubne zaki yi nadamar butulcin da kika yi mini.
Kafin sarki sha'aran ya gama rufe bakinsa sai Lafirat ta tari numfashin sa tace, Kai tsohon banza annamimi mai abin kunya, kayi sani cewa har abada ba zan yi nadamar butulcin da nayi maka ba, domin na tsaneka kamar yadda na tsani mutuwa ta.
Nayi kuka da bakin ciki matsanaici da ya zamo kaine mahaifina, tabbas inda ina da ikon sauyawa kaina asali da suna da tuni na sauya.
Har abada tsakanina da kai da duk wani mai goyon bayan ka babu kauna kuma babu abinda zai rabamu face kaifin takobi.
Koda ji haka sai sarki sha'aran ya bushe da mahaukaciyar dariya wacce amsa kuwwarta ta cika dajin gaba daya.
A wanna lokaci ne sarki sha'aran ya lura da kurayensa na tsafi wadanda su Uzaifat suka karkashe.
Nan take jikinsa ya kama tsuma, zuciyarsa ta kama tafarfasa kamar zata kone.
*DAKARUN MUSULUNCI*
Littafi Na 3
Part C ✍️

Na:Abdul Aziz Sani Madakin Gini
Typing Muhammad Umar Zango.
Posting Najibullah Muhammad 🥷🥷

Marubucin yaci gaba da cewa..

Kawai sai ya dubi sazirat da ukashat yace, ku sauka izuwa kasan tsaunin nan ku gama da abokan gwaminku.
Ya sake dubdan sarkin yakinsa yace, kai kuma ka sauka ka kashe Abul shaja'a dama yana daga cikin manyan mayakan birnin Darul husuf masu ci mana tuwo ak w arya.
Ni

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login