Showing 21001 words to 23330 words out of 23330 words
Chapter 8 - Dakarun Musulunci Book 3 By Abdulaziz Sani M Gini.txt
cikin gawarwakin mutanen mu ya tafi da ita izuwa sansanin su.
Saboda haka nima sai na sati gawar nasu badakaren na taho da ita.
Wannan tunanin da kika ga na shiga ba ta komai bace face ta kasa gano abinda ukashat zaiyi da gawar da ya sata, wanda shine nima abinda ya kamata nayi.
Saadda uzaifat yazo nan a zancensa sai lafirat ta bushe da dariya, sannan tace hakika kai bakon fita yaki ne.
Inda ace ka saba fita yaki da dole ne ka gano abinda zaiyi da gawar.
Abinda zai yi da ita shine, tufafin gawar zai cire yasa a nasa jikin domin ya sami damar shigowa nan sansanin a cikin dare, ko domin leken asiri ko kuma domin ya saci wani abin.
Don haka sai mu san matakin da zamu dauka akansa.
Koda jin wannan batu sai uzaifat yayi murmushi wannna ya dubi Lafirat yace, kada kk damu yake Lafirat, ki tafi izuwa tantinki ki kwanta kiyi bacci har da munshari babu abinda zai faru.
Na san dan uwana ukashat kuma na san duk irin motsinsa zan kuka da shi.
Dajin haka sai Lafirat tayi murmushi tace, na yarda da kai gwarzona dari bisa dari.
Na san zaka iya yin abinda yafi haka. Sai da safe, Allah ya tashemu lafiya.
Koda gama fadin haka sai Lafirat ta juya tafi ce daga cikin tantin ta tafi nata tantin ta kwanta.
Fitarta ke da wuya sai uzaifat ya mike tsaye ya cire tufafin dake jikin wannan gawa ya adanansu a cikin akwatinsa na karfe. Wanda ya zubo wasu makamansa na yaki, sannan ya kwalawa wasu dakaru biyu kira dake tsaye a kofar tantinsa suka shigo da sauri.
Uzaifat ya dubi dakarun yace, maza ku dauki wannan gawar ku fita da ita waje ku binneta.
Cikin biyayya dakarun suka dauki gawar suka fice da ita, a zuciyar su suna mamakin yadda akayi gawar ta shigo cikin tantin yarima uzaifat.
Uzaifat bai kwanta bacci ba sai da dare ya fara rabawa bayan ya gabatar da nafilfilinsa da adduoi sannan ya kashe fitilar tantin nasa ya kwanta yayi lamo kamar yana bacci.
* * * * * *
A can sansanin su ukashat kuwa lokacin da dare ya raba sai ukashat ya mike tsaye ya dauki tufafin gawar da yasato ya sanya a jikinsa sannan ya daukko wata sharbebiyar wuka ya baiyeta a cikin rigarsa ya fita daga cikin tantinsa.
Da fitarsa ya banga can inda sansanin muslmai yake yaga gaba daya nahiyar wajen a haskake yake sakamakon fitilun itatuwa da aka kukkuna masu yawa.
Sai ya tabbatar da cewa babu yadda za'ayi yaje wannan wuri batare da an ganshi ba.
Haka kuma ya tuna cewa sarki shaaran ya gaya masa cewa sihirin tsafi ba zai yi tasiri ba ballatana ya bace bat ya baiyana a can kawai.
Nan fa hankalinsa ya dugunzuma yayi shiru yana tunani.
**DAKARUN MUSULUNCI**
Littafi na Uku 3
Part H ( Last )
Marubuci :- Abdul Aziz Sani Madakin Gini
Typing- Umar Farouq Zango
Posting Najibullah Muhammad legends 🥷🥷
Marubucin ya ci gaba da cewa...
Daga can sai ya dubi kasa ya ga ai kariyar ciyawace a wajen tun daga bakin sansanin su hat izuwa can sansanin musulmi.
Kuma ciyawar tana da dan tsawo har ta haifar da yar karamar duhuwa.
Nan take dabara ta fado masa yaje ya tsinko koriyar ciyawar da yawa ya manne ta a jikinsa gaba daya da ita sannan ya kwanta a kas yai ruf da jiki ya dinga tafiya da ina ciki a kas a hankali har ya durfafi sansanin musulmi.
Haka yaci gaba da jan ciki, da zarar ya ga wani motsi a gabansa ko giftawar wani sai yayi luf a cikin ciyawa, sai kaga ya saje da ciyawar ko alamarsa ba a gani.
Sannu a hankali har ya isa har cikin sansanin musulmi ba tare da wani ya ganshiba. Babu abinda zai baiwa mutum mamaki face yadda ukashat ke ratsawa ta tsakiyar kafafun dakarun musulunci yana wucesu amma basu ganshi ba kuma basu ki motsinsa ba.
Akwai lokacin da ma wani badakare ya taka masa yatsun hannunsa na hagu yaji mugun zafi da zogi saboda takalimin karfe ne mai nauyi a kafar badakaren.
Har ukashat yaji kamar ya tsandara ihu amma sai yayi ta maza ya daure ya dauke numfashinsa har sai da badakaren ya dauke kafarsa daga kan hannun nasa ya kara gaba, sannan shima yaci GBA da jan ciki ya durfafi tantin farko dake gabansa.
Da zuwansa bayan tantin yana daga kwancen a cikin ciyawar sai ya zaro wannan sharbebiyar wuka tasa ya tsaga tantin ya leka ciki.
Ai kuwa sai yaga ashe sarki uwaisul karni ne.
A lokacin sarki uwaisul karni na zaune bisa buzu ya idar da nafila yana lazimi.
Kawai sai ukashat ya bar wajen ya matsa gaba izuwa tanti na biyu, shima yasa wukarsa ya tsagashi ya leka.
Duk da cewar fitilar cikin tantin a kashe take ukashat ya gane cewa uzaifat ne a ciki a kwance domin ya karewa siffar jikinsa kallo ya shaidashi.
Ukashat ya kara wucewa gaba izuwa tanti na uku wanda Lafirat ke ciki.
Ukashat na barin wannan tantin na biyu sai uzaifat ya mike zumbur ashe yana ganin saadda ukashat ya tsaga tantin nasa da wuka ya leko ya kare masa kallo.
Shi ukashat bai san cewa kallon kallo akayi ba.
Cikin sanda uzait ya dauki wannan tufafi na gawar daya dauko yasa a jikinsa sannan shima ya cisgi ciyayi ya lullube jikinsa gaba daya da su kamar yadda ukashat yayi ya kwanta a kas yai ruf da ciki ya bi ukashat a baya ba tare da ya sani ba.
Lokacin da ukashat ya isa tanti na uku yasa wukarsa ya tsaya tantin sai yai arba da Lafirat kwance tana ta sharar barci abinta har da munshari.
Cikin sanda ukashat ya mike tsaye ya shiga cikin tantin ta cikin wannan kafar tsaga da yayi yaje kan Lafirat ya tsaya. Kawai sai yasa hannunsa a cikin aljihu ya dauko banji ya shaka mata a hanci.
Nan take barcinta ya kara nauyi. Duk da wannan abu dake faruwa uzaifat na labe a kasa bayan tantin yana lekensa.
Ukashat ya juyo da baya ya nufi inda ya shigo cikin tantin. Sai uzaifat yai sauri ya matsa gaba ya kwanta a cikin ciyawa yai lamfo.
Kawai sai ya ga ukashat ya fito ya cisgi ciyayi da yawa sannan ya koma cikin tantin ya lullube Lafirat da ciyawar sannan ya janyo ta a kas shima ya kwanta a kas ya ci gaba sa jan ciki kuma yana jan hannun Lafirat da hannu daya.
Koda ganin haka sai uzaifat ya bishi a baya a hankali ba tare da ukashat ya ankara ba.
Sannu a hankali suka isa har can sansanin.
Da zuwa sai ukashat ya mike tsaye ya saba Lafirat a kafadarsa ya shiga da ita cikin tantinsa ya kwantar da ita bisa shimfida.
Nan take ya cika da tsananin Farin ciki bisa wannan gagarumar nasara da ya yi ta sato gimbiya Lafirat.
Kawai sai ya juya da sauri da nufin ya tafi izuwa tantin sarki shaaran domin ya sanar dashi cewa ya cika umarninsa cikin nasara.
Juyowar da zaiyi haka sai yaji biri ya debeshi ya kama tangadi, bai Sam saadda ya sulale kasa ba ya kama barcin dole.
Ba komai ne ya haddasa hakanba face banji da uzaifat ya watsa masa a fuska ya shaka.
Koda uzaifat ya ga ukashat ya baje a kasa yana barci sai yai sauri ya janyeshi izuwa wajen tantin yayi ruf da ciki ya ci gaba da jansa a kas har ya isa can tantin musulmai janye da shi.
Ita kuwa Lafirat sai ya barta a can tantin ukashat dake sansanin kafirai.
Lokacin da gari ya waye sai mayaka suka fito sansanin yaki na kowanne bangare suka yi sahu sahu ana kallon juna. Wannan karon dai mutum dubu ne zasu kara da mutum dubu.
* * * * * *
A can bangaren sarki uwaisul karni babu uzaifat kuma babu Lafisai Habibullah, Hirama da uwar mayu da sauran dakaru, kuma ko kadan sarki uwaisul karni bai damu ba domin tun a daren jiya uzaifat ya dankara masa ukashat a hannunsa.
Nan take sarki uwaisul karni yasa aka daure ukashat da murtukekiyar ankwa kafa da hannu a jikin katon turke na karfe.
A daren uzaifat ya yai bankwana da sarki uwaisul karni ya sanar da shi cewa shi kam Yanzu zai durfafi can birnin shumbul domin yaje ya kubutarda rayuwar lahira da sauran mutanen su da aka tsare a kurkuku.
Nan take sarki uwaisul karni yacika da tsananin Farin ciki yayi ta sawa uzaifat albarka. Kuma ya bukaci sa ya bashi dakaru wadanda zasi masa rakiya.
Amma sai uzaifat yace dashi baya bukatar rakiyar kowa face ta Lafirat, don haka shi da ita zasu tafi.
Nan dai suka yi sallama uzaifat ya tafi ba tare da ya sanar da sarki uwaisul karni gaskiya lamarin ba cewar yabaro Lafirat a can sansanin kafirai.
Abinda yasa yaki gaya masa gaskiyar kuwa shine baya son hankalinsa ya tashi kuma akwai hikimar sa tasa ya barta a can din.
* * * * * *
A can sansanin kafirai kuwa,lokacin da dare ya tsala da yawa sarki shaaran yaji shiru wato har a sannan baiji dawowar yarima ukashat ba sai hankalinsa ya dugunzuma ya muje zumbur daga zaune ya ruga izuwa tantin ukashat.
Da zuwa sai ya iske Lafirat a kwance akan shimfidar sa ta na shara barci, amma babu ukashat a wajen.
Nan take sarki shaaran ya cika da mutukar Farin ciki bisa ganin ya sami nasarar sato Lafirat.
Amma kuma sai yayi mamakin rashin ganin ukashat a lokaci.
Kawai sai ya ga wata yar karamar takarda akan akwatin ukashat. Cikin sauri ya dauki takarda ya warwareta ya ga ashe sako ne aka rubuta waiska.
Nan take ya fara karanta bayanin dake cikin takarda kamar haka :- Takarda daga hannun ukashat zuwa ga shugabana kuma sarki na sarki shaaran na birnin shumbul.
Dalilin rubuta naka wannan wasika shine, domin na sanar da kai cewa na samu nasarar sato Lafirat wacce ita kadai ce zata iya yiwa makiyanmu jagora izuwa cikin birninka.
Ni yanzu tini na tafi izuwa birnin Darul Husuf domin naje na tono wadannan layu guda hudu don haka zan jiraku a can sai ku taho da sauri domin mu aiwatar da abinda ke gaban mu.
Koda sarki shaaran ya gana karanta wannan wasila sai ya takarkare ya bushe da mahaukaciyar dariya.
Karfin dariyar ne yasa Lafirat ta farka da ga barcin da take mai nauyi sakamakon banjun da ta shaka.
Koda tayi arba da sarki shaaran a gabanta kyalkyala dariya sai ta firgita ainun ta bude baki da nufin ta kira sunan Allah, amma sai sarki shaaran ya gabza mata naushi a wuya ta sulale kasa sumammiya.
Nan take yayi nuni da hannunsa izuwa kanta ta sake cigaba da barci mai gaske, sannan kuma wata sarka ta tsafi ta kanannade jikinta gaba daya.
Cikin sauri sarki shaaran ya kira sunan wani aljani waishi muruzul kurbaz.
Kawai sai kasa ta stage aljanin ya Faso ta ciki ya baiyana a gaban shaaran yana mai sujjuda a gareshi.
Girman aljani muruzul Kurabz ya kai a cure giwaye goma a wajen guda sannan ya na da fuka fukai goma sha hudu manya manya a jikinsa.
Baiyanar aljani muruzul kurbaz ke da wuya sai ga sazirat ta shigo cikim tantin.
Koda taga yar uwarta Lafirat kwance a gefe daya, kuma a daure cikin sarka sai ta cika da tsananin Farin ciki ita da mahaifinta.
Sarki shaaran ya dubi aljani muruzul kurbaz yace maza ka daukemu ni da yata sazirat ka kaimu can kusa da kofar birnin Darul husuf domin mi cisu da yaki kuma mu sato muzaira.
Koda jin wannan umarni sai aljani muruzul kurbaz ya risina cikin biyaiyya yace, an gama ya shugabana.
Nan take ya rankwafa sarki shaaran da sazirat suka hau kansa suka zauna. Kawai sai ya bude fuka fukansa y luluka izuwa can kololuwar samaniya ya bace bat, a cikin gajimare.
Sarki shaaran da sazirat na kyalkyala dariyar Farin ciki.
Abinda basu sani ba shine, ukashat bai tafi can birnin Darul Husuf ba domin tono layun nan guda hudu.
Yanzu haka yana can a tsare a hannunsu sarki uwaisul karni.
Kuma wannan wasila bashi ya rubutata ba uzaifat ne domin kawai yaja hankalinsu su zata cewa ukashat na kan cikinsa.
A halin yanzu tini uzaifat ya tunkari birnin shumbul domin yaje ya kubutar da rayuwar jamaar su da a tsare a kurkuku da kuma rayuwar Luhaira yar likita abu sharhaz.
A dai-dai Nan littafi na uku ya kare, marubucin ya ce mu hadu a DAKARUN MUSULUNCI na hudu don Jin yadda zata kaya tsakanin Uzaifat a birnin Shumbul..