Showing 18001 words to 21000 words out of 23330 words

Chapter 7 - Dakarun Musulunci Book 3 By Abdulaziz Sani M Gini.txt

daga cikin dakarun kafirai.
Mutum ashirin sun raunana ainun yadda bazasu iya moruwa ba. Watakila ma anan gaba su rasa rayuwar su.
A bangaren dakarun musulunci kuwa, mutum talatin kacal aka kashe aka raunana saba'in, kuma ba Irin raunin da zai zama sanadin ajalinsu ba.
Dama anyi kaida cewa sa'a daya na cika za a tsaida yakin, walau anyi nasara ko baayi nasara ba.
Don haka lokaci na cika aka busa kahon tsaida yaki kowanne bangare ya rugo ya kwashe gawarwakinsa da raunatattunsa.
Lokacin da sarki shaaran yaga cewa wannan yakin an fisu rinjaye, gashi kuma na jiya ragas akayi, sai ya cika da tsananin bakin ciki mara misaltuwa, don haka sai ya sake kadaita da ukashat da sazirat cikin tantinsa yace dasu, ina mai yi muku tini da cewa gobe fa itace damarmu ta karshe bisa abinda muka shirya domin samun nasara akan wannan abokan gaba.
Kun sani cewa a gobe mutum dari biyar biyar zasu fafata wannan yaki, don haka lallai a cikin su ne daya daga cikinku zaiyi badda kama ya sato mana gawar abokan gana guda daya yazo da ita ba tare da kowa ya ganshi ba.
Kai ukashat lallai kaine zaka yi wannan aiki. Kuma kaine zaka sa tufafin gawar kaje can sansanin abokan gaba ka sato mana gimbiya Lafirat.
Koda jin wannan batu sai ukashat yayi murmushi yace, ya shugabana na ka kwantar da hankalinka tamkar tsumma a randa.
Na rantse da darajar burin zuciyata sai na sai na sami nasara bisa wannan aiki a gobe kuma sai na sato Lafirat na kawota nan gabanka.
Da jin wannan batu sai sarki shaaran ya cika da Farin ciki ya kama kyalkyla dariyar mugunta.
Daga can kuma sai dariya ta juye izuwa kuka har da hawaye.
Alamarin da ya matukar baiwa ukashat da sazirat mamaki kenan.
Cikin matukar damuwa sazirat ta dubi sarki shaaran tace ya kai Abbana ina dalilin wannan kuka naka ?
Sarki shaaran yayi ajiyar zuciya, sannan ya sa hannu ya share hawayen idanunsa yace, ya ke yata kiyi sani cewa ba komai ne ya sani zubar da wannan kuka ba face tunowa da masoyina salhaf.
Na rantse da darajar tsafi idan muka sami nasarar wannan yaki sai anyiwa sarki uwaisul karni da duk iyalansa kisan gilla irin wanda ba a taba yiwa wani bil adama ba a duniya.
Koda jin wannan batun sai ukashat yaji ransa ya baci saboda jin cewa za'ayi wa mahaifinsa kisan gilla duk da cewa ko kadan baya kaunar mahaifin nasa a cikin zuciyar sa, amma kuma sai ya danne damuwarsa a cikin ransa bai nuna na a fuskar sa.
Nan dai sazirat ta shiga rarrashin sarki shaaran tana bashi baki.
Shikuwa ukashat sai ya mike tsaye ya fita daga cikin tantin ya barsu su biyu.
A can sansanin mayakan sarki uwaisul karni, a cikin tantinsa hankalin uzaifat dana Lafirat a tashe yake domin tun daga lokacin da aka kashe Aba Huraira sai sarki uwaisul karni yashiga cikin wani irin hali na rashin ci da sha da kuma rashin baccin dare ida rana ya zamana cewa bashi da aikin yi sao jan carbi, tunani da zubar hawaye.
Da kyar da Sidin goshi uzaifat ke lallabashi yaci dabino guda biyu rak, kuma ya karbi ruwa sau daya a tsawon rana guda.
Alamarin da ya jefa kowa cikin damuwa kenan saboda sanin cewa rashin yin baccin sarki uwaisul karni ba karamar ila bace akan samun nasarar yakin.
Dama idan har sarki uwaisul karni zaiyi bacci, to tabbas Allah zai nuna masa duk irin kaifin abokan gaba da zasu shirya a yakin da za'ayi kashe gari.
Yanzu gashi kowa yasan cewa abu ne mawuyaci sarki uwaisul karni yayi bacci a daren yau saboda alhinin masoyinsa Aba Huraira kuma gashi yakin da za'ayi gobe mai zafine tunda mutum dari biyar biyar ne.
Bisa wannan daliline uwaisul da lafirat suka tafi izuwa tantin da uwar mayu da hirama suke suka zauna tare da domin suyi shawara bisa irin matakin da ya kamata su dauka a yakin da za'ayi gobe.
Kafin kowa ya fara magana sai Hirama tai gyaran murya tace, ina da uzuri guda daya.
Cikin mamaki uzaifat ya dubeta yace, fadi uzurinki muji yake Hirama.
Hirama tayi ajiyar zuciya tace, ina mai rokon alfarma guda biyu rak a wajenku.
Alfarmar ta farko itace, ina so ku shigar dani cikin wannan addini naku yanzu take.
Alfarma ta biyu ina so koda bayan wannan yaki ne mu koma can dajin Huzurul Has mu yaki iyayena mu kawar da su domin indai suna nan a raye ba zasu daina cin naman mutane ba dana aljanu kuma ba zasu bari a rinka ratsa dajin ba.
Saãd uzaifat da lafirat sukaji wannan batu sai suka cika da tsananin Farin ciki. Uzaifat ya dubi Hirama yace, ke kuwa menene ya janyo hankalinki har kikaji kina son ki karbi addininmu?
Hirama tace, ai na ga abubuwan alajabi da yawa a cikin tafiyata da ku.
Duk balain da muka shiga sai na ga mun kubuta da zarar dayanku ya nemi taimakon ubangijin musulunci.
Hakance tasa na tabbatar da cewa lallai wannan addinin shine addinin gaskiya domin babu wani tsafi ko wata dabara da ta isa ta cecemu.
Koda jin haka sai uzaifat yayi kabbara, nan take uwar mayu ta biyawa Hirama Kalmar shahada ta maimaita sannan suka rungume juna.
Uwar mayu na cewa, tabbas yanzu kin zamo cikakkiyar yar uwar mu.
Da ni dake da uzaifat mun zama tamkar jini daya.
Cikin alamun matukar damuwa uwar mayu ta dubi Lafirat tace, yake wannan jaruma me yasa kema bazaki karbi addinin Allah ba yanzu take domin ki zamo cikakkiyar yar uwarmu tunda dai kin aminta dashi?
Kodajin haka sai lafirat tayi murmushi ta ce, kada ki damu yake kawata tabbas nima ina daf da samun wannan babbar rabo.
Yanzu dai sai muyi shawara bisa abinda ke gabanmu, wato dangane da yakin da za'ayi gobe na mutum dari biyar.
Koda jin haka sai uzaifat yayi murmushi yace, to yanzu sai ku fadi taku shawarar naji domin nima ina da tawa shawarar a zuciyata.
Uwar mayu tayi gyaran murya tace, ni dai a ganina babu abin da ya kamata muyi face muje mu sami mahaiimu sanar da shi cewa ya dakatar da wannan salon yakin da ake yi yanzu.
Gwara kawai ayi fito na fito gaba daya a karar da yakin kowa yasan makomarsa a huta da fargaba.
Koda jin haka sai uzaifat yayi murmushi yace, ai wannan shawarar taki ba abar karba bace, ina tabbatar miki da cewa shi kansa sarki bazai aminta da hakan ba, domin akwai dabarun da muka shirya a sirrance don ganin mun sami nasarar da muke nema.
Idan kuwa muka katse yakin da wuri bukatarmu bazata biya ba.
Ke kuma fa Hirama fadi taki hikimar muji, domin na gamsu da cewa ke mai hikima ce tunda har kika iya kubutar damu a lokacin da mahaifinki ya jefamu a cikin kejinsa da nufin ya cinyemu.
Saadda Hirama taji haka sai tayi murmushi tace, ai ba hikimata bace ta kubutar daku ba, kawai dai saace da kuma taimakon ubangijin musulunci.
Ni a ganina yakin da za'ayi gobe mai hadarin gaske ne, saboda kun ga yakin da akayi yau mune da nasara kuma abokan gaba sunyi matukar bakin ciki dole ne suyi babban tanadi na ramuwa.
Abinda za'ayi shine, ya kamata kai ko Lafirat daya daga cikinku yayi bad da kama gobe ya shiga cikin dakaru dari biyar din da za'a fafata dasu domin ya ragargaji kafirai saboda babu mamaki suma sunyi irin wannan tunani.
Kodajin wannan batu sai uzaifat da lafirat suka jinjina kai da suka gamsu da wannan shawara uzaifat yayi ajiyar zuciya yace, wallahi nima nayi irin wannan tunanin naki don haka tabbas nine zan bad da kamannina na shiga cikin dakarun dari biyar din amma abinda nake so da ku shine kuyi shiru da bakinku kada ku fadawa kowa wannan shawara da muka yanke domin idan sarki yaji ba Zak yarda na shiga ba saboda bai yarda da hainci ba koda a cikin yaki. Shi mutum ne laifi daya mai magana daya.
Cikin hadin baki Hirama, Lafirat da uwar mayu su kace tabbas ba zamu bari kowa yaji wannan zancen ba.
Lafirat ta dubi uzaifat tace, abu na karshe da nake so da kai shine, ka zuba ido da kyau kuma ka lura da dukkan abubuwan da kowanne abokin gaba keyi a lokacin da kuke yakin a gobe saboda a cikin wannan yamutsin na mutum dubu za'a iya shirya makirci wanda ba lallai bane wani ya gani ba.
Uzaifat yayi ajiyar numfashi yace, tabbas wannan batu naki gaskiya ne don haka da izinin Allah zan kuma sosai.
**DAKARUN MUSULUNCI**
Littafi Na Uku 3
Part G

Marubuci :- Abdul Aziz Sani Madakin Gini
Typing:- Umar Farouq Zango
Posting:- Najibullahi Muhammad 🥷🥷🥷

Marubucin Ya ci gaba da cewa

Kashe gari, wato rana ra uku dakurn musulunci da dakarun kafirci suka sake fitowa filin daga kamar yadda aka saba.
Nan take dakarun kafirai suka fito su dari biyar sanye da bakaken kaya kuma dukkanin su sun rufe fuskokin su da bakaken rawani idanunsu kadai ake gani.
Wani abin mamakin kuma kowannensu ya sanya katuwar bakar alkyabba a jikinsa sannan suna haye akan bakaken dawakai. Al'amarin da ya bawa dakarun musulunci mamakin kenan domin basu taba ganin an fita yaku da irin wannan shiga ba.
Lokacin da sarki uwaisul karni yaga dakarun kafirai su dari biyar sun fito filin daga, amma dakarun musulunci sun yi jinkiri basu fito ba sai ya fusata ya dakawa sarkin yakinsa na wannan runduna tsawa yace, ya Kai habinullahi ina dakarun da nace ka waresu ne tun jiya, me suka tsaya yi haryanzu basu fito ba.
Cikin rawar baki habinullahi ya budi baki da nufin ya ba da amsa kawai sai ya ga dakarun musulunci su dari biyar dukkanin su sanye da fararen tufafi da kjam fararen alkyabbu, kuma bisa fararen dawakai.
Dukkanin su sun rufe fuskokinsu da fararen rawuna.
Al'amarin da ya mutukar bawa habinullahi mamaki kenan domin shi akansa bai san da wannan tufafi ba da fararen dawakai.
Abinda yazamo kamar hadin baki, sai dai shigar da dakarun musulunci sukayi tafi ta dakarun kafirci ban shaawa da birgewa.
Koda sarki uwaisul karni ya ga dakarunsa a cikin wannan shiga sai ya cika da tsananin farin ciki ya rinka yiwa habinullahi kirari harma ya yi masa alkawarin bashi kyauta ta musamman saboda wannan hikima da basira da ya baje a filin yakin a wannan rana.
Nan dai dakarun musulunci suka iso tsakiyar filin daga suka ja linzamin dawakan su suka yi turjiya suna fusknatar abokan gaba.
Yarima ukasha ne akan gaba a cikin dakarun kafirci.
Haka ma yarima uzaifat ne akan gaba a cikin dakarun musulunci.
Duk da cewa kowannensu ya rufe fuskarsa da rawani suna yin arba da idanunsu suka shaida juna.
Nan take ukashat yaji zuciyar sa ta buga da karfi domin ya san cewa uzaifa zai iya hanashi aiwatar da babban shirin da yazo aiwatarwa yanzu.
Amma da ya tuna cewa ai cikin gwamutsi suke na mutum dubu, kuma da zarar an fara yakin kowa zai rasa nutsuwa. Sai hankalinsa ya kwanta ya gamsu cewa lallai sai ya sami nasarar abinda yazo aiwatarwa.
Bayan an yi kallon kallo tsakanin bangaren biyu sai aka busa kahon fara yaki. Nan take aka ruguntsume da masifaffen yaki, kura ta turnuke sararin samaniya.
Ihun mazaje da haniniyar dawakai da Karar karafa ta cika dodon kunne.
Nan fa aka fara turmutsi da yamutsi. Jim kadan kuma aka fara sarki ya hana dawa tsaiwa.
Wani lakacin sai dai kaga an safe kan mutum ya yi sama jini ya yi tsartuwa da feshi gangar jikin ta rikito kasa ana tattakata.
Abin da Ya firgita kowa shine, an kasa gano bangaren da ke samun nasara domin musulmai na zubewa suna shahada, kafirai na zubewa suna mutuwar banza.
Ana cikin wannan gumurzu ne uzaifa ya fara kokarin zuwa ya hadu da ukasha, amma da zarar ukasha ya ga uzaifa Ya tunkaroshi sai ya sulale ya bar wajen.
Haka ya yi masa zulliya ya ki yarda su yi gaba da gaba.
Kuma a hakan ci gaba suke da yaki kowannensu yana mummunar barna.
Yayin da aka sami kudan rabin Saa ana wannan bakin gumurzu sai rabin dakarun dake filin suka zamo gawa.
Koda ukasha ya fahimci hakan sai hankalinsa ya dugunzuma domin ya san cewa idan baiyi da gaske ba abin da yake son yi ba zai sami damar yi ba.
Kawai yana cikin yin yakin sai yayi wuf! Ya duro kasa akan wata gawa ta musulmi, ya lullube gawar da bakar alkyabbarsa.
Cikin tsananin zafin nama ya cure gawar tamkar an dunkule kayan wanki ya cafota da hannu daya ya dafa kasa da daya hannun nasa ya yi tsalle sama ya dira akan dokinsa ya na lullube da gawar Ya ci gaba da yakin a haka har ya tarwatsa dakarun musulunci dake gabansa da karfin tsiya, ya ratsa ta tsakiyar su ya sukwani dokinsa izuwa inda sansaninsu ya ke.
Ashe uzaifa ya ga saadda ukasha ya duro daga kan dokinsa amma bai ga abinda ya dauka ba a kasan amma tabbas zuciyar sa ta raya masa cewa lallai wani abu ya dauka. Cikin hanzari uzaifa ya tambayi kansa menene a filin yaki wanda ukasha zai dauka ?
Ai babu komai face gawa ko makamai.
Ya bawa kansa amsa.
Nan take ya aiyana a aransa kawai nima na sci gawar daya daga cikin gawarsu na tafi da ita tunda dai ban ga amfanin da makamin wani zaiyi ba.
Daga baya idan nayi nazarin gawar wakin da suka rage a filin yakin da dakarun da suka tsira da rayuwarsu zan iya ganowa idan ma gawar dayanmu ya sace.
Gama aiyana hakan ke da wuya sai shima uzaifa ya duro kasa daga kan dokinsa ya lullube gawar kafiri guda daya ya cureta kamar yadda ukasha yayi, ya daka tsalle sama ya dira akan dokinsa ya tarwatsa abokan gaba shima ya durfafi inda nasu sansanin yake.
Koda ganin haja sai sauran mayakan da ke faman yakin suka daina yakin kowa ya ruga da baya izuwa sansanin su. Al'amarin da ya mutukar baiwa sarki uwaisul karni mamakin kenan kuma ya fusatshi ya dubi habinullahi a fusakce yace, wannan wane irin shirine na banza da wofi?
Cikin biyayya habinullahi ya dukar da kansa kasa yace, ka gafarceni ya shugabana, hakika nayi kuskure.
Gama fadin hakan ke da wuya suka ji an busa kahon tsaida yaki.
Cikin fushi sarki uwaisul karni ya kada dokinsa ya nufi can sansanin su inda tantinsa yake.
A sannane kowanne bangare ya ruga ya debo gawarwakin jamaarasa.
Kafin a binne gawarwakin musulman da aka kashe sai da uzaifat yazo ya kirgasu sannan yaje ya kirga wadanda basu mutu ba, take ya gane cewa ba aga gawa daya ba.
Kawai sai yayi murmushi domin ya tabbatar da abinda yake zargi.
Bayan magriba tayi anci abinci. A can bangaren dakarun kafirci sai sarki shaaran ya rungume ukashat cikin tsananin Farin ciki sannan ya janye jikinsa daga cikin nasa yace, da kyau sadaukin sadaukai, aikinka yayi kyau, ka samo nasarar matakin farko.
Yanzu idan dare ya raba sai ka cire tufafin dake jikin wannan gawa da ka sato kasa a jikina ka sadada kaje har can sansanin mayakan su ba tare da an ganka ba ka binciko tantin da lafirat ke ciki ka satita ta kowanne hali ka kawota nan.
Koda jin wannan batu sai ukashat yayi murmushi yace, ya shugabana ai shan ruwa yafi wannan aiki sauki a wajena. Lallai zaka sameni nai cika umarninka.
Wannan shine abinda ya faru tsakanin yarima ukashat da sarki shaaran bayan an gama yaki.

* * * * * *

Alamarin yarima uzaifat kuwa, bayan ya Kai wannan gawar ta abokin gaba cikin tantinsa ya lullubeta da alkyabbarsa sai ya zauna ya kurawa gawar idanu ya shiga tunanin mai zurfi bisa abinda ya kamata yayi da gawar, amma babu wata dabara data fado masa.
Yana cikim wannan hali ne Lafirat ta shigo cikin tantin ta sareshi.
Koda taga yayi tagumi kuna ya kurawa kunshin kaya idanu yana tunani sai ta cika da mamaki.
Kawai sai ta wuce kai tsaye izuwa inda kunshin kayan suke ta yaye alkyabbar, nan take tayi arba da gawar badakaren mahaifita
Cikin kasuwa da mamaki ta dubi uzaifat tace, me zakayi da gawar abokan gaba?
Uzaifat yayi ajiyar zuciya yace, abinda dan uwana ukashat zaiyi da gawar bamu badakaren shi nake son yi da gawar tasu badakaren.
Lafirat ta sake dukansa cikin mamaki a karo na biyu tace, ni fa ban gane abinda kake nufi ba.
Uzaifat ya dubeta a nutse itace, lokacin da muke wannan yakin na fahimci cewa ukashat ya saci daya daga

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login