Showing 27001 words to 30000 words out of 66338 words

Chapter 10 - MAWAKIYA Book Complete Document original by Zee MD.txt

Zee MD   

12 Jul 2024

6943

15.


Hajiyar Dubai cikin fusata ta dubi Nabeela tace " wato kece kika kuma dawowa cikin Rayuwata ko ? inaso kisani a wancen lokacin ma ba k'yaleki nayi ba , kawai na barki xuwa wani lokacin dan insan irin matakin da zan d'auka akanki , ki kalleki ki kalli irin gidan da kike rayuwa a ciki taya zaki had'a kanki da 'Yata ? inaso kisani tun wuri ki fita daga harkar Junaid domin shid'in mijin 'Yatane halak malak , Umman Nabeela tace " Baiwar Allah meya had'aku da Nabeela dan Allah kuyi hak'uri bazata k'ara shiga lamarinku ba , Hajiyar Dubai tace " Malama munaso kijawa 'Yarki kunne tunkafin kirasata dan daga gani itace take nema muku na Abinci tare da yimiki jagora , Nabeela tuni taji ranta yakuma b'aci dan duk yadda take da mutum batason ana tab'a Umman ta , cike da jin zafin furucin Hajiyar Dubai tace " yakamata kisan irin maganar dazaki fad'awa Mutane , duk da nasan bakisan darajar iyayeba saboda bakitaso dasu ba , Hajiyar Dubai a fusace tayi kan Nabeela zata daka Junaid yayi saurin sha gabanta , tsayawa kowa yayi yana kallon Junaid d'in , Mumynsa ranta a b'ace tace " Junaid irin wannan yarinya mara tarbiya ita kake rayuwa da ita ? a kanta kake k'in jin maganata har kake wulak'anta Matar da zaka aura ? tabbas wannan rawar k'afar da kakeyi a kanta da alamar ba haka tabarka ba , Nabeela sai sannan ta dubi Mumyn Junaid taga tsantsar kama dasukeyi , kuma take tagane itace mahaifiyarsa , tuni jikinta yayi sanyi sosai dan bataso Mumyn sa tafara ganinta a wannan kalar ba , Umman Nabeela hak'uri tashiga bawa su Hajiyar Dubai tare da yi musu Alk'awarin insha Allah Nabeela zata daina kula Junaid , Umman tana lalub'e tace " ina kike Nabeela ? Nabeela tarik'e hannun Umman tata tace " ganinan Umma kanajin muryar Nabeela kasan dab take data saka kuka , kawai dauriya takeyi Umman tace " dan Allah Nabeela kidaina shiga sabgar madu kud'in nan banason irrasaki , ke kad'ai ce gatana a duniya wacce nake gani naji dad'i , Nabeela ta goge hawayen ta tace " meye laifin mu a duniya dan kawai nayi mu'amala da d'an masu kud'i ? dukan mu d'ayane a gun Allah Umma , Mumyn Junaid tayi caraf tace " kitsaya matsayinku na talakawa wad'an da basu dashi , inaso ki sakarmin kurwar d'ana yarabu dake banason halak'ar ku dashi ko kad'an , Junaid zaiyi magana Mumynsa ta d'aga masa hannu alamar karyayi magana , Nabeela tace " kiyi hak'uri Mumy insha Allah bazan k'ara kulashi ba , tana gama magana ta rik'e hannun Umman ta suka nufi cikin d'aki , Mumy tasaka Junaid a gaba suka fice daga cikin gidan , Hajiyar Dubai ita da Bahijja rai fes suka fito daga cikin gidan , amman a cikin ranta ta k'udurta sai taga Bayan Nabeela sannan hankalinta zai kwanta....


Nabeela tunda suka koma cikin d'aki take kuka tamkar ranta zai fita , Umman ta ita kanta sai da tayi kukan sosai , tabbas tasan suma kansu zasuji rashin dad'i na daina zuwan Junaid cikin gidan su , bare kuma Nabeela wacce zuciyar sa takamu da son Junaid d'in , sai da tayi kukanta me isar ta sannan tace " Umma shikenan yanzu anrabani da Junaid ? Umman tace "kiyi hak'uri Nabeela indai Junaid rabonki ne zai dawo gareki nan ba da jimawa ba , da k'yar Umma ta lallashi Nabeela tayi shuru , sai dai zuciyarta cike take da kewar Junaid dan tana mutuk'ar k'aunar sa ....
Wayarta ta d'auko tashiga b'angaren Record tafara yin wata wak'a tamkar wacce ake zuba mata ita a k'wak'walwa , tanayi tana kuka haka har bacci yayi gaba da ita....


Yau jirgin su Alhaji Ghali da Jidda Ya sauka a garin kano , sosai Jidda ta k'arayin kyau tamkar balarabiya , komai na jikinta ya canza , a gidan saukar bak'in da Alhaji Ghali yasa aka komar da su Innar Jidda a nan suka sauka , daman su Innar sunsan da zuwan su dan haka komai angyarashi a cikin gidan tsaf , sunyi musu girki kala kala na tararsu tare da lemuka masu dad'i , suna zuwa aka shiga gaisawa d tambayar bayan rabuwa , Alhaji Ghali bayan yayi wanka a b'angarensa ya shirya ya fice daga gidan , Nan Jidda take tambayar su Innar ya'akayi suka dawo gidan Alhaji dazama ? nan suka shiga bawa Jidda labarin abubuwa da suka faru , tab'e baki Jidda tayi sannan tace " aibata da hankali ne shiyasa , a can ma bakiji irin Magan ganun datake gayamin ba in suna waya shida ita , Inna ta dubi Jidda tace " nifah inajin tsoron kartayi miki wani abin Jidda , musamman yanzu taganki da ciki alhalin ita bata haihuba , Jidda tayi murmushi tace " ki kwantar da hankalinki Inna Alhaji bazai tab'a barinta tamin komai ba , musamman wannan cikin daya d'auki son duniya ya d'ora masa , Jidda ta mik'e tace " bari naje na kwanta na huta inna tashi nazo naje gidan su Nabeela naga yatake ..........


Hajiya Sara tunda taga Alhaji yadawo tasakashi a gaba da bala'i sai yakaita taga Jidda ,ta inda take shiga daban ta inda take fita daban , shiko ko ajikinsa kallo ma bata ishe shiba , suna zaune yana cike wasu takardu wayar sa tahau ring. Kafin ya d'auka tuni Hajiya Sara ta d'auka , duba screen d'in wayar tayi taga anrubuta My Hapiness , d'agawa tayi taji muryar Jidda tana fad'in " hello my dear kana inane inaso kazo ka kaini gidan su Nabeela tunda ka hanani driver saboda Bbynka dake cikina , tuni Hajiya Sara tasaki wayar ta fad'i k'asa ji kake tatsatsa....


Alhaji Ghali yana ganin hakan yafara fad'a yana fad'in " wannan wanne irin Abune haka saikace mara hankali , ji yadda kikamin da waya dan Allah , Hajiya Sara batasan ma abinda Alhajin ke cewa ba , kawai kalmar Jidda ce take mata yawo a kunne wacce tace " kahanani Driver da kaina saboda Babynka , cikin zuciyar ta ta furta " wato ciki gareki Jidda , duk wani shirina kina neman rushemin shi kenan , tabbas yau basai gobe ba zanzubar da wannan shegen cikin da kika samu , cike da fusata ta fito daga d'akin Alhaji Ghali ta nufi sama d'akinta dan shiryawa ....




Jidda kuwa dataji Alhaji Ghali baiyi magana ba ta d'auka ko yana wajen meeting d'in dayace mata zashi , dan haka ta shirya ta nufi gidan su Nabeela a sabuwar Motar ta.....




Nabeela na zaune tana sana'ar tata wato wak'a taji sallamar Jidda , da sauri ta d'ago kanta tana duban Jiddar kafin ta mik'e da sauri tanufi Jiddar ta rungumeta , itama Jiddar rungume Nabeelar tayi tana fad'in " Oyoyo k'awata nayi missing d'inki , sosai sukaji dad'in ganin juna sannan suka nufi cikin d'aki wajen Umma , gaishe da Umma Jidda tayi cike da so da k'auna Umman ta amsa , Umman tace " Jidda Innar ki ta yadda ni ko nemana batayi , Jidda tayi murmushi sannan tashiga bawa Umma labarin duk abinda yafaru dasu tun farkon zuwansu gidan Alhaji Ghali da yadda Hajiya Sara ta dunga yi musu barazana da yadda har ta auri Alhaji Ghalin har zuwan dasu Hajiya Sara sukayi gidan su saida tafad'a musu , sosai Umman Nabeela ta girgiza da jin yadda abubuwa sukaita faruwa amman ko kad'an Nabeela bata tab'a gaya mata ba , Umma tace " tabbas wannan Mata shed'a niyace sosai , Allah yatsareki daga sharrinta , ai Umma bata gama rufe baki ba sukaji anshigo cikin gidan ana d'ura ruwan zagi , Nabeela da Jidda tuni suka mik'e don ko bacci sukeyi sukaji muryar Hajiya Sara sunsani , tuni jikin Nabeela yafara rawa tana fad'in " Jidda zo kishiga nan ki buya kar tamiki lahani , tuni Umman Nabeela tagane wacce suke nufi wato itace tazo gidan tabbas akwai k'ura.......






Kuyi Maneji🀨 ina da fitaπŸƒπŸ»β€β™€οΈπŸƒπŸ»β€β™€οΈ


*'Yar* *Mutan* *Kanawa* _Ce_😍🌹*MAWAK'IYA*
🎀🎀🎧🎀🎀




_NA_
*Zee* *MD*




*Hamdala* *Writer's* *Association* πŸ’ͺ
https://www.facebook.com/111403834371046


✨✨ *{{* *H.W.A* *}}*✨✨


*Bisimillahir* *Rahamanir* *Rahim*




πŸ…ΏοΈ 16.


Jidda ta dubi Nabeela wacce take a firgice tace " ki kwantar da hankalinki 'Yar uwa , Babu abinda ta isa tayi min duk irin rashin kunyar ta , Nabeela ta dubi Jidda tace " kinsan da dayanzu ba d'aya bane Jidda , kinsan kina da ciki karta zo tamiki wata illar plss , Umma ta mik'e tana lalub'e hanya tace musu ina zuwa bari naje nasameta , Nabeela da sauri ta rik'e hannun Umman tata tace " Umma karkije gurin wannan matar dabatasan ciwon kanta ba , banaso tagaya magana ko kuma tayi miki rashin kunya wacce zanji rashin dad'i , Umma tayi murmushi tace " inaso kisani babu abinda zatayi min yazama sabon Abu a gurina , ko kin manta cewa d'azu wasu ma sukazo sukayi mana suka tafi , Nabeela duk wanda zai d'aukaka a duniya dole zai jure tarin k'alu bale a cikin Rayuwarsa , dan haka kibari nafita muyi magana dasu , haka Nabeela ta k'yale Umma tafita itakuma taci gaba da rik'e Jidda dakeson fita .....


Umma na fita Hajiya Sara ta k'araso gabanta tace " Ke makauniya nasan ba gani kikeyi ba bare ki sheda fuskata , nice wadda nazo gurin yarinyar ki kwanakin baya , to yanzu ma naxone akan maganar k'awar tata wacce nake da tabbacin tana cikin gidan nan yanzu haka , Umma tace " tabbas ba k'arya kikayi ba ni Makauniya ce kuma koda nake Makauniya Allah bai hanani gani ta ikonsa ba , Inaso kisani Hajiya Sara " duk wani jin kanki da tak'amar Allah yabaki rai da lafiya , yabaki ji da gani , yabaki k'afafuwa inaso kisani a yanzu in Allah yaso ikonsa zaki wayi gari baki da ko d'aya acikin Abinda na lissafo miki , Hajiya Sara tana d'aga hannu ta wanke Umman Nabeela da mari sannan ta cire glass d'in dake idonta tace " karki k'ara jifana da wannan mugun bakin naki , Nabeela wacce akan idonta Hajiya Sara ta mari Umman ta tuni ta fito daga cikin d'aki ranta a mutuk'ar b'ace , tana zuwa ta shak'i wuyan Hajiya Sara tahau ta da duka , tuni Jidda itama ta fito daga cikin d'akin tazo ta rik'e Umman Nabeela wacce take zubar da Hawaye saboda takaicin Abinda Hajiya Sara tayi mata , yaran da Hajiya Sara tazo dasu tuni suka bugawa Alhaji Ghali waya suka sanar dashi komai , dan tuni yagama siyesu da kud'i komai Hajiya Sara tayi sai sun gaya masa , yanzu ma da suka biyota bawai sunzo ne dan bin Umarnin taba sunzo ne dan kare Jidda daga abinda zatayi mata , dukan da Hajiya Sara takesha a gun Nabeela ba k'aramin shigar ta yakeyi ba , tuni tafara neman ceto gun yaran nata , dukansu banza sukayi da ita tamkar basuga ana dukanta ba , kafin kace kwabo Nabeela tayiwa Hajiya Sara dukan tsiya duk ta canza mata kamanni , shigowar Alhaji Ghali shine yasa Nabeela ta k'yale Hajiya Sara , sai dai worning tashiga yi mata tana fad'in " inaso kisani ko a yanzu kinga ne bambancin wacce tataso a gaban Mahaifiyarta da wacce ta taso a kwararo , inaso kisan cewa " munsan mutuncin Iyayen mu ba kamar yadda ke kika watsar danaki iyayen ba , daga yau nakuma ganin k'afarki a cikin gidan mu wallahi saikin fita babu k'afa ko hannu , Jidda ta matso kusa da Nabeela tace " kinyi dai dai k'awata kuma duk d'a nagari da yasan mutuncin iyayensa hakan zaiyi , ta dubi Hajiya Sara tayi murmushi sannan tace " How market ? badai saboda kinji ina da ciki ba kika taho dan kiyimin illah ? to kisani wannan cikin sai yafito duniya yashak'i k'amshin mahaifinsa , daman kinsan kece bakya haihuwa ba Alhaji ba dan haka sai dai ki mutu haihuwa ce tamkar nayita nagama , k'arasawa tayi jikin Alhaji Ghali tace " My luv kaga irin jahilcin matar taka ko ? inaso daga yau kayi mata iyaka da zuwa gidan su Nabeela dan inta zama gurguwa bazamuyi asarar biyan kud'in muba dan gyara mata k'afa , Alhaji Ghali ya rungume Jidda sannan yace " nagode Allah dabatayi miki komai ba sannan nagodewa Nabeela sosai da irin hukuncin datayi mata , ya dubi su Duna yace " nagode kuma sosai da had'in kan da kuke bani , ya dubi Hajiya Sara yace " Inaso daga nan ki tattara kibarmin gida nasakeki saki Biyu bana fatan sake ganinki , yana fad'in haka ya rik'e Jidda sukayiwa Umma da Nabeela sallama suka fice , suma su Duna ficewarsu sukayi daga cikin gidan , Hajiya Sara haka ta mik'e tana d'ingishi ta fito daga cikin gidan sai dai wayam babu motar ta a wajen , haka tadinga d'ingisawa tana tafiya harta fita titi ta hau Napep ta nufi gidan Hajiyar Dubai.....


Junaid tunda suka bar gidansu Nabeela da suka koma gida zazzab'i me zafi ya rufesa , juyin duniya Mumyn sa tayi akan yatashi suje asibiti amman yak'i , dole haka ta hak'ura ta zuba masa idanu , wayar Nabeela yakira yafi sau shurin masaki amman bata d'agawa daga k'arshe ma tasashi a black list....


Bayan kwana biyu : Nabeela ta cigaba da zuwa wajen aikinta , domin yanzu suna shirye shiryen fitar da sabon Album d'insj na Audio , kullum zuciyar ta cike take da kewar Junaid wani lokacin har kuka takeyi a b'oye batare da kowa yaganta ba , kullum tamkar k'ara mata son Junaid takeyi , wani lokacin kuma sai tatafi tunanin yanzu haka yana cen tare da Matar sa wacce zai aura , wani kishine yake rufeta duk lokacin data tuna kalmar tarabu dashi ankusa aurensa da Bahijja , yauma tana office d'insu tana aikin tunanin nata aka turo k'ofa , wani masinja ne yake sanar mata tana da bak'o a reception , da kamar tace bazata zoba sai kuma wata zuciyar tace " kije kigani ko Junaid ne watak'ila , ce masa tayi yace " gatanan zuwa .....


Bayan fitar sa da minty 5 ta mik'e ta nufi Reception d'in , tana zuwa taga wani had'add'en Guy a zaune ya juya bayansa , sallama tayi masa cikin muryarta me sanyi , amsawa yayi yana juyowa dukansa gaba d'aya , Nabeela d'auke idonta tayi daga kallonsa dan idanunsa irin sexy eyes d'in nan ne wanda in mutum yana kallonka tamkar mejin bacci , samun waje tayi ta zauna suna fuskantar juna , gyaran Murya yayi yace " sannu da aiki malama Nabeela , nasan aiki kikeyi na katse miki shi , Nabeela tayi murmushi tace " babu komai inajinka , dama wak'a nakeso kiyiwa Hajiyata ta k'arin shekaru wato birthday , inaso kiyi mata wak'ar da baki tab'a yiwa waniba , kifad'i nawa zanbaki ko kituromin account Number naki , Nabeela binsa tayi da kallo tabbas yana son Hajiyar nan tashi daga ganin yadda yake magana , Nabeela tace " kabani list d'in sunayen dakakeso asaka tare da sunan Hajiyar taka , sannan maganar kud'in dazaka biya kaje kasamu Oga saikuyi magana dashi , murmushi yayi sannan yace " ga sunan Hajiyar tawa da duk wanda yadace kisaka , mik'a mata takadda yayi sannan ya mik'e yasaka hannu cikin Aljihunsa ya zaro bandir d'in 'yan dubu d'ai d'ai na dubu d'ari biyi ya ajiye mata a gabanta , yace " wannan kyauta ce nabaki maganar biyan kud'in wak'ar kuma zansamu Ogan naki kamar yadda kika buk'ata , nabarki lafiya sai kinjini ......
Tunda ya fita Nabeela take binsa da kallo , kasa tashi tayi har saida Oganta ya turo taje zasuyi magana , mik'ewa tayi tare da d'aukar kud'in ta nufi wajen Oganta , tana zuwa tafad'a masa duk yadda sukayi da bak'on dayazo har kud'in dayabata saida ta nunawa Ogan nata , murmushi yayi yace " tabbas Nabeela zuwanki wannan Studio namu ko yaushe k'ara samun ci gaba akeyi , Alhmd ina godiya sosai da samun hazik'ar Jaruma , wannan da kika yazo sunansa Anwaar d'ane tilo ga Hajiya Maimuna me Gwala gwalai , duk fad'in Nageria da k'asashen waje bawanda baisan Hajiya me gwala gwalai ba , gashi ankawo miki aikin yi mata wak'ar Birthday wanda zata yi rana ita yau , inaso ki nutsu sosai kiyi mata wak'ar dazata ji dad'inta hakan zaisa ki k'ara samun d'aukaka a duniya , domin wannan damar da kika samu dubban mawak'a sundad'e suna jiranta basu samu ba , Nabeela tadad'e tanajin sunan Hajiya me gwala gwalai amman bata tab'a ganinta ba , tabbas zata nutsu sosai tayi mata wak'a me dad'i dan tasamu tak'arawa Studio su girma da matsayi , Oga yace " ki rik'e wannan kud'in tunda shine yabaki sannan yakamata kubud'e Account dan kina saka kud'i aciki , muma saida ya turo mana million 2 yanzun haka zanyi miki transper dubu d'ari biyar , Nabeela ko a mafarki bata tab'a rik'e dubu d'ari bama bare har dubu d'ari

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login