Showing 15001 words to 18000 words out of 66338 words
Chapter 6 - MAWAKIYA Book Complete Document original by Zee MD.txt
gida tashiga gurin Umman ta tana fad'in " nabarki da yunwa ko Ummana ? wallahi wani bak'o nayi me d'an karan surutu , Umman tace " kema ai kina da naki sai kuhad'u kuyi tayi , da Raihan nanan ni data dad'e da siyomin garin kwaki nasha , Nabeela tace " yi hak'uri bari nazo nadafa mana abu me sauk'i kinji Ummana , wuta tafara had'awa tana zaune gaban murhun , tafi wajen minty ashirin tana hura wuta amman tak'i kamawa , icen ne d'anye dayake garin damuna ne , Sallama takuma ji anyi a soron , wannan karan tanaji tasan Junaid tunda tagane muryarsa , cikin zuciyar ta tace " yanzu kuma meye yadawo dakai ? jitayi yakuma yin Sallamar akaro na biyu , Umman ta wacce take zaune a tsakar gidan tace " wai Nabeela ina kinajin ana sallama ko bakida kunne ne ? hayak'i yacika mata idanu sai hawaye take tace " inaji Ummana wallahi wannan bak'on ne dana cemeki yazo d'azu , bata gama rufe baki ba kawai taga Junaid yashigo tsakar gidan......
Mik'ewa tayi dan tayi saurin neman Hijab tasaka , shikuwa tunda yashigo ya kafeta da ido yana tasbihi da sarkin dayayi wannan sura kyakkyawa haka , tabbas yasha ganin mata kala kala amman bai tab'a ganin me irin surar Nabeela ba , K'arasawa kusa da Umma yayi yana mata sallama , Umma ta amsa tana gyara kallabin kanta , gaisheta yashiga yi cike da girma mawa , amsawa tayi itama tana masa sannu da zuwa , Nabeela rik'e da dadduma a hannu ta k'araso ta shimfid'a masa , ledar dake hannunsa ya ajiye sannan ya zauna shima , Duban Nabeela yayi yace "kitashi ki d'auko kwano kizubawa Mamana Abinci tunda yau kinbarta da yunwa duk da nine naja hakan , Nabeela mamaki ne fal acikin ranta cikin zuciyar ta take fad'in " wanne wanne irin mutum ne daga had'uwar hanya yana neman shigar mata rayuwa , kallon ta yayi yaga tayi tsaye tamkar bataji meyace ba , sake mai maita mata yayi tayi firgigit ta nufi cikin d'akin nasu , koda ta dawo d'auke da kwano ya ansa ya bud'e ledar , tuwon shinkafa ne da miyar agushi dataji Naman kaji , juyewa yayi saikuma lemuka da ruwan roba , cemata yayi tasamo filet ya zubawa Umman taci , mik'ewa Nabeela tayi taje ta d'auko , ita abin har mamaki yake bata sai bata umarni yake ita kuma tana bi , zubawa Umma tuwo yayi yace da miya ya ajiye mata agabanta yana fad'in "Umma bisimillah ga abincin nan , nasan kafin tagama girki zakiji yunwa dayawa , Umman tace " Dan Allah yaro a inah kake daga zuwa zaka fara hidima damu haka ?Junaid yayi murmushi yace " Umma karki damu ki d'auka tamkar nima d'an dakika haifana , kuma kusa a ranku had'uwata daku alkairi ne Allah ya rubuto , a yanzu jina nake tamkar d'an gidan nan danhaka komai kukeso nad'au alk'awarin yimuku shi , Umma godiya tashiga yi masa tare da saka albarka , tashi yayi yaje ya wanko hannunsa yasaka a kwanon Umma suka fara cin tuwon tare , hira suke sosai tamkar sundad'e dasanin Juna , tun Nabeela nak'in sakin jiki harta fara sakin jiki suna hirar da ita , sai dai tuwon ne tak'i ci kwata kwata ......
Alhaji Ghali tuni yasaiwa su Jidda wani gida madaidaici me kyau dashi , yanzu haka shirye shiryen komawa sukeyi , Jidda ta riga da ta mallake Alhaji Ghali da kissoshinta yanzu sai yadda tayi dashi , shikuwa yasakar mata bakin Aljihu tamkar baisan ciwon nemaba , Hajiya Sara tuni tafara damuwa sosai , dan yanzu duk wacce zata had'a da Alhaji Ghali yadaina sauraren kowacce mace inba Jidda ba , Ita kanta Hajiya Sara ko kallo bata ishe shiba yanzu , kullum cikin kwanan hotel yake shida Jidda dan gidan sa ma yayi masa k'aura , tuni Hajiya Sara tasaka yan dabanta akan lallai su kamo mata Jidda sukawo mata ita gidan gonar Alhajin.....
Innar Jidda kuwa yanzu sunshigo gari suma , yanzu basa damuwa da abinda Jiddar takeyi tunda ta d'auke komai na cikin gidan su , dan yanzu girki ma a gas sukeyinsa saboda samhn hutu , kayan Abinci kuwa babu irin wanda basu dashi a cikin gidan su , ga uwa uba suttura yanzu data wadace su sosai , Yaya Sa'ade angoge sosai sai fizgar kai itama takeyi Tazama 'Yar gayu , kusan kullum mijinta yana hanya yana magiyar tadawo amman tace masa Allah yakiyaye ita yanzu tafi k'arfin gidansa...
Junaid sosai yazama d'an gida agidansu Nabeela , dai dai dasu Inna Zulai da Raihan sunsaba sosai da Junaid , kusan kullum yana cikin gidan suna hira , a haka yagama fahimtar halin da su Nabeela suke ciki na rashi da k'arancin Abinci , Kuma anan ya fahimci k'udirin Nabeela nasan zama Mawak'iya , sosai take burgesa yadda take tafiyar da rayuwarta , gata da Dirin jikin da kowanne namiji zaisota amman hakan baisa ta shiga tallar kanta a duniya ba , tazauna a yadda Allah yayita wataran su samu wataran sukwana haka , Junaid tuni ya k'udurci niyar taimakawa Nabeela tazama mawak'iya ....
Kuyi manejiππ
*Comment* *Kawai*βπ»
*'Yar* *Mutan* *Kanawa* _Ce_ππΉ*MAWAK'IYA*
π€π€π§π€π€
_NA_
*Zee* *MD*
*Hamdala* *Writer's* *Association* πͺ
https://www.facebook.com/111403834371046
β¨β¨ *{{* *H.W.A* *}}*β¨β¨
*Bisimillahir* *Rahamanir* *Rahim*
π
ΏοΈ 9.
Jidda tare da Alhaji Ghali suna cin chips. Ta dubeshi cikin kissa tace "Honey yakamata ace yanzu munmallaki juna fa , Alhaji Ghali yace "Sonake indawo daga China sai muyi maganar auren , Jidda tayi k'asa da murya tace " Mezai hana kafin katafi kawai a d'aura mana auren kaga kawai sai mutafi tare ko yakagani ? Alhaji Ghali yayi shuru yana nazarin maganar Jiddar , tabbas bazai iya wata biyu a wata k'asar batare da mace ba , shikuma baya iya neman matan k'asar China , d'agowa yayi ya dubi Jidda tabbas iya mace takai mace , ga ni'ima da yake gamsuwa da ita , Yasan ko ta inah Jidda ta kerewa Hajiya Sara , dan haka kawai zai amince da buk'atar ta kawai suyi auren yatafi da ita , dubanta yayi yace "inaso kisanar dani inda dangin Mahaifinki yake inaso naje can neman auren naki , Jidda jitayi tamkar tatashi tafara uban tsallen murna da dad'i , cike da jin dad'i ta sumbaci Alhaji Ghali tace " karka damu indai wanna nan ko yanzu inka shirya ganinsu zamu iya zuwa....
Nabeela wata shak'uwa ce tashiga tsakaninta da Junaid , koda yaushe suna tare da ita , yanzu haka Junaid yazo d'aukar Nabeela zasuje studio Buga wak'a , tunda Garin Allah ya waye Nabeela take ta faman fara'a tamkar anyi mata albishir da gidan Aljannah , da wuri tagama komai tayi wanka ta zauna zaman jiran Junaid , tana zaune tana rera wak'ar datakeson bugowa me suna *Kamin* *Halacci* sai rera wak'ar take su Umma da Inna Zulai sunajinta , a haka Junaid yayi sallama yasa meta ..
Yana shigowa ya gaidasu Umma sannan Nabeela ta gaidashi itama , dubanta yayi yana dariya yace "Nasan jiya bakiyi wani baccin kirki ba saboda zumud'i , Ummanta tace "ai yau tun safe ta tashi tacika mana kunne da wannan wak'ar tata , dariya sukayi su duka sannan Junaid yace " zuwa nayi daman ince miki wanda zaisa miki kid'an yayi tafiya kiyi hak'uri sai wani lokacin , Nabeela tuni fuskar ta ta canza tayi shuru batare da tacewa Junaid komai ba , dariya yasaka yace "tashi mutafi kinji k'awata wasa nakeyi miki yana can yana jiranmu....
Hararar wasa Nabeela tayi masa sannan ta mik'e tashiga d'aki ta d'akko Hijab d'inta , tana fitowa Junaid ya zuba mata ido tamkar ya cinyeta , k'asa Nabeela tayi da kanta tak'araso tacewa Ummanta "zamu tafi Ummana inaso kimin addu'ar Allah yasa daga wannan yazama na d'aukaka a duniya Allah yasa nayita a sa'a , Umman ta dafa kan Nabeela tace " a koda yaushe baki da burin da ya wuce ki faranta min , kinsha wuya sosai Akaina Nabeela ta , inaso Allah yasa miki Albarka a duk Abinda kika saka gaba , inayi miki fatan Alkairi Allah yashige miki gaba , gaba d'aya suka Amsa da Ameen , Nan Inna Zulai itama ta musu fatan Alkairi tare da yiwa Junaid Addu'a shima suka fice....
Tunda suka shiga motar Junaid Nabeela bata ce komai ba suna tafe tamkar kurame , can Junaid yace "wai yau duk naji bakinki yayi shuru saikace meyin azumin kurame ? Murmushi tayi sannan tace "bazaka fahimci irin dad'in danakeji ba Ya Junaid sunan datake kiransa kenan , taci gaba da magana "inaso yadda kake faranta mana Kai ma Allah ya faranta maka , tabbas bani da abinda zan saka maka dashi face addu'a domin kaid'in nadaban ne Ya Junaid , Murmushi yayi sannan yace " Nabeela inaso kisani tun ranar had'uwa ta dake naji Allah yahad'a jininmu , inajinki tamkar wata 'Yar uwata ta jini , ina ganin Ummanki sai naga tamkar Ummata nima Allah yaruga daya saka min sanku araina , kuma duk abinda zan muku bana buk'atar godiya , nayi ne kawai dan Allah dakuma taimako , suna tafe suna hirar su cike da nutsuwa har suka iso Studio , k'ato ne Studio d'in me kyau dashi , samun waje d'aya yayi ya faka motar sa sannan suka fito , tunda suka fito idanuwan mutane yake kansu , da suka jero kuwa ba k'aramin burge mutane sukayi ba , da sukazo shiga ciki wani matashin Saurayi yace "gaskiya wannan had'in yayi Allah yakai mu lokacin zamu sha wak'ok'i , Junaid ya kallesa yana dariya yace "to 'Yan saka ido wannan d'in sister d'inace , itama tazo tazama Mawak'iya tamkar ku , Matashin Yace " wow gaskiya nasan muryarta zatayi zak'i ina kamun muryar zanyi wani sabon Album sai agayamin price , dariya Nabeela tayi batace komai ba suka wuce Ciki.....
Alhaji Ghali ya tura neman Aurar Jidda anbashi , ansaka musu ranar aure sati biyu dan ma akwai wani Abu da zai jira Amman da sati d'aya za'asaka , duk wannan Abin da'akeyi Hajiya Sara bata saniba , dan ita hankalinta yana kan bikin wata k'awarsu da zata auri Governor Lagos , kullum suna hanyar fita siye siye ta manta da sha'anin Jidda ,
Jidda suntare a sabon gidan su bawanda suka gayyata bare asan gidan , kuma Jidda ce ta hana a gayyaci kowa saboda tana tsoron irin hukuncin da Hajiya Sara zatayi mata duk sanda tasan ta auri mijinta , yanzu ma motar Alhaji Ghalin yabata take hawa , Shopping Jidda taje tayi na kayan Abinci nik'i nik'i ta nufo gidan su Nabeela dashi , tana zuwa ta tsayar da motar ta a k'ofar gidan ta fita tasamo yara suka fara d'ibar kaya suna shiga dashi cikin gidan , saida suka gama sannan tabawa wani Babba daga cikinsu ambulan da sak'o aciki tace " inyashiga cikin gidan yace inah Nabeela sai yabata wannan , Bayan yashiga ya kai komai sannan ya fiti suma ta sallamesu taja motar tatafi abinta....
Umman su Nabeela tana zaune sai mamaki take waye ya aiko musu da wannan kaya , dan Inna Zulai tace mata kayan Abinci ne masu yawan gaske da kuma kayan girki , kuma yaran da suka kawo sunce Mace ce tabasu tace akawo wa Nabeela , zaman jiran Nabeela tashiga yi tana tunani wace ce wannan d'in...
Nabeela ba'asha wuya da itaba aka nuna mata komai sannan tafara , kowa dake gurin saida ya yaba da wak'ar tata , ga murya tamkar ana busa sarewa , take me Studio d'in yacewa Junaid "Aboki in zaka amince dan Allah inaso ind'auketa aiki , dan wannan muryar tata zamu samu tarin alheri da ita , Junaid yayi Murmushi yace "zamuyi shawara da ita in munkoma gida , to Allah yasa ku amince dan ina da aikin da zamuyi sosai da ita , haka suka cigaba da hira har suka fitar mata da fefen sidin Wak'ar tata , Junaid ya ansa sannan yasa suka tura masa a memory d'insa na waya , Nabeela sai Murmushi takeyi tanajin wani dad'i har cikin ranta , wai yau itace ta buga wak'a burin ta yau yafara cika , d'aga hannu tayi sama tace "Allah nagode ma da ganin wannan rana me albarka , a haka sukayi sallama akan Junaid gobe zaizo dan gaya mishi yadda sukayi ....
Tunda suka taho hanya Nabeela take tajin wak'ar a cikin motar har duka k'araso gida , suna zuwa da sauri ta bud'e motar ta fita tashiga cikin gidan tana k'walawa Umman ta kira , dukansu suna zaune suna hira ita da Inna Zulai har Raihan data dawo daga sch itama , Umman tace " wannan kira Nabeela na lafiya ne kuwa ? fad'awa jikin Umman tayi tana fad'in "Umma kinji Muryata kuwa ? wallahi Umma bakiji yadda murya ta tayi ba tamkar batawa ba , Murmushi Umman tayi itama tana fad'in Alhamdulillah Nabeela ta Buri yafara cika , Allah ya nuna mana ranar da zamuji ana hira dake a gidan Radio. Inna Zulai tace "Ameen ya Allah , sallamar Junaid itace ta katsesu yashigo , yana k'arasowa tun bai zauna ba Umma tafara yi masa godiya tana saka masa Albarka , sosai yaji dad'i aransa yakumajin k'aunar su sosai har cikin jikinsa , samun guri yayi ya zauna yana fad'in "Umma kubud'e kunnenku kuji wak'ar tata kowa yaji saiyace batayi dad'iba , Ya kalli Nabeela yayi mata gwalo ita kuma ta hararesa a wasa , dariya Umma tayi tace "Haba ai nasan koba asaka kid'a ba muryar Nabeela ta akwai zak'i , Junaid yayi dariya yana fad'in "Umma harda su zugata kenan , kunna musu wak'ar yayi a waya yace " to ga wak'ar Nabeela , Me taken *Kaimin* *Hallaci* Sosai su Umma suka shiga yaba wak'ar tare da jinjinawa Nabeela akan k'ok'arin datayi .....
Nabeela sai murmushi take baki yak'i rufuwa , Junaid shikuwa idonsa yan kanta duk motsin dazatayi , a haka har suka gama jin wak'ar tata , Junaid ya mik'owa Nabeela wani kwalin waya yace "yakamata kifara rik'e waya a hannunki , tunda kinkusa fara zama celebriti dole sai da waya a hannu , Murmushi tayi tate dajin wani sanyi aranta ta mik'a hannu ta karb'a , kallonsa tayi hawaye suncika mata idanu yayi mata alamar tayi shuru kartayi kuka , goge hawayen tayi sannan tahad'e hannuwanta biyu tana masa godiya , Junaid yadubi Umma yace " Umma a can Studio sun nemi da Nabeela tadunga zuwa sund'auketa aiki , to nidai ban basu amsa ba sainaji ta bakinku keda ita , Umma tace " indai kana ganin bawata matsala to nima daga guna babu Allah yasa Albarka , Junaid yace "babu matsala Umma indai har Nabeela ta rik'e mutuncin kanta , Nan suka shiga tattaunawa har Inna Zulai sannan Junaid yayi musu sallama akan zaisamu Me Studion Nabeela tafara zuwa aikin......
Koda Nabeela tashiga d'akinsu sai ganin kayan Abinci tayi kala kala jibgi guda , tsayawa tayi tayi sororo tana tambayar kanta " wannan kuma kayan daga ina ? fitowa tayi tasamu Ummanta tace " Ummana wad'ancen kayan Abincin dana gani waye yakawosu ? Umma tace "Yadda kika gansu Nabeela nima haka nagansu , sai dai wad'anda suka kawo sunce wata matace a motar takawo kayan , sannan ga wata takadda tace a baki ita , Umma tasa hannu k'asan tabarma ta d'aukowa Nabeela takarda tabata , Nabeela ta ansa ta bud'e ta , kud'ine suka zubo yan dubu dubu , kwashesu tayi ta shiga k'irgawa dubu talatin cif tagani , sai wata takarda da akayi rubutu kamar haka :
( _Inafatan_ _kina_ _cikin_ _k'oshin_ _lafiya_ _ga_ _kayan_ _Abinci_ _Nan_ _da_ _kud'in_ _cefane_ _inaso_ _kicigaba_ _da_ _kulawa_ _Da_ _Ummana_ _Ina_ _Miki_ _Fatan_ _Alkairi_ _kigaidamin_ _da_ _Ummana_ )
_Sak'o_ _daga_ *J*....
Nabeela nagama karantawa ta b'ata fuska , wato Jidda da kud'in Haram taje ta siyo musu kayan Abinci , sai yanzu tagane wato ranar da aka dawo da ita gida daga gidan Alhaji Ghali wato Jidda ce , wato da Jidda za'a had'a baki abata lemo tasha ta bugu suyi amfani da ita , tabbas yau saitaje gidansu Jidda tayi mata rashin mutuncu , kuma wannan kayan Abincin yadda takawosu haka zata zo ta d'auki abinta , dama wannan kud'in data ajiye mata lokacin suma suna nan bata tab'a ba , Umma taji Nabeela tayi shuru tace " Nabeela takarda tameye ita kuma ? sannan wace ta aiko miki dasu , Nabeela tace Ummana Jidda ce ta aiko dasu , Umman tace " ikon Allah Jiddar kud'i take samu haka