Showing 6001 words to 9000 words out of 15331 words

Chapter 3 - Subul Da Baka Book 1 Complete Document by Zul.txt

cikin kulawa, ya
naga kamr kinyi kuka? Hawaye suka zubo min
kafin na fara bata lbrn abinda ya faru ta jinjina
kai cikin tausayawa ,kiyi hakuri humaira Allah
yana tare dake kedai
ki sanya tsoronsa a cikin zuciyarki kuma komai
zakiyi kisa a ranki yana ganinki. Inna bazaki
gane
ba... Iyakar ganewar kenan tunda na ambaci
Allah kuma komai a duniya idan akace Allah an
gama saimu bar lamarin a hannunsa, nayi shiru,
tace dauko kwano na zuba miki danwaken da
zafinsa nasan kinason me zafi. Nadan bata fuska
cikin nuna damuwa nce wllh inna kinason
wahalar da kanki yau ma kiga uban abincin
danazo dashi ina maganar ina bude kwanon da
ledar dankalin yau naman ma yafi na kullum
yawa. Tace nasan haka nima kwadayin
danwaken
yasani yinsa. Inna banason kina wahala kinga
hayakin nan matsalane ga lfyrki batace komi ba
har muka gamacin danwaken nace yau kam inna
gsky bazanje Islamiyya ba kaina ke ciwo,
Sumayya tace yaya malam yace mu fada miki
wann watan ma an yafe mana kudin wata nayi
murmushi Allah ya saka da alhairi inna tace
ameen. Da safe kamar kyllum nagama bayan
nagama duk aikina yauma idonsa biyu amma ya
barbaza takardu akan gado yana rubuce-rubuce
akai. Na gaisheshi ya amsa min a takaice sbd
aikin yasha kansa. Harna kammala komai yana
nan sannan na fita na kawo masa kalaci lokacin
yana kwashi takardun na ajiye cikin girmamawa
sannan na koma gefe ina jira ya karasa na
kwashe. "Kinga nifa nayi wanka ina jiranki ne
kizo
ki bani kayan da zan saka, gabana ya fadi nayi
saurin tashi ina bashi hakuri na nufi gurin
kayan,
to meyasa gimbiya bata fada min wannan ba ko
mantawa tayi sbd ban taba sanin har kaya ni
zan
zaba masa ba na dade tsaye sai nayi la'akari da
ranar na zabo masa jeans brwn kolo da shirt
cream kolo mai ratsin layin red nd blue na ajiye
akan gado ina karanto Innalillahi...a zuciyata.
Abin mmki har ferfesun kan ragon yasha kai
gsky
yau yaci abnci sosai kwai da plantain ne kawai
bai ci ba. Na kwashe kayan nakai kicin na ajiye
sannan naje store na samo ledoji ina cikin
juyewa
kawai naga mutum a tsaye akaina ya kura min
ido nayi saurin durkusawa nace ko yana bukatar
wani abu? Ya girgiza kai naci gaba da juye
abincin na ajiye bread din daban, ya wuce
abinsa
nagama na koma dakin na gyara wajen daya
bata
na ninke kayan daya cire na zubasu a kayan
wanki. Falo ya dawo ya zauna abnd bai tabayi
ba
kenan anan gimbiyar ta tarar dashi yau kam yan
arzikin suna kansa tunda fitowa 2 sai naga suna
dariya. Nansuka kusa yini don ni har lokacin
tafiyata
anan na barsu na harhada kayana nayiwa su
Rabi
sallama na tafi. Misalin karfe shida saura kwata
na dawo islamiyya natarar ciwon inna ya tashi
abun yau yafi na kullum hnklina ya tashi na
rude
na shiga neman maganinta bangani ba kusan 7*
ina tambayarta amsa ta gagara duk inda nake
zato na duba bangani ba na dinga kuka nan da
nan na fyalla shagon dayyabu na fada shagon
kamr mahaukaciya ina fadin dayyabu ka
taimakeni don girman Allah ciwon inna ya tashi
ka bani inhealer wllh an kusa biyanmu a gidan
sarki kasa a lissafi..... Ke fitar min a shago bazan
bayarba...! Na rushe da sabon kuka na durkusa
ina rokonsa amma ko a jikinsa naga cewar babu
Sarki sai Allah (dama shi kadai ne Sarkin) sai
kawai nabi hanyar gidan a guje watakila su Aisha
sun dawo sun san inda ta aje adaidai kwanar
lungunmu wata rantsatstsiyar mota tasha
gabana
neman yanda zanyi ta kaina nake bata ita nake
ba abun mmki sai naga amira ta fito daga motar
ta taho ta rikeni humaira lfy kika gigice kamar
mahaukaciya? Nace wllh Amira ciwon inna ne ya
tashi narasa maganinta, SubhnAllah dama tare
muke da yarima gashi can a mota yace na
rakoshi (chai! Diaris God ooo! Har anzo gurin?)
Nayi saurin fiddo da idanu yarima? Lfy? Meya
kawoshi gidanmu? Tace kinga yanzu ba wann
tym din tambayoyin ta karasa mota cikin
sassarfa. Da sauri naga ya fito zo nan! Ya kirani
da sauri naje shiga mota! Kamar jira yake ya
fizgi
mota da gudu ya nufi wani katon shagon magani
ya shiga gudu ya siyo magunguna ya kara fitowa
da gudu ya kuma fizgar motar har gidanmu na
fito guje ya bani inhealer daya na shaka mata
na
kara shaka mata sbd ta riga ta gama galabaita
cikin less dan 20seconds ta sami kanta nnayi
ajiyar xuciya sai sanann na farga da yarima
dake
tsaye na janyo jakar kayana yana kallo na fiddo
zaniin shiga taro na shimfida masa akan kujerar
katakon na umarce shi da ya zauna, sai kawai
ya
yane zanin ya mikomin tare da zama akan
katakon na sunkuyar da kaina ya kalli inna cikin
girmamawa yace sannu ya jikin? Tace da sauki
yace Allah ya sawwake, ya miko ledar yace
magungunnan nan danAllah a daina bari suna
karewa nace inna yarima ne fa mijin gimbiya ta
kara kallonsa mungode fa mungode yace bakomi
inna zan koma Allah ya kara sauki tace ameen.
Nida Ameera muka rufa masa baya har bakin
mota na durkusa har kasa nace masa nagode da
taimakon da kayi min Allah yasaka da alhairi ya
biya da gidan aljannah (nima nace ameen)
Yace amin Allah ya bata lfy, Amira tace Allah
ya taimaki yarima ni daganna zan karasa gida
tym din tashina yayi, yace badamuwa mu kwana
lfy ya figi mota yayi gaba nayi ajiyar zuciya na
dubi amira nace lfy yarima yazo gidanmu kuma
ya akai yasan unguwarmu daya? Ta kalleni sosai
tace muna tsaye ni Rawila muna ban ruwa in
gaya miki ya fito a hanzarce sai naji yana cewa
wasila ke xonan ina wann yarnyr da take gyara
min sashena? Tace wa yallabai? Yace yar farar
marar jiki zaki ganta magana ma bata dameta
ba
ya daka mata tsawa ke yar doguwar nan nake
nufi wacce bata fiddo gashinta waje. Nan da
nan
na ganne ke yake nufi na rugo nace ko humaira
kake nufi yallabai zaka ganta kullum tana nade
da
carbi a hannunta? Yayi saurin cewa kwarai ita ce
kirawo min ita yanzu tana ina? Ya karasa mgnr
yana dube-dube, nace tana gida dama aikin
safe
takeyi yace kinsan gidan? Tambayr ta bani mmki
amma nace eh yace muje ki rakani, wllh gimbiya
batasan ya fito ba kuma kinga da kanshi ya tuko
motar, na dubi amira nace ko lfy yazo nemana
amma wata kila wani abun yake nema bai gani
ba shine.....wllh bashi bane na fahimci sonki
yake
baki lura da kallon da yake miki a dakin inna ba.
Na kyalkyale da dry amira baki da hnkli kawai
na
fahimci yarima mutum ne me tausayi kawai
yana
tausayawa rayuwarmu ne Yanzu ko daura min
shi akayi amira ina zan
kai yarima? Zata kara mgn na daga mata hannu
kibar maganar nan kin jahilci yarima ba haka
yake ba a dole tayi shiru, bayan na rakata na
isa
gida na tadda inna harta tashi, tace yo ke ashe
wann maganin ba irin wanda nake sha bane na
amsa na duba sainaga babban ne me tsada ya
siyo a kwalinsa me 24 kuma da gani zai dade bai
kare ba sbd yafi wancan girma da karfi nayi
murmushi nace ai wllh mungode. Ina kuka hadu
ne? Nace wllh inna Allah ne ya kawo yarima na
bata lbr kamr yanda mukayi da amira har yanda
mukayi da dayyabu. Ta girgiza kai kawai tayi
ajiyar zuciya hrt har 2* kafin tace Allah kenan
buwayi gagara misali donAllah gobe ki kara yi
masa godiya, nace wann ai dole ne inna
sumayya
da Aisha sunyi tsuru-tsuru sun kasa cewa komai
na wasance su sbd naga sun kidima, da wuri
muka kwanta bacci yau a gidan
*****Gimbiya ta kwala min kira na juya da
sauri ina mmkin wann sammako tare da adduar
Allah ysa bata ji lbrn zuwan yarima gidanmu ba,
ta mikomin doguwar takarda kibawa yarima idan
kin shiga na karba nayi wata irin ajiyar hrt,
harna
gama komai bai tashi ba na kawo kalaci na
zauna ina jiran tashin shi. Tunani kawai nake in
banda rashi da talauci wann aikin bai dace da
yar
musulmi, katon namiji yana kwance a gado ni
ina
dakin kuma ba muharramina ba na daga hannu
ya Allah ka karemu daga sharrin shaidan. Na
mike na dauko masa kayn da zaisa na aje a
gadon. Sai 12:30 ya fito ina zaune a gefen kujera
daga kasa yazo ya zauna a kujerar dake
fuskantata nayi zaman yan makaranta na
gaidashi ya amsa ya tambayi jikin inna da sauki
na fada ina murmushi na sake satar kallonsa
nace gsky naji dadin hallacin dakai min jiya
bazan
taba mantawa ba inna tace a kara maka godiya
ya kalleni yace ba wani abu kije ki kawo kayan
kalaci, harna kai bakin kofa yace waya baki
takarda kikawo min? Nace gimbiya ce ita
gimbiyar tace ki ajemin takarda kibani a
hannuna? Da sauri na zube cikin kidima na
rantse
da wanda raina ke hannunsa babu ruwanta
naga
cewar kana bacci kuma..... To ki dauki takardar
ki mayar mata yanda ta baki na kalleshi idanu
jajur kayi hakuri laifinane, Humaira kinada
matsala wllh abu kankani saiki tada hnklinki
musmmn aka ambaci gimbiya a ciki ba aikoki
tayi
ba? Na daga masa kai to ni kuma na aikeki. ,Na
mike kamr wacce kwai ya fashewa a ciki
tana falo ta kalleni cikin kulawa lfy dai ko? Na
durkusa na mika mata nace yarima yace na
kawo
miki ta amsa ta bude sai naga tana murmushi
kice masa nagode, na juya cikin kwarin guiwa
naje na gaya masa harna fito yace Humaira zo
nan, ya nuna mini wuri na durkusa na sunkui
da
kai ina sauraronsa jiya inaso na tambayeki na
mance ina babanku? Ya rasu! Yafi 6mins baiko
motsa ba,dama inna ita kadai ce? ,Nace amsa
masa uhm ita kadai ce, yayyenki nawa? Nace
nice babba,
wadannan yanmatan kannenki ne? Nace eh,
sunawa ne? Su biyun daka gani, skul
fa? Na daina zuwa amma su zasu koma wann
hutun idan an koma, kefa? Nayi
shiru, kinji? Baki magana ne? Nakasa cewa uffan
wllh saina sami bakina da yin
nauyi, tashi ki tafi to tunda na bata miki rai kiyi
hakuri (wai shema tana kallon
daukaka) tsoro ya kamani ni wacece da yarima
zai bata wa rai har ya bani hakuri,
wann abu kamr asiri nakasa cewa kala, ya dan
sassauta murya yanzu ya kikeson
ayi kinki magana nace ki tafi kinyi jugum?
Magana tana miki wuya ko? Na girgiza
kai yayi murmushi yace to tashi ki tafi na mike
na nufi kicin na fice ta kofar baya
na tarar da mutanen ana sana'ar ko kallonsu
banyi ba nace Allah ya ganar daku,
wata irin yunwa nakeji na debo kalaci cikin
wanda ya rage a bakar leda dankaline
da kwai na tafi can baya na zauna inaci kamar
daga sama na ganshi wani irin
kallo yake min na tausayawa yace donAllah
zauna kici kalacin ki na zauna amma
na kasa cigaba da ci, a gsky baki kyauta ba
dama baki kalaci ba ki hau aiki tun
safe sai yanzu kusan karfe daya da kwata? Ya
karasa zancen yana duba
agogonsa,
Nayi dan murmushi wllh na karya tun a gida
yanzu ne dai na dan jin yunwa,
bai kara mgn ba ya wuce abinsa. Suna zaune
shi da gimbiya a saman wasu kujeru
na fito da shirina cikin wata kokakkiyar atamfata
kafata sanye cikin kodadden
silifas da hijabina har kasa na wuce su ina ga
yau ce rana ta farko dana taba tafia
gida ya bini da kallo harna tsargu, gimbiya ta
ware murya ta kirani na taho da
sauri na zube gabansu tace yarima yace ku ba'a
koya muku bankwana bane? Kafin
nayi magana gimbiya ta surfan zagi dama bakice
masa zaki tafi ba ko yana
bukatar wani abu? Jikina ya dauki rawa yace tayi
min bankwana dazu yanzu ne
dai batayi min ba (Allah Sarki yarima bai san
za'a zageta ba) kana bukatar wani
abu ne da zata yi maka? Yace a'a to meye nayi
mana wani bankwana keyi
tafiyarki, sai naji yana dariya nidai har tuntube
nakeyi don sauri ina isa natarar da
inna sun shirya cikin kayan da basu da wata
nagarta tausayin kanmu ya kamani
nace sai ina kuma inna? Tayi murmushi tace ai
nayi babban kuskure na manta yau
ne ake bikin Harira yar gidan babanku Auwalu
raina ya baci amma na kasa
nunawa sai nace shine zaku tafi yau baku
hakurin gobe? Ta dan harareni suwaye
masu aikin abncn idan ba muba? Nace kai Inna
har yaushe zaki dinga wahalar da
kanki akan wann mutanen da basu san ciwonki
ba cinmu da shanmu da suturarmu
da uwa uba karatunmu?
Ai ba 6angaran dahuwar zan tsaya ba,kinga
akwai gyaran kayan miya,yankan
albasa,alayahu,fere ka6ewa da sauransu".na
ta6e baki kawai.na sauya maganar
da cewa,"cikin satin nan naji ana cewa za'a biya
mu saboda haka gaskiya inna har
dunkuna sai munyi". Kuruci dangin hauka,in ba
hamaira ba yaushe ana ta ciki za ai
ta tsumma?Allah dai yakawo albashin lfy,biyan
bashi dai shine farko idan Allah
yaso". Nace,"Amin". Na fiddo abincin da nazo
dashi,suka ci suka yi kat,sannan ta
mike,"kiyi kokari ki lega gurin 'yanmatan kafin
lokacin islamiyyar". Da kai kawai na
amsa mata. Ta yi murmushi,"mgn ku,a ta kulle?"
Na dai yi shiru."Don Allah kada
kije kiyi wannan miskilancin cikin jama'a,ki saki
jiki wani abun daurewa ake yi".


Zaharaddeen Shomar
Whatsapp 08168575100






Subul da Baka 1 page 2
Posted by ANaM Dorayi on 06:04 AM, 21-May-15
Under: Subul da Baka
*
Na dai yi murmushi kawai ta fita tana
fadin."Hali zanan dutse".na dan watsa
ruwa sannan na fiddo wasu riga da siket a
sosassen leshi wanda akalla zai yi
shekaru 4,yana 1 daga cikin na ganin sarki
wanda nake takama da shi. Na
yayyyafa masa ruuwa tare da bigewa saboda
cikwikwiyewar ta tashi.farin gyale
duk. Ya tashi saboda tsufa na yafa,sannan
nasaka takalmin robata na zuwa biki,ko
suna ruwan hoda. Na fito tare da jawo kofar
gidan nadan sanya tsinken kara da
dan icce gurin hancin na kulle kamar yadda
muke idan zamu fita tare da kudurtar
insha Allah da an biya mu kudi zan sawo mana
kwado. Tafe nake kaina a kasa na
wuce gungun samari kusan 5,kwanar karshe da
zan bita kai ni kofar gidan nayi
karo da wata majalisar. Na dan gifta kadan na ji
wani yace,"kai yarinya har yarinya
amma ba galihu".karaf naji wani ya
amshe,irinsu kuma sai shegen girman kai na
banza, waccan yarinyar ita ake yiwa kirari da
danwake kafi ubanka,a unguwarsu
gidansu na dan nesa da na su ibrahim
balarabe,an ce girman kan tsiya gareta
saboda..." Maganar tayimin nisa,ban karasa jinta
ba na shige gidan kawai inda sabo na
saba da irin wadannan maganganun bakin
samari,shi yasa bana mai da kai.dalili
kuwa shine ina yawan yin samari da
farko,amma duk wanda zai zo sai ya yi
amfani da talaucinmu ya nemi yi mini maganar
banza,korar karen da nakeyi musu
ne yasa suke yi mini shaidar mai kashin
tsiya,kuma girman kan tsiya gareni,sannan
danwake ce ni. Na kan yi mamaki,TALAUCI
HAUKA NE? Ina ganin tsira da
mutumcin 'ya mace shi ne babban arzikin
duniya da lahira. A nawa fa tunanin.
Kamar duk lokacin da hidima ta tashi a kullum
muna raku6e gefe,haka ma wannan
lokacin.zaune nake kusa wasu tsofaffin maroka
ina kallon kowa yadda ake shagali
bare wanda bai hada komai dasu ba,ya fi ni
sakewa da gata saboda BABU....
,Babu wacce ba ta ganni ba,amma ko kallon
arziki har aka kira la'asar ko ruwa
na shiga nace,"yaya harira sai Allah ya kaimu".
Tayi watsi kamar ba taji ba,na kara
maimaitawa,ta daka mini tsawa,"naji". Na juya
cikin abokanta naji wata ta ce "kin
sallame su?" Ta ce,"wa?" Ta nuno ni da
yatsa,"ba 'yar marokan can ba ce?" Na
dan juyo dan kallon wacce ta yi maganar. Ta
yatsina fuska, "wai 'yar uwarmu ce".
Dayar na zaune da waya a hannunta tana
latsawa tun shigowata ta kyalkyace da
dariya,tare da fadin,"shegiya harira,wato wai
ma ne?" Gaba daya dakin ya dauki
shewarsu,ni dai na yi waje ina mai takaicin irin
wannan salon wulakancin,a ce duk
sabga da salon irin wanda za ayi mana? Dama
waecan karon an kira inna da 'yar
aikin gida. A tunanina zan tarar da su inna su
ma sun dawo saboda zuwansu Aisha
islamiyyar,sai na ga cewa ba su dawo ba. Na
dauki littatatfaina da hijabi bayan na
gama sallah na fito... Shekara 2 da suka wuce
nayi saukar alkur'ani,yanxu ta 2 zanyi,wacce
nake
hadda,ga shi na gama littattafai da dama kamar
su;ZADUl MUSLIM,HAKKUL
MUBIN,KHAMSUNA HADITH,HUSNUL
MUSLIM,BULUGUL MARAM...kai za su kai 12
yanzu wasu sabbi muka shiga irin su,ma'anar
addu'a da fassarorinta,tarihin
Annabawa da kissoshinsu,da sauransu. Acan na
tarar da su sumayya suka ce daga
gidan bikin suka taho,inna sai anjima na kada
kai kawai cikin raina nace ba ta
gama bautar ba ko? A gida muka tarar da ita
bayan mun tashi da nairarmu
300,wacce aka bada sadaka wani bawan Allah
ne ya kawo.tun a hanya na siyo
mana taliyar leda daya,naira 110.magin
20,gishirin 10 sai mai na 20 kwanti. Na
san muna da dan sauran busassen tattasai
muka rago 150,su Aisha sai tsalle ake
yi gobe za a yi kalacin koko har da kosai. Ba
karamin dadi wannan labari ya yiwa
inna ba,na ba Aisha ta siyo mini icce na 20
ashanar 5. Nan da nan na dora
dafadukat taliya.saboda rashin kamawar iccen
ya sanya ana kiran isha'I na sauke.
Bayan munyi sallah na zuzzubawa kowa na
gyara wurin na kauda duk kayan da na
yi amfani da su,sannan ni ma na karasa saman
tabarma nan waje farin wata ya
haske ko'ina. Lomar farko almajiri yayi sallama
da robarsa a hannu nayi saurin
hadewa da hanzari don samun damar amsa
masa sallamar. "Ance ana magana da
humaira". Wani gululu ya taso mini, dama na
hango tsayuwar mutum jikin
katangarmu tunda karamace,nasan cikin 'yan
iskan samarin nan ne saboda yau na
wuce majalisa da yawa,shi yasa ban ciki son
zuwa gidan baba Auwalu ba,unguwar
da hanyarta kamar nan aka tara samarin KANO!
Ko motsi nakasa yi har yaron ya fita da amsar
inna,wato. Tana zuwa". Na fi
minti 5 a haka cikin nuna fushi inna tace. Baki
da halin zuwa kika sa nayi
karya?.Raina ya kara 6aci,wani abu sai
iyaye,shin inna ta manta da cewar abinci
nake ci? ko kuwa nice na ce ta byr da amsa?
"sai kin gama shawara Zaki
tashi?"Ta katse ni tana fada . Na mike kawai ba
tare da nace komai ba. "wnn
miskilancin? wnn miskilancin?? Allah ya rabaki
da shi Humaira, ace duk aikin
duniya babu mai miki wuya sai MAGANA? "Na
dan yi murmushi lkcn da na sako
hijabi, maganar taso bani dariya, Inna kenan.
Na fada a raina. Wani kamshi ya
doki hancina, kamshi mai kwantar da zcy da
tarwatsa tunani zuwa wuri guda .
tsaye yake ya jingina da katangar hnnynsa goye
a kirji.
Na kasa klln fuskar na dan jingina ni ma dan
nesa dashi kadan muna fuskantar
juna. Ya yi magana shiru! har kusan 25mins a
kiyasina. Tun Ina daurewa har
tsayuwar ta fara gundurata, km da alama ni
kadai yake kallo. Gaba da gabanta, na
fada a zuci, Inna da mutanen gari na kirana
MISKILA, yau ga wnd ya shafeni. A
tunanina shi yazo ba tare da na gayyatoshi ba.
Wasa sabon aji hr ana neman
kusan 40mins haushi ya turnikeni, wnn
wulakanci da yawa yake, amma zan ba shi
20mins nan gaba, matukar bai yi magana ba to
zanyi tfyta. "Kai zo nan".Tattausar
muryarsa ta katsen lkcn da ya kira wani
almajiri.Tsoro, fargaba da kuma razana
duk a ckn wdnn 'yan sakanni suka shige ni, na
dago Kai tare da kallonshi. Tuni ya
maida kallonsa ga yaron, har ya karaso. Ya ce
"shiga ciki ka ce YARIMA ya ce
yana son shigowa ya gaisa da inna". Na
sunkuyar da kai ckn jin kunya, da kyar na
kalato klm 3, "wlh ban San kai ne ba..."Yaron ya
fito, "Ta ce, ka shiga".Ba tare da
ya kalle ni ba, ya gitta ta gabana tare da
wucewa ciki, sai a lkcn na lura hnnynsa
akwai leda baka. Simi-simi ckn faduwar gaba na
rashin kyautatawata na bi
bayansa... ,Aisha,sumayya duk sunyi barci anan
inda muke zaune inna ta bashi tabarma ita
kuma ta dan tsugunna a kofar daki. Na dinga
addu'ar Allah ya sanya su sumayya
basu zubda taliyar ba,saboda fararen kayansa
karsu nadi manja?."Mun same ku
lfy? Ya fada a hankali,sai ka ji zaka san irin su
magana na basu wuya. Inna tace
lfy kalau,ya kuke? Lafiya ya fada a gajarce. Na
koma kusa da inna na tsugunna ni
ma. Sai dayayi 'yan mintuna 2 kafin ya ce,ya
jikin? Tace "Alhmdllh". Ya bude ledar
ya fiddo magunguna. Ga wadannan. Ya mika
mata 1 wannan kuma 1 ne kwal zaki
shanye a daren nan. Sai wadannan sau uku-uku
guda 2 kowanne kullum. Mamaki
ya kamani,ashe

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login