Showing 12001 words to 13311 words out of 13311 words
Chapter 5 - Subul Da Baka Book 2 Complete PDF .txt
muka
gaisa. Idanuna suka suka zubo da hawaye
na kalleshi, " Don Allah ka yi hkr zan koma
gida akwai aikin da nake yi".
Yayi murmushi, " To naji, amma kukan fa na
mene ne? ko duk aikin ne? " Na runtse ido
mgnrshi ko na ce tmbyr ta soke ni kmr
mashi. " Humaira ban boye miki
damuwataba, don me Zaki boye mini taki?"
Na kalle shi, " Ba ni da damuwa sai Wacce
kake neman saka ni ciki, don Allah ka rabu
dani na koma gida ". Na rushe da kuka tare
da durkushewa. Shi ma durkushewar yayi,
tare da sassauta murya. " Haba Humaira
ynz Amira ta kirawo yayanta muna tare, ta
sanar da shi wayar da kuka yi. Don me zaki
damu kanki? ki share hawayenki gani na zo
zan je na gabatar da kaina wurin iyayenki,
wlh Zaki same ni mijin da kowace mace ke
mafarkin samu, zaki yi alfahari da aurena".
A tsiwace na kalleshi ina girgiza kai, yayi
Kasa da murya.
"Ki yi hkr, nasan baki sona, to wlh zan yi
hkr har zuwa lkcn da Zaki so ni, ni ma
marayane Humaira, matsalar mu daya ynz
haka nima irin auren da za a yi miki ake son
yi mini a gidanmu". A langabar da kai ckn
zubar hawaye, " safwan wlh ba zan iya
amsa maka ba..." "sbd me? " Na kwantar
da fuska, " Baza ka gane ba ". Ya yi
murmushi, " zan gane Humaira, fada mini
shin zaki cutune?" Na yi masa shiru. "kiyi
mgn ko kina ganin wancan auren zaki
amince da shi, na dattijo? Kinsan halinsa?
su waye matansa? ko kina tunanin tsufan
ne kawai ba matsalar iyali?
shin yaransa nawa? ko kina da labari mafi
yawa kishin ynz da 'ya'ya ake yi bada
iyayeba? " Na mike, " wayyo ni
Humaira,safwan zan rungumi kaddara, sbd
kai din ma bansan wane ne ba? shin ya 'yan
uwanka da kishiyar mahaifiyarka Zasu
dauke ni? cewar baka da matsala ne zai
tabbatar mini hkn? Na girgiza kai, " safwan
kada ka ya bi kanka, shi yabon kai
jahilcine". " Humaira kiyi tunani, zan dawo
jibi komi kenan, pls kada ki so kanki da
gobe zan koma, amma zan jira hr naji
amsarki. Allah yayi mana jagoranci, zan
wuce ki je ki kwanta, amma kiyi kokarin
tashi ckn dare kiyi nafila, domin neman
zabin Allah".
Ban ce komai ba na wuce ciki, amma ko bai
fada ba dama ina da wnn niyar. kwance
nake na rasa abinda ya ke yi mini dadi, sbd
lallai mgnr safwan shi su waye iyalan
dattijon? Da farko ina tunanin auren sa
shine mafita, amma ynz km hnklna ya
tashi. " Innalillahi wa'inna Ilaihi raji'un ".
Har karfe 2 idona 2, na mike nayo alwala na
dinga salloli ina addu'o'i ckn sujjada, snn
ban tashi wurin ba sai da aka yi sallar
asuba. Na tashi da matsanancin ciwon kai,
na samu na kwanta bayan na sha (Boska).
Idona rufe wayata ta fara ruri, na duba
Amira ce. " ya naji muryarki haka Humaira?"
Na fada mata ydd muka yi da safwan, ta yi
shiru kafin tace .
"Turkashi, Humaira ki dage da addu'a nima
ina yi miki nawa kokarin Insha Allah
matsalar ki ta zo karshe". Na yi murmushin
takaici. " Hm Haba Amira, wai har su baba
Auwalu ke cewa, ba zan taba auren mai
rufin asiri ba, don bana fin yaransu, Yaushe
na taba zabin irin wnd nake son aure
Amira? " Ta yi ajiyar zcy, " wlh hassada ce
kawai suke yi miki, don hk kedai ki
fauwalawa Allah komai. Bari ina ina zuwa ga
Gimbiya can tana kirana". Ta kashe. Kmr
abin jira, Kiran Ibrahim ya shigo, naja wani
dogon tsaki, wnn waya tana neman
jawomin matsala, sbd ko motsin tsintsiya
ba a son ji wlh.
Ina dauka bai jira mun gaisa ba yace, " INA
yau zan baro kasar nan ki saurare ni zuwa
gobe da yamma". Na bude baki, amma sai
na ji ya kashe. Da sauri na tashi zaune
daidai lkcn da inna ta shigo, na ce. " kin ji
wai Ibrahim yana hanya". Ta zaro ido, "
zuwa ina? " "Nan zai taho, wai na saurare
shi zuwa gobe da yamma". " Innalillahi
wa'inna Ilaihi raji'un, ni kam a gaskiya ni
kaina mgnr Ibrahim ina fa tangarda da ita,
sbd hatsabibiyar matarsa tnd har ta furta
kisa ko na kasa..." Kiran Amira ne ya shigo,
na dauka, ta cigaba da lallashina tana bani
hkr, nace ba komai, muka yi sallama. Jin wnn
mgn yasa na fada mata mgnr
safwan, ta girgiza kai. " Haba Humaira,
kawai daga ya zo sai a amince da shi mun
san halinsa? " " Nima hk na gani inna. shi
baba bai gaya miki wane dattijon ba? Tayi
dry, " bai fada ba, wlh jiya hr gidan naje ki
kyale wdnn mutanen, Allah ya fi su".
Washegari ya kama sauran kwana 2 tnd
safe safwan yazo, na fita. Ya kalle ni, " yau
ma kukan ne? " " A'a.Na fada a gajarce. "
To gani ina mgn ta kwana? " " Na fidda
wani" " wane ne? " " wani ne na fada kaina
a Kasa. "Bashi da suna? " " yana da shi". "To
fada".
Na yi masa shiru. " Haba Humaira, me yasa
ki ke son koyon karya, km da alama kmr ba
halin ki bane". "Ya za a yi na yi maka karya?
" "wlh karya kike yi, sbd hk ni zan je na
gabatar da kaina". Na yi saurin dago Kai. "
A'a wlh kada kaje, ban turaka ba". Ya
kyalkyale da dry. " kin kama kanki, ni zan
tafi sai kin ji daga gareni, sbd na lura baki
da tunanin kanki, baki da shawarar kanki,
haka baki da zabi".Yana gama fadin haka
yayi tfyrsa. kmr na kirashi ya dawo muci gaba
da
tattaunawa har ya fahimce ni, amma na
kasa. Na koma gida rai jagule. Ina ckn
damuwar abinci Ibrahim yayi sllm hr ckn
raina gaba na ya fadi, ya bada kululu. Da
inna suka yi mgn snn ta ba mu wuri. Ya
kalle ni ckn tausayawa, " wayyo Humaira dk
kin rame, sannu ko wane tsanani tafe yake
da sauki. Inna ta yi min bayani, na kuma
gamsu, km nima ta fahimce ni, sbd hk zan
tafi gida jibin itace ranar karshe, zamu zo
da iyayena a yi komai, yau kinga yaushe na
zagaya dangi har aka yi mgn? Gobe kuwa sai
na sanar jibi tunda safe mu
taho". Na dai yi shiru kawai, rayuwata ta
kara jagulewa. " zan wuce, ki ci gaba da
addu'a, zan aiko Yaro da kayan ki, suna
waje ckn mota".Ya ajiye min bandir din
kudi ya mike. Inna ta karaso, " yaronan ya
bani tausayi Humaira, ki yi hkr da shi dk ya
Snr da ni komai, kuma na amince da shi".
Shiru kawai nayi mata. Da magariba ina
zaune ina lazimi, yaro ya shigo ana sallama
da Humaira. saura kadan in kurma ihu. Na
kalle shi, " kace ta daina fita, sbd an yi mata
miji, mata aure ce ynz". Inna da ke sallah
ta yi gyaran murya. Takaicina ya karu, wai inna
me ke damuta?
Na fita raina kmr garwashi, zcyta sai zafi
take yi. kamshin da ba ni taba mantawa ya
daki hancina, nayi saurin kallonsa. Tsaye
yake ya harde hnny a kirji, ni yake kallo, na
durkushe sai kuka. Ya sunkuyo, " ki yi hkr
Humaira, nasan kin yi fushi dani, wlh
Humaira ba laifi na bane. ki daina kuka don
Allah, menene damuwarki zuwa nayi muyi
maganinta tare, Amira ta sanar dani
komai". kuka nake, me ya kawo ka a wnn
lkcn, me yasa kazo ka famamin ciwon da
yaki wankewa? " Innalillahi wa'inna Ilaihi
raji'un, don Allah ki saurare ni..." Na mike, "
Don Allah ka tafi, wlh bani son
ganinka a rayuwata, ba don na tsanekaba,
a'a sai don na tsira da mutuncina, kai kuma
ka gama da iyayenka lfy..." " saurara..."
Nayi gida da gudu. Abin mamaki na kasa
sanar da inna ko waye, ita kuma bata tmby
ba. Zaune na kwana, duk wnd ya sani a da
ynz ya ganni sai na bashi tausayi, nayi
muguwar rama ga baki. Tashin hnkl sai
ranar da adadi ya cika da safe, misalin karfe
10.30 na safe sai ga baba Auwalu su uku da
buhun goro. jikina ya dauki rawa da yake
zaune muke ni da inna a bakin kofa. Ya kalle
mu a wulakance, sannan ya nefo ni
da 20k. " To barkanki, wlh da na ba tsoho
ha goran daurin aure nan mun dauki 2, Kuyi
amfani da wnn, Na daura miki aure da wnd
kika turo yau da safe karfe 9.30. Don haka
ki shirya gobe zaku wuce babu mgnr taro".
Na kalli inna itama ta kalle ni. kash!!! Nima
ku nake kallo masu kr2, da wane ne aka
daura auren da shi? safwan ko Ibrahim? Me
ya kawo? mu tara a ltf na 3
Zaharaddeen Shomar
Whatsapp 08168575100