Showing 75001 words to 78000 words out of 142577 words
Sadik d'in yaja hannun Ummul d'in ya tsaya a gaban Sadik d'in cikin tarin bak'in ciki
murya na rawa idanunshi sunyi jazir sai shek'in hawaye yakeyi cikin fad'a da d'aga murya yace,
"Zo nan".
jin muryarshi yasa gaba d'aya mutanen gidan suka firfito tsakiyar gidan dan basuma san ya
dawoba,
shiko ido ya zuba musu d'aya bayan d'aya cikin rawan murya da fad'a yace,
"Sadik amman dai dama can haushina Kake ji ko? bazaka iya duka na bane shiyasa kai ma
Ummul duka dan ka huce a kanta ko? ".
Gaba d'aya shiru sukayi ganin yadda jikin shi ke rawa dan basu tab'a ganin wannan bacin ran a
fuskar shiba,
shi kuwa cikin fad'a yaja hannun Ummul zuwa gaban Adam baki na rawa yace,
"Adam ka tsani Ummul ko meyasa baza kayi min adalci da kawaici ba ka tsane ni shiyasa ka
tsani Ummul tunda aka Aura minta ko?".
shi kam Adam da Sadik sai jujjuya kai sukeyi alamar a, a,
shiko k'ara jawo hannun Ummul d'in yayi zuwa gaban Nenne cikin rawan murya da k'ok'arin
maida hawayen shi yace,
"Nenne ki rink'a ganina a jikin Ummul na tabbata a ko wanne hali kike zaki kulanmin da Ummul
Nenne ya za'ayi kina ji kina gani a doki mutun hud'u Nenne Ummul a gareta Ammina a gareta
d'an Uwana Usman a gareta d'ana da zata haifa a gareta ni kaina".
Nenne kam kasa cewa komai tayi.
shiko jawo Ummul d'in yayi gaban Abba dake tsaye a k'ofar parlour shi suka durk'usa cikin rauni
da karya wuya yace,
"Abba kayi hak'uri abin ne yayi yawa gara in fad'a musu yadda nake ji in sun tozarta ta,
Abba nasan sonane yajanyo kai watsi da Ummul,
Ayyah Abba in dai soyayya tace to na rok'ek'a dan Allah ka kulanmin da ita ka hana su Adam
dukan ta Abba kallifa da tsohon cikin nan suka daketa in sun mata illafa me zasu cemin".
ita kanta Ummul yau ta fara gano wani irin son da Hamma Umar ke mata hakan yasa ta cika da
mamaki ziryan.
Shiko Hamma k'ara jawo hannun Ummul yayi ya tsaya a gaban Usman, cikin tuhuma ya kafe
Usman da idanu sai kuma hawaye car-car na bin fuskarsa,
murya na rawa cikin kuka yace,
"Ashe Usman bazaka iya kula da iya lainaba in bana nan ?
Usman ashe baka damu da abinda ni d'an uwanka nake soba? shin in ban barmaka amanar
Ummul ba wa zan barwa amanarta a wannan duniyar?,
wallahi wallahi bazan yafewa duk wanda ya takura min itaba hankalina bazai kwantaba,
Usman hakan yana nufun
kenan in nayi tafiya zatasha wuya a gaban ka?."
kai Usman ya rink'a kad'awa cikin kuka da tashin hankalin ganin yasa Hamman shi kuka cur-cur
shima kukan ya rink'ayi yana matsowa jikin Umar d'in dan wani irin suka da zuciyarshi tayi a
take jikin shi ya rink'a rawa,
shiko Hamma Umar kamo hannun Ummul din yayi yace,
"Khairi na mu tafi kai kuma Aliyu azatona ko kowa zai juyawa Ummul baya ai kai abokin kukanta
ne dole ka lallasheta in kana son inji dad'i,
Nenne wallahi gata d'aya zakumin inji dad'i ku kulanmin da Ummul in bananan Adam! Usman!
Sadik! wallahi da kunsan yadda nake ji a kan Ummul da ko hararta baza kuyi ba".
sai kuma yaja hannun ta ya nufi harabar gidan da ita tare da ce musu,
"Adam! Usman! Sadik! kuci gaba zata dawo in yaso saiku kashemin ita ku huta".
sannan yaja hannun ta suka fice
suko gaba d'aya bayanshi sukabi da sauri Usman yana kuka har jikin shi na rawa yace,
"Ayyah Hamma Umar kayi hak'uri ba hannuna a dukan Ummul Hamma bazan sake barin ayi
mata komaiba kar kayi fushi dani d'an uwana ."
Bai kulashi ba sai bud'e mota yayi yasa Ummul d'in a ciki ya zagaya zai shiga kenan Abba ya
matsoshi a hankali yace,
"Farouq kayi hak'uri".
girgiza kai yayi cikin sanyi da zubda k'ollah yace,
"a, a Abba raina nane ya b'aci kuma wallahi dazan iya tafiya da ita duk inda zanje da da ita
zanje,
amman bazaiyuwu ko ina muje tareba anan kad'ai zan iya barinta amman sunk'i samamin
konciyar hankali".
Sadik ne da Adam da Aliyu su kace,
"Hamma kayi hak'uri ka gafarcemu".
tsaki yaja ya bud'e motar zai shiga Kenan Usman ya ruggumeshi cikin kuka yace,
"in kayi fushi dani ya zanyi?".
shima ruggume Usman d'in yayi cikin rawan murya yace,
"Ba komai! ba komai! ba komai! Allah zai zama gatanta tunda dukanku kun tsaneta,
Kai kuma waya cema zan iya fushi da kai,
bani da kamarka fa duk duniya ina sonka d'an Uwana".
sai ya sakeshi ya shiga mota ya tafi yana juyowa yana kallon Usman shima Usman d'in binshi
yayi da d'an sassarfa yana d'aga mai hannu alamar bye-bye tare da cemai,
"Hamma na ina sonka".
shima hannu ya d'aga mai yace,
"Usman ina sonka".
daga nan ya bar harabar gidan ya dauk'i hanyar damaturu,
suna isa
kai tsaye hospital ya wuce da ita yana zuwa shida kanshi ya duba lafiyarta a cikin asibitin
sukayi sallah sannan ya dauketa suka wuce Restaurant abinci suka ci
suka sha sannan ya wuce gida da ita.
Bayan sun isane ya wuce d'akin shi yayi wonka ya fito kenan ita kuma Ummul ta shigo daga
dukkan alamu itama tayi wonka,
a hankali ta tako tazo gabanshi cikin sanyi ta fad'a jikin shi murya can kasa tace,
"Hamma Umar ina son k..........
*By*
*GARKUWAR FULANI*
ν ½ν³ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½
*RUBUTACCEN AL, AMARI*
Page 2β£8β£
*Na*
*AYSHA ALI GARKUWA*
ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½
*A* hankali tayi taku cikin sanyi ta matsoshi ta fad'a jikin shi tayi lub a k'irjin yayin da ta manna
kanta a kafad'arshi ido ta lumshe cikin yanayin sanyin zazzab'in,
shi ko Hamma Umar hannu yasa ya ruggumeta tsam a jikin shi sai ajiyan numfashi yake
sauk'ewa ya lumshe idon shi yayi shiru yana jin bugun zuciyarta na harbawa kan nashi sai ya
k'ara tallabo ta tare da shafa fuskarta,
lumshe ido tayi a hankali tace,
"Hamma Umar ina son kak'ira ya Usman ka lallasheshi,
ka ganifa yana kuka muka barshi,
Hamma kayi hak'uri karkayi fushi da ya Usman".
jawota yayi suka zauna tsakiyar gadon nashi sannan ya zauna ya d'an jingina da jikin kan
gadon ita kuma ya jawota jikin shi sannan ya d'an sunkuyo kanta yana kallon fuskarta kallo mai
cike da wasu yanayin a hankali ya fara magana cikin lumshe ido yace,
"Usman wani sashi ne na jikin Umar Usman rabin jiki nane Usman d'an uwanane da bani da
madadin shi Usman aboki nane kuma amini nane kuma shak'ik'ina ne Usman wani babban
jigone a rayuwa ta,
Ummul kin tab'a ganin mutun yayi fushi da d'an uwanshi Ummul indai zanyi fushi da Usman toh
zanyi fushi da karan kaina kenan Ummul ba fushi nayi da Usman ba a a hannun ka mai sanda
nayi mishi".
shiru tayi tana jin wani irin yanayi daya bak'onci rayuwarta tun sanda taga Hamma Umar d'in na
kuka a gaban su Abba yana kuma yiwa su ya Adam fad'a,
haka kawai ta tsinci kanta da k'ara ruggume shi sai kuma tayi luf a jikin shi kamar maiyin bacci,
shima shirun yayi a haka har zuwa wani lokaci sannan ta d'an d'ago kanta ta kalleshi a hankali
tace,
"Hamma ka kira ya Usman kaji kayi hak'ari shifa ya Usman baimin duka ba".
baiyi magana ba sai hannu yasa yajawo wayarshi dake kan dressing mirror sannan ya kira
Usman d'in tare da sa amsa kuwa,
shiru sukayi suna jin yadda woyar ke ruri bai d'agaba,
a gida Kuwa su Hamma Umar d'in na fita Abba yayi tayiwa su Adam fad'a,
Hajjajo Kuwa gaba d'aya mamakin Umar take,
shiko Usman suna watsewa,
kai tsaye d'akin su ya nufa yana zuwa kan gado ya fad'a cikin tarin k'uncin zuciya da zafi
haushin kanshi da kanshi yakeji tunda ya kasa samawa Hamman shi farin ciki mutumin da
kullum burin rayuwarsa yasashi farin ciki amman shiko yau sai kuka yasa d'an Uwan nashi gaba
d'aya sai yaji ya tsani kanshi da kanshi cikin kuka ya rink'a cewa, "Hamma na kayi hak'uri ka
gafarceni Hamma na bazan sake yin abinda zai bata ma raiba insha Allah nima zan saka farin
ciki".
yana cikin haka ne yaji woyarshi na suwa,
hannu yasa ya amsa kiran tare da manna woyar a kunnen shi, shiko Hamma yana jin a ya
d'aga cikin sauk'e numfashi yace,
"B'iyaye na fushi kayi da nine?
toh kayi hak'uri kaji ko d'an uwana Usman ka gafarce ni."
kai Usman ya rink'a jujjuyawa tare dasa tafin hannun shi ya share hawayen shi murmushi yayi
mai d'an sauti sannan yace,
"In dai zanyi fushi da Hamma na kenan zanyi fushi da mutanen duniya baki d'aya Hamma na ni
zan nemi gafararka ba kai zaka nemi nawaba ka gafarce ni Hamma na karkayi fushi dani".
murmushi yayi jin dad'in Usman baiyi fushi dashi ba sannan yace,
"Ni bakayi komai ba na yafe maka kaima ka yafe min sannan ka samu Adam da Sadik da Aliyu
kace su gafarceni nima na yafe musu".
dariya Usman yayi yace kai Hamma mune da laifi kuma mu za, a bawa hakuri har ka huce
kenan".
murmushi yayi yace,
kai Usman da kana kusa dani da sai na rongwoshe ma kai na kuma matsema kunne tunda
bakajin magana".
dariya Usman yayi sosai dan yaji dadin hucewar da Hamman shi yayi,
shiko Hamman a hankali yace,
"Usman inajin kunyar Nenne da Abba nayi ta fad'a a gaban su watak'il na b'ata musu rai,
dan Allah ka basu hak'uri kace su gafarceni".
da sauri Usman ya katseshi da cewa,
"Tab Abba fa da Nenne da katafi saida sukayi ta fad'a kamar su ari baki Abba harda marin
Sadik,
sai kace badasu akayi wa Ummul d'in hukunci ba duk suka ware kansu laifi ya koma kan Sadik
da Adam nima da Aliyu sai muka zille kanmu".
dariya sukayi baki d'aya sannan Ummul dake jinsu kuma tace,
"Ya Usman ba cin zalina kukayi ba duk kun tsaneni ba mai sona dan kunga Hammana baya nan
kukamin halin yan ubanci".
dariya yayi yace,
"ai ked'in ce bakya jin magana".
ruggume Hamma Umar
d'in ta k'arayi da k'arfi sannan ta d'ago kai ta kalleshi baki ta d'an tura tare da cewa,
"ina jin magana mana ya Usman ka tabbayi Hamma shi yasan inajin magana".
sai ta kuma kalli Hamman a hankali tace,
"Hamma inada jin magana ai ko?".
ruggumeta shima yayi sannan yace,
"sosai ma kuwa Khairina tana da jin magana".
Murmushin jin dad'i tayi shiko Usman dariya yayi ya katse kiran,
ya kife kanshi cikin pillow numfashin sa na fuzga,
shiko Hamma Umar ganin yadda Ummul ke mak'ale dashi a hankali ya jawo blanket ya rufe
musu jiki hannu yasa yana shafa cikin nata,
ita ko hannun ta ta kife kan kirjin shi tana d'an murza yatsarta a jikin shi,
a hankali yace,
"Khairi! Khairi! Khairi! ".
shiru bata amsa ba,
sunku yowa yayi ya lek'a fuskarta abin mamaki sai yaga tayi bacci tuntuni sai jikinta da ya k'ara
zafi da zazzab'in haka yasa ya gyara mata kwanciyar ta a jikinshi sannan yayi musu addu'a ya
shafa musu sannan ya d'auki woyarshi ya fara karatun qura'an,
a haka har bacci yayi awon gaba dashi.
washe gari lahadi da sassafe Hamman ya tashi kamar yadda ya saba ya kimtso komai sannan
ya zauna da kanshi ya bata abinci Sauri-sauri dan duke da yau lahadi ne yauma zaije gidan
govnr zai k'ara duba lafiyarsa,
9:20 Am ya gama komai ya fita kai tsaye gidan gomnatin jihar yana nufa.
Itako Ummul a gida Hamman nata yana fita ta koma d'akin shi ta zauna haka nan ta tsinci kanta
da yin abinda bata tab'ayi ba duk da zazzab'in da take ji amman taji k'arfin guiwar jikin ta d'akin
ta fara tattarewa ta kimtsa duk abinda ya watsa kafin ya fita zanin gadon ta canza mai ta nad'e
wannan d'in sannan ta share ko ina ta goge komai ta killaci d'akin sannan tasa turaren wuta mai
k'amshi daga nan ta koma d'akinta ta gyara ta fito parlour su har dinning area da kitchen nasu
kab ta gyara komai sannan ta shoga kitchen d'in,
karo na forko kenan da tayi niyar tayi girki tare da rebon Hamma Umar d'in dan takanyi girki
kam amman bata tab'ayi da rebonsa ba,
shiko in zaiyi itace forkon ci kuma duk inda yake zai dawo ya mata abinda zataci ko yana office
yakan dawo yayi girki ta kuma ci,
amman yau da niyarta a cikin ranta zata yi girkin dan inya dawo ya huta,
bayan ta kammala aiki ne ta koma d'akinta wonka tayi mai rai da lafi sannan tana fitowa karano
na forko a da ta zauna tayi kolliya na gani na fad'a sannan ta zira doguwar riga a jikinta duk ta
feshe jikinta da turaruka tare da murje humra a jikinta,
k'arfe 2:00 pm ta fito parlour bayan tayi sallan azahar,
a k'asa ta konta kan carpet tayi matashi da pillows d'in kujerun
lokaci d'aya kuma gajiyar aikin da tayin ya rufeta sai mik'a takeyi,
shiko Hamma Umar a gidan govnr yayi sallan azahar ana idarwa ya koma ya sallamesu sannan
ya nufi gida,
da saurinshi dan yana tunanin Ummul ba lafiya,
yana yin parking ya fito ya nufi cikin gidan a parlour ya sameta tana konce abun mamaki ko ina
fes gashi ta raggad'a kolliya sai shek'i takeyi,
cikin mamaki ya zauna gefenta yana kallon dinning table nasu daya ga an shirya kuloli a hankali
yace,
"Hmmmmm Halima ce tazo? ".
kai ta juya ba tare da ta fahimci manufar tabbayar ba,
shiko a zatonshi Anty Haliman ce tazo tayi musu wad'an nan aiyu kan,
k'ara matsota yayi yana shak'ar k'amshin jikin ta a hankali yace,
"Kinyi kyau Ummu na wannan kolliya haka duk ni akayiwa ko?".
hararan shi ta d'anyi sannan ta juya kai,
shiko matsota ya kumayi yace.
"Naga kamar kin gyara gidan kamar har da girki ko?",
tureshi tayi sannan tace,
"Kamace ma kenan? ,
kuma ai dama ina wonka ni dai ba k'azama bace girkin ma ai inayi dama banayin mai yawane
yau kuma naga baka dawo da wuri bane kuma naga kamar ka gaji shiyasa nayi girkin da
rebonka".
wani irin murmushin jin dad'i yayi wanda har a fuskarsa za, a ga tsantsar farin cikin sa ajiyan
zuciya ya rink'a sauk'ewa tamkar wanda aka cirewa abu mai nauyi,
Ita kuwa mik'ewa tayi ta koma gefenshi a hankali tace,
"ni fa yunwa nake ji".
mik'ewa yayi da sauri hannun ta yaja sukaje suka zauna,
kamar wasa Ummul ta had'a mai komai sannan ta sawa kanta,
ta faraci ba tare da ta kalleshi ba,
shi kam gaba d'aya ya cika da mamaki a haka sukaci abinci,
sannan ya wuce bedroom nashi a nan ma yasha mamaki wonka yayi sannan ya zira jallabiya
parlour ya fito ganin bata nanne ya lek'a d'akin ta sai yaga tana sallan la'asar haka shina ya
wuce masallaci,
koda ya dawo bata parlor kamar zai lek'a
d'akin nata kuma sai ya fasa ya zauna dan yayi zaton ko tayi bacci,
itako tana jin motsin shigowar shi ta mik'e a hankaki ta fito yana ganin ta ya zuba mata ido dan
wani irin kyau tayi wanda bai tab'a ganin tayi irin wannan kyawun ba,
kanshi ta nufa a hankali har tazo gaban shi,
shiko sai ware ido yake yana kallon ta,
kauda kai tayi sannan ta zame a hankali ta zauna a jikin shi,
gaba d'aya yau Ummul ta cikashi da mamaki donko duk abubuwan da takeyi bata tab'a yinsu
ba ,
ita kuwa lafewa tayi a jikin nashi tana rik'e da hannun shi duk motsin da zaiyi ta k'ara shigewa
jikin shi ta kanainayeshi,
ganin hakan shima ya wore hannun shi ya ruggumeta sannan ya tallabo kanta ya manna
bakinshi kan nata,
ido ya bud'e ya tsurawa ma tasu jin yau ba musu Ummul ta bud'e mai bakinta,
idonshi kan nata idanun ya lalubo harshenta yana mata wani irin salo mai tafiya da hankali,
itako sai lumshe nata idanun tayi tana k'ara narkewa a jikin shi,
abu kamar wasa gaba d'aya salon Ummul na wunin yau ya canza ko motsi mai k'arfi ta hana shi
yayi duk yadda zai juya tana mak'aleshi,
shi kam har yanzu mamakin ta yakeyi.
A haka har aka kira sallan magrib a hankali ya d'an
d'agota cikin kula yace,
"Ummul na muje muyi al'awala lokacin sallah yayi".
tana jinshi amman sai tayi shiru a jikin shi tana k'ara manne tafin hannun ta da nashi,
murmushi yayi tare da d'agota suna fuskantar juna murya can k'asa yace,
"Ummul na yau dai kin fara son Hamman ki amman rigima ta hanaki ki gane bare ki gaya min
inji dad'i".
janye jikin ta tayi da sauri ta mik'e ta nufu hanyar bedroom nata tana k'unk'ini tare da cewa,
"Ni dai a a,
dan kawai na rab'eka to ni bana son k...!".
karo na forko da ta kasa