Showing 21001 words to 24000 words out of 142577 words
jinjina muku reedars damu writers daku d'ayane bamai rabu daku sai Allah kui
hak'uri ga pagenku ya fito kanawa sunce mini GARKUWAR a baya kinyi wani kuskure duk
novels da kinkayi a social media dad'in su yayi ta kewaya nahiya sun shiga sak'ok'in Nigeria
shin meyasa kika ware hausawa bakya yin novels da su sai FULANI? Hausawa ne sukayi min
wannan tabbayar shaidar suna k'aunata gaba d'aya, NIKO NACE MUSU , dole naje duk inda
rebo yake dan bani Rena masoya na kuma ban raina ranar da novel yayi mini ta sanadi an
sannu garuruwa INA alfahari da Gombe Taraba ADAMAWA YOLA gida nake tun fari su sukayi
mini GARKUWA tunda nazo a cikin y'ay'an Adam duk ajizi an sanshi da kuskure kuyi hak'uri
novelna na gaba da hausawa yana nan tafe, dan ni garin mosoya nisa bai mini da na fad'a
kuma yanzu ina tuni Allah ya kaddara in zamto Zuma dana fito ai tayi mini sansani, yau hak'uri
zan bawa hausawa dan sunfi so na tsaya tamkar gini, RABBI nufeni silar novel da zanyi mutan
k'asarmu su zauna lfy,
Forko mutan KANO zanai kira wanda fagen nema basa jira maza da mata Manya da k'ank'ana
a gsky na sansu da Hattara sunce nazo naga yadda abin yake sannan na tabbaya ni sukayi jira
na mori so da k'aunar da suke mini sannan sunce na dage fannin k'irk'iraKanawa wannan
shafi naku ne```
*Y*ayi mata wani irin kallo cikin tarin mamaki da jin zafi a ranshi murya can k'asa yace.
"Ummul duk wannan kukan kina yinshi ne dan an had'a auren ki da Hamma Umar?
Ummul duk wannan zafi da tarin bak'in ciki dan an shigar da Hamma na cikin rayuwar ki ne
kike haka?."
Sai kuma yayi shiru tare da dafe k'ahon zuciyarshi a hankali cikin jin jiri ya koma baya kad'an ya
zauna ido ya rumtse da k'arfi sannan ya jingina da jikin gini,
numfashi ya rink'a furzarwa da sauri-sauri yana mai cushewar tunani.
Ita kuwa Ummul cikin kuka tace.
"Na tsaneshi na tsani Hamma Umar bana sonshi duniya da lahira ko fuskar sa bana k'aunar
gani,
Hamma Umar ba abinda yake jazamin a rayuwa sai bak'in ciki ya zame min bak'in jakada a
rayuwa ta."
K'ara ta saki da k'arfi tare da dafe fuskar ta jin wani irin zazzafan mari da ya Sadik ya zuba mata
cikin huci da zafin rai ya nunata da yatsa murya a hargitse yace.
"Ki kula kisan furucin da zakiyi ki san waye Hamma Umar wallahi a kanshi zamu iya miki komai,
shi Mustapha ko tare kuka fito duniya bake ba shi."
Kife kai Ummul tayi a bakin gado ta saki wani irin kuka mai cike da zafi a zuciya kuka mai
cushe zuciya gaba d'aya jikin ta sai b'ari yake lokaci d'aya ciwon mararta da ciki da k'ugunta
suka taso a tare,
kuka take cikin tausayawa kanta da Mustapha.
Gaba d'aya sukuwa shiru su kayi cikin jin sautin kukan ta, ya Usman ne yake tunani a ranshi
tabbas Ummul akwai kuna a ranta akwai zafi da ciwon rabuwa da masoyi,
sannan ga cushen mak'iyi da akayi mata,
har cikin ranshi yake tausayawa mata,
a sashin zuciyar shi kuwa,
yana jin zafi da bak'in ciki da takaici yadda Ummul ta tsani d'an uwanshi mafi soyuwa a gareshi.
Nenne kuwa itama shiru tayi tana jin sautin kukan y'ar tata har cikin ranta take tausayawa mata,
amman a zahiri tafi jin dad'in auren Ummul da Umar akan ace da Mustapha dan ita Nenne tana
son Umar da Usman tamkar yayanta na cikinta bata son abinda zai b'atawa Usman rai da
yanayin ciwon sa bata k'aunar taga damuwa a fuskar Umar dan shi jigone mai burin samawa
kowa farin ciki shi baya shiga sabgar daba tasaba, shi ba a gane matsalar sa dan ba fad'a zaiyi ba duk halin da yake ciki dan shi mutun ne mai
kunya da zurfin ciki da kara da kawaici shiyasa bata son abinda zai cutar da Hamma Umar d'in,
haka yasa take ji a ranta dole zata iya juya d'iyarta tayi mishi biyeyya.
Ya Adam kuwa wata iriyar kunyace ta rufeshi ganin yadda a gaban Usman Ummul ke kuka
kamar ranta zai fita dan an hada ta Aure da Hamma Umar,
kunya yake ji ya Ummul zata nuna bata son d'an uwan shi alhalin shi a koda yaushe cikin nuna
mata kulawa da gata yake.
Ya Sadik har cikin ranshi yake jin tsanar Mustapha tunda a kan Mustapha ne Ummul take furta
kalaman k'iyeyyar Hamma Umar d'in nasu haka kuma yake jin zai iya yiwa Ummul ko wanne
hukuncin matuk'ar zatayi wa Hamma Umar d'in rashin da'a.
Auta Aliyu kuwa abokin fad'in Ummul kuma kaninta mai tausayawa mata ganin yadda take kuka
ba wanda yake lallashin ta gashi dama ya Usman ne mai kareta kuma yau shima fad'an ya
shafeshi,
kawai shima Aliyu sai hawaye yake zubda wa a hankali ya matso kusa da Ummul d'in murya na
rawa yace.
"Ayyah Anty Ummul kiyi hak'uri kibar yin kukan haka."
Cikin tausayawa kanta da kanta ta fad'a jikin Aliyu kanta ta kife kan cinyar shi ta saki kuka mai
cushewar sauti,
shima Aliyu sai hawaye car-car yana jin tausayin ta a ranshi,
cikin kuka tace.
"Aliyu yau kowa baya sona duk an tsanani sabida Hamma Umar ! sannan an rabani da
Mustapha sabida Hamma Umar ! Auta kalli yau ya Usman ma fushi yake yi dani sabida Hamma
Umar! kalli ya Adam da ya Sadik ji suke kamar su kashe ni sabida Hamma Umar! Abban mu da
Nenne duk basa sona a yau sabida Hamma Umar! Aliyu ba wanda ya tausayawa min sai kai."
sai kuma ta saki wani sabon kuka.
Ya Adam ne yayi kanta cikin nunata da yatsa murya a fad'ace yace.
"Kifa dena cika mana kunne da kuka wallahi in ba hakaba zan tattakaki."
Ya Sadik kuwa tsaki yaja cikin zuciya yace.
"Kiyi duk yadda kika ga dama ya rege naki tunda bakya ganin alkhairi zab'in da iyayen mu suka
yi miki,
Mustapha ne dai bazamu bashi auren kiba."
Daga nan suka fice ita kuwa Nenne tsaki taja ta fice ta shiga kitchen ta kama aikin ta,
Aliyu kuwa tafin hannushi yasa yana gogewa Ummul d'in k'olloh dake bin fuskar ta,
shi kuwa ya Usman zama yayi kusa da Ummul d'in daketa murk'ususu tana ta cike lips d'in ta
zufa na keto mata tako ina sai kukan da takeyi cikin raunin da wahala.
A hankali ya kalleta cikin sanyi ya d'an yi murmushi yace.
"Ummul khairi banyi fushi da keba ,
ki sani ke tawace kamar yadda Hamma Umar yake nawa ni Usman Ku duk nawa ne ba Wanda
zank'i a cikin Ku kiyi hak'uri k'anwata kiyiwa kanki da Hamma na addu'a Allah ya muku zab'in
abinda yafi zamewa alkhairi a gare Ku."
Kai kawai ta juya tana mai azabtuwa da ciwon cikin da tarin damuwa.
Shi kuwa Usman haka yayi ta bata baki ,
Amman ina Ummul bata ma san yana yiba,
ganin haka yasa. Usman ya fita kai tsaye parlour Hajjajo yaje,
cikin sanyi yayi mata maganar abinda ke faruwa,
kai ta d'an jinjina cikin k'arfin guiwa ta kalli Usman tace.
"Ku kanta na d'an wani lokacin ne zatayi ta bari ta saduda ta zauna da Umaru cikin aminci,
aini naji kukan nata zuwa ne bazan yiba,
dan inta ga ana damuwa da kukan nata dayin lallashin ta toh bazata bariba ku fita sha'anin ta."
Ido ya tsurawa Hajjajo cikin sanyi yace.
"Hajjajo indai Hamma Umar na son wannan had'in toh ina farin ciki da auren nan domain farin
ciki B'iyayen na shine nawa."
Haka suka d'an tattauna kan zancen.
Itako Ummul tunda suka waste suka barta take kuka kamar zata had'iyi zuciya ta mutu,
Aliyu yayi ta lallashin ta amman ina dan abin ya had'e mata ga ciwon ga bak'in ciki,
haka Aliyu sai ya fito yaje kitchen ya dawo gunta yana ta sintiri ya kasa zama.
Haka har dere yayi Nenne kam ko ta kanta bata kuma biba dan inta tsaya kusa da ita tana jin
tausayin d'iyar tata,
ta dai sa abinci Aliyu ya kawo mata,
ita kuwa Ummul yau abincin bazai ciwuba.
9:00 pm har yanzu Ummul tana kuka ne hannun ta dafe da mararta da k'ugunta akaro na biyu
Aliyu ya shigo cikin tausayawa yace.
"Ummul naje na gayawa Nenne baki da lafiya Abba kuma yace kije gun Hamma Umar ya duba
ki."
Kai ta kuma kifewa kan kago ta ci gaba da kukan da sautin shi baya fita dan muryar ta ta dashe,
Ya Adam ne dake zaune a parlour Nenne jin Abinda Aliyu ya fad'a yasa shi mik'e wa ya shigo
bedroom d'in cikin tsuke fuska da bada umurni yace.
"Ke mike kije Hamma Umar d'in ya duba baki,
kin zauna kin wuni kuka shin kukan zai miki magani ne?
ki mik'e ko nace."
Cikin kuka dabin umurnin mahaifin nata da Yayan nata da tsoron ya Adam d'in ta mik'e cikin
wahala hannun ta damk'e da mararta ta fice tana kuka,
kuma Ita da kanta ta san in Hamman ya mata Allurar tana jin sauk'i,
cikin kukan ta nufi part d'in su Hamma Umar d'in.
Shi kuwa Hamma Umar duk kukan da Ummul keyi yana ji dan lokacin da tafara kukan yana
parlour Hajjajo jin kukan yayi yawane gashi yaji bala'in da su Adam ke mata yasa ya zame jikin
shi ya dawo parlournsu cikin sanyi jiki ya konta kan kujera yasa tafin hannushi ya rufe fuskar sa,
zuciyar shi cike da tausayin Ummul ,
yana koncen yaji sautin kukanta a hankali yana ratsa parlour cikin rawan murya yaji tana
sallama,
ido ya lumshe cikin jin zafin kukan da takeyi ga kunyar da ta rufeshi,
a hankali ya amsa mata sallamar,
Ita ko da zuwa yanzu ko tsawonta bata iya mik'ewa,
a sunkuye ta shigo parlour hawaye cike a fuskar ta da tayi jazir da kuka ida nunta duk sun
kumbura,
a hankali ta durk'usa gaban kujerar da yake konce cikin kuka da rawan murya tace.
"Abba yace inzo kamin al..! alluran da kake min."
Shiru yayi zuciyar shi cike da tausayin ta gaba d'aya yake jin haushin kanshi tunda sana dinshi
take irin wannan kukan.
Ita kuwa ganin bai kulatan ba ta saki kuka mai cike da raunin gaba d'aya jikin ta rawa yakeyi,
jin yadda take kukan ne ya mik'e cikin sanyi bedroom ya shige yana zuwa ya had'a allurar,
sannan ya dawo parlour yana zuwa gabanta ya k'afa guiwowin shi a k'asa kan carpet suna
fuskan tar juna,
kanshi a sunkuye yasa hannushi ta bayan ta a hankali ya murza siket d'in atampa dake jikin ta,
ita kam Ummul ido ta rumtse da k'arfi zuciyar ta cike da tsanarsa a ranta,
fuskarta ya d'an kallah sannan ya zira bakin allurar a cikin jikin ta,
k'ara ta saki cikin kuka da zafi ta fad'a jikin shi.
Ido ya rumtse da k'arfi sannan yasa hannushi d'aya ya matso ta cikin sanyi da raunin murya
yace.
"Kar kiyi inji miki ciwon ki nitsuba ba zafi."
kuka ta kuma fara cikin dashewar muryar,
shi kuwa idoya lumshe sannan ya k'ara saita allura a hankali ya rink'a cusa ruwan a jikin ta,
yanayi a hankali yana ce mata .
"Sorry."
Ita kuwa jin zafin yadda ruwan ke ratsata yasa ta ya matso shi ta rik'eshi gam,
yana gamawa ya zare allurar sannan a hankali ya tureta baya ya janye jikin shi,
ya mik'e kenan ya kalli Usman dake dafe da bak'in k'ofa ya zuba musu ido sai kallon suyake
cikin wani irin yanayi.
Ita kuwa yana tureta ta mik'e cikin jin jiri ta ratsa gefen ya Usman d'in ta wuce.
Tana fita Hamma Umar ya kawo hannun Usman d'in cikin tsantsar kulawa ,
kan kujera ya ajiye shi sannan ya d'auki maganin shi yazo ya bashi yasha,
a hankali yace.
"Usman gobe zamuje gun Ammin mu."
murmushi Usman yayi sannan yace.
"Toh Allah ya kaimu."
"Amin"
yace sannan suka she ga bedroom d'in a tare sukayi shirin baccin su.
Washe gari da safe bayan sun gama shirin su tsab sannan suka shiga cikin gida a parlour
Nenne suka zauna bayan sun gaida Nenne suka fito parlour Hajjajo suka wuce suna zuwa
Hamma Umar d'in ya shiga kitchen d'inta da niyar zai d'auki cup,
Sai kuma yayi baya a hankali ya tsaya a bakin kofar yana jin abinda Ummul ke fad'a,
ya Adam da Hajjajo dake bayan kitchen d'in ma suna jin abinda take fad'in ta window ita kuwa
cikin sanyi taci gaba da cewa.
"Nayi alk'awarin har Abadan.....
By
*GARKUWAR FULANI*
*RUBUTACCEN AL,AMARI*
Page
*NA*
*AYSHA ALI GARKUWA*
*'Yan KADUNA duk Nisan da nayi musu Amman dani sai al'fahari suke in sunga novel na ko a
fushi suke farin ciki gurbi nasa zai shige da zana jeni mu zauna so suke basu da niyar tsigen
fiffige, da gaskiya nunan k'auna suke dan sun kirani sunai mini magiya, na jinjina muku
mutan Kaduna domin kuna da karamci hakan yasa na sadaukar da wannan page a gareku*
*C*ikin kuka murya na rawa tace.
"Habibi Mustapha nayi ma al'kawarin ni taka ce har Abadan bazan bari wani yayi nasarar
rabamu ba,
nayima alk'awarin zan adana maka kaina zan killace maka jikina ba wani mahaluk'in da zai
zama hijabi a tsaka nin mu."
Sai kuma tayi shiru tare da sheshshek'an kuka murya na rawa tace.
"Hamma Umar zai rayu cikin bak'in cikin rayuwa tunda har ya kasance a sanadin shi za,a
rabamu ,
bazai sake samun farin ciki da konciyar hankali ba gidan shi zai zame mai tamkar kurkuku zai
rayu cikin k'unci da bank'in ciki ta yadda shida kanshi zai sauwa k'amin ba tare da neman
shawarar kowa ba,
Mustapha tun jiya duk wani tsoron Hamma Umar ya fita a raina na tsaneshi ji nake kamar na
kashe sa."
Sai kuma ta saki kuka mai sanyin sauti,
shi kuwa Mustapha lallashin ta yake cikin raunin murya yake cewa.
"Kiyi hak'uri Ummul ki daina kuka ki sani har Abadan kina cikin raina bazan dena sonki ba,
amman kuwa duk yadda nake sonki bazan so sanadi na ki sab'awa iyayenki ba,
Ummul kiyi biyeyya ga mahaifan ki."
Cikin raunin tace.
"Mustapha zanyi biyayya ga iyayena amman bazan yi biyeyya ga Hamma Umar ba zan
d'and'awa zuciyarshi bak'in ciki mai tarin yawa sai yaji irin d'acin da ya jiyar dani,
tabbas sai zuciyar shi ta raunatu jinin shi sai ya hau hankalin shi bazai sake konciya ba."
Haka ta rink'a fad'in irin uk'uba da cin fuskar da ta tana darwa Hamma Umar d'in yana jinta,
Hajjajo kuwa da ya Adam bushewa sukayi suna kallon juna cikin jin tsoron furucin Ummul d'in
da mamakin yadda take k'ok'ari da niyar cusawa bawan Allah bak'in ciki.
Shi kuwa Hamma Umar a hankali ya juya cikin sanyi fuskar sa a raunane lips d'in shi ya kamo
ya ciza cikin jinjina kai ya juya ya fita,
a parlour suka had'u da su ya Adam da Hajjajo cikin mamaki ya Adam ya kalleshi ganin daga
kitchen d'in ya fito ita Hajjajo kallon shi take,
shiko ganin kamar zasu zargi wani abu yasa ya d'an yi murmushi cikin yanayin sanyi ya gaida
Hajjajo sannan ya kalli Usman dake tsaye gefen Hajjajo yana mik'a mata hannun shi da alamar
ta d'aure mai agagon hannushi ,
Ita ko sai kiciniya take ta kasa,
matso su yayi cikin sanyi ya matso ta ya d'an bugi k'eyar Usman cikin kula yace.
"Kai komai baka iyaba agogo ma bazaka iya mak'alawa ba sai da taima kon tsohuwa."
Murmushi yayi yace.
"Toh Hamma Umar ai kaine ka b'atani haka komai kace bazan iyaba banda lafiya kai zaka min."
Dariya sukayi baki d'aya shiko Umar murmushi yayi daga nan suka sallami Hajjajo suka fita
suka tafi kai tsaye dicency super market suka wuce suna shiga suka yiwa Ammin su shopping
komai na buk'atan rayuwa suka had'a mata kamar yadda suka saba,
daga nan gidan su Ammin su suka nufa.
Suna isa bakin gate ko parking Hamma Umar bai k'arisa yiba,
Usman ya b'alle marfin motar cikin jin dad'i da raha ya d'an d'aga murya yana.
"Ammi ! Ammina ! Ammiiiiii ! Ina kike ne?."
Shi kuwa Hamma Umar murmushi yayi ya juya gun mai gadin ya mik'a mishi key d'in motarsa
cikin sanyi yace.
"Isah shigo da kayan cikin gida."
cikin mutuntawa Isah ya karb'a, sannan shi kuma yabi bayan Usman d'in.
Ita kuwa Ammi tunda tajiyo muryar Usman tayi wani irin murmushi mai cike da jin dad'i da
k'aunar y'ay'an nata,
ido ta lumshe tare da shak'ar kanshi turaren da ta sani na Hamma Umar ne,
dan shi kafin ya isa wuri turarenshi keyin sallama.
Kai ta jinjina tare da ture y'ar roban da ta k'wab'a lallen gargaji da nufin zatasa a k'afafun ta,
tana k'ok'ari tashi taga Usman har ya iso,
kawai sai ta koma ta zauna cikin yin dariya,
cikin happy tace.
"Lale marhabin da yaran kirki yara na gari y'an albarka abin alfaharin Ammin su."
Da sauri ya k'arisa gaban ta cikin k'aunar mahaifiyar tasu ya zauna gaban ta ,
hannu ya mik'a mata itama hannu ta mik'a mishi sukayi musabaha,
sannan ya zame gefen ta cikin lumshe ido da yana yin shogoba ya konta a hankali ya d'aura
kanshi kan cinyarta tare da sauk'e ajiyan zuciya murya a tausashe yace,
"Ammina ina sonki'