Showing 99001 words to 102000 words out of 142577 words

Chapter 34 - DA SAURAN KALLO Book Complete by Zainab.txt

Advertisement

Xayyneb   

30 Jul 2024

17497

Aliyu yace yakai ma Ummul suyi magana,
amma idan Aliyu ya kawo sai tak'i karb'a shima wani lokacin baya kawowa sai yace
tana bacci dan shima bayason damuwar ta.


Farouq nada watanni 17 ya k'ara wayo da kyau yana yawon shi ko ina sannan Ummul
ta yayeshi,
Ummul da ya Usman kuwa kullum shakuwar su k'ara k'arfi take indai yana gida bai
fitaba to suna tare a palour Nanne ko na Hajjajo, Ummul bata tab'a rasa wani abuba
dan koda yaushe Usman na cikin tarairayar ta da tambayar me take buk'ata inko ya fita
zai dawo to da tsara barta kala-kala yanzu Farouq ya cika shekara biyu har ya shiga na uku.

Wata ranar Jimmy'a da yamma Abba da Daddy suka shigo palour Hajjajo suka inda suka
sami yaran nasu dukkan su suna ta hira suna shiga Farouq yaje gaban Abba da gudu ya
taho yana oyoyo Abba,
cikin happy Abban ya bud'e hannu wan shi Farouq ya fad'a ya d'agashi sama yace,
"sarkin wasa ya akayi".
Daddy ne yayi murmushi yasa hannu ya karb'e shi tare da yace,
"zo nan in tafi dakai gidana".
wuri suka samu suka zauna bayan sun zauna ya Usman ne yafara gaida su suka amsa
sannan kowa ya mik'a tashi gaisuwar. saida suma suka gaida Hajjajo sannan Abba ya
kalli Usman cikin kulawa yace,
"Usman naji d'azu wani abokina yana waya da yaranshi yana fad'a musu ankirashi ance
anfara saida admission form na NCE a nan FCE(T) shine nace inna sameku zamuyi
shawara tunda k'anwarku tak'i maganar aure ko zaku saya mata saita fara kara?".
gyara Zama Usman yayi sannan yace,
"to Abba zamuyi shawara insha Allahu zamu sanar daku duk abinda mukayi mungode".
Daddy ya jinjina kai yace,
"to Allah yayi maku al'barka".
Dukkansu suka amsa da "amin".

sannan suka d'an tab'a hira jimawa kad'an suka tashi suka fita,
suna fita Ummul da zuciyarta tafara bugawa tunda Abba yafara magana ta mike jiki
ba kwari ta fita, Usman ma mik'ewa yayi yabi bayanta Adam kuwa ya zuba musu idanu
cike da tausayin yadda Usman d'in yake fama da soyayyar k'anwar tashi.

Shiko Usman yana shiga yasame ta zaune kan kujera yasami gefenta ya zauna a
hankali cikin tattausan lafazi
yace,
"Ummuna meyasa su Abba na fita kika taso kika baro gurin mutane kikazo nan ke
kad'ai ? kinsan bana son damuwar ki kuma banaso ki b'oyemin komai".
d'ago kai tayi tare da yin rau-rau da ido alamar zatayi kuka murya na rawa tace,
"Ya Usman wlh bana son karatun na hakura da komai a rayuwa ta zan zauna in dauwama
ina yiwa Hamma Umar addu'a,
banajin dad'in komai a rayuwa ta bani da wani sauran farin ci daya wuce inga ina yiwa
Hamma na addu'a,
dan Allah kacewa Abba bana son kara tun wanda nayi a baya ya isheni, yayi hak'uri ya
barni". tana gamawa ta kwab'e fuska zatai kuka,
Da sauri yasa hannu ya tallabo hab'arta cikin tattausan lafazi yace,
"farin cikin ki zai dawo bazamu dawwama cikin k'uncin rayuwa ba Ummuna ki bani dama ni
Usman zan dawo da farin cikin ki ta yadda Hamma na zaiyi Al'fahari dani".
lallashinta ya rink'ayi da kalamai masu taushi da sanyaya zuciya,
itako Ummul sai cigaba da zubda k'ollah take tana d'an narkewa, dakyar yasamu ta
hakura sannan yace,
"ba wanda zai kaiki makara tar anan zamuyi zaman mu ko har sai Allah ya dawo mana da
farin cikin mu?".
Dakai ta amsamai sannan ta matsoshi ta kwantar da kanta a kafad'ar shi numfa shin ta
na fita a hankali tuni Usman yafara zaucewa a hankali yakai hannu ya d'an tureta sannan
ya rumtse ido yana shafa kanshi zuwa wuyan shi yanajin kaunar ta na tsuma ko ina na
jikin shi, cikin sanyi yace,
"Allah ya d'ayyiba".
kai ta d'ago ta zura mai ido cikin murmushi tace,
"Ya Usman ina son ka".
ido ya bud'e da sauri sannan ya k'ara matsowa kusa da ita a hankali yace,
"Da gaske kina sona?".
kai ta gyad'a mai tare da kad'a harce tace,
"ehh mana ina sonka".
kai ya juya cikin k'arfin hali yace,
"Allah ya d'aiyiba nima ina sonki so na hak'ik'a,
Ummu ina sonki zan aureki mu reni Farouq da hannun mu,
ina sonki ina shawa'awar rayuwa da ke a k'ark'ashin inuwar aure bisa sunna Ummu ina sonnnn
ki zan dawo miki da farin cikin ki nima ki tallafawa rayuwa ta".
Ido ta zazzaro tare da fuska tsuke cikin zubda k'ollah murya a carke tace,

"Na shiga uku ya Usman".
sai kuma ta mik'e da sauri ta gudu d'akinta ita da Ammi,
a haka tasu hirar ta watsent a palour Nanne,
inda ita ko Nenne duk taji abin da suke cewa dan tana cikin kitchen,
shiko a nan ya zauna ya kasa tashi inda ya sametan,
sai lokacin sallah la'asar yatashi tafiya masallaci,
sai ya shiga d'akin nata dan yasan Ammi tana parlour Hajjajo,
yana shiga ya d'ago ta yasa hannu ya shafa fuskarta yakai yatsan shi kan lips d'inta ya
lumshe idanuwan shi da suka canja launi sannan ya juya ya fice tare da cewa,
"Ina son ki Ummu so irin na aure ban saniba ko nima zaki tsanene kamar Hamma sai randa na
mutu ki soni".
yana fita itema tashi tayi tashige toilet wonka takeyi tana kuka ta rasa matsayin Usman a
gareta shike tayata batun kartayi aure yau kuma shike cewa zai aureta me sunanta inta aureshi
ta auri yaya ta auri k'ani yau ya Usman ke mata zaurancen saida Hamman ta ya rasu take
sonshi a haka tayi ta kokenta, sannan ta fito dan yin Sallah.



Ranar wata lahadi Ummul na kwance a cinyar Aunty Halima datazo tun safe tanayi
mata kitso,
Aliyu ne ya shigo ya zauna gaban Ummul yace,
"Aunty Ummul Dr Bashir yazo yana palour yana jiranki, kamar bazata amsaba saida ta
d'au lokaci sannan ta ce,
"ina zuwa, ina Farouq fa?".
cikin jin dad'i Aliyu yayi y'ar dariya yace,
"ai muna ball yana ganin motar yatafi da gudu saida na rik'eshi motar ta tsaya yana
fitowa na sakeshi yatafi da gudu gunshi".
Aunty Halima ce ta d'anyi murmushi tare da cewa,
"ya ganeshi kenan?".
Sadiq ne dake kwance kan kujera yana latsa wayar shi yace,
"ai Farouq ko sau biyu kazo gidan nan a na uku sai yanuna ya ganeka,
balle Hamma Bashir da duk sati sai yazo indai yana gari".
murmushi sukayi baki d'aya sannan ita kuma Ummul ta
d'auko hijabi tasaka tafita.

zaune tasame shi a k'asan carpet yabud'e ledar da yazo da ita yana b'arewa Farouq
sweet din dayasaba kawo mishi,
sallama tai tasami guri ta zauna sannan cikin nutsuwa ta ca,
"ina wuni?".
da fara'a d'auke a fuskar shi ya d'ago kai yace,
"lafiya Ummul khair ya mutanen gida?".
Kanta a k'asa tace, "suna lafiya".

shiko Farouq cikin kici-kici yasa hannu ya k'ara d'aukan sweet d'in nashi sannan ya mik'e
cikin gwarancin sa na yarinta yace,
"Abpa Ayeeh".
gaba d'aya ya sasu dariya har Ummul saida tai d'an yi murmushi balle Dr Bashir dayaketa
kyal-kyalawa shiko cikin gudu dib-dib da kuzari yayi waje abin shi yana,
"Abppa Ayeeeh jo cuwit".
Cikin son yaron Dr Bashir ya dawo da kallonshi ga Ummul yace,
"Wai me yace ne?".
k'asa tayi da kai a hankali tace,
"cewa yayi Bah Ali". dariya yasa keyi yace,
"Aliyu zai kaiwa kenan?".
da kai ta amsamai, murmushi yayi tare da sauk'e numfashi sannan ya tashi yakoma kan
kujera ya zauna ya dai-dai ta nutsuwar shi sannan ya fuskanci Ummul cikin kulawa da
wata irin murya da shima ya rasa inda ya samota yafara magana, "Ummul khair yau
zuwana yanada banbanci da kowanne zuwa da nakeyi, sabida wannan zuwan ina tafe
da magana mai muhimmanci wadda ta dad'e a zuciyata tana hanani sukuni".
tunda ya fara magana Ummul ta tsinci kanta cikin fad'uwar gaba mai tsanani,
shiko bai gusheba yaci gaba,
"Kiyi hakuri ki daure da kisaurari kalamai na sannan kuma zan baki lokaci da zakiyi
tunani akai,
amma dan Allah Ummul kada kisa damuwa a ranki akan abinda zakiji sannan dan
Allah ki tausa shi zuciyar ki saboda kukanki yana k'onamin zuciya".
saida yad'anyi shiru kamar mai tunani sannan yace,
" Ummul ina sonki, inason kizamo uwar y'a y'ana, ina sha awar zama dake a k'ar
k'ashin inuwar aure".
Duk kalaman da yake yak'i kallon Ummul, itako tuni jikin ta ya mutu tunaninta ya tsaya
cak tanajin wani irin zafi a ranta. Katseta yayi da cewa, "kiyi tunani akan maganata zan
dawo naji amsa".
yana fad'in haka ya mik'e jiki a mace shida kanshi ya tuno abokin shi a haka ya fice,
yabarta tana share k'ollah,
yana fita a farfajiyar gidan yaga Usman da abokinshi Nura cikin jin dad'i suka fara
gaisawa anan Ummul ta fito daga palour ta wucesu tunda ta wuce Usman hankalin shi
ya koma kanta dan yadda ya ganta ya tabbatar akwai matsala dan haka sunayin
sallama da Dr Bashir ya kalli abokin shi Nuru yace, " kajirani a d'aki ina zuwa".
Bai jira amsar Nuraba ya shige cikin gidan da sauri,
A bakin k'ofar parlour Nenne ya tsaya cake Dan abinda kunnen shi yajiyo maine ya hanashi
k'arasawa ciki ya jingina jikin k'ofar yana sauraren Ummul data fad'a cinyar Aunty
Halima tana cewa,
"ku gaya musu banason kowa bazan auri kowaba bazan iyaba dan Allah kuce su
kyaleni".
Ya Sadiq dake kwance kan kujera ne ya mik'e zaune cikin b'acin rai yace, "wlh
banason wanda muna zaman mu zaizo ya tada hankalin yarinyar nan, mutane basusan

damuwar mutumba
ke kuma Ummul ai aure wajibi ne a gareki zaman shekara biyu da wata 9 ya isa haka dole kiyi
aure kam".
sai kuma ya taso ya matso inda Ummul d'in take ya d'ago kanta yace,
"kyaleshi Ummuna kiyi shiru kinji".
sannan ya mik'e zai fita Usman dake lab'e yana sauraronsu juyowa yayi da sauri
cikin k'unar zuciya yanufi b'angaren su yana tafiya da kyar.


A palour ya sami Nura da Adam suna hirar ball yayi sallama ya fad'a kan kujera ya
fidda dogon tsaki ya lumshe ido, Nuru ne dake kusa dashi ya dafa kafad'ar shi yace,
"aboki na ya a kayi ne? ". d'ago kai yayi ya kalli Nura sannan ya maida kallonshi ga
Adam daya zuba mai ido yace, "Wai dan Allah yazanyi ne mekuma yake shirin samuna wacce irin rayuwa zanyine?".
Adam cikin yanayin tausayawa d'an uwan na shi yace,
"Wai tambayoyin nan na meye haka? me a kayima?".
saida ya rik'e kirji sannan yace,
"Adam wai Dr Bashir ne yacewa Ummul yana sonta".
Adam da shima yaji bugun zuciyar shi ya k'ara k'arfi yace,
"Usman dan Allah ka ka gayawa Abba ko kuma kabarni in fad'a musu Abban kana son
Ummul Insha Allah nasan nanda wata biyu Abba zai aurama ita."
da sauri suka d'ago kai cikin sanyi dan ganin wanda ya shigo......




*Sadaukarwa ga

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login