Showing 30001 words to 33000 words out of 142577 words

Chapter 11 - TAWA TA SAME NI BOOK 1 COMPLETE DOCUMENT by Halima Abdullahi k. Mashi .txt

gashi ina bid'ar addu'arsa gashi kuma baya raye."

ganin yadda suke kukan ne jikin kowa yayi sanyi haka yasa Ya Adam ya jagoranci abokan
Hamma Umar din suka koma cikin gida a gefen baki Anty Shuwa kuwa taja k'awayen Amarya
suka tafi,
Anty Halima kuwa cikin kuka ta kamo hannun Ummul dake kuka kamar ranta zai fita sukayi cikin
gida,
haka aka watse taron,
Ammi kuwa dama tuni tayi cikin gida kai tsaye d'akin Hajjajo ta wuce tana wani irin kuka mai
karya zuciyar mutane,
Hamma Umar kuwa shida Usman suna tashi suma suka wuce d'akin Hajjajo, suna zuwa suka
zauna gaban Ammin su ita kuwa Ammin ta k'asa magana sai kuka,
Hamma Umar ne ya matsota kanshi ya d'ora kan cinyarta cikin kuka da rauni ya jawo Usman
kuma jikin shi ya rugume shi baki na rawa yace.
"Am! Ammi! Ammeee! ki dena kuka Ammi ki samin al'barka kimin Addu'a Allah ya bani ikon

cika al'k'awarin dana d'aukar wa kaina,
bani da mai tayani Addu'a bayan ke da d'an uwana Ammi kibar kuka karki sa Usman a rud'ani."
Hannunta ta dafe kanshi...




*Kuyi hak'uri da Wannan Yau bak'in ciki kamar na d'aki kaina na gama typing 1 page mai Reed
more 7 wlh garin gyara nayi delete nashi da ker nayi wannan*


By
*GARKUWA FULAni*
📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

*RUBUTACCEN AL,AMARI*

Page 1⃣3⃣

*NA*
*AYSHA ALI GARKUWA*

🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇









*K*anshi ta dafe cikin muryar kuka tace.
"Farouq Allah yayi muku albarka kai da d'an uwanka Allahu rabbi ya jibanci lamuran ka hak'ik'a
yau ina al'fahari da kai,
kuma na tabbatar yau da mahaifinku na raye zaiyi al'fahari da kai ,
domin ka cika d'a na gari d'a na hallas tabbas yau kasa farin ciki a zuk'atan iyayen rik'onku kai
da d'an uwanka domin wannan abin da kayi zai sama musu nitsuwa a zuk'atan su ta yadda
zasu samu k'arfin guiwar cewa ko bayan ransu zaka kula musu da y'ar su bisa amana da
gaskiya, naji dad'i da samun yara nagari Umar Farouq da Usmanu shehu Allah ya muku al'barka ya k'ara
muku k'aunar juna Allah ya sanya al'khairi a rayuwar Ku."

Murmushi suka rink'a yi zuk'atan su cike da farin ciki da aminci jin irin addu'oin da mahaifi yarsu
ke musu,
Hamma Umar kuwa k'ara jawo Usman yayi jikin shi ,
shi kuma kanshi ya kara kontarwa kan cinyar Ammin sun,
Hajjajo da Inna ma Addu'a sukayi tayi musu da sanya al'khairi da sa musu al'barka.

Anty Halima kuwa tunda ta kamo hannun Ummul suka koma cikin gida kai tsaye d'akin Nenne
ta wuce da ita,
tana shiga ta saki hannun Ummul taje bak'in gado ta kifa guiwowin ta a k'asa kanta ta kife kan
cinyar Nenne cikin kuka mai cike da tausayi murya a raunane baki na rawa tace.
"Nenne Hamma Umar ya bani tausayi Nenne kiga irin al'k'awarin da Hamma Umar ya d'auka a
kan Ummul Nenne sai kinga yadda Hamma Umar yake kuka cur-cur da hawayen shi ya rugume
ya Usman suna ta kuka sun bani tausayi Nenne sun tuno Abban su."

sai ta kuma d'ago kanta cikin zubda k'ollah ta kalli Ummul dake ta kuka tamkar zata amayo da
ranta cikin sanyi tace.
"Ummul ke kukan dad'i kikayi naki kukan najin dad'i ne iyayen ki na raye gaba da baya,
bawan Allah Hamma Umar shiko kukan rashin uba yakeyi domin shi yasan zafin rashin Uba dan
shi kam ya Usman Hamma Umar d'in ya meye mai gurbin mahaifin su,
Hamma Umar bawan Allah maraya duk da tarin k'iyeyyar da kike nuna masa bai hanashi yin
al'k'awarin zai rike da amana ba."

Daga nan kuma sai ta mik'e ta fice ta nufi part d'in Abban ta,
ita kuwa Ummul kuka take da bak'in ciki mai yawa a ranta a fili take gani duk an tsaneta tunda
babu ko mai lallashin ta inba Ya Usman ba kowa harara ke had'a su ganin yadda su Anty
Shuwa ke cilla mata harara yasa ta mik'e cikin kukan ta nufi part d'in Hajjajo,
a parlour ta samu su Hamma Umar d'in da ya Usman dasu Hajjajon da Ammin su,
har yanzu Hamma Umar kanshi na kife kan cinyar Ammin yana kuka k'asa-k'asa dan gaba
d'aya jikin shi da zuciyar shi Abban shi kawai suke tuno mishi a yau d'in,
shi kuwa Usman kukan Hamma Umar ne yake sashi kukan,
itama Ammi ta kasa d'aure zuciyar ta sai k'ollah dake ta bin fuskar ta,
itama Ummul nata kukan take ta wuce bedroom d'in Hajjajo kai tsaye kan gadon ta konta ta kife
kanta cikin pillow taci gaba da kuka,
ita kuwa Anty Halima a baki k'ofar parlour Abba tayi sallama cikin muryar kuka,
cikin sanyi ta shiga bayan Abba ya amsa mata sallamar , Abban ta samu shida Daddy suna
zaune sai fufun goro kusan guda 12 da katon-katon na sweet da k'oren dabino dake gaban su,
gefen Abban nata taje ta zauna cikin sanyi ta gaida su sai kuma ta fara magana cikin raunin
murya tace.
"Abba Hamma Umar!
Abba Hamma Umar da ya Usman sunata kuka sun tuno Abban su,
Abba Hamma Umar ya bani tausayin Ammin suma sai kuka takeyi,
Daddy kuje ku rarrashe su,
Hamma Umar ya bani tausayin yanata kuka ya Usman ma yana kuka."

kusan a tare Abba da Daddy suka mik'e suka fita kai tsaye parlour mahaifi yarsu Hajjajo suka
nufa Anty Halima na biye dasu a baya,
suna shiga parlour suka zauna gefen Ammi da yaranta Daddy ne ya jawo hannun Usman cikin
kula yace.
"Ya isa kukan ya isa haka habba Usman k'afa san zuciyar ka bata da cikekken lafiya."
A hankali Usman ya kalli Daddy cikin sanyi yace.
"Daddy kalli yadda Hamma Umar yake kuka ,
hawaye na bazasu bar zuba ba muddin idanun Hamma Umar na zubda k'ollah."
Abba ne ya kalli Hamma Umar d'in cikin sanyi yace.
"Farouq Kaine nake ganin kana da k'arfin zuciya sai gashi ka k'asa iya daurewa ga yadda kake
kuka kalli yadda kukanka yasa d'an uwanka yin kuka kalli mahaifiyarku yadda kuka sata a
rud'ani,
shin ka manta zuciyar d'an uwanka ne?
Farouq a yanzu ba abinda mahafinku keso daga gareku da mu da mahaifiyar mu sai
Addu'armu."
da sauri yasa hannu ya share hawaye shi cikin k'arfafa zuciyar shi yace.
"Abba na bari,
Usman kayi hak'uri ka koyi dauriya kajiko d'an uwana?."
Kai Usman ya rink'a juyawa tare da goge k'ollah,
daga nan su Abba sukayi ta musu nasiha sannan suka fita tare dasu dan jin an kira sallan
maggariba,
har sun fita gaba d'ayan su ,
sai kuma ya Usman ya juyo cikin sanyi ya shiga d'akin Hajjajo kai tsaye bak'in gadon da Ummul
ke zaune yaje ya zauna cikin sanyi ya zaro hankicif d'in shi ya mik'a mata,
bata karb'a ba sai d'ago kanta tayi ta zuba mishi ido cikin kuka tace.
"ya Usman shike nan Hamma Umar zai rabani da Mustapha har *Abadan* shike nan nayi ban
kwana da farin cikina,
ya Usman kalli al'k'awarin da Hamma Umar yayi dan tsabar mugunta ya Usman shike nan
Hamma Umar ya zame min k'arfen k'afa Ya Usman kasan ina son Mustapha gashi Hamma
Umar ya rabamu gashi Abba na ya kwace woyata shike nan ya Usman ko muryar Mustapha
baza a barni Mayo ba, ya Usman Hamma Umar ya binne min rayuwa ba Mustapha ba karatu na."
sai kuma taci gaba da kuka,
shi kuwa Usman ido ya tsura mata ,
sannan ya d'ago hannun shi ya dafe kahon zuciyar shi cikin tsura mata ido yace.
"Ummul kece sanadin bugawar zuciyata zaki kasheni ki huta ki sani idan na mutu kece sila."
cikin tsoro da mamaki ta zaro ido woje baki na rawa tace.
"Ya Usman ni kuma? ni dai? in kasheka kuma? sabida me zan kasheka?."
Kai ya jinjina mata cikin sanyi yace.
"Ehh kasheni kike son yi tunda na lura bazaki bar koke-koken nan ba,
na kuma gaya miki bana son inji kina kuka,
Kukan ki nasa zuciya ta tayi nauyi bana son kina kira min sunan Mustapha in kina ki ranshi ji
nake zuciya tana harbawa da k'arfi, kamar zata fashe."

da sauri tasa hannu ta karb'i hankicif d'in sannan ta goge k'ollah cikin rawan murya tace.
"Nayi shiru ya Usman na bar kukan ,
bana son ka mutu."
Murmushi yayi sannan yace.
"Allah ya d'aiyiba."
itama murmushi tayi sannan tace.
"Ina sonka ya Usman."
cije lips d'in shi yayi da k'arfi sannan ya juya cikin sauri yayi hanyar fita har yaje bak'in k'ofar fita
sai kuma ya tsaya cikin sanyi yace.
"Allah ya d'aiyiba,
nima ina sooon ki k'anwata Ummul."
daga nan kuma sai ya fita,
part d'in su ya nufa yana zuwa ya samu abokan Hamma Umar d'in duk sunyi al'wala shima
al'walan yayi sannan suka nufi masallaci,
bayan sunyi sallan maggariba basu dawo ba saida akayi sallan ishah sannan suka dawo gidan.

9:00 pm Hamma Umar ne da abo kanshi suke ta hira a parlour shi hira sukayi sosai cikin
shak'uwa da sabo Abdallahn Maryam ne yayi murmushi cikin tsokana ya kalli Hamma Haiydar
din Minali yace.
"Kai General Aliyu wai ina Hamma Yusuf d'in Aysha ne ban ganshi ba?."
Amadin Nadiya ne yayi murmushi tare da cewa.
"You ai Hamma Mahmoud d'in Khadija ma ban ganshi ba."
Salim d'in Tawa ne yayi murmushi tare da cewa.
"Toh sa idawa."
Abun batul kuwa murmushi yayi sannan yace.
"Mutun da matar sa ai sai adena sa musu ido."
Hamma Bashir d'in Rukayya ne yayi murmushi tare da nuna Hamma Hassan d'in Fateema
yace.
"Kaima ko zaka zillene kayi gaba da matar ka?."
Hamma Haiydar d'in Meenarl ne ya d'an yi murmushi sannan yace.
"Kai Aisar d'in Bintu sai dariya kawai kake kuma kaima anjima za'a nemeka a rasa zaka tafi gun
matar ka."
Al'ameen d'in Fauziyya ya mik'e cikin raha yace .
"Nima nayi gaba."
Ridwan d'in Zakiya kuwa shima sai murmushi yake yana woya da zakiyarsa Ahmad ana Muslim
kuma shima dariya kawai yake.

Suna cikin hira da dariyar su Hamma Yusuf ya shigo hannun shi rik'e da robobin inabi dasu
Apple da reke sai kwakwa da dibino,
ajiye su yayi a tsaki yarsu ya zauna gefen Abuturrab cikin murmushi ya kalli Aisar yace.
"Ga inabi nan kusha ,
Aysha ce ta kirani tace in seyo mata shine kuma na kawo muku ku d'ana."
dariya sosai Abban Rukky pinky yayi yace.

"Aysha ta kiraka ko kai ka kirata."
murmushi Hamma Umar d'in Ummul yayi tare da cewa,
" Ku dai kuci kar kuyi tone -tone."
dariya sukayi baki d'ayan su sannan sukaci gaba da hirarsu,
suna hira suna cin lodin fruits din da Hamma Yusuf ya kawo musu,
can sai kuma Hamma Umar d'in ya mike cikin sauri Key din motar Aisar ya zara sannan ya fice
da sauri yana fita yaje ya lodowa Ummul fruits d'in da yacin gaba d'aya sannan ya dawo gida,
Parlour nashi ya shiga inda ya samu su Abu har yanzu suna hira,
Amadi ne ya kalleshi cikin tsokana yace.
"Kaima Ummul tayi kira ne kaje ko?."
murmushi kawai Hamma Umar d'in yayi tare da juya kai sannan ya zaro woyar shi auta Aliyu ya
kira,
Jim kad'an Aliyu ya shigo rik'e da hannun Hannah yarin yar Hamma Haiydar da Meenarl,
robobin fruits d'in Hamma Umar ya mik'a wa Aliyu cikin yana yin aike yace.
"Gashi ka kaiwa Ummul kace abokin nane ya seyo mana mukaci shiyasa itama na seyo mata
nata."
"Toh" Aliyu yace sannan ya karb'i robobin yayi cikin gida,
kai tsaye parlour Hajjajo ya nufa, yana zuwa ko ya samu Ummul d'in tana zaune fuska duk a
jeme ,
a hankali ya ajiye mata fruits d'in cikin kula yace.
"Anty Ummul sarkin son zak'i gashi wai inji Hamma Umar wai abokin shi ne ya seyo sukaci
shine kema ya seyo miki naki."
ido ta d'ago cikin tsuke fuska ta buga mishi harara sannan tace .
"Bana so ka meyar mai da abunshi."
Kallon ta yayi cikin sanyi yace.
"Kai Anty Ummul kinfa san ba kyau meda hannun kyauta."
K'afa tasa ta ture robobin,
Shi kuwa Aliyu hannu yasa ya d'auki robaa inabi guda d'aya ya fice tare da cewa.
" ni dai zanci."
Hajjajo kuwa tire ta d'auko ta tattara fruits d'in duka ta lodasu kan tiren cikin yin hamdala ,
ta rink'a nuna wa mutane tana cewa.
"Ku gani Ku shida Farouq ya fara cika al'k'awarin d'aya d'aukar wa kanshi."
suko sauran mata sai sunyi ta yabawa halin Hamma Umar d'in,
ita kuwa Ummul ji take kamar taje ta shak'e shi ya mutu ta huta da bak'in cikin sa,
kamar wasa Hajjajo ta dage tana bin d'aki-d'aki tana nuna musu abinda Umar ya aiko wa
Ummul harsu abba sai da taje ta nuna musu,
Ummul kuwa haka ta kwana cikin k'unci shiko Hamma Umar yana tare da abokan shi..

Washe gari misalin k'arfe 11:00 Am dai-dai
dubban al'umma suka shaida daurin auren Umar Ibrahim Umar Shuwa tare da Rabi'atu
Hassan Umar Shuwa Ummul kenan,
d'aurin auren d'aya samu halartan manya-manyan bak'i kama daga gwamnan Yobe Ibrahim
gaidam dan Hamma Umar shine doctor dake duba lafiyar gwamnan nasu na jihar Yobe tare da

sarkin su,
bayan an gama d'aurin auren ya Usman ne yazo ya rugume Hamma Umar d'in cikin happy
yace.
"Ina cin farin ciki Yau Allah ya nuna min auren d'an uwana Allah ya tayaka rik'o."
murmushi Hamma Umar yayi tare da cewa.
" Amin."
daga nan abokan shi suka rink'a yi mishi musabaha suna tayashi murna,
cikin zugar mutanen dake tayashi muryar ne yaga Mustapha ya mik'a mai hannu cikin sanyi
sukayi musabaha sannan Mustapha yace.
"Hamma Umar inayi maka fatan al'khairi a Rayuwar auren ka kaida Ummul ina taya ka farin ciki
a matsayinna na d'an uwanka musulmi."
sai kuma muryar shi ta fara rawa sai hawaye cur-cur a fuskar Mustapha,
cikin tausayawa Hamma Umar ya rugume shi a hankali yace.
"Mustapha ka gafar ceni na shiga rayuwar ka kai da Ummul Amman bayina bane Mustapha
wannan rubutaccen al'amari ne bani da niyar rabaku,
su Abba ne suka had'a aurena da Ummul,
ku gafar ceni Mustapha domin na zame muku bak'in jakada a Rayuwar ku Mustapha ka gafar
ceni."
Cikin rawan murya Mustapha yace.
"Hamma Umar na yarda da kaddar ta fatana ka rik'e min Ummul bisa amana."
kara rugume shi yayi sannan ya sake shi cikin sanyi Mustapha ya juya ya tafi,
shiko Hamma Umar haka yayi ta sallama da abokan shi dan duk yaune zasu tafi tunda biki ya
kare gashi kuma abokan duk y'an nesane,
Hamma Haiydar har Kaduna
zai koma Hamma Yusuf kuwa Taraba Hamma Mahmoud Adamawa Yola Hamma Hassan
Gombe yayin da Hamma bashin kuwa zai koma kano,
haka Hamma Umar da ya Usman suka tsaya a harabar gidan nasu suna ta ban kwana da
bak'on nasu,
bayan duk sun tafi ne,
saura baki matama dake cikin gida duk sun tattafi sai y'an kad'an da suka rege.


Da daddare bayan Anyi Sallan maggariba da ishah Abba ya Tara family d'in shi harda Ammi da
Inna da sauran mutanen gidan bayan sun zazzauna Daddy ya bud'e musu taron da Addu'a ,
sannan daga nan Abba kuma yayita musu nasiha mai ratsa jiki da zuciya,
Ummul kuwa zuwa yanzu kuka ya zame mata jiki.

Bayan Abba ya gama musu nasihar ne ya mik'e tsawon sa gaban Ummul yaje ya tsaya cikin
bada umurni yace.
"Ummul taso kizo."
mik'ewa tayi cikin zubda k'ollah,
shi kuwa Abba hannun ta ya kama yaja har gaman Hamma Umar d'in cikin kula ya kamo
hannun Umar d'in ya tsaida shi sannan cikin girma da jagoranci yasa hannun Ummul cikin tafin

hannun Umar d'in a hankali yace.
"Farouq ga matar ka rik'e hannun ta ku tafi gidan Ku."
kallon Abban yayi cikin sanyi sannan ya manner tafin hannun shi ya rumtse hannun Ummul d'in
kamar yadda Abba ya umur ceshi,
shi kuwa Abba Ummul ya kalla cikin tsuke fuska yace.
"Kibi mijin ki ku tafi Allah ya baku zaman lafiya."
"Amin Amin." sauran mutanen dake wurin suka amsa,
shi kuwa Hamma Umar hannun Ummul d'in ya jawo cikin yin k'asa da guiwowin shi suka
durk'usa gaban Abba a hankali yace.
"Abba nagode Allah ya k'ara zumunci."
"Amin Amin."
Abba yace tare da shafa Kansu ,
sannan shi kuma Hamma Umar ya sake jan hannun Ummul gaban Daddy ya mishi godiya a
haka ya rink'a jan Ummul suna zagaya wa har suka iso gaban Ammi da Nenne kamar kullum
Hamma Umar hannun shi d'aya yasa ya ciro hularshi sannan ya jawo ummul suka durk'usa a
gaban su cikin sanyi yace. "Ammi ! Nenne ! nagode Allah ya saka muku da al'khairi."
dafa kanshi Ammi tayi kamar ko yaushe sannan tace.
"Allah ya sanya haske a wannan Aure naku Allah ya taya ka rik'o Allah yayi muku al'barka."
haka tayi ta musu Addu'a sannan tayiwa Abba ma godiya da kyautar y'ar shi d'aya bawa d'an ta.

Shi kuwa Umar yana rik'e da hannun Ummul yaje ya rugume ya Usman cikin sanyi da k'aunar
k'anin nashi murya na rawa yace.
"Kamin al'k'awarin zaka kula da kanka, kasha maganin ka karkaci duk wani abu green kaji
B'iyaye na,
nanda kwana 5 Kaima zaka koma gidana inci gaba da kula da kai."
murmushi Usman yayi cikin yanayin shi na abin dariya yace.
"Nayi ma al'k'awarin zan kula da kaina kafin nima na auru matata taci gaba da kula dani,
kaima ka kula da matarka Allah ya d'aiyiba."

gaba d'ayansu dariya sukayi sannan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login