Showing 3001 words to 6000 words out of 23305 words
Chapter 2 - KARYA DA GASKIYA ORG.txt littafin Yaki writing by Mansur Usman Sufi
wata irin zazzaƙar murya ya ce "ya kai wannan dattijo kayi sani cewa ba ni da masaniyar abin da ya wakana tsakanin zakanyar da gimbiya ba sai dai kawai na jiyo kururuwar ta ne kuma na fahimci tana buƙatar taimako shine na kawo mata ɗauki,
Game da tambayarka ta farko kuwa ita ce suna na jarumi MUHASSIN IBN SHA'ABAN na fito ne daga nahiyar larabawan yamma a wani birni da ake kira da Madinatul-yusra, domin yaɗa addini na na bautar Ubangijin talikai a faɗin duniya.
Koda jarumi Muhassin yazo dai-dai nan azancen shi sai dakarun dake wajen suka cika da matuƙar mamaki ainun jin Muhassin ya ambaci Ubangijin talikai.
Boka kaddad kuwa sai ya murtuke fuska tamkar an aiko mishi da SAƙON MUTUWA ya dubi Muhassin babu annuri a tare da shi cikin kakkausar murya ya ce "naji dukkan bayanin ka kuma na fahimci cewa ba kayi yunƙurin cutar da sarauniyar kyawawa ba, saboda haka sai ka kama gaban ka bamu da buƙatar wani dogon jawabi",
Har Jarumi Muhassin ya buɗi baki da nufin ya sake furta wani abu sai boka kaddad ya ɗaga mishi hannu yana nuni da ya tafi ya basu waje.
Amma sai aka ga gimbiya Aslaima ta miƙe tsaye tsam! Tamkar babu wani rauni a tare da ita ta dubi Muhassin fuskantarta cike da wani irin ƙayataccen murmushi mai ɗimauta zuciyar duk wani ɗa namiji, cikin tattausan murmushi mai daɗi tamkar sarewa ta ce "ya kai wannan saurayin ma'abocin kwarjini da taimako ka yi sani cewa kai ne mutum na farko da taɓa ceton rayuwata a lokacin da nake gaɓar mutuwa, duk da kasancewar a halin yanzu ina ɗauke da cutar makanta amma idanuwana suna iya ganin ka, saboda ina neman wata alfarma a wajen ka da ka biyo ni izuwa gagarumar tafiyar mu ta nemo mini maganin lalurata, na yi maka alkawarin bayan mun samu nasara zan sanya mahaifina ya baka duk wani abu da kake buƙata da ya danganci sarauta ko dukiya.
Koda gimbiya tazo nan azancen ta sai gaba ɗaya jama'ar dake wajen suka cika da matuƙar mamaki, daga can sai ya ci gaba da cewa "idan har ka na tantama akan abin da na faɗa bari na bayyana maka surar ka da tufafin dake jikinka.
Nan take Aslaima ya shiga bayanin sura da tufafin Muhassin. Tana kammalawa mamaki ya turnuƙe kowa kuma suka fahimci cewa Aslaima kallon haƙiƙa ta yi mishi ba labari ta ji ba.
Nan fa mamaki ya turnuƙe kowa domin tun da gimbiya ta makance koda aljani bata taɓa gani ba, amma ga shi yanzu tana iya ganin bil'adama, shin mene ne ya sanya idanun nata iya jarumi Muhassin suke gani? Ko kuwa ƙarfin sihirin shi ne ya sanya hakan?
Amsar tambayoyin da suka kasa bawa kansu kenan.
Shi kuwa boka kaddad koda ya ji abin da gimbiya ta furta sai zuciyarshi ta buga da ƙarfi tsoro ya kama shi ainun, ya ce a ran shi shin ya aka yi gimbiya take iya ganin Muhassin bayan cewa na wa'adin sihirin da na yiwa idanunta bai ƙare ba, haƙiƙa akwai lauje cikin naɗi, amsar tambayar da ya kasa bawa kanshi kenan.
Shi kuwa Jarumi Muhassin koda ya ji gimbiya ta ce tana iya ganin shi nan take ya fahimci cewa matsalar aiki ne sihiri, domin kuwa da makanta da gaskiya ba zai yiwu ta iya ganin shi ba.
Ana cikin wannan hali ne ya lura cewa gimbiya na satar kallo shi wanda ke nuna alamun so da ƙauna, nan take ya ji zuciyarshi ta buga da ƙarfi a karo na farko ya ji wani abu ya ɗar su a ran shi wata 'ya mace ta ƙayatar da shi.
Muhassin ya buɗi baki cikin murmushi mai taushi har fararen haƙoranshi suka bayyana ya dubi gimbiya ya ce "Ya ma'abociyar kyawu ki yi sani cewa idan har zan yi maku rakiya a wannan tafiya to akwai bana buƙatar wani lada face sharaɗi guda shine ke da mahaifinki za ku bayar da gaskiya ga Ubangijina, ku daina bautar gumaka da dodanni har abada".
Koda jin wannan batu sai gimbiya ta ja gwauron numfashi ta yi ajiyar zuciya sannan ta ce "Na amince da wannan sharaɗi naka, kuma na tabbata cewa Ubangijin da ya baka nasarar tseratar da rayuwata daga sharrin zakanya zai baka nasara a wannan tafiya. Sai dai na manta ban faɗa maka cewa a wannan tafiya muna da shugaba wato boka kaddad, kuma shi ne ya san wajen da zamu samu abin da muka fito nema, saboda dukkan wani umarni muna karɓa ne daga gare shi"
Koda gimbiya ta zo nan a zancen ta sai ta juya ta yi taku ɗaya, take kuyangi suka yi mata jagora domin komawa zuwa sansanin da aka yada zango, take boka kaddad ya rufa masu baya fuskarshi a murtuke har gyatsine take yi, dakaru na biye da shi jarumi Muhassin ne a ƙarshe, 'yar gajeriyar tafiya aka yi aka iso izuwa sansanin kowa ya kunna kai izuwa cikin tantinsa, shi kuwa jarumi Muhassin sai ya koma gefe ya yi alwala ya haye bisa kan wani faffaɗan dutse ya fuskanci alƙibila ya fara sallah.
Wannan shi ne abin da ya wakana da su boka kaddad akan hanyar su ta nemo maganin makantar gimbiya Aslaima, wato tekun Baharul-imfal domin ɗauko ALLON TSAFI a cikin masifaffen kada.
***
Lokacin da aka garƙame da azababban yaƙi tsakanin rundunar sarki Madsur da ta shugaban 'yan fashin duniya sadauki Fitinatul-Amir bisa jagorancin sadauki Huzlaif. Sai yaƙin ya zamo abin tsoro kuma tashin hankali domin ɓangarorin biyu sun wanzu suna kaiwa juna sara da suka cikin matuƙar zafin nama JURIYA DA BAJINTA, nan fa ƙarar karafniyar ƙarafa, haniniyar dawakai haɗe da ihu da kururuwar MAZAJE ta cika dodon kunne, sararin samaniya ta yi duhu tamkar dare biyu ya haɗu waje guda,
Wohoho! Haƙiƙa maza sune maganin maza, idan ka ji an ce ga mugu na ɓarna bai haɗu da mugu ba ne, kuma KARON MAZA sai GWARAZAN JIYA da suka sha JININ SADAUKAI a artabun GOGA SHA FAMA, inda ace mutum yana wannan waje lokacin da sassan jikkunan bil'adama ke shawagi a sama, JINI DA ƘASA suka cakuɗu waje guda, sai ya rantse cewa YAKIN DUNIYA ne ya taso domin hatta dawakan abokan gaba hari suke kaiwa junun su.
A ɓangaren sadauki Huzlaif kuwa duk inda ya sanya a gaba sai dai ka ga abokan gaba suna zubewa ƙasa matattu tamkar yana karkaɗe busassun ganyayyakin bishiya a lokacin hunturu. Haƙiƙa Huzlaif ya cika SARKIN SADAUKAI domin da ace mutum zai ga yadda yake yaƙin babu alamun gajiya a tare da shi, sai ya rantse cewa jikinshi na ƙarfe ne ba jini da tsoka ba, a wasu lokutan har da ƙafa make abokan gaba yake yana sanarwa kan shi hanya.
A ɓangaren sarki Madsur kuwa ya zamto tamkar ANNOBA ƊARI tsakanin dakarun Fitinatul-Amir duk inda ya sanya gaba sai ka ga gawarwaki na zubewa ƙasa, a wasu lokutan sai ka ga ya taka kawunan abokan gaba ya sanya KAIFIN TAKOBI yana sare kafaɗunsu suna zubewa ƙasa tamkar ruɓaɓɓiyar kabewa. Kai wasu lokutan ma badakare yake janyo wa daga kan dokin shi ya take mishi wuya ya sheƙa barzahu, ko ya gabza mishi wawan naushi a wuya ya jefar da gawarshi gefe guda.
BABI NA BIYAR
Lokacin da sarki Madsur da sadauki Huzlaif suka ga irin muguwar ɓarnar da suke yiwa junan su, sai zukatansu suka kama tafarfasa tamkar za su ƙone, domin hakan sai kowannen su ya ruga izuwa kan ɗan uwanshi yana mangare dakarun dake gaban shi domin samarwa da kan shi hanya.
Lokacin da suka iso daf da juna sai suka taru juna aka ruguntsume da azababban yaƙi mai matuƙar muni daban tsoro, suna artabun ne cikin zafin nama JURIYA DA BAJINTA ta gaban kwatance, duk sa'adda makamansu suka haɗu da juna sai kaga tartsatsin wuta ya tashi gami da ƙara mara daɗin saurare. Sai da GWARAZAN JARUMAN suka shafe tsawon rabin sa'a suna wannan ɗauki ba daɗi har makamansu suka lalace suka yi jifa da su duka cire waɗansu sabbi a jikkunansu, suka sake kacame da sabon artabu da ya fi na ɗazu tare da canza salon faɗan su.
Ana cikin wannan GUMURZU ne kowannen su ya kaiwa abokin gwamin shi hari a fuska, cikin nasara suka yanki juna akan kumatu jini ya yi tsartuwa. Cikin zafin nama suka yagi wani baƙin yanki a tufafinsu suka ɗaure raunin domin tsayar da jini, sannan suka ja da baya kamar taku huɗu suka tsaya cak! Suna cirko-cirko suna haki tamkar waɗansu zakaru.
A lokaci guda tamkar haɗin baki suka sake yin kukan kura suka afkawa juna, kaico! Hakika KARON MAZA abin tsoro da tashin hankali, lokacin da jaruman biyu suka fara wannan sabon artabu a karo na uku sai abin ya yi tsamari yazamana cewa a wannan lokaci sun yiwa junan su miyagun raunuka jini na zuba a jikkunansu, ma'ana an yi KARE JINI BIRI JINI jiri na ɗibar su, ana cikin wannan hali ne suka zube ƙasa magashiyan numfashin su na fita saman-sama.
Lokacin da tawagar rundunonin biyu suka ga halin da jagororin su ke ciki sai aka tsayar da yaƙi suka ruga izuwa gare su, aka ɗauke su kowannen su ya durfafi sansanin sa.
Wannan shi ne abin da ya faru tsakanin dakarun sarki Madsur da ta sadauki Huzlaif shugaban tawagar dakarun sarkin 'yan fashin duniya.
Lokacin da ma'aji Kulairu ya durfafi ƙofar fita daga cikin gidan sarauta dakaru na take mashi baya, bayan ya samu nasarar hallaka wannan hadimi mai ɗauke da sura irin ta waziri Yazid, kuma ya yi umarni an shiga da sarki Nu'umanu izuwa turakarshi domin ba shi taimakon gaggawa sakamakon sukar takobin da hadimin ya yi mishi.
Sai suka ci-gaba da ratsa saƙo da lungu na gidan suka hallaka dakarun sumame. Lokacin da suka shiga gari sai ƙarin waɗansu dakarun suka rufa masu baya, suna masu ƙwalla kabbara da ƙarfi suka tari abokan gaba aka ruguntsume da azababban yaƙi.
Sa'adda mata,yara da tsofaffi suka ji gari ya kaure da kabbarar dakarun musulunci sai suka shiga addu'a suna kai kukan su wajen Ubangijin Musulunci akan ya bawa MUJAHIDAI RINJAYE. Al'amarin da ya jefa tsoro a zukatan dakarun sumame kenan.
Duk inda Kulairu ya sanya a gaba sai ka ga dakaru na zubewa ƙasa matattu tamkar yana karkaɗe busassun ganyayyakin bishiya a lokacin hunturu.
A ɓangaren dabarun sumame kuwa duk inda waziri Yazid da sarki Rakibu suka sanya a gaba sai dai ka ga dakarun musulunci na zube ƙasa, lokacin da waziri Yazid ya fahimci cewa idan aka cigaba da wannan artabu a haka dakarun musulunci za su samu nasarar murƙushe su, sai kawai ya shafi wani gurun tsafi a damtsenshi yana mai nuna sarki Rakibu da sarkin yaƙi Lauzar da yatsanshi na hagu take suka ɓace ɓat! Tamkar ba su taɓa wanzuwa ba.
Sa'adda sa'a ɗaya ta shuɗe a dai-dai wannan lokaci ne dakarun musulunci suka samu galaba akan dakarun sumame, nan fa gari ya kaure da koke-koken yara da mata, kaico! Komai rashin imanin mutum idan ya ga yadda yara ke rungume da gawarwakin mahaifansu suna rusa kuka dole ya kamu da matuƙar tausayin su, har ƙwalla ta cika masa idanu, babu abin da zai ɗimauta mutum face irin mugun kisan da aka yiwa jama'a waɗansu an farke cikinsu tumbinsu ya fito waje, wasu an sare kawunan su wasunsu ƙafafu da hannuwa abin babu kyawun gani.
***
Koda ficewar hadimi Masnur daga tantin sai sarki Lamsarul-Azlam ya runtse idanuwanshi ya karanto waɗansu ɗalasimai, yana gama rufe bakinshi sai wani narkeken aljani ya bayyana a gare shi, aljanin yakasance mummuna mai kwarjini da ban tsoro, yana da ƙwala-ƙwalan idanu masu girma tamkar gwanda, hancinshi a takure yake kofofin sirara tamkar ba da su ne yake shaƙar iska ba, bakinshi makeke ne mai kama da bakin rijiya, a tsakiyar kanshi yana da dauƙe da wani ƙaho irin na ɓauna, gwiɓin hammatarshi yana ɗauke da waɗansu fuka-fukai guda huɗu irin na jemage,
Hakika komai dakewar zuciyar jarumi idan ya yi arba da wannan aljani dole ya ɗimauce.
Aljanin ya zube ƙasa ya kwashi gaisuwa, sarki ya dube shi cikin kakkausar murya ya ce "yakai Husubul-luzwar ka yi sani cewa bakomai ne ya sanya na kira nan ba sai domin ina so ka tafi izuwa sansanin dakarun musulunci ka ɗauko mini sarki Rayyan a raye cikin ƙoshin lafiya, ka kawo shi izuwa gare ni"
Koda jin wannan batu sai Husubul-luzwar ya buɗi baki cikin kakkausar murya mai kama da kukan jaki ya ce "An gama ya shugabana amma kar ka manta cewa akwai wani sirri da sarki Rayyan da jama'ar shi ke amfani da shi wanda matukar ka kusance su sai komai naka ya lalace, sannan kar ka manta cewa wannan shine aiki na ƙarshe da zan yi na samu 'yanci daga ƘANGIN BAUTA a ƙarƙashin ka",
Koda jin wannan batu daga bakin Husubul-luzwar sai sarki Lamsarul-Azlam ya dube shi ya ce "kar ka bawa maza kunya mana kaine fa ANNOBA ƊARI mai saukar da gajimaren musifa, magajin GAWUTACCIYA kake mai shanye JININ SADAUKAI, SARKIN SADAUKAI kake duk wanda ya ja da kai zai faɗa TURBAR AJALI"
Lokacin da sarki ya zo nan a kirarin sai Husubul-luzwar ya kama tsuma yana kyarma, ganin jikinshi ya mimmiƙe ya buɗi ya ce "kwantar da hankalinka ya mai duniya na rantse da gemun kakana boka Luzwar sai na kawo maka sarki Rayyan cikin ƙoshin lafiya".
Yana gama faɗin hakan ya bugi ƙasa da hannunshi ɗaya ya ɓace ɓat! Tamkar bai taɓa wanzuwa ba, kawai sai sarki Lamsarul-Azlam ya bushe da dariyar mugunta sai da ya yi ta ishe shi sannan ya ƙwallawa sarkin yaƙin shi kira bayan ya bayyana gare shi ya zube ƙasa ya kwashi gaisuwa sai ya dube shi ya ce "ya dirkar birnin Darul-Ashmar ina so ka tafi izuwa masarauta ka ƙaro mana dakarun yaƙi mafiya ƙwarewa a harbin kibiya ka tabbatar ka sanya a cikin duhuwar bishiyun dajin dake dai-dai wajen da zamu fafatawa a da abokan gaba, za su amfani ne a lokacin da za mu gwabza domin za su yiwa abokan gaba MAMAYAR BAZATO".
Koda jin wannan umarni sai sarkin yaƙi ya ce "an gama ya shugabana".
Yana gama faɗin hakan ya juya ya fice daga cikin tantin ya kama dokinshi ya haye ya sakar mishi linzami ya sukwane shi ya durfafi hanyar fita daga sassanin.
Wannan shi ne abin da ya wakana a sansanin sarki Lamsarul-Azlam.
BABI NA SHIDA
Koda ɓacewar makiyar sai sadauki Fitinatul-Amir ya taƙarƙare ya kurma wawan ihu wanda ya ɗimauta duk wata halitta dake fadar, jama'a suka shiga guje-guje gami da ifice-ificen tsira da rayuka, domin rabon da Fitinatul-Amir ya yi wannan kururuwa yau tsawon shekaru ashirin tun ranar mutuwar Mahaifiyarshi.
Sai da ya shafe tsawon daƙiƙa talatin a cikin wannan hali sannan daga bisani ya murtuke fuska tamkar an aiko mishi da SAƙON MUTUWA ya ɗauko madaidaicin madubin tsafi a cikin aljihun rigarshi ya shafe shi da hannunshi na hagu yana mai runtse idanuwanshi gami da karanta waɗansu ɗalasiman tsafi, yana gama rufe bakinshi sai ga taswirar mikiyar ta bayyana a sararin samaniya ɗauke da Rusayyat, Usaiba mai hatimin takobi tare da Hairat, tana tsala gudu tamkar giftawar tauraruwa mai wutsiya,
Koda ganin wannan al'amari sai kawai ya ƙwallawa 'yan majalisar shi kira cikin hanzari suka fito daga maɓuyar su jikkunansu na ƙyarma! Kaifin ɗayan su ya furta wani abu ya nuna su da ɗan yatsanshi na hagu nan take shi da su suka bayyana akan wata jibgegiyar mikiya mai kwarjini daban tsoro, cikin hanzari mikiyar ta tashi zuwa sama ta ratsa rufin fadar ta ɓace ɓat! a sararin samaniya.
***
Al'amarin wannan mikiya kuwa da ta ɗauki Rusayyat uwar shugaban 'yan fashin duniya, yaro Usaiba tare 'yar uwarshi Hairat, sai ta yi wanzu tana ratsa giza-gizai babu sassauci. Duk wannan tafiya da ake yi su Usaiba ba su san halin da ake ciki ba domin suna cikin halin suma su duka ukun.
Lokacin da sa'a ɗaya ta shuɗe a wannan lokaci ne ta iso wani ƙasaitaccen daji domin haka sai kawai ta saki fuka-fukanta ta yi ƙasa luhhhh! Ta sauka a turba a daf da wata ƙorama mai ɗauke da ruwa garai-garai, kawai sai ta gicciya gadon bayanta ta sauke su yaro Usaiba, sannan ta kafa bakinta a ƙoromar ta guntsi ruwa ta fesa masu, Rusayyat ce ta fara farfaɗowa ta hanyar buɗe idanuwanta, sannan yaro Usaiba yana mai jan dogon gwauron numfashi, Hairat ce a ƙarshe tana mai motsa ƙafafuwanta, nan take kowannen su ya yunƙura domin ya miƙe zauna amma sai hakan ya gagara bisa dole kowanne ya haƙura zukatansu na bugawa cike da matuƙar tsoro da firgici.
Ana cikin wannan hali ne kwatsam sai aka ji wani abu mai nauyi ya sauka a daf da hanyar shigowa dajin, ba wani ba ne face sadauki Fitinatul-Amir tare da 'yan majalisar shi guda sha biyu zaune a bisa kan wannan mikiya.
Da yake tazarar dake tsakanin su bata huce taku talatin ba dai aka fara kallon-kallo na tsawon daƙiƙa goma, daga can wannan mikiyar da ta ceci rayuwar su Usaiba ta yi girgiza take ta rikiɗa izuwa surar wata kyakkyawar budurwa.
Budurwar takasance mai matsakaici jiki mai launin fata wankan tarwaɗa tana sanye da tufafi na fatun dabbobin daji da suka kama jikinta har surar kyawun ƙirjinta ya bayyana a tsaye suke ƙyam! Basu rankwafa ba tamkar nunanniyar gwanda, tana da sharɓa-sharɓan cinyoyi, ƙugunta daga gaba a tsuke yake ta baya kuma ya yi tudu inda za a sanya tuffa zata ita zama daram, dara-daran idanuwanta farare ƙyal da baƙin cikinsu ya kasance siɗik mai kwarji da haiba haɗi da yalwataccen gashin kanta da ya zuba har ƙasan kwankwasonta sune abubuwan da suka sake tona asirin kyawun ta.
Haƙiƙa babu wani ɗa namiji mai hankali da zai tozali da wannan kyakkyawar sura face