Showing 6001 words to 9000 words out of 10311 words

Chapter 3 - AUREN DOLE BOOK COMPLETE BY 'YAR MUTAN DIKKAWA.txt

19 Nov 2024

3605

akeyi,Hakan gefen Yaya yaseer da Raudhat,Qawarta soyayya ta dunke,A dalilin zuwanda takeyi inda yaseera,An sa ranar auren su dukkan su alokaci daya."
[1/10, 11:05 AM] Nordin: *NABEELA DIKKO*






SHAFI NA BIYAR












"A yau jumma'a Dubban jama'a suka shaida da daurin auren Alaramma Najibullah Usman,Da Yaseera Aminu sai Muh'd yaseer Aminu da Raudhat mas'ud ,Wanda aka daura a masallacin Makka da ke sabon garin kanta Argungu,Daurin auren yasa mu halarta manyan malamman Addini da jami'an gwamnati,Da sarakunan gargajiya da ke ciki da wajen jihar kebbi."








"Gefen Amare ba laifi domin gagarumar walima,Aka shirya ta mata Zalla,Domin taya su murnar aure,Haka da dare an sake baje kolin wa'azi a masallacin,Sannan aka kai amare dakin su."Bayan sun sha nasihohi da dama awurin magabata,Yaseera na unguwar lowcost,yayinda yaseer ke zaune a shagari quarters Argungu."Dukkansu sunyi gini na zamani yayinda iyayen suka baje basirar su da iyawar su wurin sanya albarkatun daki,Raudhat da yaseera kowaccen su gida saidai masha Allah."










"Fadin irin farin cikin da iyayen Yaseera da najibullah suka samu Kansu aciki baima taso ba."Saboda suna alfahari da yaran su yadda sukayi biyayya akan hadin su,fatan su Allah ya basu zaman lafiya da zuriya dayyaba."




















**********Lamarin Asma'u sai dai Addu'ah domin ta koma yau ciwo gobe lafiya,ga bakin cikin rayuwar da take agidan Alh.kalle."Gashi yanzu tayi nauyi domin cikinta ya tsofa sosai."










"Alh.kalle zaman hakuri yake da Asma'u,Yaki sakinta ne saboda kakanta(Baba mallam)Yasan shi sarai da masifa,kuma irin su mutanen daaa,ba'ayi masu garaje mayarda mutim kunkuru ko wani abu mai muni,ba komai ne ba,Agun su."saboda haka yake shakkun sakinta, amma ya dauki aniyar walakanta ta, har sai tagaji ta bar gidan da kanta!"sai shirye shiryen sa aure yakeyi,Ba ruwansa da matansa!"








"Watarana Asma'u tasamu ta fita da kyar,taje gidan su a hanyarta ta dawowa ta hadu da kamilu!"








"Cikin firgici ta ce kamilu!!!!!ne...."






"Da mamaki ya waigo!Domin sam bai ganeta ba!tayi baqi ta rame!ga qaton ciki!!!!"Ko a mafarki ba zai taba manta fuskar da yafi kauna ba,Arayuwar sa!!!"








"Asma'u!!!!?Kece nike gani kodai idona ne!Kemin gizo!?"Kamilu ya ce a razane."






"Hawayen da take kokarin hadiyewa ne ya zubo mata a fuska!!!Ta ce nice kamilu daga ina!?"Na ganka da jakar kaya!?Kamilu shi ne ka tafi ka barni akai min *AUREN DOLE!*"






"Innalillahi wa'inna ilaihir raju'un yace tare da sakin jakar kayansa ya durkushe agabanta yana kuka!!!!"






"Itama kuka take har cikin ranta!Abinda ke cikinta sai da ya motsa!"Tashin hankali ne ya bayyana afuskarta!"Cikin kuka tace kamilu kai min magana ko zanji sanyi araina,wallahi ina sonka!!....."










"Dakata!!!!Asma'u kina so na kika zauna gidan wani da sunan *AUREN DOLE!* Ina can ina haramar dawowa in aureki ashe ke har cikine da ke!"Asma'u ki cuceni!!!"Nayi dana sanin dawowata garin nan yau,domin nayi tozali da abinda zai zama silar mutuwata!"kamilu ya qarashe zancen yana kokarin tashi domin barin wurin da kayansa..."








"Tafiya ya fara...A hankali ta rike jakarsa tace kamilu...ina son kasan cewa har gobe kana raina!"Kuma wallahi ban auri kalle ba!Sai domin in fito injira dawowarka na aureka,bayan shekara daya kamar yadda mukayi alkawari!Sai dai kaddara ta riga fata!domin yaki ya sakeni har Allah ya hadani da cikinsa!!!"Amma wallahi ban sonsa,ban taba kaunarsa ba!Kamilu ka yarda ni ka aminche da soyayyata na dauki alqawarin zan rabu da shi nan ba da jimawa ba!!!!!!"Asma u tace cikin kuka!Tana kallon kamilu da yayi mur kamar bashi baah."








"Lura da yaran unguwar sun fara taruwa suna kallonsu yasa,Asma'u sakin jakar kamilu tana share hawaye!"Wani kallon tsana yayi mata yace ba komai Asma'u nagode,Amma kisani sonki da kaunarki tare da kishinki zai zamo ajalina!!!"Ficewa yayi abinsa yana hawaye!"Asma'u ma kuka tayi har tagaji kana ta lallaba da kafafunwanta da sukayi sanyi,rai babu dadi,Tare da daukar alqawarin sai tabar gidan Alh.kalle ko da dadi ko da ciwo..."












"Rayuwar Najibullah da yaseera rayuwa ce,mai dadi cike da fahimtar juna,suna mutunta junan su sosai!"Auren su kamar auren soyayya,suna zaune lafiya cikin tufin Asirin Allah.''








"Hankalin Muh'd yaseer da Raudhat ya kwanta domin kowa ya samu abinda yakeso."Raudhat yarinya ce mai kirki,ta fito daga gidan mutunci,iyayenta basada makosa."Shiyasa tasu tazo daya da yaseera,har yanzu suna kawancen su tare da girmama juna."
















"Kamilu da kyar ya isa kofar gidan su saboda jiri! Da ke dibansa,A daddafe yaqaraso kofar dakin Mahaifiyarsa malkah!"Jin abu tiiiim...A kofar dakinta,yasa ta fitou da sauri!"Ganin kamilu akwance dafe da zuciya yasa ta razana!"Tasalima tayi kana tace"me zan gani!Kamilu!?"Yaushe ka dawo!?"Meke faruwa na shiga uku!"Kuka takeyi tare da tallafo shi!"Ruwan randa ta doubo tana bashi yana shaaa,Ajiyar zuciya yayi!yana kallon innarsa dake kuka!!!!"










"Shima kuka yakeyi!yace inna kuyi hakuri mutuwa!zanyi ciwon so zai kasheni!!!"Inna Asma'u nagani yanzu da ciki!" *AUREN DOLE!* da akayi mata yayi albarka!"Ina caan na gudu kuma na dawo akanta!"Amma ashe ita tama manta dani...."Kamilu yace yana nishi...cike da wuya!"








"Malkah tace kamilu ko ita naji labarin baso take ba!"Zaune kawai take domin ba yadda zatayi,na tabbata har gobe Asma'u kai takeso!"Amma aure ya rabaku,kayi hakuri kabarwa Allah kamilu,Allah yabaka wacce ta fita,cikin sigar rarrashi inna malka ta ida maganar."








"Kokarin tashi yayi,tare da taimakonta,ya isa dakin sa,kurar da dattin da yayine yasa Inna tace suje dakinta,kwantawa yayi,ita kuma abincin zaici tayi kokarin sama,masa."












"Asma'u tana zuwa jugum tayi adaki tana Neman mafita,tashi tayi tare da shirya kayanta tsaf a akwatina,Daman ka'idarsa ne duk dare sai ya yada zango adakinta,shiyasa ta shirya komai nata,yadda ta tsara!"










"Misalin karfe 11:30 dare ya diro dakin,yana kada kafarsa ya subule suuuuuu sai qasa titif!!!!!!"kokarin tashi yayi da kyar!domin har jiri saida yagani,tare da rike kugunsa da ya bugu!!!"Sai dai yana mikewa ya dauki kafarsa daya yasake subulewa ya fadi kaaakaaas!!!!!"ya bugu da gefen gadonta nan take,goshinsa ya fashe,Da karfi yace wayyo!!!!!Wayyo!!!!Wash!!!!!Ina kike Asma'u!!!?"tare da dafe kai!!!!"








"Asma'u da ke kwance kan gado ta lafe!,tana kyalkyala dariya,ta motsa tare da hamma kamar agigin bacci ta tashi!!!"Ta ce lafiya!?"








"Cikin yanayin ciwo yace subulewa nayi na fadi taimaka min in tashi!!"






"Mtwssss!!!wallahi bazan iya baah Allah ma yasa ka mutu in huta!!!"Asma'u tace








"Alhaji yace "Dan Allah."






"Tashi tayi tadauko tsumma ta goge duk ruwan omo da karkashin da ta lema a qasan tayils din, sannan ta koma gado tayi kwanciyarta cike da murna."Tace wallahi banajin tausayin,mugu!Azzalumi!Yadda baka jin tsoron Allah ba,kasa aka tilasta ni aurenka adole,Bazan ji kunyar ramawa ba!Ina son ka sakeni Dan Wanda nike kauna,matashin yaro kamilu ya dawo!"












"Kuka da nishi yake,"Ya ce ashe bakida kirki Asma'u!To anqi asake kin!"Marar mutunci!"Meye amfanin zamanki agidana!!!!"Sai nafadawa iyayenki rashin mutuncin da kikayi min."Alhaji yace yana murza goshinsa da ya taso ya kabe!"








"Kanka akeji yanzu saki kuma ba fashi!Ko kuma ka hadu da danasani,Saboda banson ganinka arayuwata!"Asma'u tace tare da juya masa baya!"








"Cikin bacin rai!"Da zafyn nama ya tashi yana jan kafarsa ransa abace har wurin gadon ya sharara mata mari,ya ce!Asma'u daman ina ragamiki ne saboda Mallam Buba amma na gane bakida tarbiya,ni sa'anki ne da zaki min rashin mutunci,To ubanki zanci sannan in koraki gidan Ku,Na sakeki saki uku!Daman dalili nike nema!!!"Dukanta ya dinga yi,cikin zafyn Nama ta tureshi,tace tafi nono fari,Allah na gode ma yanxu basai gobe ba!"Zan tafi gidanmu...."Sake dukanta yayi abaki!saida ya fashe!Aykuwa cikin bacin rai ta ture shi,saboda taga zai illata ta,da ciki!"Abinka da jiki yafara mayyanta suluuuuu!Sai qasa ya fadi,Nan take kafafunsa da hannu suka kwange!"






"Mayafinta ta dauka!Tsalke shi tayi ta fita da akwatinta!harabar ba motsin kowa,bacci suke,Kofar fita tayi,cikin sa'a ta bude kofar ta fita abinta,Misalin sha biyu na dare,kafafun mutane sun dauke,sai yan kadan haka,ababen hawa sun rage,"A hakan Asma'u tajanyo akwatinta cikin duhun dare!"Karnuka na mata haushi!!!"A daddafe ta kawo kofar gidan makera."Tana tafiya tana kuka! Amma faah na farinciki takeyi."Kauren gidan ta tura daga ciki Wanda aka rufe da qaton turmi,tayi sa'a turmin ya fad'i tuiiii..."






"Shigowa tayi da akwatinta da kyar!Saboda ta gaji!"Hasken fitilar Baba mallam ce,ta haskake mata ido,






"Cikin daga murya yace"Ashe!Waye nan..."Yana kokarin fitowa daga cikin gidan sauron da yake kwance atsakar gidan."








"Gabanta ya fadi raaas!!!"Ta ce ni ce!"








''Ke wa!!!"






"Ma'u ce Baba mallam."








"Da hanzari ya qaraso wurinta yana zare ido,wasu abu ya karanto ya tofa mata,sannan ya taba ta,yace eh,lalle tabbas mutim ce,ba aljana,ba daga gidan uban wa kike!!!?






"Hawayenta ta goge,tace Kaka,Alhajine ya dakeni kuma ya sakeni saki uku...Wai domin zai kara aure, kuma yace ko na haihu bayason D'an ya bar mana...."Ta qarashe zancen tana kuka!"Hijab dinta duk jini bakinta yayi suntum.."








"Baba malam,Ya hasala!"Sai huci yakeyi!"Ya ce'kwal uba!ni kalle zaiyiwa rashin mutunci!yayi inda akeyi!Allah ya kaimu gobe lafiya!"Muje ki shige lunguku!"Da karfi ya fara buga kofar gidan yana cewa kai Isuhu!!!"Duk mazan gidan sai da suka fito waje,Ganin Kaka da Ma'u yasa su,tsayawa domin sun san tatsuniyar gizo bata wuce koki!"Yusuf ne ya bude kofar yace Baba lafiya!"






"Ina lafiya mutumen banzan caan ne ya turo ma'u cikin dare nan harda tsarabar saki,abin bakin ciki babu gyara!"






"Duk ranshi ya sosu amma yaki nunawa yace Allah ya sauwaqa shige daga ciki Asma'u kiyi hakuri da kaddara!"








"Tana shiga mamanta lami ta rungumeta suna kuka!"




"Kaka juyawa yayi ya koma yana masifa!"Tare da tsinewa Alhaji kalle."






"Matan gidan sai murna sukeyi,tare da cewa kwadayi mabudin wahala,A haka dai kowa ya koma bacci wasu na murna wasu kuma na bakin ciki."










********Wayewar garin Assabar ya zamewa Asma'u mafi munin rana arayuwarta!"Saboda tunda safe labarin mutuwar kamilu saurayinta ya bazu agarin,Wanda ya mutu sanadin shan maganin bera dalilin soyayyar sahibar Asma'u."










"Tashin hankalin da Asma'u ta shiga aciki baya,misaltuwa domin wayewar gari take jira taje gidansu,ta shaida masa mutuwar aurenta,Babban burinta da zarar ta haihu ta auri kamilu!Amma wai ya kashe kansa sanadinta!!!"Kuka Asma'u tayi Wanda akarshe ya haifar da daukewar shedarta ta fadi sumammiya!!!"Lami sai kuka!takeyi yayinda Yusuf ke kokarin yayyafa mata ruwa!"Baba malam ya rude hawaye yakeyi!"Tare da danasani domin tun safe mutane ke zaginsa,Wai ya raba masoya yayiwa yarinya *AUREN DOLE!* har gashi kamilu ya mutu!"Yanzu ga Asma'u ta fadi ba rai!"Duk da baya bari akai yaran gidan sa asibiti, dole yabari aka wuce da Asma'u asibiti babba."Saboda ciwonta ya tsananta!"












"Cikin adaidaita sahu suka wuce da ita, Asibitin tare da Baba mallam,Lami da yusuf ,Hankalin su atashe!Suna zuwa aka yanka mata kati,sannan aka bata gado,Likita ya dubata daga karshe dakin haihuwa aka wuce da ita,domin lokacin haihuwarta yayi kusa bacin rai!ya tadota ga jininta ya hau!"A hakan likitoci da ungozuma suka dinga kulawa da Asma'u."Babanta Yusuf sai kai,kawo,yake!Lami tayi zaune tare da tagumi tana jiran hukuncin ubangiji!"Baba mallam ko zaune yake yana tunani aransa ko yaje gidan Alh.kalle domin jin ba'asi saboda sai ya ci mutimcinsa,sai ya nuna masa ba irin jikokinsa ake cin amana ba!!!"








"Tafiya sukeyi da sauri domin isa dakin sayarda magani da ke cikin asibiti!!!"Ido sunyi musu jajur,sai suka hango lami....Da sauri Sahura takaraso wurints,uwani da yaransu maza biyu da mata uku na biye!"








"Sahura ta ce "Lami Ina Asma'u muna nemanta!"






"Hawayen da ke mata zuba ta goge,tare da nuna musu kofar dakin haihuwa!Tace tana ciki!"








"Uwani tace"tirkashi Allah ya sauwaqe,Ashe bakusan meke faruwa ba!Mu fa bamu ma san bata gidan ba wallahi!!!"








"Baba mallam,da Yusuf ne suka qaraso wurin bayan sun dawo daga masallaci,ganin su sukayi cirko-cirko."






"Lami tace"meyafaru sahura,uwani kusanar da ni,kuna nufin bakusan dukan da Kalle yayiwa Asma'u ba!!?"






"Duka!Sahura tace tare da Buga kirjinta da zaro ido,Wallahi bamu San ya daketa!Mu dai mun tashi!bamuji motsin su ba har lokacin fitar shi kasuwa,yayi bai fito ba,har sha daya,shiyasa muka leqa dakin bamuga Asma'u ba!kwance mukasame shi harshe ya kare!yana magana bamu fahimta,Shiyasa muka kira yaran gidan da abokinsa aka kawo shi nan,yanzu hakan likita yace mana!!!!Kuka!ne ya kwace sahura saboda bacin rai,majina ta sharce!"Tace wai Alhaji ya hadu da bugun zuciya mai karfi,kuma ya fadi dalilin hakan yasamu mutuwar barin jiki!"Jininsa ya buga sosai,."Yanzu hakan magani ne zamu sayo ashago na ganki,Amma wallahi lami mu Neman Asma'u mukeyi ta fada mana yadda sukayi da Alhaji domin shi harshensa ya kare ba ajin maganarsa!!!"Sahura ta ida zancen tana hawaye!"








"Baba malam,da ke tsaye yana sauraron sahura yace "Ai kalle bai gama gani ba!"In banda yana azzalumi yarinya da ciki ka daketa!Kai mata sakin uku!Ta Yaya Allah zai barshi ya kwana lafiya da wannan hakki!!"






"Uwani tace Mallam saki fa,innalillahi wa innailaihir raju'un!!!"Mukam bamu da labari!"Har muna zargin Asma'u!!!"






"Asma'u batada laifi inaga bayan sun samu hatsaniyar ya korata gida acikin Daren zuciyarsa ta buga akan bacin rai!"Gashi itama sanadin Bacin rai!Ya haifar mata nakuda,kuma jinintaa,hau,sai dai Addu'ah Allah yabasu lafiya!!"Lami tace."








"Ameen sukace dukkan su banda Baba malam,da yayi tsaki ya zauna yana jan tasbahar shi,Jikansa madou yazo da hanzari hannunsa,dauke da langa,ya mikawa kakan Nsu,Ya ce Gashi nan inji malam tankari,"ya ce,abata tasha awanke mata fuska,"








"Madallah Baba mallsm,yace tare da ba lami,taje takai rubutun taimakon haihuwa aba Asma'u tasha."








"Amsa tayi ta shige dakin tare da sallama da su sahura da ke kokarin wucewa,Yusuf ko abinda duniya ya dameshi fatan shi Asmau ta sauka lafiya."
[1/10, 11:05 AM] Nordin: SHAFI NA SHIDDA










****************


"Alh.kalle agadon Asibiti,sai dai Addu'a!Saboda ciwonsa ya tsananta,Komai baya iya yi sai an masa!duk gefen jikinsa na dama ya mutu!!!"Iyalansa sun sha kuka har sun godewa Allah,Gashi baya kula yan uwansa shiyasa suka juya masa baya!"Ba mai zuwa gidansa ko yanzu asibitin ba Wanda ya zo!"












"Cikin hutuncin ubangiji bayan tsawon awowin da Asma u ta dauka tana nakuda,Tasha wuya da azaba!A karshe ta haiho 'yartah qatuwa,wacce nauyinta da ya wuce misali,Bayan likitoci sun gama gyara Asma'u da yartah,Dakin hutawa aka wuce da su."Su uwani sun zo sun duba yarinyar cikin murna da godiyar Allah Asma u ta sauka lafiya."








"Bayan mintici gab da magariba qannan lami suka bayyana a asibitin da su Gwaggo husai da Mariya suna farin ciki agefe suna tausayin Asma'u tare da zagin Alh.kalle,anan sukaji labarin shima bayada lafiya."








"Mutuwar Kamilu,ta kasance abin cecekuce a cikin gari!Kowa da abinda yake fad'a,Wanda a haqiqanin gaskiya,Maganin bera ya sayo a kanti,ya sha saboda ciwon so da kaunar Asma'u wacce aka raba shi da ita akai mata *AUREN DOLE* da Alh.Kalle,"




"Innar Kamilu tayi kuka kamar ranta zai fita,yaro mai hankali kamar kamilu ace ya kashe kanshi saboda macce,Abin ya kona mata rai!"Saboda ba halinsa bane!"Kowa ya sanyi da nutsuwa!"Wannan kaddarar ta afka masa."Rarrashinta yayyensa da 'yan uwanta keyi!yan gulma ko sunzo daukar rahoto!"Nan ne wata makociyar su Balki ta ce"Allah dai ya sauwaqa ya Baku hakuri malkah,Abin nan shi kadai ake yi kuma duk fa wannan masifa akan *AUREN DOLE* Ku duba nan shekaranjiya wata yarinya ta sanya hetur ajiki tasa ashana ta kone kanta akan *AUREN DOLE* da iyayenta zasuyi mata shi kuma saurayin yana jin labari ya kashe Kansa!!!




"Ke balki yaushe wannan labarin ya faru wata mata ta tambaya cike da mamaki."






"Wacce ke kusa ga balki tace wallahi ko nan garin ga anyi shi kun mance yarinyar nan Asabe yar gidan dillaliya...da tasha guba akan za'ayi mata *AUREN DOLE* tanada Wanda take so,shima faah ance yanada sana'arsa da yasamu labari,duk kudaden dinkinsa gina yayi ya turbudesu aqasa sannan shima ya sha guba ya mutu!sai lahira."






Kuka inna malka ta fasa tace kaicoh!yanxu shima kamilu za a fara jera shi acikin masu kisa Kansu akan soyayyah Allah ka yafe mai ya Allah!!!!"








"Kiyi hakuri malkah,wannan kaddara ce!kowa da tashi!haka Allah ya nufa da shi!Domin kowa na yabonsa, Allah dai ya yafe masa!"Inji qanwar ta."




"Ameen sauran jama"ar wurin sukace."Nan dai suka cigaba da hirar su da yan gulmace gulmace da yake yanzu an mayarda gidan ta'aziyya kamar gidan buki,Yanzu zaman ba yada wani amfani,ba asamu lada ba akwashe zunubi,Hattara mata!!!!"













"Baba mallam ne,Ahanyarsa ta dawowa daga asibiti Wanda da kyar dansa Yusuf ya rarrashe shi,akan yadawo gida ya huta,tunda ma'u tana bacci,kuma tasamu sauki har zuwa gobe, ganin dare yayi."yana shigowa unguwarsu wato Allugu,majalisin su ya biya cikin sa'a yasamu su mallsm Iro,da dauda suna fira!"Da Sallama Malam Buba,Ya isa tare da musayar gaisuwa da su malam Iro."








Mallam Iro,Ya ce lafiya yau duk bamu ganka ba!?"






"Ina lafiya!Ma'u ce kwance a asibiti!"






"Ma'u ko mijinta Alh.Kalle!?Shi mukaji labarin ya fadi rai a hannun Allah!"inji malam iro.








"Mallam Buba,Ya ce"Haihuwa ce ma'u tayi shi kuma ance ya hado da mutuwar barin jiki!"






"Malam Dauda dake gefe zaune ya ce "Allah ya sauwaqa."






''Ameen,Dauda inji Baba mallam."






"Mallam iro ya kalli amininsa cike da damuwa yace "Ashe yaron nan kamilu ya rasu,kanada labarin maganin bera yasha akan jikar ka ma'u da kace har abada shi da ita!"






"Haka naji ana fadi agari shi ya mutu kafiri ba wani ba!Allah ya qaddaro Ma'u ba matarsa bace haukar banza ce sukeyi,kuma duk Wanda yace ni ko jikata ne sanadi Allah ya isa!"Mallam Buba yace ahasale!!!"






"Allah ya bamu hakuri Buba kasan ita duniya daman budurwar wawace!"Inji Dauda.








"Kaga ni daman tahowa niyyi na ganku mu gaisa daga asibiti nake,zan wuce gida na kwanta duk jikina ciwo yake!!"sai gobe idan Allah ya kaimu






"To Buba agaida gida Allah ya huce gajiya ya basu lafiya!"Inji Iro






"Ameen,Buba yace kana ya nufi gidansa."














**************
"Najibullah da amaryarsa Yaseera ne,suka kawowa iyayen su ziyara,Amarya an sha kyau cikin shiga ta alfarma,fuskarta sai haske da sheki take cike da annuri,kyaunta ya qara fita tayi jiki gwanin Sha'Awa,Da zarar kayi tozali da yaseera da najibullah zaka fahimci akwai zaman lafiya fahimtar juna da kwanciyar hankali arayuwarsu,Shi kanshi Najibullah,ya qara cika,kwarjini ya wadace shi,Hankalinsu akwance."






"Bayan sun gaisa da iyayen su sun sanya masu albarka cike da farin ciki,cike da murna suka nufi gidansu yaseera nan ma sukayi sa'a kowa na gidan,A babban falon suka same su har yaseer da matarsa Raudhat tana cin Dan wake batada lafiya ta kamu sai kwadayi da sangarta take ma su Umma,suka ma sai rarrashinta ake komai takeso shi ake mata."








"Bayan sun gaisa umma ta kira Abbu shima ya fito,Gaisawa sukayi sunyi farin cikin ganin yaseera a kamile,batada wata damuwa,nan fa najibullah da yaseer suka samu wurin fira,Umma madafa ta nufa domin shirya musu abinci,Abbu ma kanti ya wuce domin sayo masu kayan masarufi azuciyarsa yana godewa Allah akan zabin da yayiwa yarsa,Yaseera tuni yawunta ya tsinke ganin qawarta bata sammata Dan waken ba,yasa ta dauke kwanon duka tayi hanyar madafa tana ci tana dariya."








"Bayanta Raudhat tabi tana mitar ta bata kayanta ba dandane."






"Yaseera tace "nasan ke kade ce mai cikin,to nima ina da lalurar kwadayi."






"Umma suka samu tana daura sanwa,Kallon su tayi tana murmushi tace"toupha kun fara ko!?"Shin ke yaseera bakisan batada lafiya ba!?"Dan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login