Showing 9001 words to 10311 words out of 10311 words

Chapter 4 - AUREN DOLE BOOK COMPLETE BY 'YAR MUTAN DIKKAWA.txt

19 Nov 2024

3606

Allah ki daina wahaladda ita, ki bata Dan wakenta duk kin kusa cinye mata abu,naga dai yanxu yayarki ce ba qawa ba,to raini na meye!?"








"Raudat tayi dariya tace yawwa ummana gaya mata"






"Dariya yaseera tayi tace''Yanzu Umma,akan dan waken yaya babba ake min hakan!"Nima fa ina son sa,kuma ta ci fa,Amma ba komai nima zance surukar tawa tayi min,sai ma yafi naku dadi!"




"Munji Raudat,tace tana yiwa yaseera gwalou,




"Nan suka hada hannu suna taya Umma girkin faten tsakin masara da kayan lambu."A lokacin ne ma umma ta fahimci ko yaseerarta ta kamu saboda yawan rufe hanci ba qamshin komai takeso ba da zubarda yawo,Ta ce yaseera kenan kema sai ahankali!?"Sunkuyar da kanta tayi cike da jin kunya."




"Umma tace lalle zan qara yiwa Abbu albishir na biyu kenan,Allah ya saukeku lafiya yabaku zuriya dayyaba ya qarou arziki da farin ciki arayuwar ku,Tabbas muna alfahari da samun Ku amatsayin yaranmu,Allah yayi muku Albarka."








"Ameen,Umma sukace dukkan cike da jin dadin kalamanta,sannan suka cigaba da ayyukan su."






_Allah Sarki,Hakan rayuwar Duniya,take yadda duk ka dauketa da sauki,ko wuya,sai tazo maka ahakan,Zabin iyaye ba aibu ba ne,idan har kayi dace da zabi nagari,Hadisi ne ingantacce,Annabi Muh'd (S.A.W) yana cewa "yardar Allah tana tare da yardar iyaye,haka fushin Allah yana tare da na iyaye"Shiyasa aduk lokacin da iyaye suka baka umurni,to ka umurnin matsawar ba sabon ubangiji ba ne,Domin babu d'a 'a ga abokin halitta wurin sabawa Allah."Saboda hakan mummunan umurni kawai iyayenka zasu saka aikatawa,ka girgiza,musu koshi acikin sigar rarrashi da nasiha,Babu auren Dole,Domin Hakkin iyaye ne su zabawa yaran su maza nagari masu ilimi,mazan da suka yadda da addinin su,da kuma nasabar su tsakani da Allah.Ba domin kwadayi ko buri ba,Saboda wajibi ne suyiwa yaransu Adalci."_




_Abin lura anan duk lokacin da D'a ya bi umurnin iyayensa sai yaga haske arayuwarsa sannan aduk lokacin D'a yake baqantawa iyayensa sai duk al'amuransa su jagule!"Ita Tarbiyya abu ne mai Kyau,arayuwa muyi kokari mu kasance yara nagari wadan da duniya zata yaba!"Kuma iyaye suyi alfahari su,Duk abinda kayi khairan ko sharran kada ka manta yana bibiyar rayuwarka da zuriyarka,Auren zumunchi,Auren Abota,Auren Hadi da sauran su duk sune aka rikede aka mayar *AUREN DOLE!* Saboda da wuya asamu dukkan yaran nason junan su,Daman karshen wuya sai dadi,kuma dogaro ga Allah jari ne,Kunga yadda Yaseera da mijinta najibullah suka kasance abin alfahari ga iyayen su,suka samu jarin rayuwa da haske mai daurewa arayuwarsu dalilin biyayya,Allah yasa mudace Ameen._












*********Tunda Asma'u ta dawo hayyacin ta,take kuka har yanxu takasa hakura da mutuwar kamilu!"'yan uwa da dangi sai hakuri suke bata."






"Bayan kwana biyu aka sallameta suka dawo gida!"Sai dai sabon ciwon da ya bayyana agareta bata iya riqe fitsari ko da aka koma asibitin ciwon yoyon fitsari ya kamata aiki akai mata tare da bata magani!"A hakan ta cigaba da fama da lalurar,Bacin rai da suke ciki itada iyayenta baya misaltuwa,






"Kishiyoyinta sunzo duba yarinya,Da diyan Alhaji da ke jin haushinta domin aganinsu itace sanadin ciwon mahaifin su,Da kyar da rarrashi suka zo gidan su Asma'u,"








"Abokin Alh.kalle ya kawo ma yarinya kaya Asma'u zanen atamfa uku,da rago ayanka ma yarinya."Duk acikin kudaden Alh.kalle da ke kwance asibiti babu bakin magana."Gashi yaran sa uku maza suka sako yana kwancen ba lafiya yanzu hakan suna nan zaman gida,mutim dayan ma nata na garaje!"Ga yammata biyu ba mazan aure!"Banda nadama tare da danasani ba abinda ake hangowa acikin idanuwansa da ke zubar da hawaye ba dare ba rana."






_"Daman ance idan zaka gina ramin mugunta....."Duk abinda kayiwa Dan wani sai anyiwa naka!"Kayi kokari ka Gina rayuwarka da ta iyalanka akan turbar gaskiya sai kaga sakamako mai kyau,Idan zakayi kayi Dan Allah haka idan zaka aikata kayi Dan Allah,Kasance mai Sara kana duban bakin gatari!"_












"Ranar suna yarinya ta ci sunan (Anna) wato Amina sunan kakar Asma'u Wanda mahaifinta Yusuf yayiwa innarsa takwara!"Duk jama'ar gidan sunji labarin Alh.kalle ya saki Asma'u yanzu kuma ta haihu ta gama iddah."






"Mallam Buba ya tausayawa rayuwar da ma'u ke ciki ga raino ga fama da cutar da ke damunta,Yayi kuka da nadama aganinsa kamar shine sanadi!"Saidai ana cigaba da nema mata maganin asibiti Dana gargajiya."










"Bayan wata daya abubuwa da dama sun faru,Wanda akarshe mallam buba yayi kokarin kashe duk wata fitina da ta kunno kai agidan makera,da gulma tayi yawa acikinsa,ya hada kan iyalansa duka komai ya zama tarihi,Kuma yace''Daga Asma'u ba zaya qara tilasta Iowa *AUREN DOLE!* ba sai dai da kashedin duk Wanda za a kawowa to akawo mai kirki da ilimi."Idan akasamu sabanin hakan bazai aminta ba!"








"watarana da safe mallam Buba ya fita majalisar su, malam Dauda ya samu shi kadai zaune a teburi yana shan kunu,da kosai,da yake yanayin sanyi ne,hantsi na rasa jikinsa,Bayan sun gaisa ne,Malam Buba,ya rokeshi akan ya yafe masa duk abinda yake masa,Dan Allah yayi hskuri!saboda ada can baya ya kullace shi,kamar yana bakin cikinsa,sai yanzu ya gane!kuransa na tilastawa Asma'u auren da bataso domin gashi akarshe abin baiyiwa kowa dadi
ba!"na tabbata kai mai sona ne,domin masoyinka kadai ke gayamaka gaskiya!"








"Murmushi malam Dauda yayi yace komai ya wuce malam Buba daman naso ace ka fahimce ni amma giyar kudaden da Alh. Kalle ke baka,ta bugeka bakaji baka gani sai yanzu ta sakeka,bayan wasa takarewa Dan kada!!"




"Shi *AUREN DOLE* Da kake gani mallam Buba akan gina shi ne abisa tilasta yaro auren Wanda bayaso kamar yadda kayiwa Ma'u!"Sannan mafi yawan lokuta akan samu banbamcin ra'ayi ko shekaru masu yawa tsakanin ita yarinyar da Wanda aka tilasta mata aure."kamar Alh.kalle mai shekaru sittin da ma'u mai shekaru sha bakwai warin yarsa ta kusan biyar,Sannan son abin duniya shine son dukiya gaba da soyayya,irin wannan aure ana yinsa domin tsammanin asamu dukiya,ko hanyar samunta,Yanzu mallam Buba kaga duk abinda kasamu ka Tara adalilin auren ma'u yanzu yaqare gurin nema mata magani!"Meye amfanin badi ba rai!!"






"A ganina *DALILIN da ke sa AUREN DOLE!*


*sune idan akayi la'akari da iyayen yaro ko mijin suna da nasaba.*


*Anayinsa domin kasancewar yaro jarumi.*


*Anayinsa Dan kara dankon zumunci ko abota.*


*Anayinsa domin kwadayi da son abin duniya!*




*Anayinsa domin rashin Sabin hakkin 'ya'ya.*




*A karshe anayinsa idan anga yarinya tafara lalacewa.*




"Mallam Buba anan ni nasan cewa kaima kasani Alh.kalle kowa yasan cewa ba'san asalin su ba!Taho nataho ne!"Sannan baida mutunci,auri saki yake!Kuma kasan ya tsofewa ma'u sosai,Ance hadda sallah bata dame shi ba!"Amma ka hadashi da yarinya kamila mai kirki wacce dubban mutane sun yaba da hankalinta,ka rabata da Wanda takeso yake sonta!"




"Wallahi Dauda na tuba!"Yanzu meye mafita!?"Malam Buba ya tambaya cikin damuwa!"






"Malam Dauda yace *"MAFITA* daya ce shi ne Mallam Buba


*Adinga yin Aure domin Allah.*




*Asan Hukunce-Hukuncen Aure.*




*Ladabtar da mata kafin aure*




*Sannan Adaina tilastawa 'ya'ya Auren Dole!*




"Kaga yin hakan shine mafita!"Buba




"Tabbas haka ne nagode Dauda kuma daga yanzu nayi karatun ta nutsu!"Domin ga ma'u nan da ciwon da bamusan raner warakarsa ba!"inji malam Buba yana share kwallah!!"






"Allah ya sauwaqa!zanje na karbo kekana wurin tanko mai faci!Iska nakai asaka min tun jiya da dare,malam Dauda yace yana kokarin tafiya!"




"To nagode!Dauda sai ka dawo,malam Buba yace,nan ya cigaba da zama shi kadai yana nazarin zantukan Dauda."








"Bayan wani lokaci Asma'u ta warke harda Ameena ta yaye tayi wayonta,wacce tuni mahaifinta Alh.kalle ya amsa kiran Allah."Asma'u har tayi aurenta da wani Jamilu duk da auren soyayya ne tayi da shi amma zaman hakuri takeyi agidansa!"Nan taga izina domin auren Marigayi kalle,tace auren dole ne!"Gashi yanzu tayi na soyayya da Jamilu bawani dadi takeji ba!"Sai dai hakuri,Tabbas kowane aure,"Aure ne addu'ar nagari shiyafi dacewa ga kowacce mace!"




_Hattara mata da maza masu kokarin hallaka kan su,kashe Kansu,shiga duniya duk akan *AUREN DOLE!* ya kamata kuyi karatun ta nutsu kuji tsoron Allah Ku gujewa sabawa Allah,Ku daina bijirewa umurnin iyaye,matukar kuna son ganin haske da cigaba arayuwar Ku."Wannan shi ake kira da "JIRWAYE NE!MAI KAMAR WANKA,SAi naga Kuma ai gyara kayanka ba sauke mu raba ba!"Amma fa tun rana gini ran zane! Haka komai Nisan jifa qasa zai dawo!ALLAH YAYI MANA JAGORA AMIN._










*_TAMAT BII HAMDILLAH._*

2
3
4

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login