Showing 6001 words to 9000 words out of 163596 words
 cewa  t... 
a matukar tsawa ce ta daga masa hannu ta hanyar tadakar dashi  "please  stop  stop doing that fu'ad "don't dare to do that to me "me kake nufi  da nuna kanka da kakeyi kana min magana irin haka kmr kai da wata yarinyar cikinka duk ma me akayi daka d'auki zafi hk? 
"gaskiya bana son irin haka kad'ai na min domin yana maseefar 'bata min rai har naji brain dina ya fara craking ka daina dan bana bukata ... 
"even if you want to chastise me, not not in the presence of a woman .. 
"you are a disappointment woman to me me'ad, "wallahi nayi danasani aurenki arayuwata kwata kwata baki cancaci zama uwa arayuwarki.....
rai 'bace nurse tak'ara gyarawa NASREEN  kwanciya  tare da lullu'be mata rabin jikinta ,sannan tasoma kokarin karasowa inda suke zaune "madam wai me  ya faru haka kuke hayaniya.. ..?
"ihunku na dustub  din yarinyar nan ,gsky bama bukatar yadda kuke kokarin hana yarinyar samun natsuwar datake bukata,dan haka kuje doctor nasan ganinku ...
me'ad ta juyo ta kalli nurse tana yatsin fuska sannan tace "kiyi hkr  ba yin kaina bane tunzira zuciyata akayi.
  ta juyo ahankali gefen da fuad yake zaune "honey kaje doctor nasan ganinka..
bud'e bakinsa yayi cike da matsanancin mamakinta  km at the same time yana dubanta.. 
"ya ka bud'e baki kana kallona ko bakaji abinda nurse ta fad'a  mana bane cewar doctor nasan ganinka.. 
"what ?
"idan ni naje gurin doctor ke fa ,zaman me zakiyi  ?
a matukar tsorace itama ta bud'e baki tana dubansa domin bata tsamacin jin haka daga garesa ba.. 
"i have been here since morning you go and see the doctor ...
"honey what do you mean by you go.. you go ? 
tayi mgnr a fusace tana zabga masa uwar harara,
"  yanzu idan muje gurin doctor yace za'a siyawa yarinyarmu magani ni kake expecting zanje ko me   ?
 "da kake wani cewa you go , kai   zaman me zakayi idan ni naje?
",karka manta wannan bangaren hakinka ne  tunda NASREEN ba shegiya bace kaine kayi  silar zuwanta duniya..
"can you imagine  what you are saying? 
"kai kai wallahi kwata kwata ba laifinki bane.. laifina ne da banzabawa yarinyata uwa ta Gari abin alfaharinah va, jifa abinda yake fitowa daga bakinki.. "ke yanzu baki ji kunyar abinda kike fad'a min ba? 
"dan Allah dan annabi ya issheni hk ... kacika min kunne da maganganunka marasa dadi i think bani kad'ai na haifi NASREEN  ba tunda karigada karigani xuwa ,karigani kenan .. 
Ya tsurawa karamin bakinta idanunsa yana kallonta cike da matsanancin takaicinta Yana girgiza kai.. 
nurse dake tsaye tazama tamkar picture agabansu tana dubansu  ta d'an waiga taga har lokacin NASREEN bacci take, ta juyo ta fuskancesu sosai kana tace "kunga ku daina jayayya akan wannan matsalar  gabadayanku doctor yace yana son gani dan kuje office din doctor yana jiranku. 
ransu a'bace suka mike atare  batare da kowanensu ya dubi d'an uwansa ba, domin kuwa cike suke da  tsantsar jin haushin juna ,ita me'ad najin haushin fa'ud akan insult dinta dayayi agaban nurse ,yayinda shima zuciyarsa ke tattare da bakinciki abinda tayi masa na yana fad'a tana fad'a kuma agaban nurse, bugu da kari rasa tilon diyarsa dayaso yi  adalilin sakacinta na  rashin d'aukar wayarta," yanzu da wani abu yasamu yarinyar su "me zatace masa? 
"yasara wace irin mata yake  aure data fi bawa aikinta mahimmanci akan diyar cikinta dashi karon kanshi, a tun sanda ya aureta har zuwa  lokacin data haifar masa NASREEN  bai da kwamciyar hankali, kasancewar aikinta data fifita akansu ,yayinda su kuma suke matukar bukace da kulawarta ,a matukar fusace ta suri hand bag dinta tayi hanyar waje  tabarshi tsaye yana sake  duban gadon da NASREEN dinsa ke kwance tana fidda numfashi ahankali hawaye na bin gefen idanunta, ahankali ya karasa bakin gadon yana cigaba da dubanta ya kai hannunsa  ya shafa sumar kanta yana me jin wani irin ajikinsa, yana jin ina ma yana da hali,wallahi  daya cire ciwon ya meida jikinsa domin shi yafi dacewa da wannan ciwon bakaramar yarinyarsa ba.
" yana matukar son NASREEN arayuwarsa baya son bayason abinda zai ta'ba masa lafiyar jikinta ita kad'ai garesa.. ita kad'ai Allah yabashi a tun tsawon shekara goma dayayi aure ,kusan minti goma  ya d'auka  tsaye agurin yana kallonta yana Shafa sumar kanta hawaye na gangarowa ta gefen idanunsa ,ya ciro  hanky  cikin aljihun gaban rigarsa ya goge hawayen  sannan ya gyara gashin daya zubo  wanda ke kokarin rufe mata fuska sannan ya fito daga cikin d'akin.
" abinda yabashi mamaki ba wuce ganin me'ad tsaye abakin kofar d'akin tana jiran fitowarsa ba, wanda shi a tsamaninsa ta dad'e da isa office din doctor, dogon tsaki yaje a fusace ya wuceta yana Allah wadai da halinta har ma da mata masu irin halinta. 
har suka Isa office din likita tunani yake ta yadda zaiyi da al'amarin me'ad gabadaya  zuciyarsa tasoma tsirewa da halaiyenta  abubuwa dayawa zuciyarsa ke raya masa  akanta.... 
doctor najin motsin shigowarsu ya d'ago  yana nuna musu gurin zama sannan ya sake meida kansa kan file din NASREEN dake gabansa, ahankali fu'ad yaja daya daga cikin kujerun dake gaban doctor ya zauna yana ware kafafunsa tare da jijiga kafarsa daya, itama  dayar kujerar kusa dashi taja ta zauma  tana cicci magani.. 
zaune suke gaban doctor  suna jira daga garesa, doctor ya numfasa kana ya sake d'ago idanunsa yana dubansu  daga bisani ya mikawa fu'ad hannu suka gaisa .
doctor yace "ammm ..i salute ur courage for all your effort on your child, Allah yabata lfy yasa muci amfanin yaranmu gabadaya.. 
ahankali suka had'a baki gurin amsawa da "ameen   kana suka ja bakinsu sukayi shiru suna sauraron doctor. 
doctor yacigaba mgn "amm thank God   NASREEN  has been responding better to treatment now, better than before but her condition now is some what critical  than before. 
me'ad ta zaro idanuwanta waje tare da dafe daidai saitin zuciyarta tana duban doctor "inna lillahi wa inna ilaihi rajiun  ," wannan wani irin tashin hankali hk ,ya Allah karkasa nashiga uku akan yarinyar nan .... takarasa mgnr jikinta na wani irin rawa, take kuma hawaye yasoma ciccikowa a idanunta .
fu'ad batare da ya kalli inda me'ad take ba yace "doctor ban fahimci zancenka ba .
doctor yace "no,  just calm down  okay , it's not as if her  condition is that critical  but you know she's a sickle cell patient ,there for, she need a lot of attention.. wanda nake tunani dole daya daga cikinku zai ajiye aikinsa    at least for a mouth domin bawa NASREEN kulawar data dace .
atare gabansu yaba wani irin rasssss saboda jin abinda doctor yace... 
"saboda zaman daya daga cikinku yana da matukar mahimmanci domin irin magungunan dazamu bata  yana bukatar   kaida,domin ana bukatar  ta dinga shan maganin akan lokaci zuwa lokaci ,and most importantly, she need ur care, love and attention more than before...
" atakaice dai yarinyarku na bukatar kulawarku da duk wani abinda iyaye yakamata suyi domin kwantarwa ya'yansu da hankali, me'ad tayi tsuru tsuru da idanu tana sauraron doctor daki daki tamkar zata shige cikin tunaninsa, yayinda fu'ad  yayi shr kawai a tun sanda doctor yasoma bayani  kai kawai yake girgizawa tare da had'e hannuwansa guri daya yasanya tafukan hannunwansa ya rufe fuskarsa dashi,  shi kad'ai yasan irin rad'ad'in da zuciyarsa take ciki akan wannan matsalar... 
fu'ad ya cire hannunwasa yana duban doctor da idanunwasa da suka gama canza kala "doctor idan na fahimci zanceka sosai  wani daga cikinmu  zai natsar da zuciyarsa ya zauna tare daita ? 
doctor yace "haka nake nufi saboda kulawarku is very important agurinta. 
"saboda ina yawon samum masu irin lalurarta amman yadda nayi muku bayani haka nake   treated  a similar case dinta, before wani lokaci sai kuga yaro yasamu lafiya ,ina tunanin wannan tsarin dana kawo muku ,zai samu kar'buwa domin itama  ina son tasamu irin wannan kulawar daga gareku ,ina me tabbatar muku matsawar daya daga cikinku zaiyi kokarin bata gudumuwarsa wallahi zakuyi mamakin yadda yarinyarku zata dinga samun saukin ciwon ... 
"dan haka atsakaninku sai ku zartar da wanda zai zauna gida tare daita, ka ko ba dan komai ba dan Allah kod'an saboda ni ku taimaki rayuwar tilon diyarku dan Allah you guy's should do this. 
murmushin fariciki me'ad tayi tana duban doctor "no no karka damu doctor da wannan matsalar Inshaallahu zamu san abin yi ,ai wannan bazai zama wani abun damuwa ba ,dan tabbas zamuyi yadda kace zamuyi magana da juna idan muje gida..
docto yace" thank you. 
shi kam fu'ad shiru yayi yashiga duniyar tunanin yadda abinda Doctor yace, gabadaya ya kasa magana saboda cajin da kwalkwaluwarsa ke yi, yana jin kmr ya zubda hawaye ne akan NASREEN yana matukar tausayawa rayuwar yarinyar ahankali ya juyo ya dubi me'ad dake zaune a gefenshi ,ganin murmushi kwance akan  fuskarta, ya d'an sanyaya masa zuciya ,hannusa me'ad ta riko cikin tafin hannuta tana murzawa,  da kyar yasamu ya mike tsaye suka fice daga office din likita zuwa d'akin da NASREEN take kwance , tare da sanyata gaba suna dubanta gabadaya ta sake ramewa , ji suke ina ma ciwon ya dawo kansu ta tsira da lafiyata... 
 
daren ranar sam me'ad da fu'ad basu samu damar runtsawa ba ,hatta bacci barawo wannan karon baiyi nasarar d'aukar daya daga cikin iyayen NASREEN ba, tunani kawai suke ta yadda al'amarin zai kasance, "cikinsu waye zai ajiye aikinsa domin bawa yarinyarsu faricikin da kulawar data dace ? 
"shi ne zai tallafi rayuwar diyarsu ya zauna agida ko  me'ad da rayuwarta ce kawai ,bazata iya bawa aikinta ba, saboda mahinmmacisa gareta? fu'ad ya tambayi kansa yana satar kallon inda take . har kusan asuba fu'ad na zaune rike da hannu  NASREEN  ya tasata gaba yana kallonta still hannunta daya cikin nasa, yayinda me'ad ke tsaye bisa kafafunta tana kaiwa allah kukanta daman ita macece me yawon ibada, kullun daren duniya bata runtsawa batare da tayi  ganawa ta musamman da ubangijnta ba, ita din mace me yawon ibada  da kamewa tare da tsayuwar dare ,a duk inda ta tsinci kanta  zata tabbatar da ta tsaya bisa kafafunta  gurin bautawa Allah, illarta daya saurin d'aukar zafi akan abinda bai kai yakawo ba, da kuma d'aukar aikinta da mahimmanci datayi akan bawa yarinyarta kulawar data dace .. 
kwanansu daya aka sallamosu daga hospital suka nufo  gida tare da jakar magagunguna ,yinin ranar da suka fito daga hospital me'ad na d'aki tare da NASREEN  rungume  ajikinta  tana shafa sumar kanta  tana zance zuci kasancewar week end ce ranar babu aiki "Allah sarki haka hukuncin Allah yake gashi dai daga ita har mahaifinta lafiyarsu kalau basu d'auke da wata lalura sannan su ba ss bane  balle as, gabadayansu aa ne , gashi sun haifi sickle cell ..
  "ina matukar sonki  NASREEN dina ,Allah ka raya min ita,saboda  banason rasata arayuwata duk da kasancewarta sickle cell kabarni na rayu daita ,Allah karka jarabeni darashinta " hakika wannan matsalar yancine gab iyaye mata akan yaransu naganin sun kula dasu sosai fiyye da komai hawaye ne ke gangaro mata daga cikin kwarnin idanunta .
ganin baccin NASREEN yayi nisa sosai yasa ahankali ta lalla'ba ta kwantar daita  tare da sanya pillow tayi mata makari dashi had'e dayi yi mata kiss a goshinta sannan ahankali tashiga shafa sumar kanta  tana jin wani irin tsantsar  tausayin yarinyarta me gauraye da  kauna mara iyaka,  ta lullu'beta da blanket me taushi , sannan ahankali ta sauko daga kan gadon tasanya takalmanta ta d'auki tire dake ajiye akan bed side Wanda ke d'auke da ruwan databawa NASREEN magani ta sha, bud'e kofar d'akin tayi ta fito, kai tsaye  main parlour'n din gidan ta nufa yayinda fu'ad ke zaune akan doguwar kujerar dake zagaye da parlour'n ,sanye  cikin jallabiya ash colour  kafarsa daya ya lankwasashi karkashin dayar kafarsa, yayinda dayar kafar ke mike system ne agabansa wanda ya d'aurashi akan cinyarsa ,yana dane dane tare da tura sakonnin , tazo ta wuce shi tashige  kitchen sanye da wata yar karamar riga iya cinyarta da hula net wanda ya bayyana gashin kanta .
ta ajiye tiren hannunta sannan tasoma 
gyaran kitchen   tare da goge koina daga karshe ta isa gurun  gas tana gogewa tana tunanin wanda zai ajiye aikinsa acikinsu domin bawa yarinyarsu kulawa ,aiki take sai dai zuciyarta na can ga satar kallon fu'ad dake zaune yana aikinsa, saboda farin glass dake  tsakanin kitchen dinta da parlour'nta bai hanasu ganin juna ba, duk wanda ke zaune a parlour'n tabbas zai hango wanda ke cikin kitchen, haka zalika wanda ke  cikin kitchen zai hangi na parlour, yayinda har wannan lokacin fu'ad na zaune wanda ya mike kafafunsa yacigaba da aikinsa hankali kwance yajiyo sautin muryarta daga cikin kitchen "honey   .
batare daya d'ago kansa daga abinda yake yi  ba yace "yes love... 
"should i serve you  food now? 
"no just give me 5 minnutes  i must finish this project, it's due on Monday.... 
cak ta saida abinda take yi tare da shiga wani yanayi na bugawar zuciya kana a tsanake ta juyo tana fuskartashi "zakayi sumint dinsa on Monday fa kace? 
yace "eh zanyi sumint dinsa ranar monday saboda mahimmancisa .
 da auri tasoma kokarin fitowa daga cikin kitchen bakinta bud'e sannan cike da matsanancin mamaki tasoma magana jikinta har rawa yake " honey wace monday kenan kake magana akai? 
"Monday jibi mana ya bata amsa, batare daya d'ago ba yacigaba da danne dannesa. 
"ta dubesa a kaikaice tana sake mamakin jin abinda ya fad'a tayi kusa dashi sosai ta yadda kowanensu zai iya fuskantar d'an uwansa "meyasa zakace zaka gurin aiki ranar monday ?
"ko ka manta abinda Doctor ya fad'a mana ne ?
"me doctor yace mana ? 
yayi mata tambayar yana me dakatar da abinda yake sannan ya d'ago ya fuskanceta .
"haba ya kake kokarin ka manta, akan NASREEN mana. 
"eh doctor yace dole cikin ni dake wani ya ajiye aikinsa ya zauna gida tare daita .
"yauwa a she baka manta ba. 
fu'ad yace "so what are you talking about? 
me'ad ta soma fusata dan haka a zafafe tace "what do you mean by.. that, dole mutun daya zai ajiye aikinsa ya zauna tare daita agida ..
"uhmm wannan kuma ai aikinki ne, ki zauna gida tare daita, ta yaya kike tunanin ni na ajiye aikina na zauna gida? 
"this is common sense now it's your duty   a matsayinki na mace" ni me zan zauna nayi a gida?
 yakarasa mgnr ahankali yana kallon cikin kwayar idanunta, gefe daya kuma wani irin bugawa zuciyarsa keyi da sauri sauri . 
ahankali ya numfasa kana yace " kiyi tunani sosai me'ad akan wannan lamari kodayake bai zama lallai ki gane, abinda nake nufi ba tunda baki aiki da kwalkwaluwarki ya fad'i hkn yana nuna gefensa kansa.. 
"no no fu'ad banason irin abinda kake min "and you know I don't like all this can of thing  kasan sarai banason kana min magana kana ta'ba kanka domin kokarin meidani mahaukaciya mara tunani.. 
ya sake kai hannusa daidai gefen kansa "wannan ai common sense ne ,kema kuma kinsa da haka ,yakamata amatsayinki na mace tunaninki yagaya miki akan kece zaki zauna agida  bani ba .
dakata fu'ad "automatically, its your duty to stay with her .
"for what? 
"me kake nufin akan saboda mai?
"okay  tunaninki nabar aikina na zauna agida alhalin ga ki ....
"me kake nufi da bazaka bar aikinka ko me ko me? 
"kai kanka kasan kai yafi dacewa ka zauna agida tare da yarinyarmu kasan wannan. 
"gsky bakida hankali da tunani wallahi ,kwata kwata tunaninki baya gaya miki gasky da har kike expecting ni yakamata na zauna gida tare da NASREEN alhalin gaki mace kina nan baki mutu ba . 
"nasan aikina nane,  ba sai ka gaya min ba, ta hanyar meidani  tamkar mahaukaciya  ,"amman ni aikina yana da matukar amfani ga rayuwarmu gabadaya, dan hk ko kaki ko ka so you will be the one that wel stay at home with  our daughter...... 
"wannan ai akinki ne me'ad meyasa kike kokarin meidashi kaina. ?
"i know  but my job is mo..re more important you just can't tell me to what's my du... 
sautin  tarin NASREEN ne yakatse mata hanzari ..tarinta  kawai suke jiyowa babu kaukautawa da wani irin sauri fu'ad ya zabura ya mike  tsaye jikinsa na kyarma "kingani ko kinga abinda maseefarki zai haifar ko dan.. ..ai kafin yakarasa fadar abinda yake son fad'i  tarin ya sake yin karfi ai da wani irin mugun sauri tayi hanyar d'akin NASREEN aguje tana ihu kiran sunanta ..... 
mmn sudais ce💗💗💗💗💗💗
       'YAN CINKI
      💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗
             ~NA~
 *AYSHA  A BAGUDO*
~DEDICATED TO~
      MRS ADAM
( YAR MUTAN KAGARA)
page 16 to 20
.......aguje  suka karasa shiga cikin d'akin, kowannensu na rige rigen isa inda take zaune dafe   da kirjinta tana cigaba da tari tamkar ranta zai bar gangar jikinta, da sauri fu'ad ya haye saman gadon ya janyota zuwa jikinsa ya rungumeta yana kiran "sorry baby!!! 
yayinda gabadaya ilahirin jikin me'ad ya d'auki rawa  "tarasa me ma zatayi ,sai sambatu take "me kuma ya sameki baby nah ? 
"some one should help me plz "wa meye hk ne.. ..?
zagayowa tayi dayan gefen  ta haye gadon tana  maimaita "me yasa meki baby nah ?"dan girman allah ki sausautawa zuciyarmu bazamu iya jure kallonki cikin wannan tashin hankali ba. "ya ubangijin ka taimakeni kabawa yarinyata lafiya tayi rayuwa kmr sauran yara. 
NASREEN









