Showing 42001 words to 45000 words out of 55607 words
Chapter 15 - A MAFARKI NASANTA BY FA'EEH BG FIRSTLADY .txt
ruwa har abada yana lumshe idanunsa s ai kuma a hankali ya na bude su.
Dr Aj ikon Allah kad'ai yake kallo atare Dr Ammar yana mai yana mai mamakin hali da da taurin zuciyh irin na d'an uwansa ace mutun kaifi d'aya ne ba chanji domin yakamata ace yanzu ya fara kula al amarin Dr.Malini saboda shekarun da tadauka tana bibiyarsa da soyayyarta,.''kaji tsoron Allah Dude,bayan yagma maganar zucinsa, na jin zantukan Dr Ammar d'in. yar karamar harara yasakar masa yana mai kau da kansa gefe,Aj ne yaci gaba da magana yanzu ita Dr malini d'ince yarinya just bai wuce kabata shekaru uku ba fa domin bazan manta ba when last birthday nata danaje ishirin da biyar tayi celebrating Amma shine kake kiranta da yarinya sannan bata cikin tsarin matan da kake so kake iya aure koh !!! hmm Dude kenan inbanda so yana haka me Dr.Malini zatayi dakai dubeka skin dinka kamar zumar dataji wuta ta kone,yakai karshen maganar cikin dan yin dariyar mugunta domin yasan Ammar yatsani wannan furucin.
Karamar harara Ammmar yasakar wa dr aj dan dagaske yatsani kalmar nan dan aj nayawan furtamasa ita duk da yasan wasa yakeyi masa fatarsa normal take kuma ahakan mugun sonta yakeyi.
Murmushi Dr.AJ yayi yana cigaba da maganar sa,"ga mace har mace Amma so na walagigiya da ita gaskiya Dude da zakaji shawarata da ka karb'i Dr.Malini saboda kaima shaida ne tayi maka son gaskiya kuma bugu da kari ta had'a duKkanin Abunda Daaa namiji zai bukata ga mace,kuma duk jarabarka nasan malini zata iya dauka domin nasan halinka inaga ka raina girmanta ne,ina kara baka shawara karkayi watsi da damarka toh!!!!!!yakai karshen maganar tasa yana dariya tare da kanne masa ido d'aya.
Dr.Ammar da ke kallonsa k'uri da ido ne Yayi D'an murmushin gefen baki sai kuma ya murtuke kyakyawar fuskarsa jin furucin aj d'in na karshe domin nafarkon bai bashi haushi ba face ma mere baki da yayi.
"cikin tsuke fuska ya furta Wai yaushe ka koma hakane bansani ba naga alamar idanunka sun bud'e fa,murmushi ne ya subuce masa tuna furucin wai malini zata iya daukar sa abu na kayan wanki,dakuma amsar datazo kansa kan maganar malinin wadda zai mayarwa da aj d'in wadda zaiji zafin ta domin tabbas yaji haushin furucinsa na karshe wai zata iya d....Kasa ida karasa tunanin yayi ta sanadiyyar zuciyarsa da tafara hasaso masa yadda komai na malini yake duk da ba wani kallon tsaf yakemata,subhanallah ya furta azuciyarsa yana lumshe idanunsa tare da bud'esu
yana cigaba da magana kace Dr.Malini Dr.Malini tacika mace ;Am nace ko zaka gwada sa,a ba ko zaka samu cikakkiyar macen tunda naga har ka hango cikarta yakai karshen maganar tasa cikin yana kanne ma Dr.Aj ido Daya kamar yadda yamasa,tare da sakin wani killer smile, aj wqnda daga farkon maganar ta Dr.Ammar murmushi yakeyi sai wannan furucin na karshe yasanyasa turb'ene fuska wata katuwar harara Dr.Aj yasakar masa wadda sai da tasanya Dr .A murmushi wanda yasanya two side dimple dinsa bayyana gwanin burgewa,tsinin hancinsa ya lakata yana mai k'ara sakin murmushi ganin shan tokar da Aj d'in.
A bangaren aj maganar ta bashi haushi matuka domin yadda suke da ammar soyayyar dayake masa bazai iya son abunda yakeson dr .Ammar dinba koda shi bayaso kamar dr malini haka..
Ya bud'a baki da niyyar yin magana sai yayi shiru, karar wayarsa da yaji tadakatar dashi daga abunda abunda yake niyyar furtawa,cirota yayi daga aljihun wandonsa na baya dan ganin wanda ke kiran nasa wanda alokacin har wani sabon kiran yashigo nafarkon yakatse saurin d'agawa kiran yayi Bayan duba sunan mai kiran nasa UNNI
sunan da ya fito baro baro da manyan rubutu.......
💫A MAFARKI NASANTA💫
In my dream I know her
By
Pha'eezah Almustapha
Daga Alkalamin✍️✍️
💫Fa'eeh BG💫
Dedicated to my lovely sis lailat Almustapha Murai💔
💫A MAFARKI NASANTA💫
YAZAMA FREE BOOK
Nama mayar muku dashi free book akan wani dalili nawa inason duk Wanda yaji dad'i yamun Addu'a,Allah ya biya mini da dukkanin buk'atuna🙏
Ina godiya da hakurin da kukayi dani har na tsawon sati biyu koma fiye🙏
Ina alfahari daku masoyan Amafarki nasanta,kud'in na daban ne agareni💋
------------------------------------------------------------------
--------------------------------------------------------------------
*PERFECT ESSENTIAL WRITER'S ASSOCITION📚🖊️
💫P.E.W.A💫
Home of perfect essential writer's together we stand🤝
ESSENTIAL WRITER'S📚🖊
Pen🖊️*is migthier than the sword *🗡️
EPISODE1️⃣
PAGE32
TYPING📲📲📲
©°••••••••••••••••••••••••••••••°©
Sallamar da akayi A dayan b'angaren ce ya amsa yana sakin murmushi,Unni yakike?ya gida?'sunan da aj ya furtane yasanya gaban Dr.Ammar fad'uwa idanu ya tsurawa Aj dake wayarsa da unni a tsanake cikin girmamawa cikin ladabi.A d'ayan b'angaren Unni ta tambayi Aj ya aiki ? bayan ta amsa masa duka gaisuwarsa,Alhmdllh ta furta ya furta yana mai sake fad'in Unni ai yanzu haka ma muna hospital d'in yau bamu tashi da wuri ba...
Ohk tau Allah yataimaka"ta furta masa,A hankali ta furta" Nur na kusa"ehh ya bata amsa atakaice yana mai d'aga idanunsa ya kalli Dr. Ammar da ya tsuramasa idanunsa masu kaifi Ba ko kyaftawa tunda yaji sunan Unni ya fito bakin dr aj gaban shi ke k'ara faduwa.
Unni ce ta juye harshen ta a yaren fulatanci,tana tambayarsa har yanzu Ammar yana nan kan bakansa ne?bazai karb'i sarautar ba,fahimtar da yayi bata son Dr Ammar d'in yagane zancen da suke yi yasanya sa shima chanja shima zuwa fulatanci,dan duk sun san Dr.Ammar baijin sa tun suna yara akayi koya musu yaren inji kakarsu Ammie gimbiya fatima,wanda itama ga mijinta margayi sarki Hamza ta iya sa da kuma kawar tata HAjiya,har ya" yan ta ma,shi yak'i maida hankali ya iya ne shiyasa bai iya yaren ba.
"Amsawa unni yayi da tabbas dai kam Unni yana nan kan bakansa,Unni bata nuna komai ba duk da amsar tasa tad'anji ba dadi ganin kafiyar yaron nata duk da tasan baizubar bane haka mahaifinsa yake da kafiya.furta masa tayi " kyalesa kar ka k'ara masa maganar komai yazo karshe in sha Allah.Sosai Aj yayi mamkin sosai da jin maganar da unni tayi dakuma rashin nuna damuwa da batayi ba kamar sauran lokutta,sai dai bai tambaye ta dalili ba saboda yanajin nauyin ya yar ta mahaifiyarsa fiye da mahaifiyartasa.Tambayar da ta masa ce ta katse tunanin zucin nasa"•••••••••
Ranar nace ka kirani inkazama less busy Amma Aminullah shiru babu kiranka,da yake haka take kiransa some times itada Sarki Ali ko son,shiru yayi na rashin gaskiya dan tabbas yana sane yak'i kiran nata gudun tambayoyin nata game da Dr.Ammar d'in akan rigimarsa da mahaifinsa,saboda kuma bayaso ya rik'a yawan yiwa Ammar maganar dan duk lokacinda ya masa magaanar sai yaga damuwa karara akan fuskar d'an uwannasa shikuma hakanne bayaso duk da yasan cewa yana cikin damuwar da shi kansa bazai iya boyeta ba a wasu lokuttan ba duk da jarumtar da yakeyi,shiyasa tun ranar da suka fito meeting d'in bai kirata ba,A yanzu ma koda yad'aga kiran yana d'ar darr ne a zuciyarsa duk da yasan unni mace ce marar daukar zafi,sai kuma yaji akasin Abunda yake tunani,yazata yaga ta nuna damuwa ko b'acin rai ko tayi fushi ma dasu.
A hankali ya furtama sorry unni kinsan aikin namu ne,shiyasa bansamu na kiraki ba,Murmushi kad'ai Unni tayi dan tasan tabbas gan gan yaki kiran nata domin baison takurawa AMmar d'in dan tana basa umurni ya tambayesa in yajanye domin ita ko takirasa shiru yake mata,DA kuma yarika convincing nasa har yajanye ra'ayinsa duk da tassan abu ne mai wuya.Shima Aj murmushin kad'ai yayi
dan yagane dalilin murmushin na unni akan maganarsa.
°©•••••••••••••••••••••©°
Bayan minti biyu dukkaninsu suka yi shiru,Unni ce ta takatse shirun nasu ta hanyar tambayarsa game da mafarkin da Ammar yasabayi tun yana k'arami wanda anyi neman taimako akai Amma ba,a dace ba kusan shekara ishirin da yan kai.
Amsa mata yayi da ehh yanayi Unni ma a wasu lokuttan kad'ai dan yasan Ammar bazai masa karyaba in yayi saboda shak'uwar dake tsakaninsu.
labarin last mafarkinn nasa yabata wanda ya banbanta da saura duk a harshenn na fulatanci suke maganar.
Ta B'angaren Ammar ido kad'ai ne ya zubama Aj din dan dukkanin abunda suke fad'a baya fahimtar komai inbanda gaisuwar daga cikin yaren,kuma tabbas yaji ajikinsa duk akansa ne suke magana sai dai bai gane kan zancenba,A hankali Ya lumshe idanunsa tare budesu wadanda suka d'an sauya daga farin madararsu yanayin nasa kamar mai jin bacci wanda haka kawai yake jin kasala na saukarmasa ta rashiin dalili.
'Ta B'angaren Unni ta razana sosai da jin labarin mafarkin da dr Ammar yayi,sosai hankalinta yatashi,Kwantar mata hankali Aj Yayi yana furta "unni karki manta fa ba duka mafarki yake zama gaskiya ba agaremu, Annabin mu muhammad saw shine kad'ai wanda yakeyin mafarki kuma ya tabbata dan haka karkisa damuwa dan sun furta zasu dawo kansa bashi ke nuna ko suwaye zasuyi nasara akansa ba Unni kawai kisanya duka wannan mafarkin nasa amizaninb sharrin shaid'an (la'anannen Allah) ba abunda zai iya zama gaske ba,sannann UNNI Addu'o'in ku natare damu mezaisa ki razana,ayanzu ya mayarda maganar sa da hausa inda duk maganar da sukeyi yanaji rad'am akunnensa.
Ajiyar zuciya Unni ta sauke abangaren ta cikin jin dadin furucin na dr aj wanda yasanyata jin sanyi aranta. wanda akullum take k'ara jin sa kamar ma ita ta sunb'ulosa duniya saboda kusan halinsu guda da aj a tabangaren iya sarrafa zance na fahimta da nutsuwa, Ahankali ta furta hakane son muna kai kam addu,a kuma kudage da Addu,a kaji,kai yad'aga mata inda takara furta Allah ya muku Albarka yakare gabanku da bayanku,Ameeen ya amsa mata cikin jin dadi har tamasa sallama Aj yamaza yatare ta daga shirin yanke kiran Unni pls karki sanarwa da kowa harda Abbah,in sha Allah ta furta suna yanke kiran.
Ajiyar zuciya kad'ai yake saukewa a jere cikin kara lumshe idanunsa kansa ya dafe jin yana juyamasa kad'an,A hankali ya bud'esu tar yakoma a mazauninsa daga d'an tsayen da yake tun dazu wanda su bakomai bane agaresu yin irin wannna tsayin saboda yanayin aikinsu na likitota.
Idanunnsa yak'ara lumshewa dasuka k'ara yin d'an jaaa na damuwa
Mafarkin nasa ne yadawo masa akai bayan zaman nasa wanda maganar da yaji aj nayi ce tak'ara dawo masa dashi sabo duk da yana ransa ne har yanzu baisan meyasa yake jin kashe yarinyar da akayi a mafarkin nasa ba yake jinsa har cikin ransa idan ya tuna da sun kashe masa ita jiyake kamar ya yi ta yin kukan da babu mai iya rarrashinsa,tambayar kansa yayi wai dagaske ne kwa?sun kashe masa dream girl d'insa,kansa ya girgiza da karfi yana furta nooo baki mutu ba Cikin d'aga murya irin tsawa d'in nan ta rashin tabbas Kan abu....
©°••••••••••••••••••••••••••••••°©
Ikon Allah kad'ai Aj ke kallo dan Shi Al amarin Ammar nabashi mamaki anya kuwa ba aljana ce ta Auresa ba ko ta shiga jikinsa take zomasa a mafarki kamar yadda su unni suka zata abaya sai dai duk iya binciken da manyan malammai sukayi masa ta hanyar yimasa rak'iya babu alamar hakan atare dashi.
Kuma yanaji ajikinsa kamar ma soyayya yakeyi da aljanar ko sonta yakeyi .Dan tabbas Alamu ya fara nuna son yarinyar yakeyi inma ba soyayya sukeyi din ba,domin ba tun yauba yana ganin wasu alamu agaresa duk da bai tabbatar ba.
Kallon Ammar yakeyi kallo na tausayi da mamaki,ganin kallon da yakemasa shima bayan bud'e idanun nasa da ke
a lumshe jin yayi sub'util kalam,yasan kallo ne yake masa na tuhuma duk da yafi hango tausayin sa acikin idanun na d'an uwansa,maganar da ke zuciyarsa ta fito fili yasan cewa sai Aj ya tuhumesa shikuma hakanne bayaso,kauda kansa gefe yayi daga kallon da sukeyi wa juna shida aj d'in yana mai tsuke d'an karamin bakinsa kar Dr .aj yaga damar sa har iya yimasa wata magana kan zancen.
Dr.Aj k'aramar dariya yayi duk da ya fahimci Ammar d'in sai yayi kamar bai gane nufinsa ba,A hankali Aj yadan duk'o da kansa yana mai furta masa anya kuwa ba son wannan aljanar kakeyi ba domin Kuwa nikam nafi tunanin ALJANA CE (oum Amjad) yakai k'arshen maganar tasa yana sakin karamar dariya,Dasauri Ammar yad'ago Dara Daran idanunsa yana sakarwa Aj wani irin kallo da idanunsa da suka kara girma kallo ne wanda sai da Aj yaja baya,shima yana kallon Ammar d'in da mamaki take zuciyarsa ta kara tabbatarwa da aljanace Ammar din yake tare da ita.
Ran Ammar ya b'ace sosai matuka wanda har sai da labbansa suka kara yin jan wahala na taunar da suka sha sanadin bacin ran da yasame sa na furucin Aj,Huci yake fitar wa mai zafi wanda shikansa aj sai da yayi danasanin maganar yakara yadda tabbas aljanace ke tare da Ammar d'in shiyasa yake wulakanta ire irensu dr malini.
Bayan kamar minti shida yafara sauka daga fushinsa A hankali ya bud'e bakinsa da kyar kamar wanda bayason yin maganar ya furtawa aj "yanzu nizaka had'a da aljannu halittar da muke neman tsari daga gareta,kuma wannnan baiwar Allahn itace Aljanar dude harararsa yayi yana furta kuma ni ba sonta nakeyi ba kawai dai inajin badadi ne sannan ita ba aljana bace then karka kara kiranta da aljana pls mutunce itama kamar kai inada yakinin tabbas mutunce duk da bansan sunantaba har yanzu bansan a ina take ba.
Kallonsa kawai Aj keyi baki asake,Addu,a kad'ai yayi aransa Allah yabawa Ammar lafiya,domin shi gani yake wannan Abu bana hankali bane.
Aiko insunje Nigeria zai sanarwa su Unni aljannu nan kamar ya kamata kara dubashi agani,anema masa magani kar abun yak'arayin girma ganin irin bacin ran da Ammar ya shiga kan furucinsa.kai kawai yak'ara kad'awa yana mai furta ohk!nagane,Amma fa dude kabani tsoro wannnan fushi haka daga kawai na furta Al......Dr Ammar murmushin da baiyi niyyar fitomasa ba yasaki jin aj yayi furucin Aljanna yakasa idasawa kenan bazai k'ara furta masa hakan ba,har ransa yaji dad'i yadda d'an uwan nasa yake gudun b'acin ransa tun kuwa suna kanana.
Aj wanda yayi shiru jin zai kara sub'util kalami ya furta baki yabawa Ammar hakuri sannann ya kara furta"nasan kaji wayar damukayi da Unni har naroketa karta sanarwa da sarki gudun fad'awa tashin hankalinsa"kallonsa kawai Dr Ammar keyi bece dashi komai ba.
Dr aj samun kansa kawai yayi shima dayin murmushi,ganin yadda yake ta kallonsa kamar wata sabuwar halitta.
Hadadden Rolex din dake daure akan tsintsiyar yakalla ganin lokacin sallar azahar yagabato yasanyasa mikewa dukkanninsu suka dauro alwallah suna dan gabatar da sallar alokacin ta.
*NIGERIA*
*ZAMFARA GUSAU*
Uwar ranar da ake kwatsawa ce ta ruwa tasanya dukkanin wani mai abun nawa yake gaggawa ya is a gida don ganin hadarin da had'u lokaci d'aya gudun shan kashin ruwa musamman masu babura.
Baba Adee ne ke ta k'ok'arin barin babban fuel station na nnpc bayan yasha man da zai kaisa garinsu Bungud'u,mashin d'insa ne d'ai daga cikin dankara dankaran motocin dake shigowa a gidan man ne,ya buge mashin d'in na Baba Adee sanadin shigar da sukayi ba dai dai ba.
Fadawan dake cikin motar ne suka fito dasauri suka rik'a masa mashin d'in nasa suna masa sannu tare da duba lafiyar mashin d'in NASA dan tabbatar lafiyar sa suna kara basa hakuri kan d'an karamin had'arin da ya auku sanadinsu,shiko yana furta musu bakomai cikin dattako.
A lokacin ne kyakkyawan dattijon dake cikin motar da duk tafi daukar hankali tafi sauran kyau kirar range rover fara tass new design yasauke glass a hankali dan son yin magana da Wanda accident din ya so faruwa kansa dan yabashi taimako a lokaci nne shikuma Baba Adee ya juyo A hankali daniyar duba bayansa yadda zai fita batare da ya buge wani ba da mashin d'in sa sai yayi dai dai da d'ago kan maimartaba sarki Aliyu Murai da ya sauke glass d'insa gabansa ne yayi mummunar fad'uwa ganin Wanda yahad'a ido dashi sak k'anensa Abdul rashid,sai dai d'an yanayin manyan taka dake tare dashi bakamar lokacin da yana saurayi ba. Wanda har yau basu San meyafaru dashi ba,sai dai kawai anwayi gari da rashinsa anyi nemansa ba,agansa ba.
Sarki Ali kuwa ido yasakar masa ganin bai nuna alamar cewa yagane saba,sai abun yabashi mamaki da alajabi Wanda har yasanya sa tunanin anya shine kuwa shine,kodai bashi bane mai kama dashi ne ,har Baba Adee yayi wucewarsa baisani ba da d'aya daga cikin fadawansa ya furta Allah yataimake sarki shin ko kasan wannan bawan Allah ne sai dai kuma gashi har ya wuce ai,sai lokacin ne hankalinsa yadawo kansa cikin tashi hankali bafaden ne cikin rashin hango tashin hankalinda sarki Ali yashiga ya furta Allah ya taimake ka har ma kama kuke dashi fa,Amma sai dai shi farar Fata ne duk da zafin ranar da ya d'an k'onasa a na hango farinsa....
Ganin samu da rashin da yake shirin yi alokaci d'aya duk da baya da tabbacin cewa shi din ne,Umurni yabawa d'ai daga cikin fadawansa cikin gaggawa da subi mutumin daya fita yanzu Wanda suka buge wa mashin,dasauri suka ja motar d'aya suka bisa.
💫A MAFARKI NASANTA💫
In my dream I know her
By
Pha'eezah Almustapha
Daga Alkalamin✍️✍️
💫Fa'eeh BG💫
Dedicated to my lovely sis lailat Almustapha Murai💔
------------------------------------------------------------------
--------------------------------------------------------------------
*PERFECT ESSENTIAL WRITER'S ASSOCITION📚🖊️*
*💫P.E.W.A💫*
*Home of perfect essential writer's together we stand🤝*
*ESSENTIAL WRITER'S📚🖊*
*Pen🖊️*is migthier than the sword *🗡️*
*Free*📙
EPISODE1️⃣
PAGE33
TYPING📲📲📲
°©•••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••°©
Fitowa motocin sukayi daga gidan man suka parker a gefe gwanin burgewa dama mota biyar ce d'aya tabi mashin d'in Baba Adee,Bayan kamar mintuna goma sai gasu sundawo,sunyi rashin sa,ar ganinsa,sarki