Showing 6001 words to 9000 words out of 55607 words
riko ba.
Abunda yafaru kafin fitar Khady gidan shine bayan tadawo makaanta
Cikin sallama ta shiga madai daicin gidan dai dai rufin asiri gida ne mai dauke da daki uku biyu suna kallon juna sai daya achan gefe wanda yake shine nasu halee biyun kuma nasu Baba Adee da Baba Asabe,sai toilet daya natsakar gida, da kichen shima chan gefe farkon shigowa gidan ga tsakar gidan ma da wali gidan masha Allah ko ina ka duba kwal kwal yaji suminti,inda ta iske Baba Asabe tsakar gidan tana fifita da yake lokacin zafi ne,Sallamar ta Baba Asabe ta amsa mata da murmushi ta na furta tagaban goshina kindawo itama khady cikin mayar mata da murmushin ta furta ehh Babata nasame ki lafiya,lfyalau Hadizata
Babata yau Dady zai dawo koh!inji Khady,ashe kina lissafi yar nan yaufa ne zai dawo murmushi mai hade da murna khady tayi tana furta yo ba dole ba Babata, Munyi missing nasa ne tana maganar tana dosar dakinsu da gudu tana kwalawa Halee kira,Halee! Halee!
Tana yaye labulen taga wayam katifarsu bakowa adakin, katifarsu kadai ce da tasha lailaya sai kayan sip dinsu wanda Khadyn ta ya mutsa kafin taje makaranta,wanda Halee ce take aikin bayan tadan ji dama damar jikinta,tana cikin aikin ne Baba Asabe ta kirata ta Aiketa kasuwa kutsa kanta tayi cikin tare da kara lelleka ko ina dan tabbatar wa indagaske Haleen bata ciki ne har toilet dinsu ta leka bayan ta kwankwasa taji shiru tambayar kanta tayi toh ina Halee taje ita da bata lafiya kuma?ganin bata da mai bata amsa yasanyata fita daga dakin bayan ta sargafe jakkarta ama 'ajiyarsu,fitowar ta keda wuya ta yo tsinke gurin Baba Asabe tana mai furta Babata ina Halee taje ne,fuska adaure Baba Asabe ta furta na aiketa kasuwa,tun yaushe Khady ta kara furtawa cikin jin haushin Babar ta ta,shiru Baba Asabe tamata wanda dama tasan tunda taji tana kwala kiran sunan Halee tasan cewa sai tazo ta tsureta da tambayoyi kamar yar jarida ,kuma ta san tana iya bin bayanta yanzu dan haka kuwa bazata bartata fita ba komai kafuwarta
Khady ganin bata bata amsa ba yasa ta furta babata kinfa san bata da lafiya kika aike cikin wannan uwar ranar tana maganar kamar zatayi kuka shine kuma kika ta har kasuwa duk wayennan kantin basu isaba sai kasuwa.....
Baba Asabe ce ta furta an aiketa din wani ta fadawa bata lafiya ne eh dazaki zo ki tsare ni da surutun banza....
Nikam nace 💁Baba Asabe adaiji tsoron Allah.
ALLAH YASA MU DACE 🙏
muhadu daku anext page
Zuwa monday in sha Allah lahadi babu update.
jiya kunjini shiru nayi typing sai da nagama na danna wani gun by mistake duka ya goge ga dan ciwon kai danake fama dashi,kusakani a addu'o'in ku
🙏🙏🙏
💫A MAFARKI NASANTA💫 FANS
INAYINKU OVER MUSAMMAN MASU BIBIYATA FACE BOOK INA GANIN COMMENT DINKU INA GODIYA 🙏KUMA NA WHATSAPP INA GODIYA SOSAI MASU COMMENT DA WAYENDA BASA YI🙏
ku cigaba da bibiyar alkalamin
💫Fa'eeh Bg💫
in sha Allah daga gobe zamu bar kasar nan domin dauko muku rahoto sai kuma mundawo,in akwai masu zuwa su fito mutafi jirgi 🚄kyautane
Wayenda badasu za,a sai gyara zama tsaf dan jin rahotannin mu.....
* Allah yasa mudace*🙏🙏
Pls like share and comment
💫A MAFARKI
NASANTA💫
In my dream I know her
By
Pha'eezah Almustapha
Daga Alkalamin✍️✍
💫Fa'eeh Bg 💫
Dedicated to my lovely sis Laila Almustapha
Murai💔
*PERFECT ESSENTIAL WRITER'S ASSOCIATION
💫P.E.W.A💫
Home of perfect essential writer's together we stand🤝
ESSENTIAL WRITER'S📚🖊️*
Pen 🖊️is mightier than the sword🗡️*
Ban amince a had'a mini document ba ko achanza mini wani sashe na littafi na inkuma kikayi nabarki da rabba👌
EPISODE1️⃣
FREE PAGE7️⃣
TYPING📲📲📲
Wuce kibani guri ko in tattaka ki gurin nan,jiki ba k'wari ta wuce d'akin su tana zagayen neman yadda zatabi bayan Halee kasuwa,tabar Baba Asabe na masifarta ita kad'ai,Chan kamar minti uku haka taji tsif dama tana tsaye ne bakin k'ofa,koda ta lek'a ta tabbatar da Baba Asabe tabar tsakar gidan aiko da sauri da sand'a ta fice gidan gudu gudu sauri sauri ta fice daga gidan har ta cimmata Dan dama tasan hanyar da Haleen ke bi har ta isketa.
💫Fa'eeh Bg💫
Itakuwa Baba Asabe data shiga toilet din tsakar gida Dan tayi fitsari,tana fitowa tafara kwala Kiran sunan Khady,Hadiza!Hadiza! Domin tagaya mata ta d'ora mata ruwan zafi,Tsif taji ba,a amsa mata ba k'ara Kiran sunan tayi sai dai shiru aiko da sassarfa ta lek'a d'akin nasu Dan tabbatar da zargin ta,aiko tana yaye labulan taga wayam babu Khady babu ba alamarta Jakarta kadai ta hango sargafe, Nan ta rike k'ugu bayan tasaki labulen d'akin tana cigaba mitar ta na rashin dawowar Halee da wuri da kuma fitar Khady gidan,ita kuwa Halee ta fiyarce tata gata ga kamar ta dama,dama bata da saurin tafiya ne,wannan kenan ....
💫Fa'eehBg💫
Mukoma cikin labari .......
Jirgin✈️ mu yayi landing lafiya😊
* INDIA,MUMBAI*
Babban Birnin India-mumbai garine Wanda yatara kowace irin al umma daga k'asashe daban daban,Wanda yakasance kowa da abunda yakawo shi garin inka cire yan asalin India din mazauna garin na Mumbai,wasu karatu wasu kasuwanci,wasu kuwa neman lafiya,wasu yawon shakatawa,wasu kuma aiki ne yakawo su.
Nasan wasu zasu ce Babban Birnin India ai new Delhi ne karku damu😊 wannan shine kawai abunda nayi ra,ayin sakawa🙏
-----------------------
Gujarat 105 unguwa ce Babba ta masu idon nera shiyasa zakaji ko ina tsif kamar ba bil adama acikin manyan ginukan na alfarma, inda na kutsa kaina acikin cikin wani katafaren gida Wanda yakasance upstair ne, kuma ya amsa sunansa house,Wanda yaji farin fenti da ash colour mai haske da daukar ido,gida ne Wanda yaji kawa ta ko ina tunda compond din gidan zaka shaidar da hakan,k'aton parking space ne achan gefen dama dauke da manya manyan motoci wad'anda ake Kira car wayenda akalla zasu Kai goma,daganin motocin dai bugun America ne new design yan 2022 sai 2023 wayenda bakowa ke taka su anigeria ba sai Wanda yaji gishiri da sugar,sai wani k'aton swimming fool dake Chan ta gefen hagu Wanda yakara kawata gidan,ruwan cikin sa har wani sky blue sukeyi gwanin burgewa, swimming pool din yadan shiga lungu da alama akwai kofar sa achan ta baya, bayan ta gaban gidan,ko ina tsaf ga iska tana kad'awa shuke shuken gidan sai kad'awa suke yi suna bada wani k'amshi mai dad'i ko ina sai walkiya yake yi part biyu ne acikin gidan iri daya gidan ya hadu iya had'uwa rabinsa duk gilas ne tundaga bakin kofar shiga ciki zaka gane hakan.
Muryar wani guy naji
Daga ciki yana kwala Kiran Ammar!cigaba da kiran sunan yayi kamar ransa abace,Ammar yakara furtawa! wai uban me kake jira haryanzu baka fitoba har na fita compound nadawo,shiru danaji ne yabani damar shiga cikin falon bayan wannan guy din yacire code din kofar,nikuma na antaya daga ciki🤗wani had'adden falo na fad'a Wanda yaji kayan more rayuwa ta ko ina gashi yasha had'addun cusions masu taushi farare kar dasu,ga katuwar Tv Nan manne abango,ga k'aton dinning table anan shima gwanin burgewa,Wanda yake kusa da wata kofa Wanda nafi tunanin kofar kitchen ne mai had'e da store, falo ne na kasa Wanda yake dauke da d'akuna uku agefe suna Dan nesa da juna agefen hagu,sai wani ahannun dama inda nake tunanin toilet, bayan nagama karema dakin kallo,kuma ina da tabbacin nan ne naji muryar wannan guy d'in,juyawar dazanyi kenan dan hawa kan upstair din da ya raba tsakanin hagu da dama,idanuna ne suka tsaya chak sanadiyyar kicibus da sukayi da wani had'adden guy a hoto yasaka kanana kaya ya daura labcoat akai irin dai shigar likitota wadda takara kawata shigar tasa,sai wani k'aton hoton Wanda yakara Jan hankali na yana sanye da kayan tiyata ajikinsa blue colour tare da abun awon Bp waton stethoscope ya rungume hannayensa akirji yana sakin wani had'adden murmushi chocolate colour skin dinsa sai sheki take yi,ga Zara zaran eyelashes dinsa cike wayenda suka Kara kawata manyan idanunsa wayenda ke kwance akarkashin cikakkiyar gashin gyarar sa,sumar kansa kuwa daganin ta kasan tana Shan gyara na musamman tare da sajen sa,pink colour din labbansa sai sheki sukeyi gwanin burgewa hancin Nan kuwa zungur kamar biro Masha Allah.
Sai wani hoton shima na wani farin guy shima dai kyakkyawane saye da irin shigar ta wancahna guy din na farko.
Maganar da naji daga saman ce ana furta Ammar Amma dai Kai Dan iska ne ace har yanzu baka shirya ba tun d'azu nabarka kashiga wanka fa Amma Dan wulakanci har yanzu baka gama shafe shafenka ba,shiyasa nayi maza nafada ciikn d'ai daga cikin dakunan wanda naji sautin maganar na fitowa,Muryar wannan guy dince tadawo Dani dai dai daganin zubin halittar Wanda ke zaune akan mirror da towel daure akugunsa daya kuma agefen kafadarsa, kwantaccen gashi ne abisa kansa Wanda dagani ya hada da jinin larabawa ko fulani daga bayan sa zaka fahimci yana da faffadan kirji tare da kwantaccen gashi Wanda yake luff gwanin burgewa jikinsa ko ina lui lui dashi daganin sa kaga Dan hutu kafafuwansa da tafin hannun sa wayenda yake ta faman murtsuka mai dasu gwanin burgewa Wanda dagani zasu yi kamar na sabon jariri,chocolate colour fatarsa sai sheki takeyi.inda wannan guy din yake furta ai narantse bazan jiraka ba tafiyata zanyi yana maganar ne kamar ransa abace kasan yau muna da meeting ga tarin patients na jiranmu Amma shine kak'i saurin shiryawa,wadannan maganganun dayake yi su suka dawo Dani daga sumar tsayen Dana yi, inda nakai duba na ga saurayin dake maganar,shima dai hadadden ne kamar Wanda naji ankira Ammar, ashe ma shine wannan fari tass din guy Wanda nagani afalo, yasha
Kyau cikin kananan kaya yadora labcoat akan kayan sa inda naga an rubuta Dr .Al Amin jabir Muhammad soja Wanda mafi yawan colleagues da abokansu suna kiransa da Dr AJ...
Dacin Raine bayyane akan fuskar Dr AJ bayan yagama mganar
Yana batun fita ne yaji anriko hannun sa,yana kucce kuccen ya kwace hannunsa kenan yaji an rungume shi dasauri ya turesa yana furta ji iskanci Kai fa Ammar Dan iska ne mtsww yaja dogon tsaki,jiyayi Ankara riko hannunsa wannan karon .....
Mu hadu next page🙏
Gobe in Allah yakaimu
Comment din ku kadai nake bukata...
💫Fa'eeh Bg💫
💫A MAFARKI NASANTA💫 FANS
INAYINKU OVER💯 MUSAMMAN MASU BIBIYATA FACE BOOK INA GANIN COMMENT DINKU INA GODIYA SOSAI🙏KUMA NA WHATSAPP INA GODYA MASU COMMENT DA WAYEN DA BASAYI
Pls like share and comment...
https://chat.whatsapp.com/HO4hVB1luhXGyRzaOdWy68
💫A MAFARKI
NASANTA💫
In my dream I know her
By
Pha'eezah Almustapha
Daga Alkalamin✍️✍
💫Fa'eeh Bg 💫
Dedicated to my lovely sis Laila Almustapha
Murai💔
*PERFECT ESSENTIAL WRITER'S ASSOCIATION
💫P.E.W.A💫
Home of perfect essential writer's together we stand🤝
ESSENTIAL WRITER'S📚🖊️*
Pen 🖊️is mightier than the sword🗡️*
Dan Allah duk wanda yakaranta wannan page yayi mini Addu,A🙏
Allah yabiya mini da dukkanin bukatu na tare da dukkan kulluhin musulmi🙏
EPISODE1️⃣
FREE PAGE8️⃣
TYPING📲📲📲
+++++++++++++++++++++++++++++++++++
wannan karon daya fisge hannunsa baiji an rungume sa ba sai dai yaji anja hannunsa,anzaunar gefen gado,baice kara cewa uffan ba har ya zauna.
Had'a idon da sukayi daDr. Ammar ne yana sakar masa wani shu'umin murmushi ne yasan ya sa galla masa wata katuwar harara yana mai jan tsaki,shiko Wanda naji ankira Ammar A hankali cikin wata kasalalliyar murya ya furta just give me three minute ohk! yakai karshen maganar yana mai k'ara sakin yalwataccen murmushi a fuskarsa, wanda maganar da yayi iya kar labbansa ta tsaya,maganar da yayi ce bayan barowar sa kan madubin,tasanya ni kara cikin natsuwa ta daga sumar tsayen da na kara yi ganin hadadden guy din da na gani ahoto falo Amma tabbas afili yafi kyau daganinsa kaga ingarman namiji mai ji da kudi,mulki da izzah ga fatar nan tasa sai sheki take yi kamar an mata wankan madara sai narasa tantance shin chocolate colour ne skin nasa ko fari ne mai dan duhu,wanda fuskar sa takara nuna hutun da yake samu....
Zazzak'ar muryar sa kuwa kamar ana kad'a sarewa inyana magana kmar kayi bacci saboda dadin ta,saboda zakin ta da taushinta in yayi magana kamar ba,a bakinsa tafito ba,daga yanayin Kallon da masa na fahimci akwai jan aji da izzah da yanga kamar mace kuma baida son magana,Ammar dai daga ni miskili ne na karshe...
Bayan ya gama maganar da iyakar labbansa ta fito inba ka kalli bakinsa ba ba zaka san dakai yakeyin maganar ba,juyawa yayi ahankali yataka kamar yana tsoron carpet din dake kwance male2 ad'akin ta huda masa k'afa,har ya isa inda doguwar sip dinsa take wadda ake bud'ewa da thumbprint inda yasanya dai daga cikin zara zaran yatsun sa na hannu take hadadden sip din tashiga budewa da kanta har ta kai karshe wow! bansan lokacin da baki na ya furta hakan ba,Allah yasa ba wanda yajini...
Kayane birjik kamar botique wasu asama wasu ak'asa,sashen ko wanne daban su trouser,men panties,t shirt ,necktie suma gasu nan atsare ta ko ina sip din kayane atsare chan daga karshe suit ne jere kala kala sai walkiya sukeyi,sai sashen shaddodi,yadukka da huluna irinsu mu hadu banki ,su ku'be, har da irin su tadara mai irin na gidan sarauta kamar yanayin na(raba gardama) labarina...sai dai na wannan likitan sunfi na (raba gardama) kyau kuma design dinsu ba,a irin na nigeria bane daga ganin su kaga bugu turai sun sha kari har sun gaji,sai daga chan sama wata hanger ce rataye da wasu fararen riguna masu kama da labcoat,dasu long sleeve,under wears,short nikers da vest,handkerchief, kowanne da gefensa akan hanger din.
................
Hannunsa ne yana jawo d'aya daya daga cikin fararen rigunan labcaot,
Shi kam Dr.Alamin Aj murmushin bakin ciki kad'ai yake yi yana jan tsaki yana mai duba hadadden agogon da ke hannunsa kamfanin apple,dogon yakara ganin har minti uku ya wuce har yakara biyar akai,Dr.Ammar kuwa duk da yaji jerin tsakin dayake ta faman saki kuma yana ganin hararar da yake ta sakar masa bai tanka saba
.....Komawa yayi yadauko wani had'dden wandon jeans bak'i,bayan ya aje labcoat din,ya juyo kenan Dan ya ajesa kan gado yaji Dr Aj yakara jan wani mugun tsaki wanda sai da Dr. Ammar ya rufe kunnuwansa yana mai yamutsar beautiful face dinsa D'an kallon Dr.Aj yayi wanda yayi tik'in tik'in da fuska,Dauke kansa yayi,A hankali yajuya gurin sip din yana sakin kayataccen murmushi a fuskarsa wanda ya bayyanar da dimple dinsa na gefe daya yatsan sa yasanya cikin kwarewa kamar wani jarumin ya lalaci tsinin hancinsa,wannan dabi'ar sa ce ta lakarta tsinin hanci in yana cikin yanayi mai dadi dakuma yan maganar sa nakai.
Dama haka yake Idan yana jin shirmen sa haka yakeyi da d'ai dai yake zabo kayan da zai saka acewar sa suna masa nauyi ne ahannu,wani lokacin ma in Dr Aj ya ga zai tsayar dasu shike zab'o masa kayan kamar wani karamin yaro
Abun da yasa yajuya ya fahimci Dr Aj yakai kololuwar b'acin rai yanajin uwar hararar da yake sakar masa,ga tsukkin da yake ta faman ja suna neman jaza masa light headache,shiyasa kawai ya juya batare da ya aje trouser dinba yakoma domin ya hado kayan baki d'aya,da isarshi bakin sip din yasanya kyakkyawan hannunsa yazaro farar vest da long sleeve fara kar mai dogon hannu,da handkerchief fari, yana gama zab'ar kayan yadanna wani madanni kamar na ura daga kasan inda ake thumprint,A hankali katuwar sip din tarufe ruff kamar dai yadda take farko.
💫Fa'eeh Bg💫
A hankali yataka zuwa bakin gadon ya aje su anan gefen labcoat din a kusa da Dr.AJ din
Wanda kallo daya yayiwa Al amin Aj ya dauke kansa, yana cigaba shirinsa cikin natsuwa wandon yafara jawowa zai sanya wanda yayi dai dai da d'ago idon Dr Aj,ganin abunda Dr yake kokarin yi ne na sakin towel d'insa kasa yasanya sa dasauri yadauke kansa yana fadin marar kunya kawai yana jan karamin tsaki,bai san cewa Dr motsinsa Dr.Ammar na ankare dashi ba har dauke kan da yayi,shi atunaninsa babu short ajikin sa shiyasa yayi saurin dauke kan nasa duk da yasan ba halin shi bane sakin tsaraici tun suna yara shi ba ya yadda wani ya gane masa jiki in za,a musu wanka dakyar yake yadda wata rana sai dai akai shi gurin Aunty....
Murmushi kawai Dr Ammar yayi yana cigaba da sanya wandon sa acikin dan short din da ya chanza tun atoilet cikin wayen da ke a lakkame a hanger,vest dinsa yasanya da long sleeve dinsa masha Allah na iya furtawa takawaa yayi zuwa kan madubi yana kara gyara lallausan gashin sa da sajensa tare da kara taje sa da murtsuka masa kalolin mayukka bayan wanda yashafa acikin toilet,sannan ya fefesa turare kusan kala biyar oud masu bala'in kamshi,man bakin sa ya shafa :lips balm: wanda yakara kawata kyakkayawar fuskar sa da aina hin kyawonsa da shekin fatar sa,dama bakin sa bai rabo da maskin lips balm domin wannan dabi'ar yasaba da ita tasha man baki kamar mace,shidai Dr Aj kallon ikon Allah kadai