Showing 9001 words to 12000 words out of 55607 words

Chapter 4 - A MAFARKI NASANTA BY FA'EEH BG FIRSTLADY .txt

Advertisement

23 Dec 2024

8995

yakeyi yabuga tagumi yana yi yakai duban sa ga agogo,ace katon saurayi yazauna ya dinga shafe shafe kamar mace, azuciyarsa yayi furucin.
Dan yin murmushi DR .AMMAR yayi jin maganar da Dr. AJ yafurta wadda yayi kasa kasa,tsinkayar muryarsa Dr Aj yayi yana furta nagode ma Allah da ba maccen nake ba kamace kagani yakai karshen maganar cikin yin dan karamin murmushi Dr aj da yaji abunda ya furta duk da baiyi tsammani yajisa ba dan ciki ciki yayi maganar,sai bai yi mamaki ba dan yasan yadda dan uwan nasa yake da mugun ji kamar kunnen maciji..
sai bai bai basa amsa ba yashare sa .
~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~
ยฉ๐Ÿ’ซFa'eeh Bg๐Ÿ’ซ
~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~
cikin dan kan kanin lokaci dakin yakara gauraye da kamshin turarrukkansa
A Hankali yajawo labcoat dinsa irinta ta Dr. Aj samfurin ta likitota fara tass sai shekin sabon taka takeyi kamar ma sabuwa ce akan kayan sa yadaura irin da yadda kuka san likitota nayi masha kawai zamu ce domin tsaya wa rubuta kyawon da yayi page din bazai dauka ba,stethoscope dinsa dake akan hadadden gadon sa ya sargafa abisa wuyan rigar sa dan danan yakara fitowa likitan sa sak,ga sunan shi nan ya bayyana radam agefen rigar tasa cikin tsari mai kyau inda aka rubuta DR. ABDUL RASHID A ALIYU da manyan baki Amma colleques nasu nasu da childhood friends na kiransa da DR.AA
wasun ma cikin colleques nasu suna kiransa Dr. Ammar a gida kuwa suna kiransa Ammar Saboda sunan kanen mahaifinshi da yaci shiyasa aka masa lakani da Ammar.


A hankali ya juyo inda Dr aj yake sannan ya kalli hadadden agogon zinarin dake daure a tsintsiyar hannunsa kirar kamfanin rolex wanda yadaura bayan tsayuwar sa kan madubin wanda yakara kawata shigar tasa skin din sa sai sheki takeyi.


A hankali bayan yataka ya zabi dai daga cikin shoerock din dake dauke da takalma iri iri masu kyau wanda sai da yafara saka sock baka aciki sannna yasanya takalman nasa masu kyau bakake rufaffi sai walkiya sukai gwanin burgewa
A gogon nasa yakara dan kallo ganin lokacin da yadiba har ya wuce wani ya zo wani yakaru, sannan cikin izza ya furta man katashi mutafi karmuyi late...
wani ...
Kallo da Dr aj yamasa ne yasa sakin wani killer smile wanda ya tsaya iya labban sa,dama da gayya yayi maganar dan yasan mutumen nasa acike yake kamar ya fashe wanda kuma yasan fushin nadan lokaci ne zai sauko ......


Shiko Dr aj dayake kan pressing phone dinsa baice masa komaiba yadauki nashi stethoscope din ya sargafa,wanda dama sargafe yake awuyansa ne,gajiyar jiran Dr Ammar ce tasa ya cire ya ajiye shi gefe,duba kansa yafara yi agaban madubin dan tabbatar da komai normal sannan ya fice daga dakin shima uban gayyar dake tsaye yana kallon sa A hankali ya matsa gefen gadon yadauki wayar sa dake chaji abisa bed side drower sannan ya fice daga cikin dakin cikin tafiyar takama da izzah yana ta faman zuba uban kamshi kamar sabon ango........


Fitar su dakin ce tabani damar
Karewa da Katon bedroom din kallo fari ne tass mai kyau wanda yake katone ne nagaske ashe ma Ciki da falo ne ban lura ba wurin uban sauri,bedroom din tana da fadi sosai gadon ya hadu iya haduwa,da sip din sa wadda take lafe abango kamar babu ta sai gefen hagu ga katon mirror mai dauke da kayan gyaran jiki irinsu mayukka masu tsada manyan manyan turarukka da man gyaran gashi da sauran kayan amfani,sai wata kofa dake gefe wadda nafi tunanin toilet ne inda na lek'a sa ya hadu iya had'uwa dukkaninsa glass ne aciki ga katon bahon wanka nan irin na turawa mai kyau da katon madubi da yaji kayan amfani irins sabulu shower gel da turarukkan wanka,toothpaste, brush komai akwai ga tsakiyar toilet din gudan fankacece komai akwai aciki na bukata ya tsaru iya tsaruwa,curtain din kuma milk ne masu kyau.


Falo na dawo bayan na fito daga toilet din inda falon ya hadu shima ya hadu komai na cikin sa yakasance lite blue and white har cusions da labulayye komai agyare gwanin burgewa kamar ba dakin men ba.


Sawun tafiyarda naji ne yasani waigawa dan ganin wanda ke tafowar
Dr Ammar ne yana shigowa direct bedroom nasa ya yi tsinke
Cikin sanda nima nabi bayansa


Gurin aje takalmi yanufa shoe rock wadda ke cike da takalma na alfarma masu kyau,wadda ke akusa da sip dinsa takalmin dake kafarsa yacire ahankali tare da ciro wasu masu masu kyau sai walkiya suke yi suma cover shoes ne kamar na farkon sai dai kalace ta banbanta wadanchan baki ne a kala su kuma waddan nan fari,bayan yachanza su ne ya dauki yar madaidaiciyar bag tasa kamar ta school mai kyau yasar gafa agefen kafadarsa yana ficewa.
Ahankali yake takonsa har ya fito falo sannan ya isa inda wata dankararriyar mota take fake kirar benz a tsakiyar compound din gidan ,dama Dr aj yayi ya kunnata har sun yi reverse, Ammar yace yayi mantuwa cikin jin haushi Aj ya tsayar da motar anan tsakar gidan.


A hankali yasanya zara zaran yatsunsa yabude front sit yazauna Dr .Aj bai cemasa uffanba duk da yaga chanjin takalmin da yayi cikin ranshi kuwa kuwa fadi yake mutun sai shegen kichifi kamar mace,kai kam Ammar matar ka tabani mtssw yana jan tsaki abayyane, Dr Ammar kuwa bayan ya gyara zaman sa har ya maida karamar jakarshi sit din baya yana jiran Dr aj yatada motar shiru sai dai yaji tsakin da yayi,murmushin mai kyau kawai yayi yana furta man gulma ta kakeyi azuciya koh yakai karshen maganar yana kafesa da manya idanunsa ......Shiko Dr.Aj harar wasa yasakar masa yana furta abunda ma yafi gulmar ka za,ayi,yafigi motarsuka fice daga gidan bayan sun sanya belt mai gadi na wangale musu katon gate din.......




๐Ÿ’ซFa'eeh Bg๐Ÿ’ซ




next page tommorrow in sha Allah


Comment dinku kadai nake bukata FANS ๐Ÿ’”๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹ domin shine kwarin gwiwata ๐Ÿ™๐Ÿ™


godiya agare ku ta musamman
..........................
fiddausi dan galadima
siddiqerh muhammad
halima bashar bello
ukuteey
anty zee
oum amjad
sha'awa hamis
Oum sudais
Umma
Da ma wayenda ban ambata ba
wannan page naku ne
๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹
Allah yabar kauna๐Ÿ’”๐Ÿ’”
ina ganiin comment dinku ina jin dadi sosai๐Ÿ™๐Ÿ™๐Ÿ™




Allah yakai haske acikin kabarin ka
Baba Bello ya yalwanta kabarin ka dana dukkan kulluhin musulmi,๐Ÿ™๐Ÿ™
Mukuma kasa mucika da imani ya Allah ๐Ÿ™๐Ÿ™pls say amin !


* Allah yasa mudace*๐Ÿ™๐Ÿ™
Pls like share and comment




๐Ÿ’ซA MAFARKI NASANTA๐Ÿ’ซ
in my dream i know her
By
Pha'eezah Almstapha
Daga Alkalamin โœ๏ธโœ๏ธ
๐Ÿ’ซFa'eeh Bg๐Ÿ’ซ


Dedicated to my lovely sis laila Almustapha Murai๐Ÿ’”


*PERFECT ESSENTIAL WRITER'S ASSOCIATION
๐Ÿ’ซP.E.W.A๐Ÿ’ซ
Home of perfect essential writer's together we stand ๐Ÿค


ESSENTIAL WRITER'S๐Ÿ“š๐Ÿ–Š๏ธ*
pen๐Ÿ–Š๏ธ is mightier than the sword๐Ÿ—ก๏ธ*


Group na whatsapp ina mai kara baku hakuri akan abunda ya faru๐Ÿ™


`ยด`ยด`ยด`ยด`ยด`ยด`ยด`ยด`ยด`ยด`ยด`ยด`ยด
EPISODE1๏ธโƒฃ
FREE PAGE9๏ธโƒฃ


TYPING ๐Ÿ“ฒ๐Ÿ“ฒ๐Ÿ“ฒ


Tafiya suke yi ahankali kan katon titin dayake da abun burgewa ta yadda aka tsara shi,ba,abun da ke tashi a cikin motar face sautin sanyayyiyar wakar rihana mai taken my umbrella ๐ŸŒ‚
Uban gayyar yayi shiru ya jingina da sit din sa yana sauraren wakar idanunsa alumshe fuskar nan sai sa,sai sa ba murmushi ba dariya,karar wayar sane da aka kirane dake ringing waka mai sanyi ta mahaifiya ne yasanya sa bude manyan idanunsa a hankali tare da daura su akan screen din wayar wanda sunan nurul hayat ya bayyana b'aro b'aro b'aro akan wayar da numban nigeria + 234......A hankali bayan ya gama karewa wayar kallo wanda har kira na biyu ya shigo yasanya kyakkyawan hannnunsa ya dauki wayar tasa dake gefensa aje kirar iphone latest one 15 pro max picking din call din yayi yana mai kara wayar akunnen sa akunnensa tare da sakin kayataccen murmushi yana furta Assalamu alaiki nurul hayat,daga chan dayan bangaren,murmushi aka saki wanda yakara sanya masa natsuwa,wslm kyakkyawan likita na takai karshen maganar cikin nuna farincikinta,murmushi ya mayar mata dashi tare da furta fatan kina lafiya nurul hayat? daga chan bangaren ta amsa da lafiya lau ya aiki?Alhamdulillah,ya furta mata cikin kulawa kamar yadda tayi masa tambayar,A hankali yakara furta inasu maheer da nisa,maheer na school kasan suna shirye shiryen graduation ne oh hakane fa jiya ma munyi magana dashi yasanar mun,Nisa fa?ya kara tambayawa cikin kulawa da ladabi amsa tabashi da dama ai nida maher kadai ne agidan sai sarki,yuhanis tana gurin sister Husaina tatare gurin sumy,A hankali bayan gama saurarenta ya furta meyasa kika barta kinsan bata son karatu ga sumayya ma duka daya suke,yakai karshen maganar kamar yana jin tsoron yin maganar yana kokarin danne wani abunda ke shirin taso masa na jin sunan sarki da ta ambata,murmushinta ne yaji tana furta nur yanzu fa ba yarda bace sun girma kowa censu tayi hankali 18+ suke fa kaga kuwa sunyi hankali da channe dai basa son zuwa makarantar kuma lokacin babu Wayo ne gashi ma yanzu suna gab da yin ss.c e.graduation Uhmm kawai yace,bawai dan ya yadda da karatun nasu ba shi atunanin sa mahaifiyar tasu tana kokarin kare su ne kawai dan yasan yadda yake fama dasu in sunje nigeria dakyar da lallashi suke samu suje school...Kuma ehh dagaskiyar ta yanzu sun girma da daine yake tilasta musu zuwa makarantar itada sumy amma ayanzu su da kansu suke zuwa dan sun mahimmancin karatun,wannan kenan......




๐Ÿ’ซFa'eeh Bg๐Ÿ’ซ


Shirun da taji yamata ne yasanyata ta A hankali furta YARIMA, gaban sa ne yayi muguwar fad'uwa jin furucin nata yanzun ma shiru yamata dama tasan abunda zai faru kenan, dama irin hakan tana yawan faruwa duk ta kirasa da sunan bakin sa yana masa nauyin amsa sunan, dalili kuwa shine takirasa da sunan ne ko zai nuna alamar cewa yasauko daga fushin da yake ne da mahaifinsa,da kuma jin in yanzu ko yana son sarautar da yake gudu wadda mahaifinsa yake son lakaba masa shima yasamu ya huta wanda kuma shine yasanya sabani atsakaninsu domin kowa kafaffe ne like father like son ,da dai taga alamun bazai ce komai ba,ta furta cikin sanyin murya ABDUL RASHID har yanzu kana nan kan bakan ka ?takai karshen maganar cikin yanayin da bazai iya juraba,wannna karon faduwar da gabansa yayi sai da yadafe kirjinsa wanda ko Dr aj dake tuk'i a hankali sai da yajuyo ya kallesa dan ganin alamar razana atattare dashi ga kuma hannunsa dafe da kirjin sa,A hankali yaji shima jikin nasa yayi sanyi ganin d'an uwan nasa cikin wannan yanayi,Dayan Hannunsa kawai ya riko da hannun da baya driving dashi ya damk'e acikin nasa, yasan cewa tabbas ko ba,a fada ba maganar sarauta ce, akayi masa,wanda ya rasa wace irin kiyayya ce tsakanin Ammar da sarauta da har baison mulkin wanda kuma yake tunanin shine abunda yasanya sa rashin son komawa kasarsu,idanu suka had'a dashi ya girgiza masa kai da alamar be strong man shikuwa Dr.Ammar dauke kansa kawai yayi batare da ya nuna wani abu afuskarsa ba .
Achan bangaren mahaifiyarsa dataji shiru ne yasanyata duba wayar dan tabbatar wa inyana online,,,,,,,,,,,,,,,,,,kuma dama akan sarautar ne yakarbi aikin da kasar india tabasu bayan kammala karatunsu,wanda shikuma Dr Aj yana da burin dawowa k'asar sa ta haihuwa domin yin aiki acikinta dan su taimaki kasarmu ta nijeriya,Amma saboda Dr. Ammar yasadaukar da nashi burin suka fara aikin tare anan kasarta india wanda izuwa wannan lokaci sunansu yayi shura a india dama fadin duniya baki daya,kowa yasan Dr.Abdul rashid Aliyu Ahmad da Dr.Al Amin Muhammad soja,inda kowace k'asa masu dauke da manyan asibitoci suke son su samu damar gayyatar su sumusu aiki koda na dan lokaci ne amma basu samun wannan damar saboda shidai Dr.Ammar kaifi daya ne acewar sa kasar india su suka fara daukarsu aiki har suka yi suna a ko ina to ayanzu bazai iya barin kasar ba dan yaje wata kasar da sunan aiki ba,haka shima Dr. aj duk da yana da burirrika,inda kawai zai iya yin aiki yabar india shine kasarsa ta nigeria ko shi dan saboda nan ne cibiyarsa take,kuma yana son taci amfanin ilimin suwannan kenann......


mukoma inda muke ......
A hankali ta furta karka damu kaji tana mai sakin murmushi,Ina d'ana yake takara furtawa,cikin sauke wata nannauyiyar ajiyar zuciya wadda har sai da taji sautin ta,Wanda shi yakara tabbatar mata da Dr ammar har yanzu yana nan kan bakansa nak'in son sarautar, da wata murya mai sanyi ya furtama ta gashi nan,to basa wayar ta furta masa,Dr aj dake driving yakarbi wayar bayan ya saki hannun na dr ammar a hankali yakara ta akunnen sa yana furta momy yakike cikin murmushi ?lafiya lau my son ta furta kuntashi lafiya,lafiya lau yabata amsa kara furta masa tayi ya aiki Alhmdllh yakara bata amsa toh masha Allah!A hankali takara furta naji kamar a hanya kuke koh?ehh momy,sai ina halan ? dan naga kunfita da wuri yau,ehh momy muna da meeting ne kuma kinga yau monday akwai tarin patients, eh hakane fa toh Allah ya kaiku lafiya akula da titi,in sha Allah yafurta mata,sannan takara furta in kun gama abunda kukeyi anjima inkana freee ka kirani akwai maganar da nake so inyi dakai,cikin girmamawa yace in sha Allah momy i will contact you A hankali takara furta asauka lafiya,Allah yasa ya furta sannan sukayi sallama tare da yanke kiran..........


Kuyi manage da wannan ba yawa...Naso inbaku page biyu but abunda yafaru dazu yadan taba ni,kaina ke ciwo ko typing din nadan yishi sai ahankali.


Allah yasa mudace,Abunda ya tsanan ta agaremu Allah ya yayemuna ๐Ÿ™


pls like share and comment ๐Ÿ™๐Ÿ™๐Ÿ™๐Ÿ™


Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/HO4hVB1luhXGyRzaOdWy68
๐Ÿ’ซA MAFARKI NASANTA๐Ÿ’ซ
in my dream i know her
By
Pha'eezah Almstapha
Daga Alkalamin โœ๏ธโœ๏ธ
๐Ÿ’ซFa'eeh Bg๐Ÿ’ซ


Dedicated to my lovely sis laila Almustapha Murai๐Ÿ’”


*PERFECT ESSENTIAL WRITER'S ASSOCIATION
๐Ÿ’ซP.E.W.A๐Ÿ’ซ
Home of perfect essential writer's together we stand ๐Ÿค


ESSENTIAL WRITER'S๐Ÿ“š๐Ÿ–Š๏ธ*
pen๐Ÿ–Š๏ธ is mightier than the sword๐Ÿ—ก๏ธ*




EPISODE1๏ธโƒฃ
FREE PAGE๐Ÿ”Ÿ


TYPING ๐Ÿ“ฒ๐Ÿ“ฒ๐Ÿ“ฒ


Dora wayar,yayi abisa laps din Dr Ammar a hankali Wanda ke jingine da sit dinsa ya lumshe da idanunsa yayi tsif kamar Wanda ruwa yaci ko kwakkwaran motsi,ba abunda yake tunani face maganar da mahaifiyarsa tamasa wadda kusan bayan dan lokaci takan yimasa maganar taji ta bakinsa ko yajanye nasa Ra,ayin bisa ga na mahaifinsa,fatan Sa kawai A wannan karon Allah yasa batayi fushi dashi ba,dan bazai iya jure fushinta ko na second ne abun yawa zai masa azuciya


Wayar Sa da Dr Aj ya aje masa ce tadawo dashi daga tunanin zucin da yaje a hankali yasa hannu yadauki wayar ya tsura mata lumsasaun idanunta kamar mahaifiyar tasa ce agaban sa,Ajiyar zuciya yasauke mai nauyi,yana kara lumshe idanunsa tare da budesu

Maganar da Dr Aj yayi ce tasa yadago idonsa daga kallon da yake yi ma wayar tasa,inda yake furta masa kar ka sanya damuwa aranka nasan awannnan karon batayi fushi mai zaifi ba kai inaji bazata tayi fushi dakaiba saboda daga yanayin yadda muka yi magana da ita na tabbatar da hakan,Wata katuwar ajiyar zuciya Dr .ammar yakara saukewa,baice furtawa Dr. Aj komai ba,Dai dai sun kawo katafaren asibitin da take Babba afadin India wadda mutane da dama ke yowar tattaki India domin samun ingantacciyar lafiya,Asibiti ce da tayi shura a fadin duniya,Babbar asibiti ce da ta Tara many an likitota ta sassa da ban da ban kama daga likitan kwakwalwa,na zuciya,likitan mata kai ko wanne fanni akwai


Su Dr Ammar da Aj suna dai daga cikin manyan likitotan dake taka rawa ta kowanne fanni acikin asibitin shiyasa sunan su yayi fice musamman Dr.Ammar.



๐Ÿ’ซ A mafarki nasanta ๐Ÿ’ซ
Daga Alkalamin
๐Ÿ’ซFa'eeh Bg๐Ÿ’ซ


MAHARASTRA 24 HOURS HOSPITAL MUMBAI INDIA


...... Asibiti ce Babba wadda ta tsaru iya tsaruwa taji kayan aiki a ko ina,da kayan more rayuwam,musamman ita wannan asibiti su suke jinyar marar lafiyar da kansu,kudi kawai zaka zube kagama naka aikin....


Bayan wangale musu gate da mai gadi yayi tare da nuna farin cikinsa na zuwan su,duk da yadda yake cike da mamaki naganin wadannan manyan likitota sukadai batare da masu tsaron su...Kunsan indiawa akwai bada kariya ga wayenda suke musu hidima dan ko kare ne tsaf za,a sanya mashi bodyguard bare manyan likitota wayenda india take ji dasu dama kasa baki daya.


Haka dai ya rufe gate yana mai tambayar kansa lafiya ?suka zo sukadai ganin kamar suna risking rayuwarsu ne tafiya su kadai, abunka da turawa..nima dai ohon nace dan bangansu tun chan gidan ba,ashe dama suna sa body guard to amma lafiya?na tambayi kaina,bani da mai bani amsata haka nayi shiru abuna.


Wurin da yaksance na musamman dansu wato parking lot nasu wanda suke motocinbsu suda sauran colleques nasu,gashi nan kowa anyi tagging din sunansa akan board din mai kya.


Inda naga an rubuta Dr.Al amin dr aj yanufa dan nan ne nafarko kafin na Dr ammar Wanda shima sunan sa arubuce yake cikin tsarin burgewa,Bayan sun parker motar tasu kowa yacire sit belt dinshi Dr.Ammar dayajawo karamar bag din shimai kama da school ba,wayarsa dake ajiye atsakanin lap dinsa yadauka,A hankali yadora kafarsa ta dama wadda take sanye hadaddun takalmansa yana mai kara gyara zaman stethoscope dinshi da labcoat dinshi yana ida fitowa da gangar jikinsa baki daya,futowar sa keda wuya yaci karo da wasu garadan maza kirar america atsaye agefenn motar tasu kowannensu fuskarsa ba Annuri,Shima Dr aj haka ce takasance dashi bayan yafito yaci karo da irin garadan mazan da Dr Ammar ya ci karo

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login