Showing 6001 words to 9000 words out of 16661 words

Chapter 3 - MAHAUKACIN SO Complete Book Na Autar Marubuta.txt

Advertisement

28 Dec 2024

3218

ta kalli Laila tana cewa.
"Na yi zatanfa da Mahmud ma zaku zo wallahi."
Kawai Yaya Nasir duk ya canza ya koma wani yanayin daban


Murmurshi Laila ta yi kana ta ce .
"A'a Uncle ne ya kawo ni ."


Kawai Yaya Nasir ya tashi tsaye , sannan ya karbi sultan a hannun Laila tare da mikawa Ummi shi ,
Fuska babu annuri ya ce .
"Tashi mu tafi."


Duk mamaki ne ya rufe su da ganin Nasir ya canza musu a wannan yanayi


"Tashi mu tafi na ce ."


Ya sake jefawa Laila maganar mai tafe da umarni


"Hakan ya sa Laila ta mike jiki a sanyaye


"Haba dai Yaya Nasir, daga zuwa kuma , ko gaisawa ba a gama ba , ko ruwa baku sha ba zaka ce zaku tafi."
Aunty Ummi tai maganar tana nuna rashin jin dadinta a zahiri


Ba tare da Nasir ya ce da ita komai ba , kawai ya nufi kofar fita kana yana fad'in.


"Sai wani lokacin."
Ya fice


Da sauri Laila ita ma ta zura takalmi tana cewa da Aunty Ummi.
"Zan dawo wani lokacin Aunty."


Tabi bayanshi da gudu gudu


Ajiyar zuciya Aunty Ummi tai tana cewa.
"Ikon Allah, Yaya Nasir fa sai a hankali ."


Anan kuwa bayan Fa'iza ta fito daga lecture ta sami guri ta zauna.


Babu dadewa sai ga Fatima ita ma fito daga tata lecture din


Kai tsaye in da tasan tabbas zata sami Fa'iza nan ta nufa


Aiko tana karasa ita ma ta sami guri kusa da Aminiyar tata ta zauna tana cewa.
"Washh Fa'iza, gaskiya yunwa nake ji ."


Fa'iza ta kalli Fatima cikin murmurshi tana .
"To sai muje muci abinci ai ."


Kafin Fatima ta maida mata ne kiran waya ya shigo mata


Wani murmurshi Fatima ta saki tana kallon Fa'iza.
Hakan ya tabbatar wa da Fa'iza cewa Abdallah ne ke kira .


"Hello Abdallah."
Abin da Fatima ta fada ke nan ba yan ta kara wayar bisa kunnenta
Fa'iza tai ajiyar zuciya tare da kauda kai gefe , amman hankalinta na kan wayar da Fatima ke yi


Yanayin yadda taji Fatima na maganar soyyaya ya sa idanun Fa'iza suka kada sukai jajir lokaci guda kuma kanta ya fara ciwo.


Mikewa tai tsaye tai nisa da inda Fatima take tana share hawaye




Update kullum ne ,idan ta kama sau biyu a rana . amman ga wa 'yanda suke bukata.


*MAHAUKACIN SO* farashin sa kan N300 kacal
Ga masu bukata su tura kudinsu a 7040805269 Fatima Abdullahi Ismail opay digital services
Sai shaidar biya a 07040805269
Bana son kati🙏




*MAHAUKACIN SO*
Na
Autar Marubuta








*AUTAR MARUBUTA CE*✍🏻👼🏻
🌹__________🌹_________🌹__________🌹_________🌹
_Faduwar wani tashin wani_
_Yau ake yi, gobe sai labarin_
_Burina Rayuwata, rubutuna dan masoyana_
_Cikawa da imani fatana_🤲🏼
<><><🌹><><><>🌹<><><>🌹<><><><>🌹<><><><><>🌹<><


________________________________________
Babu editing


Page 11 & 12


Bayan Fatima ta gama wayar ta hangi Fa'iza can nesa da ita , hakan yasa ta mike tsaye ta nufi wajen Fa'iza


Fatima na karasa wajen ta , tai ajiyar zuciya tana cewa.
"Wai nan kika taho."?


Fa'iza juyowa tai da murmurshi mai ciwo tana cewa.
"Eh ."
Lokaci guda kuma tana kokarin boye idanunta na kuka .


"Kuka ki kai Fa'iza, mene ya faru ."?
Fatima tai maganar tana fuskantar Fa'iza


"A'a ba kuma nai ba Fatima."
Fa'iza ta maida mata da amsa




Murmurshi tare da ajiyar zuciya Fatima ta yi tana kuma cewa.
"Wai ba kuka ki kai ba , dubi idanunki fa ."


Fa'iza ta sunkuyar da kai kamar wata yarinya tana murmurshi.


"Dan Allah me yake damunki Fa'iza, akwai abin da kike boye mini."


Fatima ta fada tana rike hannun Fa'iza.
Hakan ya karyawa Fa'iza zuciya, kawai ta fada kafadar Fatima tana kuka mai gwanin ban tausayi.


"Ya Allah."
Abin da Fatima ta fada ke nan cikin mutuwar jiki




Cikin wannan kuka Fa'iza ta fara cewa.
"Babu abin da yake damuna Fatima, kawai dai kwana biyu na kan yi kewar mommy, ta tafi ta barmu cikin damuwa, duk duniya bata min dadi Fatima, rashin mahaifiya babban abu ne."


Fa'iza ta aje maganar tana shekar kuka.


Murmurshi Fatima ta yi tare da d'ago Fa'iza daga kafarta tana cewa.
"Haba kawata , rasuwar mommy ta girgiza mu , amman a halin yanzu adduar mu kawai take bukata.
Dan Allah ki yi hakuri ki dena wannan kukan , Allah ya gafartawa mommy."


Ta karasa maganar tana sharewa Fa'iza hawaye da hankicin dake hannunta




Murmurshi Fa'iza tai tana cewa.
"Haka ne Fatima na gode ."


Fatima ta mika mata makullin motar dake hannunta tana cewa.
"Yau ke zaki tuka mu , karbi ."
Fa'iza ta amsa tana dariya.




Nasir ne a tsaye bakin mota tare da Batula
Batula tai murmurshi tana kallon masoyin nata tana cewa.
"A gaskiya na yi matukar farin cikin ganinka a kofar gidan mu ."


Yaya Nasir ya yi murmurshi yana cewa.
"Batula ke nan , to idan banzo gunki ba , gurin wa zan zo , ke ce fa wacce nake burin aure , uwar yayana farin ciki na , kaf mata banga ta biyunki ba , wallahi Batula ina san ki ,so na gaskiya babu yaudara."




Wani farin ciki ne ya lullube zuciyar Batula, wai yau Yaya Nasir ne ke mata wannan zance


Cikin zabura Batula ta farka a baccin da take , sakamakon ruwan sanyi da taji an watsa mata .


Tana ajiyar zuciya Batula ta farka , lokaci guda kuma tana kallon wacce ta watsa mata ruwan
Ba wata babba bace domin Batulan ma ta girmeta .
"Asararriya , har yanzu baki tashi kin yi wanke-wanke ba , to uban waye zai miki , wallahi kika bari na fadawa Daddy sai ranki ya baci ."


Tana gama maganar ta fice


Ajiyar zuciya Batula tai tana murmurshi da cewa.
"Daman mafarki nake Nasir bai zo ba ." Tai ajiyar zuciya


A lokacin Khairat ta shigo dakin tare da sallama
Batula na ganin kawartata tai murmurshi ta ce .
"Khairat ke ce."?




Khairat tai murmurshi tana cewa.
"Eh wallahi , zan biya gidansu Laila shi ne nace bari nazo mu gaisa."
Ta karasa maganar tana kallon yadda duk jikinta ya jike da ruwa


"Rahma ce ta watsa miki ruwa ko , ai naga fitarta da kofi."
Batula tai murmurshi mai ciwo tana cewa.
"Wata rana sai labari ai khairat, yanzu ina iyayena suke , haka kowa zai bar duniyar ai ."


Tsaki khairat ta ja tana cewa.
"Kullum haka ki ke cewa Batula, yanzu a ce kanin mahaifin ki wai bazai iya rike ki da mutunci ba , matarshi ta wulakanta ki yarshi ma haka , sannan shima bai barki ba ."


Murmurshin nan me ciwo Batula ta sake yi kana ta kalli Khairat tana cewa.
"Ai da babu abin da zan dana biki naje naga Nasir ko zan ji dadi ."


Khairat tai dariya tana cewa.
"Ke fa sai a hankali, yanzu ko islamiyya bakya zuwa , Yaya Nasir kuma Allah ya waiwayo da hankalinshi gare ki ."




Batula ke nan yarinya me kalli da nutsuwa, duk da ba sa'arsu khairat ba ce , amman suna tare da juna cikin aminci, sakamakon haduwarsu a islamiyya




Batula ta dade tana wahala a rayuwa, domin tunda Allah ya yi wa iyayenta rasuwa ta fara fuskantar rayuwa a gidan kanin mahaifin ta .




Wanda komai wulakancin da suka debo kan ta suke zubeshi.


Sai dai Allah ya jarafci Batula da san Yaya Nasir, domin babu abin dake faranta mata rai face ganin hotonsa ko wani jinin shi .


Duk da cewa har yau yaki bata fuskar da zata nuna masa soyyayar da take masa .


Ni ko nace Yaya Nasir a duba maraicin Batula mana🤔




Anan kuwa Yaya Nasir yanzu ya dawo daga aiki


Tun kafin ya shiga gidan ya tabbatar wa da kansa tabbas sun yi baki , cikin far'a da sakin fuska ya nufi ciki,
Duk da bai san wanne suka zo ba


"Assalamualaikum."


Nasir ya yi sallama cikin falon ya yin da yake raba idanu


Rabi ya gani mahaifiyar Mahmud zaune a doguwar kujera, kana Laila tana kusa da ita , sai kuma Mahmud din a kusa da Laila wato dai duk kujera guda.


Sannan Mama a gefe fuska cike da far'a


"Wa'alaiku mussalam Nasir."


Rabi ta amsa ita ma cikin far 'a


Murmurshin yake Yaya Nasir ya yi , sannan ya samu kusa da Mama ya zauna yana cewa da Rabi .
"Yau ku ne a gidan namu , sannunku da zuwa."
Ya karasa maganar yana murmurshin da bai kai zuci ba


"Ina wuni Yaya Nasir."
Mahmud ya fada
Sai da Yaya Nasir ya d'aga kai ya kalleshi sannan ya amsa masa


Sannan ita ma Laila ta kalleshi tana cewa.
"Sannu da dawowa Yaya."


Ya d'aga mata kai , alamun ya amsa


"Ina wuni Aunty Rabi."
Nasir ke nan


Rabi ta maida masa da fad'i.
"Lafiya lau Nasir, ya gida ya aiki .
Ya wajensu Ummi."


"Lafiya lau suke ."


Aunty Rabi ta maida masa da cewa .
"To Masha Allah, ai Mahmud ne ya dameni , in zo in ga Laila, sai kace ban taba ganin ta ba ."


Ta karasa maganar tana kallon Mahmud da cewa.
"To mun zo hankali ya kwanta ."




Dariya Mahmud ya yi tare da kallon Laila dake kusa dashi cikin matukar yanayin shaukin soyyaya.


Duk a kan idon Yaya Nasir da ke murmurshin yake mai ciwo .


"Ai in sha Allah Mahmud, Laila matarka ce."
Yaya Nasir yaji maganar har cikin kansa yayin da Aunty Rabi ke fada


"To Allah ya tabbatar da alheri, tuwo na mai na ke nan ."
Mama ta fada cikin murna .






Kawai da saurin gaske Yaya Nasir ya mike ya shige dakinsa


Nan su kuwa suka cigaba da hirasu , yayin da Yaya Nasir ya kan iya jiyo su daga daki .




Bayan Mahmud ya dau mahaifiyar tashi sun tafi..


Sannan Yaya Nasir ya fito falon ya zauna cikin matukar mutuwar jiki.


"Uncle baka ci abinci ba har yanzu ."
Laila ta fada tana kallon shi
Kawai kau da kanshi yayi gefe ba tare da ya ce komai ba


Laila ta kalli Mama, Mama kuwa bama tasan abin da ake ba , domin ta shagala da jan carbin dake hannunta




"Uncle lafiya kuwa."?
Laila ta sake masa shishshigi🤣


Agogon hannunshi ya kallah kana ya yi ajiyar zuciya.
Kamar kuma bazai kalli Laila ba , sannan ya juyo gareta yana cewa.
"Kina son yaron nan Mahmud."


Update kullum ne ,idan ta kama sau biyu a rana . amman ga wa 'yanda suke bukata.


*MAHAUKACIN SO* farashin sa kan N300 kacal
Ga masu bukata su tura kudinsu a 7040805269 Fatima Abdullahi Ismail opay digital services
Sai shaidar biya a 07040805269
Bana son kati🙏




*MAHAUKACIN SO*❤️


Na
Autar Marubuta
________________________________________
Babu editing


Page 13 & 14




Ajiyar zuciya Laila ta yi , kana ta kalli Uncle din nata tana cewa.
"Yaya ni ban za bawa kai na kowa ba , duk wanda ya dace dani daga gareka nake jiranshi."




Murmurshi Yaya Nasir ya yi, sakamakon yadda yaji abin da bai yi zatonsa ba


Kawai ya mayarmata da cewa.
"Jeki kawon abincin."




Anan kuwa Abdallah da Fatima ne cikin mota , suke tafe a hanyar zuwa gidansu Fa'iza


"Gaskiya fa kina son Fa'iza da yawah."
Abdallah ya yi maganar ga Fatima yana murmurshi


Ita ma Fatima murmurshi tai tana cewa.
"Eh wallahi, haka nima take sona Dear, wallahi rayuwar Fa'iza abin tausayi ne , zan yi komai dan farin cikinta."


Murmurshi Abdallah yay yana sake cewa.
"Hmm ai na gani , gashi zamu shopping kin ce a biya a daukota.
Nima ai ina san abin da kike so ."




Murmurshi Fatima tai tana kallon masoyin nata
Yayin data duba fuskar wayarta tana duba wani sako da ya shigo mata .
"Karki manta yau muna da ganin likita."


Hawaye ne suka ciko mata idanu , ta kalli Abdallah tana cewa.
"Ina matukar kaunar ka Abdallah."


Abdallah ya juyo yana murmurshi yayin da take ganin wannan hawaye.
Bai iya cewa da ita komai ba , domin ji yay baki da ya ta karya masa zuciya.


Fatima tai murmurshi ta fice sa'ilin da ya yi parking daidai kofar gidansu Fa'iza


Kallo ya yi ta binta dashi har ta shige ciki


Kana yayi murmurshi da ajiyar zuciya yana cewa
"Allah sarki baiwar Allah Fatima ta, kyakykyawa mai hankali, ya Allah ka bani ita a kaddarata."






"Fa'iza tashi , tashi."
Fatima tai maganar tana janye malullubin da Fa'iza ta lulluba .
Ta tashi zaune tana cewa.
"Kai Fatima na tashi to mene."


Dariya Fatima tai tana cewa.
"Ki fito , ina ta kiran wayarki, Abdallah ne a waje zai kaimu shopping."


Wani faduwar gaba Fa'iza taji ya ziyarce ta dajin sunan Abdallah
"Abdallah kuma."
Fa'iza ta nanata
"Ehh tashi-tashi-tashi."
Ta fada tana jawota , kana tasa kai waje tana cewa.
"Ki sauri ki fito muna waje."


Yadda Fa'iza take a wannan tsayen kawai ajiyar zuciya tai , ba tare data motsa ba
"Aminiyata ce Fatima, bani da kowa bayan ke , tabbas bazan rusa mana alaka ba Fatima ko zuciyata zata fashe."


Ta karasa maganar tana jawo wata doguwar rigarta mai launin marun gami da yellow


Cikin sauri ta fara shiryawa
Domin zuwa ta same su a waje .




Tana fita kofar gida ta fara hangensu daga cikin gilas din motar , sai farin ciki suke abinsu


Murmurshi tai sannan cikin nutsuwa ta fara takawa wajensu
Murfin motar baya dake a bude nan ta shiga tana cewa.
"Soyyaya ruwan zuma."
Abdallah ne ya juyo yana mata murmurshi kafin ya ce komai Fa'iza ta sake fad'i.
"To ina zamu ne ."
"Zamu je Abdallah ya siyo mana abayoyi ne Fa'iza."
Fatima ta bata amsa murmurshi Abdallah ya yi kana daga karshe kawai ya dore da dariya.


Anan kuma Laila ce ita da wani had'ad'd'en saurayi a cikin falonsu .


Bayan sun gama gaisawa da Mama, kana Mama ta shiga ciki ta barsu


"Wato Laila tunda naje America, duk rayuwata babu dadi na yi matukar kewarki sosai fatan dai alkawarin mu na nan ."


Saurayin mai suna Usman ya yi maganar
A daidai lokacin Yaya Nasir ya nufo cikin falon
Hakan yasa ya dakata sakamakon muryar Laila da yaji tana cewa.


"Nima na yi kewarka sosai , amman har gashi kayi shekaru da yawa a America, gaskiya ban yadda ka damu dani ba , ko nema na baka taba yi ba ."


Laila tai maganar cikin shagwaba


Zuciyar Yaya Nasir ce ta sake karyewa a take a wannan wajen


Cikin rashin ya ke cewa .
"Usman ne ya dawo ."?
Ya yiwa kanshi tambayar




"To Laila auren mu shi ne zai tabbatar da irin kaunar da nake miki, amman ko rana daya babyna bata wucewa ba tare dana tuna ki ba ."
Usman ya sake fada cikin soyayya
Murmurshi mai jan hankali Laila ta yi sannan ta bude baki da niyyar cewa wani abu.
"Assalamualaikum."


Yaya Nasir ya shigo da sallama ya tari numfashinta.


Sallamar ta amsa masa cikin far'a
Kana Usman ya zamo daga kujera yana gaida Yaya Nasir


Babu wani salo ko shauki Yaya Nasir ya amsa gaisuwar
Sannan ya shige ciki.
"Laila ko dai har yanzu Yaya Nasir yana fishi dani ne , ai yanzu na shiryu na gyara halayena Laila."




Laila tai ajiyar zuciya domin ganin Uncle din nata a haka duk bata ji dadi ba




Shi kam Uncle dakinshi ya shige ya zauna ,
Domin tabbas sam bai ji dadin ganin Usman ma .


A lokacin baya Usman ya shigo rayuwar su da matukar son Laila , duk da cewa uncle baya son kowa ya kusanci Laila komin mutuncinsa kuwa.


Sai Uncle yayi amfani da yadda Usman yake takadiri kuma mara ganin girman mutane ya raba shi da Laila.
Soyyayar Laila ita ce ta gyara Usman har ya shiryu ya zama mutum , domin a halin yanzu shi yake rike kasuwancin mahaifin sa Alhaji Shehu shanshani , mutum ne mai matukar dukiya.




A halin yanzu sam Uncle ba ya jin dadin dawowar Usman.
To za mu ji yadda zata kaya tsakanin wannan mutane.


Shin ko Mahmud ne zai auri Laila ko Usman ko wani daban .


Muje mu tambayi Uncle kawai, Laila 'yar gwal ce .😝


Domin kuwa duk wani saurayin Laila Uncle baya son shi🤔
Yanzu mene ai bun Usman da Mahmud Uncle?




Tom ba dai musan me Uncle yake nufi ba , mu dai mu sha bikin shalele 😆


Ga kuma bangaren Fa'iza da Fatima


Ga kuma Batula
To dai alkalamin Autar Marubuta ne.






Update kullum ne ,idan ta kama sau biyu a rana . amman ga wa 'yanda suke bukata.


*MAHAUKACIN SO* farashin sa kan N300 kacal
Ga masu bukata su tura kudinsu a 7040805269 Fatima Abdullahi Ismail opay digital services
Sai shaidar biya a 07040805269
Bana son kati🙏


*MAHAUKACIN SO*❤️
Na
Autar Marubuta
________________________________________


Babu editing


Page 15 & 16




"Haba dan Allah khairat, wai sai Uncle ya min fada ne , wallahi mun yi yawo sosai , duk na gaji."


Laila ta fada cikin mita


"Ke wallahi Laila munguwar matsala ce dake , Uncle Nasir da ba ya bari kina fita , shi ne yau kin fito amman sai mitar jaraba, ai gara ai miki auren ma , ki zaman gidan da hujja ."






Dariya Laila ta kwashe da ita yayin da suke hada kafad'a da kafada suna tafiya
Laila ta ce .
"Aure manya , ai saina aurar da Uncle tukun."




Da sauri khairat ta kalli Laila tana cewa.
"Allah sarki harkin tuna mini Batula, wallahi Laila tana son Uncle sosai ."




"Wai wace wannan Batulan kina yawan fada mini ita , kuma Uncle yana santa ."?


Cewar Laila


Khairat ta ja wo hannun Laila su kai wani lungu tana cewa.
"Zo muje gidansu ki ganta , wallahi tana san Uncle."




Wata gajiya ce ta sake rufe Laila da ganin yadda khairat tajata wannan waje .


Hakan ya sa ta fincike hannunta tana cewa.
"Wai duk ina kika san wannan wajejen, ni fa ba kowacce zan bari Uncle ya aura ba , sai wacce ta isa ."


Khairat kawai taja mata tsaki




Gidan Alaji Muktar
Yana zaune ya yi tagumi , kawai yana tunanin irin yadda yayan da ya haifa suke ta mutuwa, a lokacin da yake bukatar su .
Duk wacce danta ya mutu sai ya saketa , yana cikin wannan yanayin ne wata matarshi Hadiza ta shigo falon
Zama tai kusa dashi tana cewa.
"Alhaji lafiya kuwa."


Ba tare da ya ce da ita komai ba ,kawai ya zaro wata takarda a aljihunsa ya mika mata .
Faduwar gaba taji dasss
Hannunta na rawa ta amsa tana budewa.


"Innalillahi wa inna'laihir raji un Alaji ni zaka saki , innalillahi 😭."
Kawai ta fara kuka , ya mike ya bar mata falon .


Ana cikin haka sai ga uwar gidan nasa Hajjiya
Ma'anatu ta shigo
Tana kallon Hajjiya Hadiza da takarda a hannu tana kuka ta ce .
"Innalillahi wa inna'laihir raji un Hajjiya Hadiza sakin ne ko, shi ke nan sauran ni , tunda daman Allah ya yiwa mahaifiyar shi Hajjiya rasuwa shi ke nan tamu ta kare ."
Hajjiya Hadiza ta sake fashewa da kuka .




Anan kuwa Batula ce zaune kan kujera tana wanke-wanke
Ta yi nisa sosai kadan ya rage mata ta gama , sai ga sallamar su Laila


Sai da Batula ta fara zuba musu wannan murmurshi nata kana ta amsa sallamar cikin farin ciki


Suma cikin far'a suka karaso kusa da ita.


Kafin wani ya bude baki ya ce komai , sai ji sukai wani
"Shamm"
Wasu uban kayan wanki wata mata mai zubin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login