Showing 9001 words to 12000 words out of 16661 words
Chapter 4 - MAHAUKACIN SO Complete Book Na Autar Marubuta.txt
hajjiyoyi ta zube a kan Batula dake wanke-wanke.
"Uban me kike har yanzu baki gama ba , to ga wanki nan , maza ki gama ki dora girki sannan ki fara ."
Cikin biyayya Batula da amsa da "To Mommy."
Kana wacce ta kira da mommy ta juya ta koma ciki
Murmurshi Batula ta sake yi musu tana cewa.
"Khairat ki dauko wa Laila abin zama mana."
Ta karasa maganar tana kallon Laila da duk jikinta ya yi sanyi
"A'a! Ke da kike aiki tafiya zami ."
Laila ta fada cikin nufar hanyar fita .
Bayan sun yi sallama khairat tabi bayanta
Tunda suka fito Laila bata ce komai ba haka ma khairat, kowa yana sake-sake cikin ransa
"Wai ita Batulan aiki take yi a nan gidan , kinji harta sanni ."
Laila taiwa khairat maganar cikin sanyi
Murmurshi khairat tai tana cewa.
"Allah sarki Batula, yadda take son Uncle ba dole tasan ki , kin gan ta wallahi tana shan wahala , nan fa gidan yayan babanta ne , iyayenta sun rasu."...
Nan khairat duk ta bawa Laila labarin Batula na abin tausayi da yadda take son Uncle
A karshe duk tausayin Batula ya rufe zuciyar Laila
Fa'iza ce tsaye gaban mudubi sanye da rigar da Abdallah ya siyo musu ita da Fatima
"A gaskiya rigar nan ta yi kyau Abdallah."
Fa'iza ta fada a cikin zuciyar ta, yayin da take sake juya jikinta tana ganin rigar
Wayarta dake ringin yasa tai saurin juyawa ga wayar
Kana ta zauna bakin gado tare da daukar wayar tana karawa a kunne da cewa.
"Hello Rabin Raina Fatima."
Daga can bangaren taji muryar Fatima tana cewa
"Wallahi bana son fada miki wannan zance a waya kizo dan Allah."
Ajiyar zuciya Fa'iza tai kana ta maida mata da cewa.
"Gaskiya 'a'a Fatima."
Ba tare da Fatima taji haushin hakan ba , cikin sabon farin ciki ta sake cewa.
"An yi mana baiko da Abdallah, ashe dadi sun tsai da magana."
Yadda kasan an yi ruwa an dauke, duk Fa'iza sassan jikinta suka dena aiki
Sai bugun zuciyarta da yake yi kamar zai fito
"Uhm wai da gaske."
Fa'iza ta fada yayin da wasu zafafan hawaye suka zubo mata
Cikin farin cikin dai Fatima ta tabbatar mata da wannan lamarin mai dadin ji .
Bayan sun gama wayar , kawai Fa'iza tai murmurshi tana fad'in.
"Fatima Allah ya tabbatar da alheri, Allah ya baku zaman lafiya da Abdallah."
Ta rushe da kuka mai gwanin ban tausayi
Farin ciki ya cika zuciyar Fatima, tana zaune cikin falonsu da wannan farin cikin ne mahaifin ta ya shigo ,
Sakin fuskar shi ya yi sosai ga yartashi guda kamar rai
Zama ya yi yana fad'in.
"Me ake yi ne me sunan Mama, kin sha magani ko."
Shalelen baban nata baki ta zumburo tana cewa.
"Daddy wai shi likitan nan ya yi ta bani magunguna, ni ban sha ba na gaji."
Zaro idanu ya yi yana fad'in.
"A'a yi hakuri mana 'yata, ai lafiyarki ita ce kwanciyar hankalina dana mahaifiyar ki , daure mana ai kin kusa samin lafiya in sha Allah."
Murmurshi Fatima tai tana cewa.
"To Daddy na , amman kafin bikin mu da Abdallah daddy ina so ka kai ni Umara , daddy idan da hali hadda Fa'izata."
A lokacin mahaifiyar Fatima ta shigo tana cewa.
"To masu Daddy."
Ta karaso ta zauna
Murmurshi Alaji ya yi yana fad'in.
"Shi ke nan Fatima, zaku je in sha Allah karki damu."
Cikin farin ciki ta mike tsaye tare da cewa.
"To Daddy bari naje nasha maganin."
Ta wuce cikin farin ciki
Murmurshin Hajjiya tasa tana cewa.
"Fatima ke nan , Allah ka bawa wannan yarinyar lafiya."
Ajiyar zuciya Alaji Usman ya yi kana ya fara da cewa.
"Wallahi Hajjiya ciwon yarinyar nan yana damun rayuwata, zan so ace Allah ni ya sanyowa wannan ciwo na zuciya a maimakon Fatima, wallahi zuciyata kullum bata samun nutsuwa idan na tuna da halin da take ciki."
Cikin rarrashi mahaifiyar Fatima ta fara cewa da mijin nata Alaji Usman.
"Haba Alaji!
Ai shi bawa kowa da irin tashi kaddarar, muma irin tamu ke nan , ya jarafce mu da yarinyar da muka fi so , to mu yi tawakkali kawai mu gode masa , tunda gashi dai tana samun lafiya.
Kuma ka ga Abdallah da danginsa zasu kula da yarinyar nan , dan sun san halin da take ciki kuma suna santa ."
Alhaji Usman ya dukar da kai kasa ya d'ago yana fad'in.
"Haka ne , badaban Fatima na son yaron nan ba , kuma auren sa zai faranta mata, da gaskiya ni bana son tai nisa damu , amman farin cikin ta shi ne namu."
Hajjiya ta ce .
"Haka ne."
Anan ma Alaji Sani Shanshani ne zaune cikin wani furgitaccen had'ad'd'en falo.
A gaskiya ciki da wajen wannan gida ya matukar haduwa ba a magana.
Gefe guda kuma ga wata Hajjiya can da gani babu tambaya matarshi ce
Sannan wasu 'yan mata su biyu masu kama da juna , suma zaune a kujera kowacce tana danna wayarta
Sallamar dansu ce ta sa suka kalli kofar shigowa falon
Yayin da hajjiyan ta amsa sallamar
"Usman ina aka je ne."?
Mahaifiyar shi Hajjiya ta masa tambayar
Yana sosa keya ya karaso ya zauna yana fuskantar mahaifin sa
Murmurshi mahaifin nasa ya yi yana fad'in.
" Lafiya kuwa, meke tafe da kai ."?
Satar kallon Hajjiya Usman ya yi sannan ya dukar da kai kasa lokaci guda kuma yana sosa keya
"Daddy a kan maganar Laila ne."
Murmurshi gami da dariya Alaji Sani Shanshani ya yi
Sannan ya kalli matarshi yana fad'in.
"Ai ni nasan akwai magana."
Sannan ya koma ya kalli Usman yana fad'in.
"Ai Usman a matsayin ku na 'ya'yana , bazan gaza muku a kan komai ba, tun daga lokacin da kowannen ku ya fara numfashinsa na farko a wannan duniyar, idan akwai wanda ya nemi abu daga gare ni ya rasa ya sanar dani."
Ya kalli sauran yayan nasa
Sannan ya cigaba da cewa .
"In sha Allah zaka aure ta , bari daman ita ce sanadin shiryuwar ka , ai alhamdulillah."
Su kai dariya
Yayin da hajjiya ke cewa.
"Sai a kawo mana ita mu ganta , domin kullum kiran sunan ta ake tun kana America."
Usman ya yi dariya da cewa.
"Za ta zo kuwa mommy."
Anan gurin aikin Nasir kuwa.
Tashinsa ke nan ya shiga mota da nufin tafiya gida
Muryar kanin mahaifin sa Alhaji Bashir yaji tana kiran sunan shi
Da sauri ya fito daga cikin motar zuwa waje , yayin da ya durkusa yana gaida Alaji Bashir.
"Wai meke damunka ne Nasir, duk ka rame haka , ko akwai wata damuwar a gida ne ban sani ba."?
Alhaji Bashir ya yi maganar cikin saurin baki kamar yadda ya saba .
*MAHAUKACIN SO*❤️
Na
Autar Marubuta
________________________________________
Babu editing
Page 17 & 18
Murmurshi Yaya Nasir ya yi , kana cikin girmamawa ya fara cewa.
"Wallahi babu komai , komai lafiya lau."
Alaji Bashir ya ce .
"To ai shi ke nan Allah ya rufa asiri , ka gaida Maman."
Yana gama maganar ya juya cikin bugaggiyar shaddarshi da malum-malum ya koma ciki
Yayin da Yaya Nasir yake cewa.
"Zata ji in sha Allah."
Sannan Yaya Nasir ya sami damar shigewa mota .
Anan kuwa
Mama ce zaune ita da Laila, gama cin abincin su ke nan , domin ko kwanukan basu kwashe ba , wani ma da sauran abinci a ciki
Laila wayarta ta aje gefe , ta kalli Mama tana cewa.
"Mama Uncle ya taba baki labarin Batula."?
Mama ta maida mata da cewa.
"Wace kuma Batula."
Laila tai murmurshi sannan ta ce .
"Mama budurwar Uncle ce , tana son Uncle sosai , wallahi Mama rayuwar ta abin tausayi sosai , iyayenta duk sun rasu tana shan wahala."
Mama ta maida mata da fad'i.
"Allah sarki."
A lokacin Nasir ya bankado labulai ya shigo tare da sallama
Kusa da Mama yaje ya zauna a kujera yana ajiyar zuciya
Ido suka hada da Laila, hakan yasa ta ce dashi .
"Sannu da zuwa Uncle."
Ya ce .
"Sannunki ke ma ."
Ido suka sake hadawa a karo na biyu, Laila tai murmurshi tana sunkuyar da kai
"Uncle kana lafiya kuwa."?
Laila ta tambaya
"Duk ka rame sosai ."
Murmurshin ciwo Uncle ya yi , sannan ya ce .
"Alaji Sani Shanshani jiya da kanshi ya zo a kan maganar auren ku da Usman."
Laila ta zaro idanu cikin mamaki
Kafin ta ce komai Uncle ya cigaba da cewa.
"Amman bazan bari ki auri Usman ba bai dace dake ba Laila."
Laila ta sunkuyar da kai
Mama ce ta mike tsaye cikin bacin rai tana cewa.
"Nasir wannan abin ya ishe ni , lokaci ya yi da zaka bawa Laila miji ko ka barta ta zaba, tunda ka nuna mana kafi kowa iko da ita .
Domin bazan zuba ido yadda kaki aure ba , ka zaunar da Laila ita ma a cikin gida, abin ya isa haka ."
Wani furgitaccen zafi Yaya Nasir yaji a zuciyarshi , domin ya lura da batun Mama babu wasa a ciki
"Ko Usman ko Mahmud, duk wanda Laila take so , ka aura mata, wannan abin ya isa haka tom."
Ta shige daki
Cikin yanayin damuwa Laila ta kalli Nasir, babban tashin hankalin data gani yasa duk tunanin ta ya rude
Hawaye ta gani bisa idanun Uncle sun zaru suna shirin zubo .
Kawai ya mike ya fita kafin a kai ga wannan lokacin
Ajiyar zuciya ita ma Laila ta sauke me zafi tana kallon kofar da Uncle din nata ya fice , duk ta rasa me yasa ta damu yanzu haka , kuma tausayin Uncle duk ya kamata.
Yaya Nasir ya na fita gidan Umar ya nufa kai tsaye .
Shima Umar ya yi mamakin ganin Uncle a wannan lokacin da bai saba zuwa ba
Babu korafi Umar ya masa iso har falo suka zauna.
Shi kan shi Umar ya fuskanci Yaya Nasir yana cikin damuwa
"Abokina lafiya, tunda ka zauna kai shiru , ko wani abun yana faruwa ne ."?
Yaya Nasir ya kauda kai tare da ajiyar zuciya
"Hmmm."
Abin da Umar ya iya fada ke nan
Hakan yasa Yaya Nasir ya kalli Umar ya fara cewa.
"Mama ce ."
"So take na aurar da Laila."
Murmurshi Umar ya yi yana fad'in.
"Laaa kaji wani zance me dadin ji , alhamdulillah Masha Allah, ai Mama wannan abin da tai shi ne daidai , domin baka da niyyar aurar da ita ."
Cikin sauri da mamaki Yaya Nasir ya kalli Umar dake kusa dashi
Cikin farin ciki Umar ya sake jaddada masa da cewa.
"Wallahi wannan ya yi , a cikin Mahmud da Usman, nasan Laila zata so daya ."
Da sauri Yaya Nasir ya mike tsaye tare da wata ajiyar zuciya
Idanunsa suka canza kala
"Wallahi Umar bana son aurar da Laila ga kowa, idan naji ko naga wani na binta da sunan soyayya sai naji duk na tsane shi , bana son rabuwa da Laila Umar, ban shiryawa hakan ba."
Ya karasa maganar yana rike rigar Umar kamar mai shirin zarewa.
Tsoro ne ya rufe Umar da ganin yadda Nasir yake .
Kawai Nasir ya yi murmurshi ya sake shi sannan ya kama hanyar fita ba tare da yace komai ba
"Ikon Allah." Umar ya fada yana bin sa da kallo
Bayansu Fatima sun fito daga lecture, kawayenta sai matukar farin ciki suke da jin yadda aka sanya bikinsu da Abdallah
Fa'iza tana cikin class a zaune, domin tunda aka fita bata fita ba , ko zuwa duba Fatima ba tai ba ko sun fito
Durkusar da kai tayi bisa benci
Babu kowa cikin ajin , daga ita sai wani dalubi da yake karatu a can bayan benci
Wata me suna Maryam ce ta shigo ajin yayin da take kallon wannan dalubi da cewa.
"Munaf. Sannu da kokari."
Ya amsa mata da "sannu Maryam."
Kai tsaye gun Fa'iza ta nufa , yayin da take kiran sunanta tana kuma kokarin d'ago mata kanta sama
Cikin jajayen idanu Fa'iza ta d'ago
"Maryam ya akai ."
Maryam cikin rike haba ta fara fad'i.
"Haba Fa'iza, wai meke damunki, duk sai ramewa kike yi , haba dan Allah mene ne ."?
"Babu abin dake damuna Maryam."
Fa'iza ta maida mata da amsa
Ba tare da jira ba Maryam ta sake maida mata da cewa.
"Gashi idanunki sun yi jah , alamun kin yi kuka , ai shi ke nan , idan tayi wari maji ."
Dariyar da bata kai zuciya ba Fa'iza ta yi
Sannan ta ce .
"Ina Fatima."?
"Fatima tana can tana ta nemanki fa , bata san baki fito ba .".....
Fatima ce zaune kan gado tana kallon hotonta dana Fa'iza
Murmurshi tai tana shafa furkar Fa'iza, sannan ta fara cewa.
"Ban san meke damunki ba , wani abu ya dade yana damunki amman kin ki sanar dani ."
Zama ta gyara tana sake zumin din hoton ta cigaba da cewa.
"Aminiyata har a aljanna, ina kaunarki Fa'iza, in sha Allah zan yi kokarin sanin meke damunki, tun da baza ki sanar dani ba ."
Ta karasa maganar tana kallon saman dakinta kamar me yin wani Nazari .
"Wannan wanne irin rashin mutunci ne da cin fuska , yanzu yarinyar nan Laila kina ji wai yaron gidan Alaji Sani Shanshani zasu bawa."
Inna tai maganar bisa wayar dake hannunta ta kara a kunne
"Mene ne Alhaji Sani yafi mijin Rabi ? Tsabar cin mutunci, to wallahi wannan lamarin ba a a yi shi ba ."
Daga can bangaren Bahijja cikin muryar girmamawa ta fara cewa da mahaifiyar tata
"Dan Allah Inna ki yi hakuri abi wannan lamarin a sannu , yanzu haka ma ba haka zancen yake ba ."
Cikin wannan fada dai Inna ta sake fadin
"Kamar ya ba haka zancen yake ba , wallahi naje gidan naci mutuncin Nasir din , tunda ba shi data ido ."
Bahijja ta sake fad'in
"Ni dai dan Allah Inna ki hakuri, karki je gun Nasir da wannan maganar."
Inna ta ja dogon tsaki tare da kashe wayar tata
Anan kuwa Batula ce ke girki ta kunna wayarta
Tana sauraran wakar hamisu breaker mai taken "So Ne."
"Banza jaka kin damu mutane da waka."
Juyowa Batula tai tana kallon Rahma dake fada mata wannan maganar
Batula kashe sautin ta yi kana ta cigaba da abin dake gabanta
"Ai wallahi bari daddy ya dawo , zan fada masa Musa me gyaran takalmi yana son ki gara kawai a aura masa ke mu huta ."
Da sauri da tashin hankali Batula ta kalli Rahma tana cewa.
"A'a dan Allah Rahma, karki fadawa Daddy wannan maganar, Musa ba san shi nake ba , kuma daddy zai kama zancen ki ."
Cikin maraici Batula ta karasa maganar
"Hhhhhhhhhh to ai taimakon ki zai , banda shi waye yake son ki , can zaki talauci ya kashe ki banza ."
Tasa kai
Batula tai saurin riko rigar Rahma, hakan yasa Rahma ta dakata tana kallon ta cikin zafin rai
"Uban me zan miki kika riken riga kazama kawai."
Ba tare da Batula ta damu dajin wannan maganar ta Rahma ba ta fara cewa...
*MAHAUKACIN SO*❤️
Na
Autar Marubuta
_______________________________________
Babu editing
Page 19 & 20
"Kar ki fadawa Daddy, Musa kowa yasan ba ilmi ne dashi ba ."
Rahma tasa hannu ta doke hannun Batula, taja tsaki sannan ta wuce
Kawai hawaye Batula taji ya zubo mata
Anan kuwa Alaji Sani ne yake yin waya ,yadda ranshi yake a turbune bai canza ba ya fara cewa.
"Haba Akilu, to ita wannan yarinyar yar gidan waye, da zaka ce an nemeta a garin nan an rasa, bayan na fada maka ina tafiya a titin babbar unguwa ta taalakawa na ga yarinyar, sai da nai ta jira ko zanga inda ta shiga amman ban gani ba , gaskiya ka sake kokari Akilu ka zo min da labari mai dadi ."
Yana gamawa ya aje ajiyar zuciya tare da cewa.
"Gaskiya wannan yarinyar tamin , lokaci guda san ta ya kamani, tomm Hajjiya kishiya na tafe a gidan nan."
Ya yi maganar shi kadai yana tunano yadda yadda ya ga wannan yarinyar, sai abin yake faranta masa rai .
Sakamakon yau asabar babu inda Uncle yaje , tun wajejen hantsi yake a falo , har zuwa wannan lokacin da rana ta kusan faduwa.
Idan har kasan Yaya Nasir, to yanzu idan ka ganshi zaka iya cewa ba shi bane.
Duk da cewa shi ba mitum bane mai kiba , amman yana da matukar kyan gani
Lokaci guda kuma yanzu duk yabi ya lalace , tunda Mama ta fara maganar auren Laila.
Wayarshi tana gefe kusa dashi , yayin da shi kuwa yake kwance a kujera.
Laila ce ta fito daga dakinta sanye da hijab ta karaso gabanshi
"Uncle dan Allah me yake damunka , ko abinci har yanzu baka ci ba ."
Uncle ya kauda kai gefe kamar bai ji maganar tata ba .
"Uncle magana nake ."
Kallonta ya yi cikin wani yanayi na isa yana cewa.
"Tashi ki bani guri ."
Ta kalleshi tana sunkuyar da kai da ajiyar zuciya
Mikewa tai ta juya zata koma inda ta fito
Taji muryar Uncle Nasir yana cewa.
"Babu abin da yake damuna Laila."
Hakan yasa ta juyo ta koma ta sake zama , Shima Yaya Nasir ganin ta zaune ne ya tashi zaune.
"Uncle bani da kamarka a duniya, haifata ne kawai baka yi ba , idan nagan ka cikin wani yanayi bana jin dadi ko kadan , dan Allah Uncle idan a kan aure na ne ka dena damuwa, bazan auri kowa ba , sai wanda ka zaba mini koda bana san shi ."
Nasir ya yi murmurshi mai ciwo , sannan ya ce .
"Karki damu Laila, ina miki kaunar da bana son kowa ya rabe ki , amman akwai alamun lokaci zai raba mu ."
Mama ce ita ma ta fito rike da carbi a hannunta ta samu guri ta zauna.
Laila ta kalli Uncle cikin zumudi tana cewa
"Yawwa Uncle, shi ne baka taba fadan komai a kan Batula ba ko."
Wani dasss Yaya Nasir yaji ya dakar masa zuciya
Ya kalli Mama da sauri
Ba tare da Laila ta dubi yanayin da yake ciki ba , ta cigaba da cewa .
"Gaskiya Uncle tana san ka , naji kuma an ce ko saurararta baka yi ."
"Marainiya ce fa Uncle, wallahi tana shan wahala."
Ajiyar zuciya Yaya Nasir ya sauke tare da cewa.
"Nima ai maraya ne , sannan ke ma haka , babu wani soyyaya a tsakani da wannan yarinyar Batula, kin ga Laila ki dena maganar ta ."
Kafin Laila ta bude baki tai magana
Khairat ta turo kofa ta shigo tana sallama
Abin da ya basu mamaki ganin Batula biye a bayanta
"Wow Uncle, ka ga Aunty Batula 'yar halak."
Laila ta fada ta tashi da gudu tana rungume Batula
Yaya Nasir ajiyar zuciya yayi yana kauda kai gefe
Mama cikin far a ta kallesu tana cewa
"Auu wannan ne Batulan."?
Mama ta aje maganar daidai da inda Batula ta zube gaban Mama tana gashsheta
Nan Mama ta gaisa da Batula cikin sakin fuska, wanda hakan ya yiwa Batula dadi
"Yaya Nasir ina wuni ."?
Khairat ta fada bayan sun gaisa da Mama
Ita kuwa Laila Sam bakinta ya kasa rufuwa ,