Showing 15001 words to 16661 words out of 16661 words

Chapter 6 - MAHAUKACIN SO Complete Book Na Autar Marubuta.txt

28 Dec 2024

2902

nan , Kuma yaki bawa Laila kowa ta aura, sai ya ga kamar gaske son Laila ya ke kuwa
Amman Umar sai yayi tunani sosai , sannan ya koma ya tuba , domin lamarin tabbas ya yi muni sosai .


*MAHAUKACIN SO*
Na
Autar Marubuta
________________________________________


Babu editing


Page 25 & 26




Khairat da Batula ne a zaune, bayan Batula ta gama zayyanawa khairat tarin damuwa da yadda sukai da Alaji mahaifin Rahma.
"Amman gaskiya Batula wannan lamarin babba ne , yanzu ta ya har Uncle zai yadda da aureki , cikin kwana uku har yazo gidan ku , Tabb."


Khairat ta fada cikin gano matukar wahalar abin .
Batula ta amsa da cewa.
"Haka ne khairat, wallahi sai yanzu nima hankali na ya tashi, amman ya zanyi idan Musa shi ne kaddara ta ."


Ta aje maganar tana kuka , duk sai zuciyar khairat ita ma tai sanyi , amman haka ta fara rarrashin ta , duk da ita ma khairat bata da wani kwarin gwiwa.
"Assalamualaikum."
Laila ta shigo dakin kharait tare da sallama


Ita ta amsa sallamar ciki murya mara wadatuwar kuzari


"Ahh me zan gani haka , Aunty Batula mene ya faru kike kuka kuma."
Laila tai maganar tana durkusawa a gabansu.
"Mutuwa aka yi ne khairat."?
Laila ta sake fada.


Sai da khairat tai murmurshi sannan ta ce .
"Babu wata mutuwa, maganar auren ta ne, yayan babanta yace ta fito da miji kwana uku ko ya aura mata Musa, kuma kinsan Yaya Nasir take so . Sai kuma sauran matsaloli da baza a rasa ba ."


Cikin rarrashi Laila ta fara cewa.
"Haba Aunty Batula, dan Allah ki dena kuka , kuma in sha Allah da ikon Allah zaki auri Uncle dina , wallahi Aunty Batula zan yi duk yadda zan domin ki aure shi ."


Murmurshin farin ciki Batula tai tana cewa.
"Wallahi da burina ya cika Laila, da kuwa dukkan bakin cikina ya yaye."


Laila ta ce .
"Karki damu anuty."


Murmurshin jin dadi ita ma khairat tai sannan ta fara cewa.
"Ka ga yar gidan Uncle, daga ina haka ."
Laila ta ce .
"Hmmm daga gidan su Sadiya , kinsan yau ne Usman zai zo muje gidansu."




Dariya khairat tai tana cewa.
"Eh wannan gaskiya ne kuwa , ka ga amaryar Usman, sirikar Alaji Sani Shanshani."
Duk suka kwashe da dariya.




Sannan khairat ta sake kallon Batula tare da cewa.
"To ya maganar jarin ya baki baban Rahman."


Baki Batula ta tabe tana cewa.
"Tab! Ni na ce ma ko a kudin gadona ne ya bani , amman yaki, bazai banba , bai bani da cikakken hankali, kuma wallahi ina son bude shagon atamfofi da takalma ko salun ne ma."


Khairat tai murmurshi, yayin da Laila ta kara da
"Ummm Auntyna Batula."




Fa'iza ta gama shirin tarbar Abdallah tsaf,domin babu dadewa
Sai ga Abdallah ya zo , sai da ya kwashi gaisuwa wajen Alaji da hajjiya sannan tare da yi musu ya mai jiki, sannan ya samu damar isa inda Fatima da Fa'iza suke .


Tafiya suke cikin mota , babu wanda ya ce da kowa komai , sai dai kowa sake-saken shi yake a zuciyar shi.
Fargabar Umar kar Nasir yaje gida ya bayyana Mama wannan zancen, domin tabbas yadda ta tsufa sai ya kasheta kasheta lokaci guda, tunanukan da Umar ya ringayi ke nan ,
Ganin Nasir ya kusan kawoshi gida yasa shi fadin .
"Mu wuce gidan naku domin madam bata nan ."


Ba tare da Yaya Nasir ya bashi amsa ba ya cigaba da tafiya a mota, yayin da yake kara gudu .




Cikin kankanin lokaci suka isa gidan, Umar kamar yadda tun tuni ya saba ya fada cikin gidan yana sallama.




Sannan bayan Nasir ya aje mota , shima ya shigo .
Zama sukai a falon , lokaci guda kuma suna hada ido da juna .
Umar ya yi saurin kauda kai gefe, wanda yayi daidai da fitowar Mama daga dakinta.


"Auu kun dawo ke nan , Umar sannunku da zuwa."


Umar ya amsa da .
"Sannu Mama da gida."


"To bari a kawo muku abinci ai kunsha rana ."
Ta shige da nufin kawo musu


Ajiyar zuciya Yaya Nasir ya sauke me zafi, kamar me shirin fara magana , amman ya yi shiru.
"Nasir me zai hana ka dau hutu , kaje kaduna dangin Mama ai zaka huta ko."
Umar ya yi maganar kamar mejin tsoron Nasir.


"Ni yanzu babu wani hutu da zan je , anan ma ina hutawa ne ."




Lokacin Mama ta gama aje musu abincin sannan ta samu guri ta zauna.
"Mama ina Laila ne, tunda na shigo banji motsinta ba ."


Uncle ya tambaya


Mama ta kalli kofar dakin Laila kana ta ce .
"Tana can tana shiryawa , ko ka manta yau Usman zai zo ya kaita gidansu."




Da sauri Nasir ya mike tsaye, shima Umar yayi saurin mikewa.
"Lafiya kuwa, kaji min yara ."?
Mama ke nan
Umar ya yi murmurshin yake tare da komawa ya zauna.
Lokacin Laila ta shigo sanye da babban dogon hijabi ,


"Yau kika ce Usman zai zo Laila."?
Ta kalli Nasir da fad'in.
"Eh Uncle yama taho."
Ya koma ya zauna kamar wanda aka cirewa laka.
Ba tare da Laila ta dubi hakan ba ta fara cewa.
"Uncle dina dan Allah ina neman alfarma a gunka , dan Allah."


Ta karasa maganar tana durkusawa
"Tashi -tashi , hau kujera ki zauna.kin fi karfin haka lailata, ke rayuwa ta ce kuma babu abin da zaki nema ki rasa."
.
Ta mike ta zauna, Mama ta ce .
"Iko sai Allah, shakuwar Laila da Nasir."
Ba tare da Laila ta sake jiran komai ba ta ce .
"Uncle dan Allah ka dubi rayuwar Batula, ka share mata hawaye, ta nuna ka matsayin wanda zata aura, Uncle dan Allah ka aurota ta zamto matarka, tana cikin wani hali."


Idanunta cike da ruwa ta karasa maganar


Mama taja dogon numfashi, Umar kam lokaci guda ya rasa tunanin sa , domin ganin Nasir ya tsaya yayi jimmm yake tunanin irin amsar dazai bayar


Murmurshi mai cike da karfin hali Umar ya yi .
"Sannan ya ce .
"Masha Allah."
Nasir ya kalleshi




Wayar Laila ce ta fara ringin


Babu ko shakka Usman ne , hakan yasa ta mike cikin mutuwar jiki, Mama ta tashi ta nufi dakinta


Ganin Laila ta fita ne , yasa Umar fad'in.
"Dan Allah Nasir ka nutsu, kasan abin da zakana fade, ni wallahi idan ka bude baki zakai magana ba karamin tsoro nake ji ba , karkaji yadda zuciya ta ke zafi, gaskiya wannan ba Nasir din dana sani ba ne."




"Umar kanajin abin da Laila tace kuwa, Batula fa, bayan ba wanda nake son rayuwa da ita sai Laila, gaskiya lokaci yayi da ya kamata kowa ya sani."


Tsakiyar kan Umar ya sara , sakamakon jin maimaicin wannan zancen
"Shin dan Allah Nasir ina ilminka, dole ne na kaika wajen malam ya sake tabbatar maka babu aure a tsakaninku, haba Nasir."
Cikin kasa-kasa da murya ya yi maganar


Lokacin Laila da Usman suka shigo nan Usman ya gaidasu
Nasir ya mike tsaye tare da fad'in.
"Tare zamu tafi, kaima Umar idan zaka je ka taho, zan kai Laila gidan , ni banma san dalilin da yasa wani sai taje gidan ku ba ."


Ya yi tsaki ya dau mukullin motarsa ya fita .


Aiko haka aka tafi, motar Usman a gaba sannan Uncle da Laila a tasu motar


Haka suka isa gidan wannan shahararren mutum me kudi.
Tabbas Uncle sun ga karamci sosai, haka kowa na gidan suka gaisa da Laila cikin farin ciki.
Sai dai babban tashin hankalin da Alaji Sani Shanshani ya sami kanshi Laila ita ce yarinyar da ya ke ta neman ko yar gidan waye, domin tunda Allah yasa ya ganta kwanaki hankalinsa ya kasa kwanciya , tabbas son Laila yake bada wasa ba , sai dai kaf a cikin su babu wanda ya kula da irin yadda mahaifin Usman wato Alaji Sani hankalinsa ya tashi, bayan yaga Usman dansa ita ce yarinyar da yake burin aura.
Tabbas zamu ga yadda za ai da wannan MAHAUKACIN so.


A wannan tsakiyar daren Alaji Muktar ya tashi yana ta rusa kuka .
Haka har ya tashi matarshi Hajjiya ma'anatu.
"Lafiya lafiya kuwa Alaji."?
Ta masa tambayar tana share idanunta na bacci .
Cikin wannan kukan ya fara cewa.
"Tabbas Allah abin tsoro ne Ma'anatu, yanzu bani da komai sai tarin dukiya kawai, bani da farin ciki bani da sukuni , haka Allah ya yi wa Hajjiya rasuwa tana shirin ganar dani hanya me kyau, na zama butuulu abin gudu abin kyama, rayuwa ta babu wani kyau a cikinta."
Ya sake rushewa da sabon kuka


Duk sai tausayinshi ya kama Hajjiya, karon farko data fara ganin kukan sa .
Kafin ta ce dashi komai ya cigaba da cewa.


"Allah ya jikanki uwata, Allah ya jikanki Hajjiya, kullum gobe na kike son ta gyaru, gashi yanzu na girma, tsufa ya fara cimmin Hajjiya innalillahi wa inna'laihir raji un 😭."




"Tabbas lokaci ya yi da zan gyara kuskure na, ya Allah na tuba , ya Allah na tuba ."


Ya kwanta kafar Hajjiya Ma'anatu yana sake rangada kukanshi


Farkawar Fatima ke nan , ta tashi da niyyar yin sallar darenta kamar kullum yadda ta saba ,
Haske ta kunna cikin dakin tana kallon Fa'iza dake ta sharbar bacci .
Murmurshi Fatima tai tana cewa.
"Bari na yo alwaala kema tashin ki zan Fa'iza."
Ta karasa maganar yayin da kanta yayi wata sarawa
Hakan yasa ta koma bakin gadon ta zauna,tana dafa kanta ,
Ta bata wajen minti biyar sannan ta mike tsaye tare da shiga bandakinta dake cikin daki


Babu bata lokaci ta dauro alwala, sannan ta shinfida sallaya ,
Kana ta nufi bakin gado tana lissafin baza ta iya wannan sallar a tsaye ba
"Fa'iza."
Fatima ta fada da niyyar tashin Fa'iza a bacci .


Kafin ta sake bude baki ta kira sunan Fa'iza , taji muryar Fa'iza ba tare data farkaba tana cewa.
"Shi ke nan Abdallah, son ka ne kaddarata, amman kafi dacewa da Fatima, babu yadda zan yi ."


Cikin tashin hankali Fateema ta durkusa gaban Fa'iza dake bacci
Bisa idanunta ta ga hawaye jeri-jeri .




Ajiyar zuciya mai zafi Fatima ta sauke tare da fad'in.
"Abdallah kuma."🤔


To masu karatu alhamdulillah Masha Allah nan na kawo karshen free page na wannan labarin nawa mai suna MAHAUKACIN SO.


Ga masu son jin yadda kowanne sashi na wannan littafi zai kasance kofa a bude take Koda yaushe
masu bukatar cigaba da karanta wannan labarin, suna iya biyan kudinsu ta wannan hanyar 👇




7040805269 opay Fatima Abdullahi Ismail
Shaidar biya 07040805269
300 naira only 🙏

4
5
6

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login