Showing 3001 words to 6000 words out of 37323 words
Chapter 2 - ZAWARCI BOOK COMPLETE DOCUMENT BY Mrs Sadauki .txt
sai ki shiga kitchen ki girka min wake da shinkafa”
Idonta tab ƙwalla ta shiga kitchen ɗin ta ɗora tukunya ko kayan ba ta cire ba haka ta tsaya sai da ta tabbatar ta gama sannan ta zuba a plate ta kai wa Mamuh.
Da zafi da komai ta saka hannunta tana ci mai na bin hannunta sai wani lumshe ido take alamun yana yi mata daɗi, Sakeenatu wacce ta tsaya don ganin ko yau ma Mamuh za ta yi irin yanayin nan sai kuwa ta ga ta yi.Idon Mamuh sai wani haske-haske suke fitar wa kamar kullum muddin dai wake da shinkafa ta girka mata.
A tsorace ta nufi ɗakinta ,kayan jikinta ta rage sannan ta shiga toilet.Shower ta sakar wa kanta,kamar abun almara haka ta soma jin yanayin jikinta na canzawa tana jin feeling wanda kuma abu ne mai wuyar faruwa da ita muddin dai ba Abbas ke a wurin ba.
Abu kamar wasa amma sai yin gaba-gaba yake,kafin Sakeenatu ta farga tuni ta hankalinta ya soma gushewa ta dumulmiya duniyar son kasancewa da mijinta.Tamkar a mafarki ta soma jin kamar ana wasa da sassan jikinta,sai dai idonta sun yi nauyin da ba za ta iya buɗe su ba ballantana har ta ga shin zahiri ne ko kuwa? Sama da minti goma tana cikin wannan yanayi kafin ta dawo hayyacinta,a doli ta tsarkake jikinta ta fito tana mamakin al'amarin.Bayan ta shirya tsab cikin riga da zane sai ta fito falo,Mamuh ta gani sai sharar bacci take kamar matatta .Dining ta je ta zauna ta buɗe kulolin da ƴar aikinta ta yi girki,shinkafa ce da miyar kaji haka ta zuba ta soma ci tana mamakin yadda aka yi Mamuh ta zaɓi cin wake da shinkafa akan lafiyayen abincin nan .Bayan ta gama ta ɗauki waya ta kira Safeenat ta shaida mata za ta zo yanzu ,sai kuma ta koma ɗaki ta saka hijabinta ta ɗauko jaka ta fito.Tana fita ba ta wani wuya ba ta samu ɗan sawu ya kaita,da sallama ta shiga gidan har ta wuce can ɗakin da Safeenatu take wanda ya cika da mutane kusan dangin Bashir ne.
A mutumce take gaishe da kowa amma yanayin jikinta na bata ana kallonta,tana juyawa suka haɗa ido da Habibah wacce ta kasa ɗauke idonta kan Sakeenatu har sai da ta ji ta tsargu.Ta zauna kusan Safeenat tana mai cewa “waccan wace ce sai kallona take?”
“Ƙanwar Daddy ce fa ba ki gane ta ba?” Feenat ta faɗa tana mai miƙa mata boy bayan ta shafi kansa sai kuma ta ajiye shi aka miƙa mata girl ɗin.Wani irin shock ne ya ratsa Sakeenatu har sai da ta zabura,yayin da gabanta yayi mummunar faɗuwa ganin Babyn ta buɗe idonta tana kallon ta alhalin lokacin da aka miƙo mata ita tana bacci.Sakeenatu ba ta ida shiga tashin hankali ba sai da ta ga tamkar Babyn na yi mata murmushi......
[23/09 à 04:23] MRS SADAUKI 💫: *ZAWARCI*
LoVe aNd HoRrOr StOrY☠️
*Mallakar:* Chamsiya Laouali Rabo
(MRS SADAUKI💫✍️)
*Lambar waya:* +22795045822
*FIRST CLASS WRITER ASSOCIATIONS☀️*
Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation.
*Sadaukar wa:* Rahama Sabo Usman
_____________________
23/09/24
4-5
Wani irin abu ne marar misaltawa ke ratsa Sakeenatu tun daga kan babban yatsan ƙafarta har zuwa kwanyarta da ta soma toshe wa .Lamarin da take ji a al'aurarta kuwa kusan girme wa hankalinta ya yi,tamkar wacce ake fitar wa da wani dafi haka take jin ana yi mata motsi gami kuma da samun sassauci a doli ta lumshe ido ba ta shirya ba.Ita kuwa Gwaggo Habibah da ke can gefe sai murmushi take tare da yin zancen zuci don duk tana ankare da abin da ke faruwa.‘ Tabbas a duk inda ke da mugunta da cutar wa Allah sai ya kawo mai ceto mai magani,na zo kenan a gidan nan mutuwa kawai za ta fitar da ni zan saka ido sosai akan jaririyar nan zan raine ta da hannuna ta yadda zan taimaka mata wurin fahimtar baiwar da Allah ya yi mata da yadda za ta sarrafa ta’ sai kuma ta miƙe tana yin wani murmushin nasara.Babyn ta ɗauke daga cinyar Sakeenatu wacce gumi ya jiƙa ta har goshinta na ɗiga,babu kuma wanda hankalinsa ke wurin hatta ita Safeenat sai hira take da dangin mijinta waɗanda suke cewa shi namijin a saka masa suna Bashir a yi madadi.
Sakeenatu ta ware idonta jikinta na ɗan rawa kamar wacce ta farka daga mummunan mafarki.Idonsu ya sarƙe cikin na juna,Gwaggo Habibah ta ce “ sannu! Bari na nemo miki ruwa masu sanyi” sai kuma ta shimfiɗe babyn wacce tuni ta koma baccinta.
Kitchen ta nufa don samo ruwa masu sanyi,sai suka yi kiciɓis da Gwaggo Hajara ƴar kallon-kallon suka yi kowacce na hararen ƴar uwarta.
“In tusa za ta iya hura wuta a yi mu gani mana,sai shegen kinibibi da nuna isa kan an san ɓoyayyar duniya nan kuma ba asss ” Gwaggo Hajara ta faɗa don kuwa a goshin Habibah ta fahimci sun karya wata muguntar tsafi.
Ita kuwa Habibar murmushi ta yi don ta fahimci mi take nufi wato in ta isa ta yi wa kanta maganin damuwarta.“ Nan gishirinki zai ƙare a dafuwar ƙaho,yadda bacci ya bar ido haka za ki gaji ki bar Habibah saboda kabewar kan kabari nake baƙin cikin masu taushe”
“Aikin banza sai aukin cika baki ,a hakan kuma na yi sanadin hana ki baccin kullum cikin kukan kin ƙi haihu ba”
“Haihuwa ai ta Allah ce,kuma alhamdullah yanzu na samu irina wacce tsoron samun ta yasa kika jefo min mugun nufinki ” Habibah ta faɗa tana wani murmushi,Gwaggo Hajara ta kasa cewa komai yayin da ita kuma ta ci gaba da cewa “ ko ba ki gane abin da nake nufi ba? To Safeenatu ta haifi wata Habibar sak irina ce ko na ce ma ta fi ni don ita murucin kan dutse ce ba ta fito ba sai da ta shirya” muƙut! Gwaggo Hajara ta haɗiye wasu yawun tsoro don kuwa ta fi kowa sanin babyn Safeenatu ba normal jaririya ce ba tun da ta ga zahiri.
Ta ja wani irin numfashi jin saukar ruwan sanyi kan fuskarta,dakyar ta ware ido tana kallon Habibah wacce tuni ta juya ta yi tafiyarta tamkar ba ita ce ta gama zuba mata ruwan a fuska ba.Cike da baƙin ciki ta koma ɗakinta,a yadda take jin jininta ya hau in ba jini ta sha ba ƙila zuciyarta sai ta buga.Tukunyar tsafinta ta ɗauko ta yi ƴan surkullenta kafin ta ɗauki mayafi ta fita waje,yara ta gani suna wasa daga inda take a tsaye ta soma kiran kurwar wani yaro cike da ƙwarewa wurin maita tsafi.Yaron ya dafe gefen wuyansa inda ya ji kamar an tsikare shi da allura amma bai bar wasar ba haka yake ci gaba da gudun yana son kamo wani,idonsa ne suka soma rufe wa kafin bugun zuciyarsa ya tsaya cak kawai sai ya faɗi ga ƙasa.Ita kuwa Gwaggo Hajara da wani mugun sauri ta rufe ƙofa,tuni yara sun fara ihu suna faman kiran sunansa.
Ɗakinta ta koma ta ci gaba da tsotse jinin yaron ko jira ba ta yi ba,don ta san sarai in ta jinkirta ajiye kurwarsa Habibah za ta iya fahimtar haka.Tsawon lokaci ta ɗauka cikin siffar mugunta kafin ta dawo normal,zuciyarta ta ji fayau babu ƙunci.Tana nan zaune sai ga Munira wacce rabon ta da gidan tun lokacin da aka ce ta fita.Kusa da mahaifiyarta ta zauna ta soma bata labarin yadda yaron maƙwabciyarsu ya faɗi suna tsaka da wasa,“ je ki nemo min Munir ya dawo gida ” shi ne kawai abin da ta ce tana jin wani daɗi a ranta ba don komai ba sai don ta yi mugunta.
Habibah na shiga ta miƙa wa Sakeenatu gorar ruwa mai sanyi haka ta shanye su tasss tana sauke ajiyar zuciya.“Ki dinga kula da kan ki mana,ko barin kai a buɗe ai yana sa maƙiya su yi galaba kanka”
“To in sha Allah ” Sakeenatu ta faɗa tana mai ɗan satar kallon jaririyar ƙawarta,ido ɗaya babyn ta buɗe ita ma tana kallonta babu shiri Sakeenatu ta miƙe tsaye tana cewa “ Feenat zan tafi sai kuma gobe in sha Allah zan zo da safe tun da babu aiki”
“Na gode sosai Keenat wai ina Ma'idah?”
“Tana wurin Mama tun wancan satin na kai ta kin san Komandan ta zo”
Safeenat ta waro ido ta ce “ ki ce dai a takure kuke yanzu,kai tsohuwar nan an yi ƴar masifa mine ne na zuwa hutu ke ba ƴar makaranta ba”
Sakeenatu ta tuntsire da dariya ta ce “ kar a yi babu ita mana,duk gani take wasu kuɗi ne da shi ba ta san rabin hidimar gidan ni ke yi ba a haka kuma za ta dinga tsiro da abubuwa tana saka sharaɗin abin da take so”
Safeenatu ta ce “ ah lalle ta ci sunan Komandan ɗin” nan dai suka yi sallama Sakeenatu ta fito.Kafin ta isa gida sai da ta saya wa Mamuh kifi don ta san tana son shi,da sallama ta shiga amma ta ƙi amsa mata sai ma tambaya da ta jefo mata “ daga gidan uban wa kike? Wato kin matsu na koma ƙauye shi ne kika je gidan malamai da bokaye a yi min asiri na tafi ban shirya ba”
Jikin Sakeenatu banda rawa babu abin da yake yi,kanta ƙasa ta soma rantse-rantse tare da sanar da ita inda ta je.
“Ita ƙawar taki ce ta baki magani kika yi wanka da shi ta yadda zan ji tsoron ki? Sakeena lalacewar taki har takai ki dinga faɗawa ƙawarki ƙarya da gaskiya akan ta baki magani? In maganin za ki nema mi yasa ba ki ce a baki na haihuwa ba sai na korar maƙiyiyarki”
“Wallahi Mamuh babu wani magani da aka bani,na faɗa miki barka kawai na je” Keenat ta faɗa cikin muryar kuka.
Mamuh ta tsure ta da ido,sam babu tabon duk muguntar da ta ajiye a jikin Sakeenatun komai ya rushe ta koma normal.Sannan a baccinta aka nuna mata ta yi wanka da ruwan magani duk mugun nufinta ya fita daga jikinta,jin shiru yasa Sakeenatu ta ɗago ido da zumar kallon Mamuh mugun ganin da ta yi ne yasa zuciyarta kusan faso allon ƙirjinta ta faɗo.
Idon Mamuh sak irin na maciji yanayin fuskarta ma ya canza duk ta yi baƙi,“ in kin gama gulmar sai ki wuce ki ɗora min wake da shinkafa” Mamuh ta faɗa tare da yin gaba,Sakeenatu ta ce “ akwai sauran na ɗazu bari na zubo miki ”
Ba tare da ta juyo ba ta ce “ ban so wani nake so ki dafa min”
Jakarta ta ajiye ta shiga kitchen ta ɗora girkin,wannan karon ko waken ba ta wanke ba kamar yadda tsarin dafa shi ya zo mata daga Mamuh ɗin ,dama ita shinkafar ba irin wacce ake wankewa ce ba.Cikin plate ta zuba bayan ta tsalala mai dayawa,sai ta fito ta nufi ɗakin Mamuh da sallama ta shiga duk da ta san ba za ta amsa ba.
Cike da ladabi ta duƙa har ƙasa ta miƙawa Mamuh plate ɗin wake da shinkafar amma ta ƙi karɓa sai ido da tsura mata.Tuni gaban Sakeenatu ya fara dukan uku-uku,“ ba zan ci ba!”
“Amma ke kika ce na girka miki ” ta faɗa murya na rawa.
“Tun zuwana gidan nan na faɗa miki sai an dirje wake an waken shi da hannu sannan ake girka min mi yasa yanzu ba ki yi ba?”
“ Na zata kina jin yunwa ne sosai shi yasa na yi haka don na yi sauri”
“To sai ki je ki sake dafa wani” Mamuh ta faɗa tana mai miƙe wa tsaye,cikin dakiyar zuciya Sakeenatu ta ajiye plate ɗin ta ce “ ki yi haƙuri Mamuh akwai aikin da nake son yi yanzu,ki ci wannan ɗin gobe in Allah ya kai mu sai na yi miki irin wanda kike so ɗin”
Sam ko kaɗan Mamuh ba ta yi mamakin furucinta ba ,don dama da tsafi ne ta ci galaba har Sakeenatun ke mugun tsoronta yanzu kuma komai ya karye.Ita kuma tana gama faɗar haka ta fice,da ta fito har sai da ta ja ajiyar zuciya tana mamakin yadda yau ta cire tsoron Mamuh.
Tana shiga wanka sai ta ga period ɗinta ya zo,wanda kuma ba komai ya haifar da haka ba sai gwagwarmayar fitar da sihirin jikinta.Cikin ƙananan kaya ta shirya sannan ta haye bed tare da kiran Abbas,cike da nishaɗi suka yi hirar soyayya nan ne kuma ya shaida mata gobe zai zo sannan a karɓo Ma'idah don ita yake son fara cin karo.Har ƙasan ranta ta ji daɗin furucinsa , wannan yasa suna gamawa ta kira can gidansu ta ce a kawo mata Ma'idar.
Washegari
Kuwa tun safe Sakeenatu ta soma gyaran gida ita da ƴar aikinta wacce ba za ta wuce shekara ashirin ba mai suna Fa'iza.Mamuh dai na ta kallonsu ba ta ce komai ba don fushi take da Sakeenatu,da kanta ta yi girki Fa'iza na kama mata.
“Shi kuma waken nawa sai yaushe za a girka?” Mamuh ta leƙo kitchen ɗin tana mai faɗar haka.
Sakeenatu ta ce “ yanzu zan yi” ba ta ƙara cewa komai ba ta tafi.
“Fa'iza wanke min waken nan da kyau sai ki girka wa Komandan ban son ta kawo min cikas ina cikin farin ciki”
Ƴar dariya Fa'iza ta yi kafin ta soma wanke waken kamar mai wankin kaya,ita ce ta girka shi kuma.Sakeenatu ta zuba a plate da kanta ta kai wa Mamuh jikinta har rawa yake ta soma ci tana lumshe idonta waɗanda tuni suka soma yin hasken nan.Ita dai Sakeenatu Allah na gani tsoron yanayin nan take ,da sauri ta wuce ɗakinta ta yi wanka ta shirya cikin wani rantsatsen less tana tsaka da fesa turare Ma'idah ta shigo da gudunta ta na kiran Ammyna.Ita ma sosai ta yi kewar yarinyar sai ta rungume abarta tana cewa “ ke da wa ne?”
“Anty” ta bata amsa.
A ɗan firgice Nafisa ta shigo tana cewa “ anty Sakeena wace ce waccan a kitchen? Zo ki ga abin da take”
“Ƴar aikina ce lafiya?”
“Zo dai ki gani” cewar Nafisar tana mai yin gaba Sakeenatu na take mata baya har suka shiga kitchen ɗin.
Fa'iza suka tarar duk ta cire suturar jikinta tana fitar da wani nishi idonta a rufe suna tsiyayar da hawaye.......
[25/09 à 08:09] MRS SADAUKI 💫: *ZAWARCI*
LoVe aNd HoRrOr StOrY☠️
*Mallakar:* Chamsiya Laouali Rabo
(MRS SADAUKI💫✍️)
*Lambar waya:* +22795045822
*FIRST CLASS WRITER ASSOCIATIONS☀️*
Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation.
*Sadaukar wa:* Rahama Sabo Usman
_____________________
24/09/24
6-7
Tamkar wacce ke wata mu'amala da namiji haka Fa'iza ke yi ,hankalin Sakeenatu in yayi dubu to ya watse.Ta kalli ƙanwarta ta ce “ Nafisa ko iskokai ne? Dubi abin da take yi”
Nafisa ta ce “ anty Sakeena tun da nake ban taɓa ganin mai kalar iskokan nan ba,hatta masu aljanin soyayya ai sai in suna bacci ne suke zuwar musu dubi ita wannan fa tamkar idonta biyu fa”
“Yanzu dai don Allah ki taimaka mata tun da ke Malama ce kin ga Ma'idah har ta soma kuka” cewar Sakeenatu tana mai jan ƴarta zuwa waje.Nafisa ta cika kofi da ruwa ta tofa ayatul ƙursiyu da amanar rasulu sannan ta shiga watsa ma Fa'iza ruwan,a sannu a hankali ta soma barin abin da take daga ƙarshe ta buɗe idonta waɗanda suka kaɗa suka yi ja.Nafisa ta shiga yi mata sannu kafin ta taimaka mata ta mayar da kayan jikinta,“ dama kina da aljanu?” Sakeenatu ta tambaya wacce ta dawo.
Fa'iza ta girgiza kai,“ to tashi ki yi wanka sai ki zo ki zuba abinci ki ci”
Da “ toh” ta amsa kafin ta fita zuwa Toilet ɗin tsakar gida kamar yadda Sakeenatu ta shaida mata da ita za ta dinga amfani.
Wanka ta soma sai da ta saɓa jikinta har sau biyu sannan ta fito,wasu kayan Sakeenatu ta bata ta saka abincin ma da ta zuba gidansu ta wuce da shi.
Su kuwa a falo suka zauna suna hira Nafisa na bai wa Ma'idah abinci a baki,Abbas yayi sallama da gudu ta nufe shi tana “ Daddyyy” ya caɓe ta tare da cira ta sama yana yi mata wasa haɗi da kai mata sumba.
Cike da farin ciki ya ƙarasa ya zauna,Nafisa ta gaishe shi yayin da suke aikawa juna wani kallon so shi da Sakeenatu mai cike da kewa.
“ Mu je ka fara yin wanka ko?”
“A bani abinci tukuna don Allah ” ya faɗa yana wani murmushi,Ma'idah ta ce “ Daddy ni ma ina ci” sai aka zuba musu ya dinga bata a baki ita kuma sai surutu take yi masa.Suna tsaka da nishaɗinsu sai ga Mamuh ta fito,fuskar nan kicin-kicin,“ ita kuma wannan farar tinkiyar?” ta yi tambayar tana zunɗen Ma'idah wacce ta tsorata da ganin Mamuhn.
“Ina wuni Mamuh? Fatan na same ku lafiya?” Abbas ya faɗa cike da ladabi.
“Ka bani amsa ta”
“Ma'idah ce fa ƴar wurin Keenat” ya bata amsa a sanyayye.
“Shegiya za ka ce wacce ba a san taƙamaimai wane ne ubanta ba,kai da ka iya kwashe-kwashe ka rasa wacce za ka auro sai wadda ta gama yawon duniya ta tsiyayar da duk ƙwayaƙwayin haihuwarta a titi.To ban yarda ban lamunce wannan tinkiyar ta zauna a gidan nan ba” Mamuh ke faɗa cikin masifa ita kuwa Ma'idah tuni ta soma kuka musamman irin abin ban tsoron da take hangowa a fuskar Mamuh.
Abbas ya sunne kai ya ce “ a dai yi haƙuri Mamuh dukkan bawa bai wuce jarabawa,Ma'idah ita yarinya ce ba ta san komai ba”
“Wallahi sai ta bar gidan nan” Mamuh ta faɗa cikin ƙaraji, Sakeenatu kuwa banda kuka babu abin da take yi .
Hannun Ma'idah ta kama da niyyar jawo ta,ita kuwa baiwar Allah cike da tsoro ta ɗauki cokali mai yatsu ta caka ma Mamuh ita a ido da zumar ceton kanta ga dodo.
Wani uban ihu Mamuh ta yi tana cewa “wayyo idona! Ƴar daba ta kashe ni” jikin Abbas na rawa ya je ya kamo Mamuh wacce tuni idon ya soma fitar da jini,hankali tashe ya soma goge jinin wani na zubowa a doli ya kama ta zuwa asibiti.
Bayan tafiyarsu ne Nafisa ta soma tofa ma Ma'idah addu'o'i saboda yadda take wani irin kuka tana firgita,cikin kuka Sakeenatu ta ce “ Nafisa ki ɗauke ta ku wuce gida don Allah”
“Ke kuma a nan za ki zauna? ”
“To ina zan je Nafisa? Haƙuri zan yi dama