Showing 9001 words to 12000 words out of 37323 words
Chapter 4 - ZAWARCI BOOK COMPLETE DOCUMENT BY Mrs Sadauki .txt
ta zuba su ne a harakar boko wannan ya sa ba ta iya wasu addu'o'i ba .A halin yanzu da take tsaye ta yarda kuma ta aminta rayuwarta na cikin haɗari,tabbas ta san wannan magen ba normal ba ce muguwa ce cutar da ita za ta yi.
Ta na dab da ta kawo kusa da ita ta samu bakinta na furta “ la haula wala ƙuwata illa billah!!!” ƙiiii magen ta wani ci burki tana mai canza salon kuka zuwa na jarirai amma sam Sakeenatu ba ta yi gigin yin shiru da bakinta ba sai ma ƙaimi da ta fara wurin maimaita addu'ar.A gaban idonta magen ta soma mayar da idonta kamar na mutane kafin ta ruga a guje ta yi tsalle ɗaya ta haye katanga,daidai nan kuma aka maido wuta yaran unguwa suka hau ihun murna.Sakeenatu ta ja ajiyar zuciya tana mai yin hamdala ga Ubangiji,bakinta bai gushe ba yana ta furta lahaula wala ƙuwata illa billah a haka ta koma can ciki.Gas ɗin ta kashe saboda muguwar gajiya da ta saukar mata wacce ba ta san dalili ba,wayarta ta ɗauka Allah yayi sa'a babu abin da ya same ta abun mamaki kuma yanzu cajin wayar a cike yake saɓnin ɗazu da aka nuna mata ta kusa mutuwa.
Lambar Nafisa ta kira,tana ɗauka babu wani tsaya wa gaisuwa ta ce “ Nafi ki turo min karatun nan da kike saurare don Allah duk dare”
“Anty Sakeena lafiyar ki kuwa?”
“Ki turo min karatun dai don Allah ina son saurare ”
“Ok to bari na hauda data yanzu zan turo miki”
“Yawwa ina jira” ta faɗa tare da kashe kiran,ita ma datar ta kunna babu jimawa kuwa karatun ya shigo suratul Baƙara ce ta turo mata sai Yasin .Tamkar abun tsiya network ɗin ya ɗauke ɗif ko ɗaya babu wanda ya buɗe,juyin duniya ta yi amma sun ƙi buɗewa har wayar ta kashe ta kunna amma network ɗin ya ƙi yi.Cike da damuwa ta sake kiran wayar ƙanwarta,tana ɗauka sai ta rasa abin da za ta ce mata kawai ta fashe da kuka.Daga can ɓangaren Nafisa ta ce “ subahanallah! Anty Sakeena don Allah mike faruwa? Mike damun ki?”
Cikin muryar kuka take cewa “ Nafisa tsoro nake ji! A tsorace nake ji nake kamar ba ni ɗaya ba ce cikin gidan nan tamkar ina ....inaaa” ta kasa ida maganar saboda motsin da ta gani ana yi can cikin labule wanda ta tabbata kuma ba ɓera ne ba saboda girman halittar.Ihu ta fasa ganin ƙatuwar gafiya ta faɗo timmm da ƙasa,yayin da kuma wata ta biyu ita ma ta sake fitowa a guje ya kama waccan wacce ta faɗo a gaban idonta suka soma faɗa suna cizon junansu.Babu shiri Sakeenatu ta haye ɗaram kan bed ta na kuka,Nafisa na jin haka ta ziri hijabi ta fito ko Mamarsu ba ta sanar ma ba ta fito ta samu ɗan sahu.Allah yayi sa'a ba wani nisa ne sosai a tsakaninsu ba,da gudu ta shigo gidan tana ambaton sunan Allah daidai nan gafiyoyin suka yi ɓatan dabo hatta.
Nafisa ta je ta rungume ƴar uwarta wacce da ace tana da cutar asuma da tuni numfashinta ya fita,“ yi shiru don Allah ya isa yi min bayanin mike faruwa? Ina shi Abbas ɗin?”
“Yana asibiti wurin Mamuh,na dawo na dafa mata wake da shinkafa ne shi ne ake ta firgita ni” nan ta kwashe duk abin da ya faru ta shaida wa ƙanwarta.
Nafisa ta ja dogon numfashi bayan ta saurare ta,sannan ta ce “ wannan duk sharrin miyagu ne shi yasa a kullum ake son bawa ya keɓe wani lokaci don nemawa kansa kariyar ruhi da gangar jiki ba wai gyaran duniyarka ba kawai.Ni wallahi na fara zargin Mamuh ɗin nan,kina dai ganin yadda Ma'idah ta caka mata cokali da dukkan alamu ta hango abin da idanunmu basu gani.In ba masifa ba cikin daren nan za ki dafa mata wake kamar mayya,ke ƙila ma ita ce.Tashi mu je ki yi alwala ai zama bai gan ki ba tun da kin ji kin gani aure a inda ba a ƙaunar ki”
Da taimakon Nafisa ta yo alwala dama ita Nafisar kusan kowanne lokaci tana da alwala mace ce mai riƙo da addini ba ta da sake,hasali ma malamar makaranta ce a wata islamiyya.
Karatun Alkur'ani ta soma koya wa Sakeenatu kamar wata ƴar yarinya haka take biyawa inda ta yi kuskure kuma ta gyara mata.
“ Ki kasance kullum cikin tsarki bima'ana alwala saboda tana da muhimmanci sosai wurin bada kariya,ko sheɗanu suna shakkar mutum mai zama da alwala a koyaushe,ke ko period kike to ki yi abarki sannan ki riƙe azkhar na safe da maraice”
“Amma ai kin san ban iya su ba ko?”
“Ki koya mana anty Sakeena ,shi ilimi ai bai da ƙa'ida shekaru ko tsoho ɗan shekara ɗari zai iya shiga makaranta ballantana ke da ko talatin ba ki kai ba”
“ Ni rubutun larabcin ne ke bani wuya ”
“Zan nemo miki littafi mai fassarar Hausa ,sai na dinga koya miki yanzu bari na tura miki app ɗin Alkur'ani sai ki dinga saurare ”
Ta karɓi wayarta ta tura mata tare da saita mata komai ta kunna sautin ya soma tashi,ta ce “ to ni zan tafi gida ko Mama ban sanar ma ba”
“ Don Allah Nafisa kar ki tafi ki bar ni ki jira har Abbas ya dawo,bari na kira Mamar na shaida mata” haka suka yi kuwa,tun suna jiran Abbas har ƙarfe sha biyun dare bai zo ba a tare suka fito suka rufe gida da ko ina sannan suka je suka kwanta.
A can asibiti kuwa bayan fitar Sakeenatu,Gwaggo Rahamu ta yi wani kishingiɗa ga kujera kamar mai bacci nan kuwa ruhinta ne ta soma fitar wa daga gangar jikinta.Sawun Sakeenatu ta bi,hasali ma ta rige ta zuwa gidan duk abin da take yi akan idonta hanyar farko da ta soma bi shi ne tafiya ta shiga tunanin mai kula da nepa na unguwar ya ɗauke wuta ba tare da shi kansa ya san dalili ba a cikin wannan duhun ne ta yi ta yi wa Sakeenatu mugunta.Da ta koro ta da addu'a shine ta biya wurin wasu miyagun ƙawayenta ta basu address suka je a siffar gafiya,su ma ba su bar gidan ba sai zuwan Nafisa.
Abbas na daga can gefe Mamuh na yi masa hira tana murmushi saboda duk abin da ke faruwa ita tana gani saɓanin shi Abbas ɗin.Bayyanar esprits biyun yasa yanayin shaƙar iskan ɗakin ta sauya saboda tsabar muguntar su, wannan karon hatta Abbas sai da ya ji wani iri.Har yanzu Gwoggo Rahamu ba ta farka daga baccin ƙaryar da take ba,cikin hirarsu ta ƴan duniyar ɓoye suke bata labarin yadda suka firgita Sakeenatu tana ta yin kuka.
“Na gode sosai ƙawayena,kar ku manta in kun gama yawon Maitar dare ku biyo ta nan mu sake komawa mu uku mu haɗa ƙarfi mu shayar da ita mamaki” baƙin ruhin Gwaggo Rahamu ya faɗa ,suka yi dariyar mugunta tare da ɗaukar mata alƙawari kafin su bar wurin.Cikin ƙwarewa ta dawo da ruhinta a gangar jikinta,ta dubi Abbas tana mai cewa “ bacci ya ɗauke ni duk yau ban rintsa ba,ina sauran waken ni ma na ci yunwa nake ji”
Shi Abbas sam ya manta da wani zancen wake saboda yadda Mamuh ke masa hira,sai yanzu ya tuna Sakeenatu ta je gida dafawa.Da ya duba agogon hannunsa ransa ne yayi mugun ɓaci,“ uwar tamu ai ba ta dafo ba tana can tana gantalin da ta saba,ah to dama su likitoci ba su da kamun kai tsakaninsu da abokan aikinsu suke neman juna in aka ce miki tana can asibiti wani ƙato ya taushe kar ki yi gardama” Mamuh ta faɗa ,yayin da Gwaggo ta karɓe “ i sosai ita ma wannan shegiyarta ta ai shugabansu ne ya ɗirka mata cikin ya bar yaronmu da wahala,wai Abbasi wai ya ƙaƙaba maka aurenta?”
Kasa cewa komai yayi,haushi goma da gomiya tara ya rasa da wane zai ji abin ka kuma da zuciyar namiji sai ya ji zargi ya ɗarsu a ransa.Da ya nuna zai je gida Mamuh ta hana shi tafiya ta hanyar amfani da tsafinta,haka suka dinga kwaso sharri iri-iri suna yaɓa ma Sakeenatu sosai kuma suke samun gurbi a zuciyarsa.Can waje ya koma ya kwanta kan wani banci yana ta tunanin rayuwa baya yadda neman aurensa ya kasance yadda sam Sakeenatu ba ta samu shaidar ƙwarai ba ga mutanen unguwa amma ya rumtse ido ya ce sai ita .
Ƙarfe biyu da rabi na dare ƙawayen Gwaggo Rahamu suka biyo mata,kafin su yi tsinke gidan Sakeenatu.Sai da suka shiga kitchen suka cinye kaf abincin da ta dafa sannan suka dawo falo suka fara shawarar abin da za su yi mata,suna dariyar mugunta suka tura ƙofar falon sai dai da zarar sun yi niyyar ɗora ƙafarsu a tile ɗin bedroom sai su ji tamkar cikin garwashin wuta ne suke ɗora su.Gwaggo Rahamu ta ƙanƙance ido tana kallon gefen Nafisa inda kusan kanta ta ɗora wayarta ne sautin karatun Alqur'ani na tashi a hankali wanda ba ma a jinsa sosai,kamar ta san suna nan kuwa sai ta kai hannu ta ƙara volume a tare suka saki wani ihu wanda sai da gidan ya girgiza a firgice Sakeenatu ta farka tana zarar ido
My book is only 500 via 6042551755
Hassana ibrahim
Keystone bank DM +22795045822
[28/09 à 08:36] MRS SADAUKI 💫: *ZAWARCI*
LoVe aNd HoRrOr StOrY☠️
*Mallakar:* Chamsiya Laouali Rabo
(MRS SADAUKI💫✍️)
*Lambar waya:* +22795045822
*FIRST CLASS WRITER ASSOCIATIONS☀️*
Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation.
*Sadaukar wa:* Rahama Sabo Usman
_____________________
28/09/24
10
A wahalce Gwaggo Hajara ke bin bango don isa ɗakinta,fatar nan tata ta tsakaka duk ta yi wani taushi ta fara fitar da wani fanko.A yadda bango ke zuzar fatar cikinta ji take kamar ta yi ta ƙurma ihu sai dai ba dama sata lahira! Tana isa ɗakinta ta ɗauki siffa ta mutum nan ne fa ta yi tozali da yadda duk jikinta ya kumbura yayi ja kamar wacce aka soya,mai ta ɗauko ta shafe jikinta da shi tana matsar ƙwalla tare da jin tsanar Safeenatu na sake feso mata daga can ƙasan zuciyarta.
A fili ta furta “ sai na wulaƙanta rayuwarki,sai na saka kin tozarta a duniya,sai na shayar da ke gubar azaba wacce sai kin gwammaci mutuwa akan rayuwarki. Ke kan ki Habibah ba zan bar ki ba zan ɗora miki karatu da alamu har yanzu ba ki ji jiki ba shi yasa kike taimaka wa wata wurin ruguje plan ɗina” shiru ta yi jin an turo ƙofa.Daddy ne ya shigo da sallama a bakinsa,ba ta amsa ba sai ma saurin jawo hijabi da ta yi ta saka duk ta luluɓe jikinta.
“Ni kam Hajara lafiya kike? Kin ga yadda fuskarki ta yi suntum sai huci take kamar ƙullun wainar da ya ji yis?” Daddy ya faɗa yana ƙare mata kallo.Wani ƙululun baƙin ciki ne ya ƙara turnuƙe Hajara ta ce “ uwar waina ce....” ba ta ida kai aya ba ta ji yatsun Daddy biyar kan kuncinta,shaye da mamaki take kallonsa nan ta hango wani baƙin tauraro tsakiyar goshinsa wanda ko shakka babu aikin Habiba ne ta tura masa shi.
Ba ta gama dawowa daga duniyar mamakin da ta je ba Daddy ya soma magana cikin masifa,“ wato abun naki ya fara zama iskanci,daga tambaya shine za ki zagin uwata saboda kin san yau za ta zo.To tsaya ki ji Hajara duk wata tijararki ki tattara ta ki ajiye wuri guda muddin Hajiya ta koma da baƙin cikinki gida to wallahi akan aurenki.Ki tashi ki ɗora girki tsabar lalaci muna da mai jego a gida amma kin zo kin shige ɗaki kin haye gado tare da saka hijabi kamar matar liman kowacce za ta yi aikin ƙwarai” yana gama faɗa ya nufi ƙofa,sai kuma ya juyo ya ce “ Murjanatu na kan hanya sai ki fara shirin tarben ta” kawai ya fice.
Gwaggo Habibah da ke zaune kan kujera a falo ta saki wani irin murmushin nasara,tun da uwarta ta haife ta yau ce ranar farko da ta juya taurarinta na baiwa ta yi aiki da su.Tun bayan da ta yi wa Twins wanka ta shirya su sannan ta bai wa uwarsu abin da za ta ci kawai ta fito falo ta zauna,Daddy na fitowa ta soma yi masa transfer ɗin tauraron ta hanyar kallonsa tsakiyar ido da farko har ya tambaye ta lafiya sai kuma yayi shiru jin sabon abu a tattare da shi.
Duk abin da yake faɗa wa Gwaggo Hajara sarai ta ji alamun aikinta yayi kyau,ta saki murmushin nasara tana mai cewa ‘ mijinki zai zame miki kumurci,da haka zan raunata muguwar zuciyarki’
“Habibah karɓi wannan ko kuna da buƙatar wani abu sai a ɗauka ciki” Daddy ya faɗa yana mai katse mata tunanin zuci.Ta karɓa tana mai cewa “ Yaya Ɗayyabu na ce bayan biki sai Safeenatu ta koma can gida wurin Hajiya ko?”
“Saboda me? Ba a nan za ki zauna ba?”
“Eh to ni ma da haka na ce ɗin amma sai na ga kamar anty Hajara ba ta son zamana tun da na zo idonta kamar za su faɗo tsabar yadda take jifana da mugun kallo”
Ran daɗi ya ɓace, yanayin fuskarsa ya canza tuni tauraron goshinsa ya ƙara yin baƙi ba tare da ya ce komai ba ya ƙara komawa ɗakin Gwaggo Hajara ita kuwa Habibah har da wata dariyar mugunta ta yi tare da tashi tana taka rawar murna.
Daddy na shiga ɗaki ya yi wa Hajara wankin babban bargo,ko ina ana jin muryarsa yadda yake yi mata masifa in ta je yin magana kuma sai ya gwaɓe bakin.Da wannan baƙin cikin ya fita ya bar ta,sai da ta sha kuka wiwi sannan ta fito ta ɗora girki babu jimawa kuwa sai ga Hajiya ta zo .A ladabce Gwoggo Hajara ta gaishe ta wanda sosai ita hajiyar ta yi mamaki don rabon da ta yi mata irin wannan ladabin tun ranar da Ɗayyabu ya kawo mata ita a matsayin matar da zai aura.Cikin sakin fuska ta amsa tare da cewa “ to barkarmu Safeena an sauka Allah raya kan sunnah,kin samu mai taya ki aiki da kuma miji” Hajiya ta faɗa tana murmushi a doli ita ma ta yi murmushin yaƙen a can ƙasar zuciyarta tana cewa ‘ an haifo mana masifa dai aljanar jaririya muguwa wacce ta yi gadon jaraba ’
“Zan shiga daga ciki” hajiyar ta faɗa tare da nufar ɗakin Safeenatu,cike da murna ta zauna tana kallon jariran Gwaggo Habibah ta ɗauki namijin ta bai wa Hajiya ta karɓa tana mai kai masa sumba haɗi da yi masa addu'a sannan ta miƙa shi.Ana ɗora mata macen jikin Hajiya ya ɗau kyarma kamar mazari,murya na ɗan rawa ta ce “ wane suna za a saka musu?”
“Basheer da Baseerat ” Habibah ta bata amsa tana murmushi tana kallon mahaifiyarta wacce kambun muguntar Gwaggo Hajara duk ya dabaibaye ta yanzu kuma ya fara barazanar tarwatsewa.
Hajiya ta ce “ karɓar ta” tana mai miƙo Baseerat don ruhinta ya soma yin rauni, Habibah ta ce “ Hajiya don Allah ki riƙe t...” ba ta kai ƙarshe ba Hajiya ta miƙe ta je ta shimfiɗe Baseerat a shimfiɗa,sai aka yi rashin sa'a safar da aka saka ma hannunta na hagu ta fita wani mugun haske ya fito ya shiga ƙirjin Hajiya saura ƙiris ta faɗi saboda yadda fitilun idonta suka rufe jiri kuma ya ɗebe ta.
Safeenatu dai na daga gefe tana kallon abubuwan ban al'ajabi , Gwaggo Habibah ce ta kamo Hajiya ta taimaka mata ta zauna.Kamar mai cutar huka haka numfashinta ke fita,ruwan sanyi ta nema da sauri aka bata ta shanye ƙatuwar gora.
“Habibah bani pilow bacci nake ji” cewar Hajiya ,da sauri ta ɗauko ta miƙa mata ita kuma ta kwanta babu jimawa bacci mai nauyi ya ɗauke ta .
Safeenatu ta ce “ Gwaggo Habibah ni fa na fara jin tsoron lamarin Baseerat kina dai ganin abin da ya faru, wannan ai ba zan fita da ita unguwa ba gudun ta jawo min masifa ace mayya ce ma”
Da mugun sauri Habibah ta katse ta “ kar na sake jin kin faɗi haka,saboda ƴarki ba mayya ce ba ƴar baiwa ce”
“To amma ai wasu ba za su ganin haka ba ko? Tun yanzu tana jaririya tana haka ina ga ta girma?”
Gwaggo Habibah ta yi murmushi ta ce “ Safeenatu bari dai na soma ɗan guntsira miki labaran duniyar ɓoye, kowane mutum da kike gani a duniyar nan yana da matriculation na sama.Ko kuma lambar sirri ta samaniya,da wannan ne in aka sayar da ruhin mutum daga lokacin matriculation ɗinsa ta saminiya sai ta canza.Duk wani ɗan Adam kasance yana da taurari iri-iri waɗanda suke taimakawa wurin gudanar da al'ammuran duniyarsa.Ya zama doli kowa ya kare taurarinsa ya basu tsaro,muddin ka yi sakaci da su kuma to wannan mutumin zai iya zama cikkaken maƙasudi wurin tallafawa masu sayar da taurari su ƙwace masa su.”
Safeenatu ta katse ta da cewa “ ta ya za a ƙwacewa mutum taurarinsa alhalin mallakinsa ne?”
Gwaggo Habibah ta bata amsa da “ ba ki taɓa jin labarin wata ma'aikaciyar saloon ba mai gyaran gashi? Ki nemi littafin Mrs Sadauki na MAITAR IDO a nan duk za ki samu cikakken labarin.Ki sani cewa matsafa don su kama ruhinka ma abu ne mai sauƙi,abin da suke buƙata shi ne kawai keɓaɓen abu na gaskiya ta atomatik da ke fitowa daga mutumin da ake son cutarwar,kamar gashinsa,sunansa,date ɗin ranar haihuwarsa,zufar jikinsa wato tufafin da ya saka ba a wanke ba,ko kuma jinin jikinsa.Daga lokacin da matsafi ya riƙe ɗaya daga cikin waɗannan abubuwan zai iya buɗe katinka na samaniya kuma ya karɓe ƙarfin ikonka wato power daga nan sai yayi abin da yake so”
A sanyayye Safeenatu ta ce “ duk Baseerat za ta iya yin wannan? Gaskiya ni dai ban so in kin san hanyar da za a toshe wannan baiwar tata ni dai ki taimaka min don ina ji a jikina muddin aka bar ta da ita a gaba za ta zame mana masifa”
Gwaggo Habibah ta yi mata wani irin kallo irin na ba ki da hankali kafin ta je ta ɗauki safar hannun ta saka ma jaririyar wacce ta buɗe ido sai kalle-kalle take kamar mai wayo,kafin kuma ta kafe idonta ga madubi Gwaggo Habibah ta yi kasaƙe