Showing 15001 words to 18000 words out of 37323 words

Chapter 6 - ZAWARCI BOOK COMPLETE DOCUMENT BY Mrs Sadauki .txt

04 Jan 2025

5540

maƙoshi kamar mai yin raɗa ta soma karanto wasu ayoyin Alkur'ani da ke cikin suratul Yusuf daga aya ta 79 har zuwa 82 .Jikin Mamuh macijiya ne ya soma yin sanyi tsabar yadda ayayoyin ke dagargaza ruhinta musamman da ya zamana Nafisa ta soma ɗan ɗaga murya.Sululuuuu Mamuh macijiya ta faɗo daga jikin Nafisa ,a mugun tsiyace Gwaggo Rahamu ta bi ta ƙarƙashin ƙofa ta shiga ɗakin Mamuh don kuwa ƴan magana na cewa in ka ga gemun ɗan uwanka ya kama da wuta to kai ka shafa wa naka ruwa.

Nafisa na jin saukar macijin ta buɗe idonta a hankali tare da sauke su ƙasa inda Mamuh ke kwance har yanzu cikin siffar maciji sai wani irin numfashi take fatar cikinta na lotsawa kana gani ka san ta wahala.

Nafisa ba bakinta bai gushe da ci gaba da yin duk addu'ar da ta zo bakinta ba,a yadda take tsayen suka ƙure juna ita da Mamuh wacce duk wanda ya san ta to tabbas in ya ga macijin zai shaida wannan idon na Mamuh ne.Nafisa ta saki wani murmushin nasara lokacin da ta ga hawaye sun fara fita daga idon macijiyar,ta sani sarai har da kunya da gajiya suka hana Mamuh ƙoƙarin guduwa don babu abin da Mayu suka fi tsana kamar asirinsu ya tonu wannan yasa Nafisa ta nufi ɗakin Sakeenatu.Tana shiga daidai ita kuma ta fito daga Toilet ta yi wanka ƙugunta ɗaure da towel,“wani wankan kika sake yi?” Nafisar ta tambaye ta ba tare da ta nuna mata alamar wata damuwar ba.

“Eh wallahi,maganin nan da na yi hayaƙi da shi sam babu daɗi shi yasa na yi wanka” Sakeenatu ta bata amsa tana mai kallon Nafisa,“Me? Wannan kallon fa?”
“Fuskarki ce nake ganin kamar tana min wani iri”

“Wani iri kamar ya fa?” Nafisar ta tambaya tana mai shafar fuskarta a daidai wurin da Mamuh ta lasa.
“Babu komai! Bari na shirya na san yanzu Abbas zai shigo”

“Ni zan yi sallah” cewar Nafisa tare da shiga Toilet,har ta gama alwala tana tunanin abin da ya faru da ta zo ta yi sallah sosai ta yi addu'ar neman tsari. Sakeenatu ma ta yi sallah tare da fara bitar karatun jiya da aka koya mata,in ta yi kuskure sai Nafisa ta gyara mata suna nan zaune har aka kira isha'i suka miƙe suka gabatar sai bayan sun ida ne suka fita falo.

Nafisa ta dubi daidai wurin da ta bar Mamuh a ɗazu,tuni capet ɗin yayi alamun datti.
“Anty Sakeena ni kam ina mai aikinki?”

“Wa Fa'iza ? Wallahi kin ga shaf na manta da zancen ta.Ga shi kuma ba waya ce da ita ba ballantana na kira ta amma gobe in ba ta zo ba zan je gidan nasu na gani tun da babu nisa nan baya ne gidan Fulanin nan”

“Oh! Can take ashe,tun da babu nisa bari na je na dubo”

Kafin Sakeenatu ta bata amsa Abbas yayi sallama tare da shigowa,duk fushinsa ne ya ɓata nan take ganin uban adon da matarsa ta yi.
“Ina wuni Ya Abbas ?” Nafisa ta gaishe shi tana mai yin murmushi don tana mugun sha'awar soyayyar antynta da mijinta,ba ƙaramin so yake yi mata.

“ Lafiya lau Nafi ya gida?” ya amsa.

“Alhamdullah” ta faɗa tana mai fita,ita kuwa Sakeenatu kamar wata yarinya haka ta wani rugo da gudu ta faɗa a jikinsa tana kuka.Abbas ya lumshe ido ya na mai cewa “ mene ne kuma na yin kuka uhum?” ba ta basa amsa ba ta dai lafe a jikinsa,tsawon lokaci suna a haka kafin ta hauƙura ta ja shi zuwa cikin bedrom ɗinsu.Da taimakonta yayi wanka ya shirya cikin ƙananan kaya sannan suka fito suka ci abinci,cikin hira ne take faɗa masa ba ta da lafiya har sai da ta je gida.

Ya ja dogon numfashi kafin ya ce “ni kina Keenat ban san abin da ke damuna ba yau gani nan dai”

“Allah kawo mana sauƙi”

“Amen!”

FA'IZA

Tun da lamarin nan ya faru da ita duk jikinta ya zama wani iri,tun da take ba taɓa jin makamancin abin da ta ji ba a ranar nan.Tana da saurayi don har manya sun shiga zancen amma duk tsawon lokacin da suka ɗauka ita tun can ba ta taɓa jin sha'awarsa ba don a tunaninta ma ba ta da lafiya ne tun da ta ji ana faɗar akwai matan da basu jin feeling.Sai ga shi babban al'amari ya faru da ita mai kamar mafarki kamar zahiri an yi wasa da sassan jikinta,a ranar da ta isa gida kasa cin abinci ta yi.A washegari kuma ta tashi da zazzaɓi dalilin da yasa ba ta je aiki ba,yanzu ma tana kwance kan tabarma ta shafe jikinta da wani maganin zazzaɓi sai ga sallamar Nafisa.Duk da gidansu bai da ƙwan lantarki zamani amma suna kunna uban sanjo wannan yasa ta gane Nafisa duk da ƙarancin haskensa.Ta tashi da sauri tana mai cewa “sannu da zuwa”

Ita kuwa Nafisa gaisa wa take da Mamar Fa'iza wacce ba ma sosai take jin Hausa ba,ta zauna kan tabarmar tana mai cewa “fatan dai lafiya? Anty na ta jira shiru ba ki zo aiki ba”
“Zazzaɓi ne ya rufe ni amma da sauƙi gobe zan je in sha Allah ” Fa'iza ta bata amsa.
“Allah ƙara lafiya,ni zan koma” cewar Nafisa tare da miƙewa,har ƙofa Fa'iza ta rako ta sai a lokacin kuma ta yi mata tambayar “ni kam Fa'iza abin da ya faru da ke gidan anty Sakeenatu dama kina yin haka?”

“A'a wallahi ban taɓa yi ba”

“To ki dage da addu'a kin ji ko,saboda yanzu duniyar sai a hankali”

“To na gode” da wannan suka rabu maimakon Nafisa ta koma gidan Sakeenatu sai ta yi tsinke gidansu tun da dai ga mijinta nan ya zo.

#GIDANSU SAFEENATU

Wuni guda currr jaririya Baseerat ta ɗauka tana bacci wanda gangar jikinta ta koma kamar gawa ko motsi ba ta yi.
Idon Safeenatu taf da hawaye ta ce “ Gwaggo Habibah jaririyar nan fa ba ta motsi,ina ga ta mutu ne”
“Da ranta Safeena,don Allah ki fitar lamarin yarinyar nan tun da dai ba ki da ƙarfin zuciya.Tun farko na faɗa miki Baseerat ba normal ba ce,kenan sai ki shirya ganin abubuwan ban mamaki.Wannan kwancin da kika gani ruhinta yayi tafiyar dogon zango ne amma da ranta,ƙila sai goshin magarib su maido ta”

Hawayen da take ƙoƙarin mayar wa ne suka yi nasarar sauko wa akan kumatunta,ta girgiza kafin ta ce “ ni kam ba zan iya rainon ta ba,don muddin na ce zan zauna da ita zuciyata na iya bugawa.Su wane ne za su maido ta? Yarinya kamar ɗiyar jinnu ace tun safe tana bacci ko nono ba ta sha ba alhalin ɗan uwanta ya sha fiye da goma.Haba kuma ace ba zan yi magana ba?” Safeenatu ta faɗa zuciyarta na yi mata ciwo kafin ta miƙe ta fita, frigine ta buɗe ta ɗauko ruwa masu mugun sanyi ta juyo a roba sannan ta koma ɗakinta.Babu wani tunani ta ɗauki Baseerat ta tsoma cikin ruwan ƙanƙarar nan ,ko daƙiƙa biyu ba yi ba ta buɗe idonta farare tasss babu ɗigo baƙi kafin su rine su koma ja kamar nunnanen tumatur.Safeenatu ta yi baya da sauri cike da tsoro,tana jin wani azababen sanyi na game duk illahirin jikinta tamkar wacce aka jefa a frigini.Haƙoranta ne suka fara dantsewa suna fitar da wani ƙasƙas,sai a wannan lokacin Gwaggo Habibah ta miƙe ta cire Babyn tare da lumshe ido tana mai bata haƙuri “ku yi haƙuri uwa-uwza ce ta yi kuskure ba za ta sake ba” tana maganar ne tana jimƙe da hannun hagun Baseerat wanda ke fitar da haske,Gwaggo Habibah ba ta buɗe idonta ba sai da ta ji Sakeenatu na sauke numfashin wahala ta yi mata wani kallo ta ce “yanzu kin fahimci abin da nake son yi miki nuni?” kai ta gyaɗa,Baseerat ta soma yin kuka.
“Zo ki bata ta sha”
Safeenatu ta maƙe kafaɗata ta ce “wallahi tsoronta nake”
“Sun tafi yanzu ita kaɗai ce ,zo ki bata yunwa take ji” tana ji tana gani haka ta shayar da jaririyar.

Ana kiran sallar magrib Murjanatu ta dira a gidan da ɗirkeken cikinta,cike da murna suka rungume juna ita da Gwaggo Hajara.“Na yi kewarki sosai Mama ” cewar Murjanatu tana matsar ƙwalla,shiru Gwaggo Hajara ta yi jin ƙaton cikin ƴarta na tokare ta yayin da kuma yawunta suka soma tsinkewa tsabar maita......

My book is only 500 via 6042551755
Hassana ibrahim
Keystone bank DM +22795045822

💛💛💛GHT B-CLEAR,FEMALE CARE AND GANODERMA💛💛💛

💛💛*BACK TO VIRGIN KIT* *(SABON BUDURCI)*

💛💛Assalam alaikum Mata albishirin ku🧏‍♀️🧏‍♀️ga abin da kuka Dade Kuna mafarkin samu ya samu💃🥰

💛💛Abin nema ya samu ,Kowacce mace aduniya tana mafarkin sake kasancewa virgin

💛💛Ina manyan Mata da suka hayayyafa😁

💛💛ina zawarawa masu shirin aure😍

💛💛Ina budurwa da iftila'i ya fadawa a yayin tsallaka rame 😢

💛💛Ina Mai jego da keso ta dinke ta game tsaf ciki da waje❤️

💛💛Duk ku marmatso kusa ga GHT back to virgin set na kawo muku ,magunguna ne namu na gargajiya bana bature ba

💛💛Kuma Sha akeyi ,insha Allahu muddin kikayi amfani da wannan Kayan Zaki dawo da martabar ki ta farko

💛💛Sai kin gwada za ki tabbatar da hakan.
Sisters no 08142506271 mmn Khadeejah sai najiku
[01/10 à 07:39] MRS SADAUKI 💫: *ZAWARCI*

LoVe aNd HoRrOr StOrY☠️

*Mallakar:* Chamsiya Laouali Rabo
(MRS SADAUKI💫✍️)

*Lambar waya:* +22795045822

*FIRST CLASS WRITER ASSOCIATIONS☀️*
Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation.

*Sadaukar wa:* Rahama Sabo Usman

_____________________
01/10/24

*Last free page 13-14*

Wani irin mugun ƙishi ne ya wanzu a maƙoshin Gwaggo Hajara saboda Maitar shan jini ta motsa.Dakyar ta iya sakin Murjanatu ta koma gefe tana kallon ta,sai kuma ta kasa haƙuri sai da ta shafi ƙaton cikin da mugun sauri Murjanatu ta kai hannunta ita ma kan cikin saboda mugun juyawa da yayi.

“Washhh! ” ta furta a wahalce kafin kuma ta dafe ƙugu jin kamar ta soma naƙuda ne,“ sannu Murjanatu ki zauna mana” Gwaggo Hajara ta faɗa tana haɗiyar yawu don tsaf take kallon jaririn wanda sai juyi yake a ciki.

Kan gwiwanta ta zube tana mai ci gaba da yin gumurzu,tuni ita Hajara ta san da yau in ba wani iko na Allah ba sai ƴarta ta haihu.Da sauri ta shiga cikin ɗaki ta fito kafin ta ce “tashi mu je asibiti” a wahalce ta ɗago ta dubi mahaifiyarta ta ce “ wallahi Mama ban iya tashi”

“To haka za ki zauna? Sai nake ganin kamar haihuwar ce”
Ba ta rufe bakinta ba Murjanatu ta fasa wani uban ihu wanda ya jawo hankalin Gwaggo Habibah da saurinta kuwa ta fito tana tambayar lafiya sai kuma ta yi tozali da Murjanatu a cikin mawuyacin hali.Da taimakonta suka samu suka Murjanatu ta miƙe tsaye,Munir ne ya je ya nemo musu mai ɗan sahu.Kayan robar Safeenatu aka yi aro aka kai ta asibiti,sai uban ihu take tana kururuwa tana faɗin za ta mutu.

Daga nan waje kuma inda mutane ke zauna wa,ran Gwoggo Habibah ya ɓace sosai tun tana ɓoyen abin har ta kasa ta ce “ yanzu ke hatta ƴarki ba ki bari ba? Wannan mugun hali naki bai yi ba.Wato babu babban makunyaci a duniya irin maye,tun da har jininsa bai bari ba”

Gwaggo Hajara ta ƙanƙance idonta da suka kaɗa suka yi ja kafin ta ce “ ina ruwanki da ni ? Ke kika haifa min Murjanatun? Ƙanwar uwa ko ta uba?”

Gwaggo Habibah ta miƙe ta ce “ kina fa da gaskiya,amma ki yi haƙuri farar zuciyata ta taimakon jama'a tasa na zo na tsoma hannnuna inda ba a gayyace ni ba.Tabbas Murjanatu ƴarki ce in kina so ki haɗa har da ita duk ki cinye” tana gama faɗa ta yi tafiyarta ta bar Hajara a zaune babu jimawa kuwa Murjanatu ta haifo ɗanta namiji.

Ɗakin hutu aka kai ta,murya na ɗan rawa Gwaggo Hajara ta ce “ yo ina jaririn?”

“Nurse na duba shi ne don tabbatar da lafiyarsa” ta bata amsa.

Tsawon lokaci kafin a kawo shi jikinta har rawa yake ta karɓe shi,nurse ta ce “ a basa abincinsa ya sha da alamu yunwa yake ji”

“Toh! Toh” cewar Hajara tana wani kafe yaron da idon mugunta,ya soma kuka Murjanatu ta tashi zaune babu kunya ta ce “ Mama kawo shi” ba don ta so ba ta miƙa mata shi ta koma gefe cike da ƙwarewa ta damƙe kurwar yaron .Da ta fita wankin kayan da suka ɓace ta samu wuri ta haƙa rame ta binne ,duk da zuciyarta babu daɗi amma ji take ya zama doli ta cinye jikanta na farko ko yawunta sun koma.
Daren nan dai ba su yi bacci ba jariri nata yin kuka hatta likitocin sai da suka shigo suka duba shi,sai asubahi ya rumtsa wuraren ƙarfe tara na safe aka basu takardar sallama bayan sun biya.Hajara ce ta je ta taro ɗan sahu,bayan ta saka kayansu Murjanatu ta shiga sannan ita ma ta shige tana kallon wurin da ta binne kurwar jariri can ƙasan zuciyarta ta furta ‘ zuwa dare zan zo na tone’ haka suka isa gida.

Ta kuwa ci sa'a Daddy bai fita ba,Murjanatu ta gaishe shi ya amsa tare da yi mata barka kafin ya maida dubansa ga Hajara wacce sai raba ido take kana gani ka san ba ta da gaskiya.

“ Hakan da kika yi daidai ne? Don dai ba ni ne na haifi Murjanatu ba shine kika koro Habibah daga asibiti? ”

“Ka yi haƙuri ba koro ta na yi ba,na dai ce ta dawo gida tun da ba za a barin mai jego ita ɗaya ba a gida”

“Mi yasa ba ki kira ni kin shaida min zancen haihuwar ba? Ban cancanta ba ne ko me?”

“Ka yi haƙuri Daddyn yara,yanzu dai ka kira shi mijin nata ka shaida masa zancen haihuwar ”

Bai amsa mata ba ya fice,sai a lokacin Habibah ta fito idonta kan jaririn wanda ke baccin wahala.Cike da tausayinsa ta ƙarasa ta ce “ barka Murjanatu Allah raya shi kan sunnah”
“Amen na gode” ta amsa tare da miƙa mata jaririn,Habibah ta karɓe shi tana mai zaunawa kan kujera ta shafi sumar gashinsa tana kallonsa da kyau ta tabbata kurwarsa na gidan yari ba a cinye ba sai dai ba ta san a ina aka binne ta ba.Haka ta gaji da binciken ta miƙa shi ga uwarsa ta miƙe suna ƴar kallon-kallon ita da Hajara wacce idon nan nata suke wiƙi-wiƙi na maras gaskiya.

A sanyayye Habibah ta koma ɗakin Safeenatu,“ ya dai Gwaggo Habibah lafiya na gan ki duk kin yi wani iri?” Feenat ta tambaya.

“ Babu komai Safeena,bacci Baseerat take?”

“Eh ba ta jima da rufe idon ba”

“Mu gan ta” Habibah ta faɗa tare da yin zama, Safeenatu ta ɗora mata jaririyar kan cinya.Hannunta mai safa ta kamo ta cire sannan ta soma shafa shi ,
[01/10 à 08:45] MRS SADAUKI 💫: *ZAWARCI*

LoVe aNd HoRrOr StOrY☠️

*Mallakar:* Chamsiya Laouali Rabo
(MRS SADAUKI💫✍️)

*Lambar waya:* +22795045822

*FIRST CLASS WRITER ASSOCIATIONS☀️*
Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation.

*Sadaukar wa:* Rahama Sabo Usman

_____________________
01/10/24

*Last free page 13-14*

Wani irin mugun ƙishi ne ya wanzu a maƙoshin Gwaggo Hajara saboda Maitar shan jini ta motsa.Dakyar ta iya sakin Murjanatu ta koma gefe tana kallon ta,sai kuma ta kasa haƙuri sai da ta shafi ƙaton cikin da mugun sauri Murjanatu ta kai hannunta ita ma kan cikin saboda mugun juyawa da yayi.

“Washhh! ” ta furta a wahalce kafin kuma ta dafe ƙugu jin kamar ta soma naƙuda ne,“ sannu Murjanatu ki zauna mana” Gwaggo Hajara ta faɗa tana haɗiyar yawu don tsaf take kallon jaririn wanda sai juyi yake a ciki.

Kan gwiwanta ta zube tana mai ci gaba da yin gumurzu,tuni ita Hajara ta san da yau in ba wani iko na Allah ba sai ƴarta ta haihu.Da sauri ta shiga cikin ɗaki ta fito kafin ta ce “tashi mu je asibiti” a wahalce ta ɗago ta dubi mahaifiyarta ta ce “ wallahi Mama ban iya tashi”

“To haka za ki zauna? Sai nake ganin kamar haihuwar ce”
Ba ta rufe bakinta ba Murjanatu ta fasa wani uban ihu wanda ya jawo hankalin Gwaggo Habibah da saurinta kuwa ta fito tana tambayar lafiya sai kuma ta yi tozali da Murjanatu a cikin mawuyacin hali.Da taimakonta suka samu suka Murjanatu ta miƙe tsaye,Munir ne ya je ya nemo musu mai ɗan sahu.Kayan robar Safeenatu aka yi aro aka kai ta asibiti,sai uban ihu take tana kururuwa tana faɗin za ta mutu.

Daga nan waje kuma inda mutane ke zauna wa,ran Gwoggo Habibah ya ɓace sosai tun tana ɓoyen abin har ta kasa ta ce “ yanzu ke hatta ƴarki ba ki bari ba? Wannan mugun hali naki bai yi ba.Wato babu babban makunyaci a duniya irin maye,tun da har jininsa bai bari ba”

Gwaggo Hajara ta ƙanƙance idonta da suka kaɗa suka yi ja kafin ta ce “ ina ruwanki da ni ? Ke kika haifa min Murjanatun? Ƙanwar uwa ko ta uba?”

Gwaggo Habibah ta miƙe ta ce “ kina fa da gaskiya,amma ki yi haƙuri farar zuciyata ta taimakon jama'a tasa na zo na tsoma hannnuna inda ba a gayyace ni ba.Tabbas Murjanatu ƴarki ce in kina so ki haɗa har da ita duk ki cinye” tana gama faɗa ta yi tafiyarta ta bar Hajara a zaune babu jimawa kuwa Murjanatu ta haifo ɗanta namiji.

Ɗakin hutu aka kai ta,murya na ɗan rawa Gwaggo Hajara ta ce “ yo ina jaririn?”

“Nurse na duba shi ne don tabbatar da lafiyarsa” ta bata amsa.

Tsawon lokaci kafin a kawo shi jikinta har rawa yake ta karɓe shi,nurse ta ce “ a basa abincinsa ya sha da alamu yunwa yake ji”

“Toh! Toh” cewar Hajara tana wani kafe yaron da idon mugunta,ya soma kuka Murjanatu ta tashi zaune babu kunya ta ce “ Mama kawo shi” ba don ta so ba ta miƙa mata shi ta koma gefe cike da ƙwarewa ta damƙe kurwar yaron .Da ta fita wankin kayan da suka ɓace ta samu wuri ta haƙa rame ta binne ,duk da zuciyarta babu daɗi amma ji take ya zama doli ta cinye jikanta na farko ko yawunta sun koma.
Daren nan dai ba su yi bacci ba jariri nata yin kuka hatta likitocin sai da suka shigo suka duba shi,sai asubahi ya rumtsa wuraren ƙarfe tara na safe aka basu takardar sallama bayan sun biya.Hajara ce ta je ta taro ɗan sahu,bayan ta saka kayansu Murjanatu ta shiga sannan ita ma ta shige tana kallon wurin da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login