Showing 1 words to 3000 words out of 18345 words

Chapter 1 - BA DON SHIBA COMPLETE DOCUMENT by Prince Deejerh.txt

10 Jan 2025

1435

[16/01, 18:47] khadija ahmad dija Marubuciya Barauniya ce Frien Din Hassn: ✨ba don shiba✨
By Princes Deejerh
New Writer


Bismillahir rahmanir raheem
Page 1⃣ to 5⃣


yarinya ce yar kimamin shekara 14 take ta kai kawo a cikin tsakar gidan kallo daya zaka mata zaka gane agalaibe take aikin juyar da kanta tayi zuwa wani sashe dake tsakar hmm tace a hankali nima na kai dubana sashen da take kalla abin mamaki wani uban tulin kayan wanke wankene kamar anyi sati ana tara shi kuda kuwa sai rawar banjo suke akai hawaye ta share a hankali kafin ta doki kujera yar tsugunne ta karasa wurin zama tayi jiki a sanyaye ta fara wankewa dama ta riga ta dibo ruwan tunda safe kanta a duke yake amma duk hakan bai hana hango hawayen da ke zuba a idonta ba wata irin rayuwa akeyi a gidansu ta rashin adalci akwai yayyanta yanmata har gudu uku amma basa aikin komai sai dai kawai ayi kwalliya a fita harta kayansu ita ke wanke tana cikin wannan tunanin bata auneba taji wani uban rankawashi akanta kwass kake ni kaina sai da na tsorata dago kai tayi da sauri tana shafa gurin domin ba karamin shigarta rankwashin yayi cikin rawar murya tace ki..kiyi hakuri inna mtsww dogon tsakin da matar taja ne yasa na daga kai na kallet kibarta sai data tsora tani ga idonta manya2 bakin wargajeje duk ya baci da goro kannan kuwa dukun dukun yake kamar an shekara baa kitsa shiba hargowan da takeyi ne ya bani dama hango wawake ken wuwulon dake bakin kai wannan mata ta cika kazama cigaba tayi da masifa tana fadin shegiyar yarinya me bakin halin ubanta tun dazu na saki aiki amma kina nan kina halin na munafunci ta kara kai mata duka a baya wallahi ba zaki makarantar da ake koyo miki iskanci ba bari haladu ya zo yau sai kinfi fulawa laushi kuma ki gama ga wankinsu indo can kije ki wanke su tass tunda anhana kimin tallah aikin gida ma kawai ya isheki shegia mai kama da mayu infito inga baki gama ba tunda ta fara fadanta bata dago ta kalleta ba domin kuwa tasan me hakan zai haifar mata hawayen fuskarta ta share amma kuma wasu kara zubowa suke ba duka ko zagin a akai mata bane damuwarta ta riga ta saba duk da baa sabo da wahala makarantar ta shine damuwarta domin kuwa yau suna da test kuma wannan year din zatai junior waec da sauri sauri ta kama aikinta da yake me kwazo tuni ta gama shi mikewa tayi a hankali ta leka dakin inna asabe munsharin da take ne ya tabbatar datayi bacci da gudu ta shige dakinsu ta dakko uniform dinta kayan tsab domin kuwa a goge suke komai da sauri take yinsa saboda kada inna ta tashi bata dauki jaka ba littafi kawai ta dauka sai biro fitowa tayi fice a gidan a hankali tafiya take cikin nutsuwa duk da kuwa tasan tayi latti wannan nature dinta ne duk napep din data tara a cike suke saboda yau safiyar monday ce dakyar ta sami wani mai mashin ya tsaya mallam gumi college zaka kaini tun kafin ta gama rufe baki yace 200 zaro ido tayi ita da take naira 30 shiru tayi domin tasan ba kaita zaiyi ba dan baida alamun mutunci a hankali tace muje to (nidae nace to waye zai biya ta taro pillars) yan mintoci kadan sukai kaisu bakin makarantar sauka tayi tare da sunkuyar dakai gajiya yayi yace yadai malama kudinafa zan baka tace a hankali
acan gefen kuma wani saurayi na hango zaune a bakin get din makarantar kanshi a duke yake amma haka bai hanani gano baiwar kyau dake kunshe a fuskar sa ba tsayawar mashin diinne yasa shi dago kanshi da sauri masha allah na fada saboda duk inda ake neman mai kyau to wannan guy din ya wuce idanuwan shi manya ne farare tass hancinshi dogo har baka bakin dan mitsili pink dasu mikewa yayi ransa a bace takowa yayi har inda me mashin din yake hararar sa yayi kafin ya ciro kudi ya mika ma dan acaban wuce muje yace mata sai da suka kai bakin ajinsu yace waya ce ki hau mashin turo baki tayi tace to ban samu abin hawa bane ne ai mtsw yayi tsaki kafin yace ya akayi kikayi latti shiru tyi ke dallah kimin magana wanki nayi wankin wa nasu indo mtsw sai naci uwarsu duka yasin wannan tsohuwar kuma inbata yi a hankali ba sai na cire mata murfin kai ya fada yana wani karkta baki kallon shi tayi a tsorace domin kuwa tasan zai iya indai AMMAR ne wuce aji kin wani tsaya kallo na wucewa tayi da murmushi a fuskarta har tayi nisa ya kwala mata kira JIDDAH waigowa tayi zonan yace da sauri ta taho kudi ya ciro ya mika mata ba musu ta amsa nagode hararar ta yayi hmm tace dan tasan manufar hakan baayaso tamai godiya wucewa duka suka yi kowa yayi ajin shi




Princes Deejerh💝
[16/01, 18:47] khadija ahmad dija Marubuciya Barauniya ce Frien Din Hassn: ✨✨BA DON SHIBA✨✨


by Princess Deejerh
New Writer


Page 6⃣ to 1⃣0⃣






shigarta cikin aji yayi daidai da zuwan teacher din su na english dama shine 1s test da zasu fara,ba bata lokaci ya fara rubuta musu test kan ka ce me har jidda ta kusa gama nata domin kuma jidda akwai kwakwalwa dan ma ana dankwafar da ita,karfe 9:30 daidai ta gama mika mai tayi ya amsa yana murmushi dana kasa gane maanarna sa


fitowarta kenan daga cikin aji,a gajiye take matuka ga kuma yunwar da take ji ita ta kara galabaitar da ita don tun safe har yanzu ko ruwa bata shaba"karon da sukayi ne ya dawo da ita daga duniyar tunanin data lula dago dara daran idanuwanta tayi ta dora akan kyakkyawar fuskar sa“”kallonta yayi a kaikai ce kafin yace "ke"zo muje bai jiran me zata ce yayi gaba abin"hmm kawai tace kafin tabi bayanshi,can bayan ajinsu suka tsaya dama tasan nan zasuje domin duk time din break shi yake sai mata abinci tun tana nauyin ci a gabanshi har ta saba,zai zauna ya jirata har ta gama amma fa ba maganar da zata hada su,ita har mamakinsa take yi amma kuma idan wani ya taba ta to fa anan ne zai nuna rashin mutuncinsa mutane abin na basu na basu mamaki yanda suka ga ammar na damuwa da duk wani lamari na jidda,domin kuwa ammar bai ragawa kowa a unguwarsu inba jidda ba"mtsww" tsakin da ya jane yasa ta dawo hankalinta kallon shi kawai tayi shiko ya tamke fuskar sa"idan ba zaki ci bane yasin zan zubar dashi"da sauri ta fara cin abincin,yanda take cin abincin ya sashi murmushi wanda ni kaina sai dana yi mamakin hakan“”tana gamawa kuwa ana komawa aji kowa ya shige ajinshi sai da yaga shigewarta sannan ya wuce shima


yana shiga ya nemi guri ya zauna "yadai my man auwal ne ya zauna a kusa dashi duk makarantar shi kadai yake kulawa saboda halinsu yazo daya,daga ina kake ne uhm ko dayake nasan daga gurin jiddah kake"uhm kawai yace danshi tunanin yanda zai ci uwar inna asabe da ya'ya'nta yake shegu masu kama da birai yace a fili,da sauri auwal ya kalleshi dan yansan mutane biyu ammar ya tsana duk duniya daga inna asabe sai umma matar babanshi dukan kafadanshi auwal yayi haba man ka share mutanennan mana haka ka bari mu hadu musu target kawai,sai yanzu yayi murmushi kafin yace ai qur'ani sai na cirema asabe awazu ita da shegun yaran nan' eh naji yanzu dai tashi mu haure ta gatanga kawai kasan fa yau madrid na wasa ko ka mantane"ban manta ba muje kawai to amma wa zai raka jiddah gida🤔 dallah muje zamu dawo kafin lokacin ok kawai yace tare da mikewa suka tafi


karfe 1:30 aka tashi a fitowa tayi ta tsaya a kofar ajin su ammar amma har suka gama fitowa bata ganshi
"ke"taji ance daga bayanta juyawa tayi suna fuskantar juna"waike wace irin mayya ce ne meye hadinki da ammar duk kin bi kin makale masa“”aysha kenan wadda aka fi sani da easha tana matukar son ammar amma shi bai ma san tanayi ba easha tana kyau daidai gwargado kuma babanta attajiri ne shiyyasa take abinda taga dama a makarantar tun farkon shigowarta ta ga ammar da suna dan mutunci amma tunda tace tana sonsa shike nan ya dauke mata wuta tare bata zazzafan kashedi wannan dalilin ne yasa ta tsani jiddah matuka take kuma mata wulankaci son ranta don ma ammar din yana taka mata burki ,sai data gama jirarta sannan taja yan korenta suka wuce,ita dai jiddah kanta na sunkuye dan ba iya fada tayi ba koma ta iya din ina zata kai easha ita dake kusan 18yrs kada kai kawai tayi ta fita a makarantar a kafa zata koma gida shiyyasa take ta sauri kar tayi lattin zuwa gida ta hadu da sharrin inna asabe"duk da yanzu din ma tana san ba tsira tayi ba




tun daga nesa tage hango wata dalleliyar mota a kofar gidan su ita dai a iya sanin duk danginsu bame ko mashin balle mota tunanin tane ya tsake saboda wadda taga ni ta fito daga motar RABI ce kanwar indo diyar inna asabe ta biyu sai famam washe baki take yi shiko na motar sai riko hannunta yake yi allah ya shirya kawai tace ta shige zauren gidansu turus ta tsaya ganin inna asabe na leke ta dan sakalen kofar batason da mutum a tsaye ba duhun data gani yasa ta dagowa da sauri cikin hargowar data saba ta fara magana don ubanki matsa in kalli abin arziki shegiya matsiyaciya tana bukulun kallon abin duniya yar bakin ciki kawai wuce ki bari wuri sum sum ta wuce cikin gida tana mai tirr da halin inna asabe




ur's Princes Deejerh💝
[16/01, 18:47] khadija ahmad dija Marubuciya Barauniya ce Frien Din Hassn: ✨✨BA DON SHIBA✨✨


By Princess Deejerh
New Writer

Dx Page is Dedicated To U Ramlat armanga (Real me dambu ce) ina godiya game da tunatarwarki a gareni ina yinki irin sosai dinnan😘💝


Page 1⃣1⃣ to 1⃣5⃣




kai tsaye cikin daki ta wuce tana mai kara yin tirr da halin inna asabe,,uniform kawai ta cire taji ana kwalla mata kira daga cikin gidan.da sauri ta fita tana amsa kiran‘’haladu ne tsaye rike da tulin kayan wanki a hannun sa watso mata su yayi tare da cewa ‘ke’ ga kayana na nan ki wanke min su yanzu nan,bai saurari me ba zata ce ya kada kai zai kara gaba,da sauri tace mai ina sabulun da zanyi wankin,kallon banza yayi mata kafin yace‘’ ina kudin da yake biyanki na iskancin da kukeyi ko ance miki bamu sani ba to ki cira a ciki ki siyo harara ya wurga mata da jan idon shi kafin yasa kai ya fice a gidan yana wani dage kafada waishi ga gaye,,kwasar kayan tayi ta nufi bakin rijiya kafin ta tashi shiga daki ta dakko ragowar sabulun data ajiye idan zata wanke kayanta


har ta fara wankin sai ga inna asabe ta shigo kamar an korota sai washe baki take daga bayanta rabi ce rike da manyan ledoji a hannunta‘’sai wani yatsinar fuska take,inna asabe kuwa jikina na rawa ta dakko bukiti ta juye ruwan zafi a ciki sai data surka sannan tayi hanyar bandaki ta kai‘’rabi fito ga ruwan can na kai miki kidan watsa ko kya ji dadin jikinki,daga cikin dakin ta fito rike da ledojin da ta shigo da su ke ta ce ma jidda a tsawace,da sauri jiddah ta taso ta bar wankin a bakin rijiya ‘’gani‘’tace a hankali, cikin yatsina ta fara magana kamar ansata dole ki dauki kayan nan ki gyara su duka kawai tace ta nufi hanyar bandakin,ba bata lokaci ta dauka ta fara dubawa ledar farko kajine a ciki dakwala har guda 6 dayar kayan miya ne a a ciki a da kayan dandano biyun kuma da suke gefe duk kayan fruit ne a cikin‘’kajin ta fara gyarawa sannan ta hura ice dakyar wutar ta kama,sannan ta dora akah,kayan miya ta dakko ta wanke ta zuba a karamin bokiti‘’nufar inda inna asabe take a zaune tayi ragwajab kamar kayan wanki sai faman faman washe baki take yau yarta tayi kasuwa,inna kudin nika kayan miyan yana da yawa‘’a hasale ta dago tace dan uwarki baza a bada ba da hannunki zaki nika shi in baki kudin nika ai kinji dadi kenan kin huta niko bana kaunar in ga kina hutawa nafiso kullum ingan ki a wahale jiya iya yau kamar yadda shegiar uwarki tayi har tabar duniya,wuce ki bani guri mai kama da zabaya yarinya sai bakin jinin tsiya.juyawa tayi ta tana share hawayen bakin ciki ,mahaifiyarta na kasa amma duk da haka bata tsira ba amma akwai allah,daukan kayan miyan tayi ta nufi inda ake ajiye turmi ta fara dakawa,,,


hajia umma ce hakimce a kayatacce falonta“”gefen wata matace wadda kallo daya zaka mata kasan cikakkiyar yar duniya,duk da ita umman ta dan taba kafin ta samu alhj mu'azzam,hajia umma ce ta fara magana cike da takaici magajiya na rasa inda zan tsoma raina yaron nan ya gagareni baya shakkata ballantana tsorona na rasa ina zansa raina‘’rufe bakinta keda wuya magajiya ta antayo ashar tare da cewa kin bani kunya umma yanzu akan wannan dan yaron zaki tsaya kina tada hankalinki“katseta umma tayi da sauri‘’ tana fadin ke ammar fa da kika ganshi ko ubanshi baya shakka ballantana ni amma in yasan wata bai wata ba ba'a ja dani a zauna lafiya“”yanzu naji zance kawata kawai kisan yanda zakiyi yabar gidan nan koma kasar gaba daya,da sauri hajia umma tace kai kawata amma fa kin kawo shawara me kyau,wani killer smile tayi kafin tace ammar dani kake magana.

tafiya yake yana wani karkacewa ya zura duka hannu a aljihun wandon sa a bayansa kuma karnuka guda uku ke binsa duk inda yasa kafa kamar rakumi da a kala,duk inda yazo giftawa kafin ya karaso za ka ana darewa kowa yayi takansa,da sun san mistake kadan ne zai hadaku yanzun nan zai gwada ma rashin imani,isarsa kofar gidan yayi daidai da fitowar umma ta rako magajiya kofar gida.wucewa zatayi yasha gabanta sai data tsorata danganin fuskar sa ba alamun fara'a,cikin gadara ya fara magana ke tsohuwa bakiji jan kunnen da na miki ba ko wai gidan tsoho ne,da zaki damu mutane da zirga zirga to yasin na kara ganin ki wadan nan ya nuna karnukan sa su rakaki har gida ko kuma insa addar nan in cire miki rabin kai,kallon addar dake hannun shi magajiya tayi tare da zaro,cikin rawar tace aa basai takai mu ga haka nama daina wallahi wuce shi da sauri tayi ko waige bata kara yiba,umma dake tsaye rai a bace ta bude baki zata fara surfa balaki kallon daya mata yasata fasawa tare da shigewa gida tana mai kara tsanar sa a ranta“”wucewa cikin gida yayi dan shi dama bacci ya kawoshi gidan


sai kusan laasar jidda ta gama ayyukan da inna da rabi suka sata,buta da dauka tayi alwala sannan ta shige daki ta fara sallah taji shigowa hadaladu sallah take amma sai da gabanta ya fadi dan kuwa kayanshi na nan bata wanke ba saboda aikin daya mata yawa.



Ur's princes deejerh💝
[16/01, 18:47] khadija ahmad dija Marubuciya Barauniya ce Frien Din Hassn: ✨✨BA DON SHIBA✨✨




By Princess Deejerh
New Writer


I dedicated dx page for u Hassan atk tanko Tnx for ur luv and support



Page 1⃣6⃣ to 2⃣0⃣




cigaba da sallan ta tayi amma gabadaya rabin hankalinta yana kofar daki inda haladu ke tsaye yana ta surfo ruwan ashariya,kiran da ya kwalo mata ne yasa ta kara firgita amma fa duk haka bata katse sallan ba.cizge labulen bakin kofar yayi yana fadin ina wannan shegiyar tayi... cak ya tsaya ganinta tsaye tana sallah,kan uban can yace da karfi wanda yayi sanadiyyar fitowar inna asabe daga cikin daki..dan dama tana jinsa kyaleshi kawai tayi ya gama na shi kafin ta dora nata,shiga cikin dakin yayi tare da fincikota ya wurgo ta waje kamar kayan wanki,,ita dai jiddah baiwar allah ba bakin magana dan tasan yau allah ne kawai zai iya ceton ta a hannun azzalumi haladu..shigowar indo da talatu ya katseshi tare da cewa yauwa kunzo a daidai kuzo ku cimin uban wannan zabayar,,shewa suka sa a tare dan dama su kamar jira suke,,hakuri jiddah ta fara bashi tare da fadin kayi hakuri inna ce ta sani ayki....ai bata karasa ba asabe ta kai mata naushi a baki tana fadin''kujimin yar iska zata min sharri yaushe na saki aiki ina ce hijabi kika zara kika tafi gun wannan tantirin yaron,yau saikinci ubanki a gidannan..dukan su suka rufu akanta suna dukanta kamar sun samu jaka da kansu suka gaji suka kyaleta,,ita kuwa jiddah baiwar allah a wannan lokacin bata da bakin magana domin bakinta yayi suntum jikin duk ya farfashe sai sheshshekar kukan ta ke tashi,,daga inda take tana jiyo shewar su a can kuryar dakin inna asabe.suna yi suna cin naman da tasha wahala gun dafa shi''da kyar ta samu ta rarrafa ta shige cikin daki akan katifar ta kwanta wadda bata da maraba tsumman gogegoge ta kwanta,,kafin kace me zazzabi ya rufeta dakyar ta jawo hijabinta ta lullube tana mai kara tausayin rayuwarta,,



a bangaren ammar kuwa baccin shi yake cikin kwanciyar hankali kiran sallah la'asar ne ya farkar dashi daga baccin da yake,domin kuwa duk iya shegen ammar baya barin sallah ta wuce shi gashi da tausayi.amma fa idan ka shiga gonar shi to fa ba mutunci


sai da ya idar sallah sannan yayi cikin gidah umma ce hakimce a falo tana kallon tv tana jefa fruit a bakinta,,wucewa yazo yi ta gabanta ko kallon inda take bai yiba,,babanka na hanya gobe,, juyowa kawai yayi ya kalleta kafin ya wuce..da harara ta bishi kafin tayi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login