Showing 6001 words to 9000 words out of 18345 words
Chapter 3 - BA DON SHIBA COMPLETE DOCUMENT by Prince Deejerh.txt
sai ki koma bacciin ki,,har ta bude baki zata yi magana inna asabe ta kara katseta haba jiddah baki daukeni uwa bane kome,,aa inna ba haka bane..to kiyi abinda nace kinji jiddah ta,,,juyawa tayi taje ta dakko abincin cikin dakin su ta shige ta zauna tana godema allah daya sa inna da yayanta suka gane gaskiya,,cikin kwanciyar hankali take cin abincin can kasar zuciyar ta kuma tunanin ammar ne fal cikinta..
sai da inna asabe taga shigewarta daki sannan taja tsaki,,rabi ce ta fara cewa,,gaskiya inna jiddah wawiya ce wallahi lokaci daya muka sauya mata kuma wai harta yadda dan shashanci,,hmm kedai bari yarnan ji nake kamar in shaketa amma inaa sai lokacin da burina ya cika sannan zanyi bacci me dadi ina so inga jiddah ta wulakanta ta zama abar kwatance ta yanda ita kanta sai ta tsani rayuwar ta(nikam nace ta allah ba taki ba jiddah tafi karfinki eheee😡😡)
tunda da dare ammar ke tunanin halin da zai bar jiddah,,ya rasa gane me yake ji akan ta soyayya ko kuma tausayinta kawai yake,,maganar auwal ne ta fado masa a rai..a koda yaushe maganar shi kenan son jiddah kake matuka amma ka kasa ganewa koda yake watarana zaka gane,,hmm ajiyar zuciya ya sauke a hankali daya tuno inna asabe dole ne yakama mata warning kafin ya tafi da wannan tunanin bacci ya daukeshi...
tana gama cin abincin ta fara shirin skul fitowa tayi dan tafiya har takai bakin gida taji inna asabe na kwala mata kira,,juyawa tayi ta koma ciki,tsaye ta ganta a bakin daki,,kudi ta miko mata naira 100 gashi kyasai wani abu ko,,amsa tayi tana godiya kafin ta juya ta tafi,,,tana isa bakin layin ta tarad da shi tsaye,,shima yana ganinta ya taso ya karaso inda take,,gaeshe shi tayi a ladabce..bai amsa ba sai ma kura mata ido da yayi,,dan yaga alamun kamar tayi kuka,,tambayar yayi meya faru,,murmushin yake kawai tayi sannan tace bakomai..jinta kawai yayi amma yasan akwai abinda ke damunta,,kodai asabe ce,,da sauri ta dago ta kalleshi kafin tace ai inna ta sauya yanzu tana sona ta fada tana murmushi..me kika ce ya fada da sauri,,abinda ya faru duk ta fada mishi..shidai yaji kawai amma fa bai yadda da canzawar asabe ba,,akwai wata a kasa yace a hankali,shareta kawai yayi ya taran mata napep tahau,,tana wucewa shima ya wuce gida domin da yamma jirgin su zai tashi,,amma kuma zuciyar shi ta kasa yadda da asabe dan tabbas akwai wata a kasa amma kafin ya tafi sai yaje gidan tabbas...
karfe 1 jiddah ta dawo gida tana shiga daki ta samu abincinta a rufe sai da tayi sallah kafin ta ci abincin..wayar da ammar ya bata ta dakko tana dubawa,,daga yau shikenan ba zata kara ganin shi ba har sai bayan 5yrs hawaye ne ya fara zuba a idonta kafin ta fashe da kuka,,lafiya jidda taji an fada daga baki kofa da sauri ta fara goge hawayen idonta ta fara kokarin kakalo murmushin dole,,karasowa tayi ta zauna kusa da ita kafin tace ki fadamin meke faruwa yanzu nice mahaifiyar ki jiddah kinji fadamin,, maganar tafiyar ammar ta fada mata,,ai inna asabe kamar an mata bushara da gidan aljannah haka taji,,amma da yake munafuka ce sai ta kwabe fuska alamun tausayi ayya jiddah ni kaina naji ba dadi amma wannan shine daidai kinga fa karatu zaije kawai ki masa addu'a da haka ta rinka kwantar mata da hankali har ta samu nutsuwa,,,har ta juya zata fita a dakin ta hango waya a gefen jiddah,,dawowa tayi ta dauki wayar wannan fa jiddah,,abinka ga yarinta sai cewa tayi ammar ne ya bani har da atm card dinsa ya bani,,kinga yanzu ki kawo in aje miki su idan ya tafi saiki fara amfani dasu ko jiddah ta,,washe baki tayi tace to inna asabe
inna asabe na komawa daki ta samu su rabi zaune dama jira suke ta dawo,,ya akayi ne inna indo tace,,kwashe duk yadda suyi da jiddah ta fada musu,,kai amma fa munji dadi aikin mu zai tafi yadda akeso kenan wannan dan daban bayanan,,inna asabe ce tace ke rabi zo in aikeku unguwan rimi keda jiddah kada ki dawo har sai na kiraki a waya dan bana san su hadu har ya tafi nima fita zanyii....
Ur's princes deejerh💝
[16/01, 18:47] khadija ahmad dija Marubuciya Barauniya ce Frien Din Hassn: ✨✨BA DON SHIBA✨✨
By Princess Deejerh
New Writer
Zuwa ga masoya BA DON SHIBA musamman wadanda suke min magana ta watsap da kuma Sms plss ku cigaba da yimin hakuri ina busy ne 2days amma amma INSHA ALLAH na kusa kammala komai zaku rinka ganin shi akai akai saboda haka wannan shafin sadaukarwa a gareku kuyi yadda kukesodash😘😘
💝💝luv u oll💝💝
Page 4⃣1⃣ to 4⃣6⃣
kafin kace me har rabi ta gama shiryawa sai a lokacin inna asabe taje ta fada wa jiddah maganar da aiken data musu,,bata kawo komai a ranta sai ma shiri data fara yi tana gama wa rabi tace su tafi..kudin mota inna asabe ta basu sannan tace suyi sauri su tafi,,suna fita mota suka hau suka wuce,,koda suka isa gidan sun tarar bata nan amma sai rabi tace su zauna su jirata kila ba dadewa zatayi ba ta fada kawai domin daga ita har innan sun san bata nan,,zaman taga bana karewa bane gashi kuma ta fara tunanin tafiyar ammar har 4:30 a lokacin amma taga rabi bata da niyyar tashi su tafi,,so take ta mata magana tace su tafi amma ta kasa,,dakyar ta daure tace mu tafi gida mana tunda yamma tayi gashi kuma har yanzua bata dawo ba,,murmushi kawai rabin tayi kafin tace kiyi hakuri jiddah kinsan halin inna idan muka koma babu sakon nan mita zatai tayi,,,ita dai jiddah bata kara magana ba amma fa zuciyar ta fal ta cika da kunci kamar ta fashe da kuka haka take ji dan tasan 5:30 jirgin su ammar zai tashi allah yasa ma a fasa tafiyar(niko nace ai ba fashi jiddah)
karfe biyar dai dai ammar ya tsaya a kofar gidan su jiddah yaron da ya ayka cikin gidan ne yaga ya fito yana fadin wai batanan,,batanan ya maimaita cikin mamaki ina zataje yau friday a wannan lokacin...muryar inna asabe ce ta katseshi tana fadin ai jiddah bata nan sun fita da maman salaha ta rakata zaria kuma naji kamar suna cewa sai gobe zasu dawo...tunda ta fara magana ya bata rai taya zata fita bayan tasan yau zai tafi kuma yacea mata yau din zai zo suyi sallama,,bai ce mata komai ba kawai ya juya dan ranshi a matukar bace yace,,,tafiya kawai yake yana tunanin abinda jiddah tayi,,yana zuwa gida bai tsaya komai ba ya samu abban shi a bakin mota dama shi kadai yake jira dan sun gama komai ko kallon umma dake mai ALLAH ya kiyaye hanya baiyi ba shigewa kawai yayi ya zauna kafin shima abba ya shige ya tada motar,,umma ji take kamar an mata bushara da gidan aljannah yau ammar zai bar kasar sai kuma bayan 5yrs zai dawo,,,
tana ganin fitar su a gidan itama ta fice...
sai karfe shida jirgin su ya tashi ya tafi cike da kewar jiddah domin har hawaye sai da ammar yayi yana kuma jin haushin yanda bai hadu da ita ba,,
sai da sukayi sallar magrib amma har a lokacin bata dawo ba,,sai a lokacin inna asabe ta kira rabi tace su dawo,,shirin tafiya suka farayi,,amma jiddah jikinta a sanyaye tanaji a jikinta ammar ya tafi,,hawaye kawai takeyi a cikin mota amma ba wanda ya lura da hakan,,,suna karasa wa gida sallah ta farayin kafin a miko mata abincinta takai abincin baki kenan..taji inna asabe tace dazu kuwa ammar yazo miki sallama amma bakyanan shine yace to in fada miki ya wuce,,kasa kai abincin bakinta tayi sai hawaye daya fara zuba kamar an bude famfo fadawa daki tayi da gudu kuka takeyi kamar ranta zai fita shikenan ba zata kara ganin sa,,kuka ta kara fashewa dashi...inna asabe kuwa jin kukan take kamar sautin kida ba abinda takeso irin taga jiddah cikin kunci cikin masifa da bala'i amma da yake munafuka shiga dakin tayi ta fara lallashin ta har ta dan tsagaita,,haka jiddah ta kwana tana tunanin ammar tana kuma addu'ar allah ya kareshi duk inda yake,,(masoyin gaskiya kenan)
ammar mutanen india an sauka lafiya dama akwai abokin abba shine ya aiko a dauke shi isar su gidan keda wuya yaga kowa yana ta nan nan dashi daga shi sai matar sa da ya'ya'n su biyu duka maza dayan mai suna abbas sa'an ammar ne sai kuma karamin wanda baikai 20yrs ana ce masa annur,,yanda suka rinka tarairayar sa shi yasashi farin ciki sosai,,,sai daya yi kwana2 yana hutawa kafin ya fara shiga skul shida abbas,,,ammar ya maida hankali sosai a karatun shi ba ruwan shi da babes din dake tururuwa akanshi bakake da fararen wasu abota suke yin dashi wasu kai tsaye zasu nuna sonshi baya kula su dan shi ba tasu yake ba mace daya keda wannan matsayin kuma baya tare da ita amma kullum da ita yake kwana yake tashi a ransa,,har su abbas sun san labarin jiddan ammar,,haka rayuwa take ta tafiya cikin kwanciyar hankali,,
a bangaren jiddah sai ince maganin inna asabe ya fara ci dan yanzu tana ji ana kiran sallah amma bata damu ta tashi tayi ba,bata karatun Qur'ani ballantana kuma azkar din da takeyi haka kawai zata rinka jin kasala a jikinta ko kuma jikinta ya mata nauyi,,inna asabe tana cikin farin ciki tana lura da duk halin da jiddah ke ciki har tana shirin komawa wajen boka ya cika mata aikin da suka fara....
Ur's princes deejerh💝
[16/01, 18:47] khadija ahmad dija Marubuciya Barauniya ce Frien Din Hassn: ✨✨BA DON SHIBA✨✨
By Princess Deejerh
New Writer
Alhamdulillah na gode da addu'ar ku gareni masoyana insha allah yanzu na dawo ba wani sauran jinkiri...
Luv u oll😘
Page 4⃣6⃣ to 5⃣0⃣
Jiddah rayuwa ta fara sauya mata domin kuwa maganin inna asabe ya fara tasiri a kanta a yanzu jiddah sallah bata dame ta ba,,makarantar ma yanzu tana SS2 amma ta daina zuwa bata karatun alqur'ani data saba yi duk safiya,ita kanta tana jin wani iri a jikinta amma kuma tana son yin karatun amma data fara sai taji kasala ta rufeta,,,
tabbas asiri gaskiyar mai shi wannan haka yake ta bangaren inna asabe da ya'ya'nta domin yanzu farin ciki suke ciki kamar an basu kyautar kujerar makkah,,,
a safiyar yau ne inna asabe ke shirin komawa wajen bokanta domin yin aiki na karshe a kan jiddah saboda haka tun asuba ta tashi tana sauri ta fita dan kar ta tarar da layi haka nan take jin farin ciki a cikin zuciyar ta..ko farkawa bata bari sunyi ba ta zari mayafi sai gidan boka...tana zuwa bata tarar da kowa ba dan ta bugo sakko...yana ganinta ya fara washe wagegen bakin shi wanda ba haure ko guda daya a ciki,,magana ya fara mata da katuwar muryar sa,,lallai ke jaruma ce muna son aiki da irin ku wadan da basa bata mana aiki,,,saboda haka wannan ma aikin naki tabbas zan miki me zafi..wata laya ya ciro a kasan inda yake zaune tare da mika mata layar,,,tana rawar jiki ta amsa..wannan layar a kasan inda take kwanciya zaki haka rami ki binne ta,,sannan ya kara dakko wani garin magani ya mika mata,,wannan kuma ki zuba shi a daidai inda kika san zaka taka,,tofah da taka kuma ta kwanta akan wannae layar aikinki
ya gama,,,amma kuma da sharadi,,sharadin meye boka inna asabe ta fada,,dan kuwa ita a ranta ko meye sharadin zata yarda komi munin shi kuwa indai jiddah zata wulanka a idon duniya,,,sharadin kuwa shine duk randa aka tona wannan layar to wannamd asirin kan daya daga cikin ya'ya'n ki zai koma,,duk da ta tsorata amma hakan bae hana ta amsawa ba da ta amince,,dan kuwa tasa aranta bame tonewa,,
shidai boka maimaita mata yake yi,,amma da yake zuciyar ta ta kekyashe bata damu ba,,,kudi ta ciro ta mika masa sannan ta fito ta fara tafiya dan samun abin hawa,,,
Ammar ne zaune a compound din gidan shi kadaine amma kallo zaka masa kasan ya lula duniyar tunani ,,abbas ne tsaye akan shi amma shi baima sani ba,,,ruwan dake hannun sa ya yarfa masa,,firgigit ya dawo hayyacin sa,,,murmushi yayi kafin yace
lafiya,,ina fa lafiya kana nan ka antaya cikin tinanin jiddah koba haka bane nasan dai ita kadai keda wannadm matsayin,girgiza kai ammar yayi kafin ya fara,,hakanadm a yan kwanakin nan nakejin faduwar gaba kamar wani abu mara kyau zai sameni kuma tunanin jiddah yana fadomin cikin raina koda yaushe,,,numfasa wa abbas yayi kafin yace ni ina ga kamar rashinta a kusa da kaine ya kawo hakan amma ba abinda zai faru,,ya kamata ka kirata kaji lafiyarta,,,na fada maka na kirata amma wayar bata shiga anya lafiya kuwa ya kamata inji daga gareta dan ni wannan shirun nata bana lafiya bane dan yasan koshi bai kirata ba ita zata kirashi,,,
Ur's princes deejerh💝
[16/01, 18:48] khadija ahmad dija Marubuciya Barauniya ce Frien Din Hassn: ✨✨BA DON SHIBA✨✨
By Princes Deejerh
New Writer
Gaisuwa ta musamman gareku
Teemah sulfat
umma muhammad
noorul jannerh
asma baffa
khadeeajah candy
aneey lurv
aneesa didi
Page 5⃣1⃣ to 5⃣6⃣
WACE CE JIDDAH?
Malam salisu haifaffen garin zamfara ne a wani kauye da ake kira kiyawa,,matar sa ta aure guda daya ce tal halima tun auren saurayi da budurwa sai dai allah bai basu haihuwa da wuri ba,,har sun fara fidda rai da samun haihuwa allah maji rikon bayinsa sai ga halima da ciki,,lokacin da malam salisu ya samu wannan labarin ba karamin farin ciki ya shiga,,mutane ma na taya su farin ciki,,haka sukayi rainnn cikin nan da yake cikin mai laulayi ne sosai halima ta rame sosai tanajin ciwo a cikin jikinta amma bata nunawa saboda bata so hankalin malam ya tashi,,,a lokacin da cikin ya shiga watan haihuwa kuwa idan kaga halima sai ka tausaya mata domin ta kumbura ne ko tafiya dakyar take yinta,,,wataranar lahadi ta tashi da ciwon nakuda cikin dare,,,da sauri malam yaje ya kira ungozomar dake karban haihuwa a kauyen,,,koda suka zo tayi matukar galaiba ta domin ko numfashi bata iyayi sai da kyar,,,dabarun su na tsoffi ta fara mata amma haihuwa shiru azaba kawai take ci..malam yana daga kofar daki amma kamar shine ke haihuwan duk ya hada zufa,,har wajen asuba bata haihu a ba lokacin nan bambam cinta da gawa kalilan ne,,addu'a malam yayi cikin kofi sannan ya shigo cikin dakin,,ungozomar ce ta taimaka masa suka zuba mata a baki wani yana shiga wani na fitowa haka dai suka rinka bata har ta shanye,,,cikin abinda bai wuce minti biyar ba nakudar ta kara tasowa har tafi na farko azaba,,da sauri mallam ya fita ba zai iya jure kallonta cikin wannae halin ba,,,kamar jira take ya fita kuwa kan da ya fara fitowa sai kuma numfashin ta ya fara tsayawa,,,wani nishi tayi da karfi gaba daya yaron ya fado yana canyara kuka,,tunda halima tayi wannan nishin jikinta ya saki alamun ba rai,,daga waje malam ya fado cikin dakin ko ta yaron bai biba ya nufi inda halima take kallo daya ya mata yasan bata da rai,,,cikin tashin hankali ya fara girgiza ta amma inaaa rai yayi halinsa,,,,karar jin faduwar sa kawai ungozomar tayi wadda ke gefe rike da jariri tana jimamin mutuwar halima,,,,da sauri ta aje shi a gefe tayi waje ta kira makota,,,,kan kace me mutuwar halima ta zagayen garin kiyawa kowa nata jimami dan kuwa halima mutum ce ta gari ga son jama'a..masu kuka nayi masu addu'a nayi,,,malam kuwa tun faduwar da yayi bai farfado ba har sai da aka gama hada halima,,,Innalillahi wa inna ilaihir raji'un kalmar da yake ta maimata wa kenan kafin ya samu sassauci a cikin zuciyar sa...dakin da gawar take ya shiga ya tsugunna a gabanta addu'a yake kwararo mata yana nema mata rahamar ALLAH,,,,haka da aka binne ta ma sai da yayi mata addu'a yana hawaye kafin su dawo gida,,,,
haka aka cigaba da amsar gaisuwa har akayi addu'ar bakwai,,anan ne fa aka fara tunanin wa zaa ba muhammad sunan da malam ya sama yaron kenan,,,kowa yayi shiru alamun dai babu mai amasar sa,,,dan kuwa duk yan'uwan malam ne a wajen baida mahaifiya sai kannan uba da yayyen su,,,ita kuwa halima dama marainiya ce,,,,duk cikin su aka rasa wazai ce zai amshi yaron,,ganin haka da kawu iro ya gani,,yasa ya yanke shawarar aura mai ya'r sa TALATU kowa yayh1 na'am da hakan dan kuwa kawu iro duk shine babba a cikin su babu mai masa musu,,,,shima malam ba yadda zaiyi ne,,,a take a wajen akai komai aka gama abinka ga kauye,,,washe gari kuwa aka kawo amarya dakinta,,,
haka rayuwa ta cigaba da tafiya talatuwa bata nuna son muhammad sai malam na nan inko baya nan azaba yake sha kalakala a hannun ta,,,a haka suke rayuwa kullum tana tsanar muhammadu,,
lokacin da muhammadu ya cika shekara 25 tsufa ya kama mallam itama talatuwa haka amma duk da haka zuciyarta na nan da tsanar muhammadu,,shiko kyautata mata yake sosae domin yanzu sana'a yakeyi mallam ya bude masa provision a cikin kasuwar garin,,,ganin haka yasa talatu fara nema masa auren yar gidan kanwar ta ASABE,,,malam ya amince da hakan domin shi yana ganin talatu ba zata cuce shiba,,,
Asabe yarinya ce mara tarbiyya bata ganin kan kowa da gashi,,ba arabi ba boko sai ya yawon tallah da bin shagunan mutane,,,tuntuni take nunawa muhammadu so amma shi gani yake me zeyi da ita basu dace,,,kowa yasan asabe bata da mutunci indai zaka bata kudi tofah zata bika koma ina ne,,,dan bata dauki jikinta da daraja ba,,,da labarin auren ta da muhammadu ya shiga kunnenta kuwa farin ciki tayi mara iyaka,,,dama abinda ake nema ido rufe,,,
ba wani lokaci aka sa me tsawo ba,,,akai auren muhammadu da asabe,,sai rawar jiki take..shiko kallon ta kawai a wulakance domin kuwa bata kawo mai yancinta,,,haka zamansu ya kasance kadahan kadaran da farko asabe kamar zaayi zaman lafiya da ita,,amma ta fara fito da mugayen halayenta bai isa ya sata abu tayi ba ga rashin kunyar tsiya,,gashi bata zama a gida kullum tana hanyar gidan bokaye,,ana haka ta samu ciki farin ciki sosai takeyi shima muhammadu ba'a barshi a baya,,,lokacin haihuwa allah ya bata da namiji akuma ranar