Showing 9001 words to 12000 words out of 18345 words
Chapter 4 - BA DON SHIBA COMPLETE DOCUMENT by Prince Deejerh.txt
ne mallam salisu yace ga garin ku nan,,,muhammadu ya shiga damuwa matuka da rashin mahaifin sa,,amma haka ya fawwala wa ALLAH komae,,ranar bakwai ranar ne sunan muhammadu yace ba zaayi taro ba kuma zai maida sunan malam akan yaron,,,nan fa asabe tayi tsalle ta dire ta ce ba zaa sama danta wannan sunan ba,,magana har gurin manya amma suka goyi bayan asabe,,,haka muhammadu ya hakura tasa ma yaron haladu,,,tun daga nan fa haihuwa ta bude ma asabe,,bayan shi yara uku ta haifa duk mata,,indo,rabi,da ma,u,,,,yara sun taso kamar uwar su basu da kunya duk abinda sukayi sai dai asa musu ido dae kuwa baa dukan ya'ya'n asabe,,,
ana haka ne allah ya hada malam da fatima kallo ya mata alla ya jarabce shi da kaunar ta,,fatima yarfulani tallan nono takeyi ita da yayyenta d,,,fatima yarinya kyakkyawa er kimanin shekara15 bata da hayaniya ko kadan ga hakuri,,,muhammadu bai tsaya wani jinkiri ba ya gabatar da kansa a wajenta da iyayenta,,,,duk sun amice dashi dan haka yaje ya fadawa kawu iro......
da kamar wuya....
Ur's princes deejerh💝
[16/01, 18:48] khadija ahmad dija Marubuciya Barauniya ce Frien Din Hassn: ✨✨BA DON SHIBA✨✨
By Princess Deejerh New Writer
Wannan shafin sadaukarwa ne a gareki ke kadai kiyi yadda da kike so dashi UMMYN YUSRA ina yinki irin sosai din nan😍
5⃣6⃣ to 6⃣0⃣
Haka kawu iro ya badawa idon shi kasa yace sam ba za'a yiwa ya'r sa kishiya ba,,a wannan lokacin muhammadu yaji sam ba zai iya bin maganar kawu iro ba,,,saboda haka yana tashi gidan malam idrissa ya nufa abokin baban sa tun na yarin,,ya kwashe komai ya fada masa...malam idrissa tsoho me dattako yace zai shige mai gaba ayi komai,,,,,haka kuwa akayi shida wasu abokanan sa su biyu suka je nema mai auren,,,aka gama komai cikin mutunci kowa na farin ciki aka tsaida rana sati uku masu zuwa,,muhammadu yayi matukar farin ciki da hakan...A lokacin da kawu iro yaji labarin cewa yayi lallai sai ya sakar masa yarinya,,tijara ba irin wanda beyi wa muhammadu ba,,,takanas ya taka har can gidan su inda itama asabe ke zuba ruwan rashin mutuncinta....shima da yake baban nata dakiki irin ta sai ya dora daga inda ta tsaya,,yana cewa lallai sai ya basa takardar ta,,,ai asabe najin zance saki jikinta yayi sanyi dan itafa har yanzu tana son mijinta,,ba kunya ba tsoron allah asabe tace itafa tana son mijinta,,,kawu iro tunda yaji tace haka ya saba babbar rigarsa yayi waje tare da fadin to ai shikenan tunda kin zabi zama da kishiya,,,
Kwanci tashi ba wuya a wajen allah yau saura kwana2 bikin muhammadu da fatima,,,asabe tayi tijarar tayi bala'in tayi rashin mutunci amma duk a banza malamai kuwa sunci iya nasu amma duk ba nasara hakan yasa ta hakura amma ta kudirta a ranta kowa ce aka auro to kamar ta shigo makabar ta ne dan har ta gama tanadin irin rashin mutuncin da zata mata..
Rana bata karya sai dai uwar diya taji kunya dan kuwa a yaune mutanen kauyen kiyawa suka shaida daurin auren muhammadu salisu da fatima hamisu jauro...muhammadu sai washe baki yake kallo daya zaka masa kasan yana cikin farin ciki,,,domin shi a cikin ranshi fadi yake yanzu ne yayi auren soyayya
Ko kafin magarib tayi har ankai amarya dakinta dake gefen dakin asabe,,,,iyayen fatima sunyi kokari sosai gurin tsara mata dakin ta duk da daki ne irin kauye,,amma hakan bai hana shi yin kyau ba‘’ana gama shirya komai mutane suka fara tafiya sai ya'n uwanta na jiki,,,fatima na lullube cikin koren mayafi ba abinda takeyi sai kuka fuskar nan tayi jajir,,,,duk hidamar nan da akeyi asabe bata nan ya'ya'n ta nacan gidan su,,,ita kuma tana can bin yawon malaman ta,,,,,kan kace me kowa ya watse gidan yayi tsiiit...a lokacin ne kuma muhammadu ya shigo dakin amarya fatima ya wuce tunda yasan har yanzu asabe bata dawo,,,amarya fatima na zaune bakin gado,,kanta a kasa...da dabara sai da muhammadu yasa ta saki jiki dashi,,,ledar hannun shi ya bude tsirene a ciki wanda yaji quli da kayan miya sai turiri yake,,,,dakyar fatima taci dan ita nauyin shi takeji,,,shiko ko a jikin sa,,,haka ya lallabata,,,
wannan daren muhammadu yayi kwanan farin ciki a lokacin ji yake kamar bai taba aure ba dama,,,fatima kuwa tasha albarka dozen2,,,,
ita kuwa asabe koda ta dawo ko kallon sashen amaryar bata kalla ba tayi shigewarta dakin,,,a wannan daren asabe bata runtsa zirga zirga takeyi a dakin kamar kwancen hauka,,ji take kamar taje taita buga kofar dakin,,,,
washegari muhammadu ya tashi cikin farin ciki da kansa ya hada mata abin karya wa ya dibar mata nata ya diba na asabe ya kai mata dashi da abincin ko kallon arziki bai samu ba,,,shima bai biye mata ya fita ya koma dakin amarya fatima..
Haka rayuwa ta cigaba da tafiya fatima na kokarin ganin tayi ma asabe biyayya amma ita kuma bata gani ita da ya'ya'n ta haka suke mata rashin mutunci kala kala,,,ba halin tayi magana haka zasu je kofar dakinta suyi wasa da kasa a kwaba da ruwa suyi kaca2 da wurin su kuma tashi su bar shi,,,haka asabe ke mulkinta son ranta a gidan ta wulakanta fatima yadda ranta yaso ita ya'ya'nta,,,fatima me hakuri ce koda yaushe sai dai ta shige daki tayi kukan ta ita kadai bamai rarrashinta..ko yan'uwanta sunzo bata iya fada musu,,,,ita kuma asabe bata tashi iskancin ta sai taga muhammadu bayanan .har jifanta take sa haladu yayi idan ta fito tsakar gidan,,,shiyyasa yanzu bata ma fitowan koda yaushe tana cikin dakinta,,
Ana cikin haka sai ga cikin ya bayyana a jikin fatima,,,muhammadu murna yakeyi kamar yanzun zaa fara haihuwa a gidan sa,,,,asabe kuwa ina wuta ta jefa fatima dan tsananin takaici da bakin cikin da take ciki,,,CIKI a jikin wannan ya'r mayun to wallahi wannan cikin ba zai taba zuwa duniya tayi alkawari hakan,,,mayafi ta zara tasa shafdeden silifas dinta ta fita a gidan kamar wata mahaukaciya,,,tayi alkwarin ko zatayi yawo tsirara sai ta salwantar da fatima da abinda ke cikinta,,,,
ANYA KUWA,,,,,
Muje zuwa wai mahaukaci ya hau kura😂😂
UR's princes deejerh💝
[16/01, 18:48] khadija ahmad dija Marubuciya Barauniya ce Frien Din Hassn: ✨✨BA DON SHIBA✨✨
By Princes Deejerh
New Writer
Wanga shafin sadaukarwa gareki MISS XERKs ke kadai kiyi yadda kike so dashi sannan kuma kici gaba da antayo mana HIDAYA NOOR
Page 6⃣1⃣
to 6⃣5⃣
Bata zame ko ina ba sai gidan malamin ta haka ta kwashe komai ta fada masa,,kulli magani ya bata sannan yace mata ta tabbar fatima ta tsallake wannan maganin idan har ta tsallake shi cikin zai zube kuma itada kara haihuwa har abada,,,cikin murna ta ciro kudi ta bashi,,,
haka ta kara kamo hanya buguzum buguzum tana tafiya tana sake saken mugunta cikin ranta,,koda ta isa ta tarar da fatima zaune bakin dakin,,yaranta kuma kowa ya tafi yawon shi,,ko kallon inda fatima take bata yiba ta shige dakinta,,,ita dai fatima baiwar allah tunda ta mata sannu da zuwa taji bata amsa mata ba taja bakinta tayi shiru,,daga karshe ma dakinta ta shige tayi kwanciyar ta
asabe na daki amma sake sake take yi a ranta na yadda zata zuba wannan maganin a kofar dakin fatima,,,lekawa tayi taga tsakar gidan ba kowa komawa daki tayi ta dakko maganin sannan ta fito ta fara tafiya a hankali har takai kofar dakin fatima da take can daki tana barci bata san wainar da ake toyawa ba,,,,bude kullin maganin tayi sannan ta barbada shi a duk kofar dakin sannan ta juya ta koma tana murmushin nasara...
kiran sallar la'asar ne ya farkar da ita daga barcin da takeyi buta ta dauka domin zagawa bandaki kafin tayi alwala,,bata ko kalli kofar dakin ba ta tsallake tayi wuce,,,tana wucewa taji kamar an tsikare a mararta bata kawo komai ba a ranta ta shige bayi,,,,ta tsugunna da niyyar yin fitsari a maimakon ya fito sai jini taga yana fita kamar anbude famfo,,,cikin tashin hankali ta mike da sauri amma kuma sai taga jinin nabin cinyoyinta ga wani murdawa da mararta keyi,,dakyar ta lallaba ta fito ta koma daki duk inda tabi sai jinin ya zuba...
i
asabe na daga kofar window din dakinta tana ganin komai farin ciki ne ya kamata ganin aikin ta yaci,,,murmushin mugunta tayi tana fadin ni asabe wazai ja dani ya kwana lafiya ballantana wata karamar alhaki wai fatima kinta gani kenan keda haihuwa har abada sai dai kiga mata nayi...(nidae nace ta allah bata kiba asabe🤨🤨)
muhammadu kamar yasan abinda ke faruwa yau yaji yana son dawowa da wuri haka ya kamo a er kekensa ya taho gida,,,dakin asabe ya fara shiga,,kallon da yaga tana mai ne yasa shi kara kallonta,,ganin zai dagota ne yasa ta fara magana,,sannu da zuwa ai yanzu na dawo daga wajen kawu yace yana gaesheka,,,toh kawai yace ya fita ya nufi dakin fatima,,,asabe bata so ya dawo yanzux tasone jinin ta yayi ta zuba har azo a samu gawarta,,,,(MUGUWA😡)
jinin da ya gani kofar dakin ne ya sashi karasa wa da sauri cikin dakin inda anan ne yaga tashin hankali,,,kwance take cikin jini shame shame sai numfashin ta dake fita kadan kadan,,,cikin tashin hankali ya karasa inda take tare da tallafo yanayin daya ganta ne yasa shi fashewa da kuka,,,,da yaga haka bazata mai ba sai ya sabeta a kafada yayi waje da sauri,,haka ya rinka ratsawa har ya isa da ita karamin asibitin dake garin,,,da sauri aka amshe ja aka shigar da ita ciki,,,shi kuma ya koma gefe yana zirga zirga tare da tinanin me ya jawo mata hakan shidai yasan lafiya lau ya barta kafin ya fita,,,,
sai dai aka share awa biyu a kanta da kyar likitan ya samu ya tsayar da jinin dake zuba sannan aka mata allurar barci,,,likitan na fitowa muhammadu ya taso da sauri yabi bayan shi sai da ya shiga office din likitan kafin ya fara tambayar shi halin da fatimar ke ciki,,,,bayani ya fara cikin nutsuwa,,,,gaskiya duk iya dubarwa da mukayi bamuga wata matsala ba da har yasa wannan jinin zuba ba,,,sannan kuma har yanzu cikin nanan bai fita ba sai dai zaka bari zuwa gobe sai a sallameku,,,farin cikin da muhammadu yaji a lokacin bai misaltuwa,,,gidan su fatima yaje ya fadawa mamanta abinda ke faruwa tare suka tawo asibitin sannan shi kuma ya koma gida dakko kayan da zasuyi amfani dashi,,,
sai da fatima tayi kwana2 a asibiti jiki kam alhamdulillah taji sauki sosai,,ba wanda baije gaisheta ba amma banda asabe,,,,dan tunda taji ance fatima ta samu sauki take cikin takaici da bakin ciki
haka sanda fatima ta dawo duk makota na shigowa yi mata ya jiki asabe naji tana zaune a dakin tana fama da bakin cikin da ya cika mata zuciya,,,
haka rayuwa ta cigaba da tafiya cikin fatima na girma amma daga ita sai muhammadu suka sae tanada ciki kowa yana tinanin cikin ya zube ciki kuwa harda asabe,,,wadda keta murna shiyyasa yanzu kota kanta bata bi
ita a tinanin ta ai tariga ta gama da ita
🤣🤣🤣Asabe sai dai kiji kukan baby aradu
Pls kuyi hakuri da wannan
Ur's princes deejerh💝
[16/01, 18:48] khadija ahmad dija Marubuciya Barauniya ce Frien Din Hassn: ✨✨BA DON SHIBA✨✨
By Princess Deejerh
New Writer
Ina kuke 6ters na kwarai wannan shafin sadaukar wa gareku ina yinki irin totally dinnan
Aisha mohammed sani(Zayeeshart)
My Nusaiba mu'hd auwal(Nusy bea)
Ruqayyerh tertherr risqua(er kanwata)
Umma muhammad(Ummu aiman)
Pharteemah Ahmad(teemah sulfat)
Phertymah harun(mommy kd)
Ga masu son shiga group dina BA DON SHIBA FANS CLUB ko kuma PRINCES DEEJERH NOVEL sai ku tuntubeni ta wannan numbers
08104609894
09061274993
08060972795
07033851935
Page6⃣6⃣to7⃣0⃣
Haka fatima da muhammadu suka cigaba da rainon cikin da ba wanda yasan dashi domin kuwa kullum da hijab take kuma dama cikin nata bamai girma bane
Ranar wata talata da safe fatima ta fara nakuda bata sha wata wahala da kanta ta santalo lafiyayyar ya'rta mai kama da larabawa dan kuwa fara ce jajir babu ta inda ta bambamta da uwartt,,,farin ciki kuwa gurin muhammadu bai irguwa da kanshi yaje har gidan su ya taho da kanwar innarta ita tayi mata komai ta yanke ma jinjirar cibi ta wanke ta tass sannan aka nadeta a wani farin towel,,sannan ta hada ma fatima ruwan itama da kanta tayi mata wankan,,kafin ta dumama mata tuwaon dawa ta kawo mata,,,idan kaga fatima ba zaka ce itace ta haihu ba dan kuwa lafiyarta kalau ita da jaririyarta,,,muhammadu ne ya shigo dakin hannun sa rike kayan tea da siyo mata gurin ya nufa tare da daukan jinjirar fuskar nan fal farin ciki da annushuwa,,sai da yayi ma yarinyar addu'a kafin yayi mata huduba da suna HAUWA'U JIDDAH,,,fatima tayi matukar farin ciki da yasa mata sunan innar ta,,,sai a lokacin mutane suka fara shigowa gidan suna yi mata barka suna santin kyan yarinya,,,ita dai saidai kawae tayi murshi idan mutane na tambayar ta wai dama ciki gareta,,,ko en uwanta da suka zo mamaki suka rinka yi tare da godema allah,,,
shigowarta kenan gidan taga mutane wasu na fitowa daga dakin fatima wasu na shiga ga kuma en uwanta zazzaune a kofar dakin,,,mamaki takeyi tow meye akayi haka da har dangin mayyar can suka zo suka wani cika musu gida da hayaniya inama mutuwa shegiyar can tayi ai wlh da sai ta kira masu kidan kwarya sun buga mata ta cashe,,,sallamar muhammadu ce ta katshe mata tunanin da takeyi ko amsar sallamar bata yiba ta tsaya kallon shi ganin sai wani washe hakora yake,,,katse yayi tare da fadin amm... asabe munfa samu karuwa yau a gidan nan,,,,be tsaya jin me zata ceba ya cigaba da fadin dazu fatima ta haihu mun samu ya' mace jiddah,,,tana zaunau a kan kujera ertsugunne amma sai data wuntsila tare da bajewa a dakin tayi zaman yan bori,,,cikin zaro ido tace wata fatiman,,,hanyar waje yayi yana fadin fatima nawa garemu a gidan tareda ficewa,,,yana fita ta zube a kasa burgima ta fara a tsakar dakin ta rasa inda zata tsoma ranta kawai saita fashe da kuka da wannan ranar ai gara mutuwar ta malam ya cuceni ya yaudareni,,kuka takeyi kamar karjmar yarinya,,,fatima ce wai ta haihu ta kara maimaitawa wallahi sai naga bayanta ita da shegiyar ya'r tata,,,
Haka akayi suna cikin kwanciyar hankali rago biyu manya manya muhammadu ya yanka mata bayan kaya da ya dinka mata itama jiddah ya saya mata kaya sosae ga kuma wanda dangin fatima suka mata komae dae alhamdulillah,,,tun mutane na tambayar fatima ina kishiyar ta take har suka bari,,dan asabe bakin cikin ta take nunawa kiri kiri ba abinda ta taba ko taci wanda ya danganci haihuwar fatima kuma bata fasa bin malaman ta daka ganta kasan bata da kwanciyar hankali...
taron suna ya watse kowa na sam barka fatima ta cigaba da renon yarta itada muhammadu,,,asabe saidai ido dan ita kadai tasan tsiyar data shuka kuma tasadm tabbas wannan sai tayi nasara domin wannan ba irin wancan bane...
Wata ranar sati muhammadu ba zai taba manta ta ba da kuma iyayen fatima da en uwanta,,,a safiyar da aka nemi fatima sama ko kasa aka rasa ba inda baa je nemanta ba a kauyen kiyawa har makotan su amma ko sawunta ba'a gani ba,,muhammdu suma yayi sai da ya kusan awa biyu kafin ya farfado ,,,yana farfadowa ya tashi tare da nufar kofar gida mutane suka rike shi amma ina turjewa yakeyi yana fadin abar shi yaje ya nemo fatimar sa,,,basu kara shiga tashin hankali ba sai da jiddah ta fara kukan yunwa aka rasa yanda zaayi innar fatima ce ta amshi yarinyar tana jijjigata amma ko alamun yin shiru batayi,,,fashewa da kuka kowa yayi ganin muhammadu na kuka wiwi kamar mace,,a yau asabe tayi rawa tayi juyi tayi hawayen farin ciki burinta ya cika,,dama sabon malaminta yace kurciya zaa mata itada dawowa garin kiyawa har abada,,,
Tsawon sati biyu kenan ba fatima ba labarinta jiddah kuwa tana gurin innar fatima itake renonta a yanzu kudi muhammadu ya bada isassu aka siyo madarar jarirai kuma da akayi saa tanasha sosae,,,muhammadu a yanzu rayuwa kawae yake domin kuwa asabe saida ta mallake shi tsab komai sai idan ita tace yayi tsoronta yake matuka yanzu,,kudi take amsa a gunsa koda yaushe tana wadakarta ita da yaranta shiko ya zama konko yanzu
BAYAN SHEKARA DAYA
a yanzu kam muhanadu baida komai asabe ita da ya'ya'nta sun gama cinye kudin shi tsab yanzu shagon da yake zuwa ma ankwace saboda rashin biyan kudin haya,,,
jidda kan yanzu shekarar ta daya tana gudun ta koina har anyaye ta,,yarinya me kyau me shiga rai ga gashinta dogo baki sidik daka ganta kasan jikar fulani ce,,,
A wannan lokacin ne kuma muhammadu ya samu aiki a garin kaduna na gadi saboda haka duka zasu tafi harda asabe da yaran yaso yabar jiddah amma asabe ta rura wuta sai da ya amsota,,,
haka suka tattara suka koma garin kaduna da zama a gidan suke zaune a BQ a lokacin ne jiddah ta fara shiga matsalar rayuwa duk da kuwa kankantar ta amma haka asabe ke mata mugunta kalakala,,ana cikin haka ne malam muhammadu ya sayi wani dan karamin gida da kudin da yake ajiyewa suka koma can,,,sun koma ba dadewa malam muhammadu ya fara ciwon ajali kwana2 yayi yace ga garin ku nan,,,asabe tayi kukan mutuwar shi nadan lokaci ta share ta cigaba da rayuwas itada yaranta,,,
mutuwarsa tasa jidda kara shiga matsalar rayuwa asabe sai taga damar bata abinci yawo take kamar almajira a cikin unw a lokacin shekarta 12 su rabi kam a lokacin anza entayi galan ana kawowa inna asabe kudi tana amshewa tana murna
ana cikin irin wannan rayuwar ne ALLAH ya jefo ammar cikin rayuwar jiddah ganin farko daya mata yaji ta shiga ranshi ga kuma tausayinta da yakeji saida ya tuntubi makota suka bashi labarinta tofa tunda ga wannan rana ammar ya fara kula da jidda da kansa ya sata a makaranta ya dinka mata uniform,,shike bata duk wata kulawa,,,inna asabe zata mai rashin mutunci ya nuna mata nashi rashin mutuncin yafi nata haka nan ta hakura badan ranta na so,,,,,
CIGABAN LABARI ku biyo a next page
Ur's princes deejerh💝
[16/01, 18:48] khadija ahmad dija Marubuciya Barauniya ce Frien Din Hassn: ✨✨BA DON SHIBA✨✨
By Princes Deejerh
New Writer
AMEENTA WRITERS ASSOCIATION🤝
Page 7⃣1⃣to 7⃣5⃣
CIGABAN LABARI
Tun dawowar inna asabe daga wurin bokan ta ta kasa zaune ta kasa tsaye.domin kuwa a yaune take son ta gama duk wani mugun kullin ta a kan jiddah ta rasa yadda zatayi ta shiga dakin dabara