Showing 3001 words to 6000 words out of 18345 words
Chapter 2 - BA DON SHIBA COMPLETE DOCUMENT by Prince Deejerh.txt
kwata ka kusa kama gabanka ai,,shidai baima samd tanayi ba..kicin ya shiga ya dakko abincin sa ya fice daga sashen gaba daya,,,yana gama cin abinci ya shiga wanka be dade ba ya fito shiryawa yayi cikin wasu riga da wando rigar me dogon hannu ce wandon kuwa jeans ne amma duk amma sa crazy,wata sarka ya jawo me uban nauyi ya dora ta a wuyanshi..sannan yasa pcap a kanshi,,ya fito a dan dabanshi sak amma hakan bai hanashi yin kyau ba..ficewa yayi a gidan a 360,,,
kiran sallah magribtne yasa ta mikewa dakyar ta rarrafa ta dauki buta alwala tayh kafin ta kara komawa cikin dakin dakyar ta samu tayi sallan ta kara komawa ta kwanta dan har yanzu zazzabin bai sake ta,,tana jiyo hayaniyar inna asabe da yayanta dan dama su sallah ba damun su tayi ba ,,kwala mata kira taji anayi kuma muryar inna asabe ce..cire lullubin tayi ta maida tasa a jikinta sannan ta nufi kofar dakin,,sallama tayi ba wanda ya amsa a cikinsu.sai wurgo mata kudi indo tayi tana fadin wuce ki siyomin pad a shagon sile bana son na shagon rabe,toh kawai tace tare da amsar kudin tayi hanyar waje,tafiya take kamar zata fadi amma haka ta cigaba,,
fitowar shi kenae daga masallacin su uku ne ammar auwal da kuma nura,tafiya suke da sauri domin time din wasansu ya fara,,tun daga nesa yake hangota tana tahowa a yanayin daya ganta yasa fuskar shi sauyawa,ina zuwa yace ma su auwal kafin ya isa inda take kallonta yake tun daga sama har kasa,dagowa tayi tana murmushin dole wanda yafi kuka ciwo,,waya miki haka kawai ya ce dan sai data dago kanta sannan yaga bakin ta a fashe ga kuma idonta daya kumbura,,kan uban can yace da karfi tare da zaro mata idanu,, tambayarki fa nakeyi yace a hasale,,a hankali ta fara fada mai abinda ya faru tare da fashewa da kuka,,,,,kutumar uba yau sai naci uban uban asabe sai na karya wa haladu kafa,,kai yau duk wani daya shafh asabe sai mun mai operation huci kawai yakeyi a lokacin da zai ga su haladu ba abinda zai hana bai cire ma tsohuwar nan da yayanta kafafuwa ba,,,maganar dayake da karfi ne ya janyo hankalinsu su auwal dama sun tsaya saboda karsu damesu,,, auwal yace yadai my man dogon tsaki yaja kafin ya basu lbrn abinda ya fara,,,,yeeeehuuuu,,cewar auwal kace yau anta bomu tunda aka taba jidda kai nura jeka tattaro su duna da bahago dukakasu da sauri nura yayi hanyar barin wajen domin cika aiki,,kara kallonta ammar kafin jeki gidan maman sahala zanzo in sameki,,,,
Toooh yaufa su inna asabe an taro pillars
yawan comment yawan typing
Ur's princess deejerh💝
[16/01, 18:47] khadija ahmad dija Marubuciya Barauniya ce Frien Din Hassn: ✨✨BA DON SHIBA✨✨
By Princess Deejerh
New Writer
wannan shafin sadaukarwa ne gareku daukacin members na zahra surbajo novel facebuk commen dinku namin dadi I HEART U ALL😘😘
Page 2⃣1⃣
to 2⃣5⃣
Sai daya ga ta shige gidan maman salaha sannan ya juyo ya fara tafiya yana saka irin rashin mutuncin da zaiwa haladu da uwarsa,,a bakin layin ya hadu dasu auwal ni kaina sai dana tsorata😳ganin irin mutanen dake tare dashi,gaba dayansu ba alamun murmushi a fuskar su jira kawai suke ace kule suce cass...duna ne ya fara magana yana ciccezewa..yadai baba wai aina za ayi operation din ne kasanfa kwana2 ban fede ba,,murmushin mugunta ammar yayi kafin yace ku biyoni muje..duuu kuwa suka bi bayanshi kusan su 15 ne amma duk shine a gaba kowane da makami kuma a hannun sa tun daga nesa da an hango su zaa fara gudu..dan mutane sunsan ba alheri bane ke tafe dasu ba,,wasu daga cikin mutanen kuwa har sun tausayama wanda zasu je gurin shi..domin kuwa ba yau aka saba ganin haka ba sai dai kowa yayi gumm ba bakin magana,,
jidda zaune a acikin dakin maman salaha amma hankalinta gaba daya baya jikinta tana tsoron abinda ammar zaije yayi...da karfi maman salaha ta kira sunanta sannan ta dago a firgece,,ke kuwa jiddah me yayi zafi haka,,cikin kuka ta labarta mata halin da ake ciki,,allah na gode maka maman salaha ta fada tare da kwashewa da dariya..tabbas ammar ya cika dan halak kuma yamin daidai,,da sauri jidda tace amma fa kada su mai wani abu daga baya,,hmm tace kafin ta fara magana jiddah kenan kinsan uban ammar nada kudi ba abinda zasu iya yimai,,sai da ta kwantar mata da hankali kafin taje taci gaba da aykinta
zirga zirga kawai suke a cikin gidan daga ita sai haladu domin su rabi tuni suka fice yawon su amma fa indo ta kullaci jiddah a ranta tun dazu ta aiketa amma bata dawo ba..da tunanin rashin mutuncin da zata mata inta dawo ta fita aranta,,,,,kofar gidan sukaji ana bugawa..da karfi kamar zaa cire inna dake tace kamu ta duro ashar kafin tace wani matsiyacin ne zai ballamin kofa shegu yan bakin cikin unguwa zasuja min asara,,shiko haladu da fitowar sa kenan daga bandakin ya fara zubo nashi ruwan ashariyar dan kuwa karan buga kofar ne yasa shi fitowa ba shiri,,,daga can waje kuwa ammar ne da gang dinsa tsaye mamakin zagin da tsohuwar da danta ne sukeyi ya kamasu duk da shi ammar yasan zasu iya fiye da haka,,,cikin fushi yama kofar zuwa daya sai gata a gefe.shiyya fara shiga cikin gidan sannan sauran suka biyo bayanshi..mute bakin inna asabe yayi ganin ammar da yan jagaliyanshi sai da kirjinta ya buga domin kuwa bata manta warning din daya mata kwanaki ba...shiko haladu me danyen kai zaburowa yayi wai zai naushi ammar zuwa daya ya kamashi hannun ya murda.ihun azaba haladu yasa naushin bakinsa yayi tare da jefar dashi a kasa gwajab kamar kayan wanki,,cikin daga murya ammar yace dasu operation start...aiko basu yi wata wata ba suka fara fasa duk wata roba ko bokiti dake tsakar gidan wasu kuma dakuna suka shiga suka fara tarwatsa kayan tsummokaran data tara kai hatta igiyar shanya basu barta ba,,,tukwanen kuwa sai da duk suka taka su duk suka lauye,,nuna musu haladu yayi dake kwance har yanzu yana jinyar hannun sa,,ku kawo min shi nan dakko shi suka yi suka ajeyi a gabanshi baiyi wata wata ba ya kai mai naushi a fuska sai ga jini nabin gefen fuskarsa,,inna asabe na ganin haka tasa ihu tana neman agajin makota,,,jama'a ku kawo mana dauki ku taimako ga jujal nan da mukarraban sa...naushin da duna ya kai matane ya sata rufe baki bata shirya ba ai ko jini ya fara malala mangareta duna yayi ta fadi kafin su rufe su da dukansu bame ceton wani
Ur's princes deejerh💝
[16/01, 18:47] khadija ahmad dija Marubuciya Barauniya ce Frien Din Hassn: ✨✨BA DON SHIBA✨✨
By Princess Deejerh
New Writer
Page 2⃣6⃣ to 3⃣0⃣
Sai da ammar da yaransa suka musu wulakanci na bugawa a jarida shafin farko,,,sannan yasa suka kara buge haladu.,inna asabe kuwa tunda aka mata zuwa daya har yau tana kwance shame shame rike da kafarta da wani ya taka mata a cikinsu,,,sai da suka gama duk wulakancin da zasu musu sannan suka fice suka barsu kwance anan bamai taimakon wani a cikinsu,,
fitowar su yayi daidai da komawar kowa cikin gidanshi...dan dama duk mutane najin abinda ke faruwa
sai da jidda taci abinci tayi sallai ishai sannan taiwa maman salaha sai da safe ta tawo gida,,,tana zuwa kofar gidansu gabanta ya fadi ganin kofar a yashe a kasa tasan wannan aykin ammarne..da sallama ta shiga gidan,,su rabi ta samu zaune kusa da inna asabe tana gasa mata kafa da ruwan zafi ita kuma asiya da indo suna kan haladu suna goge mai jinin da ya bata mai fuska duk fuskar nan ta kumbura sai ya kara muni kamar irin horror dinnan....kowa ido ya bita dashi ba halin magana domin su rabi sunji labarin abinda ya faru shiyyasa ba wanda ya tanka mata..daki ta shige kawai tayi kwaanciyar ta..
Tofa tun daga wannan ranar baima dukan jiddah a cikinsu sai dai abita da harara da kuma tsaki..aikin gida ne dai haryau ba fashi,,
Haka rayuwa ta cigaba da tafiya duk da gidan ba dadi amma yafi da tunda yanzu har abinci ana bata kuma bata musu wanki saidai girki da gyaran gida,,a bangaren ammar kuwa har yanzu umma tana nan tana hada mai tarko duk da abbansa baya yadda,,amma dai bata karaya ba tayi alkawarin sai ya bar gidan duk daren dadewa,
A yanzu jiddah tayi jss c.e kuma ammar ne ya mata komai duk shima wannan shekarar zaigama scondry skul,,da kansa ya mata registration anan makaran tarsu aka bata ss1 science class,,tana makaranta cikin kwanciyar hankali da wuri take tashi ta gama duk ayyukanta na gida sannan ta shirya ta tafi,,tana fitowa zata samu ammar a bakin layi shi zai rakata har bakin makaranta sannan ya bata kudin break,tunda yabar makarantar haka yake mata duk da shima abbansa na neman masa makaranta,,,
inna asabe ce zaune ita da lami,,lami kawar inna asabe ce tun yarinta dan wasu halayen duk ita ta koya mata dan lami bata zaman aure ga bin bokaye,,inna asabe ce ke bata labarin abinda ammar ya musu har gida,,,mtsww lami taja tsaki kina aikin me har haka ta faru idan hagu takiya ai sai a koma dama,,tun farko sai da nace miki mukai sunanta gurin na bakin rafi amma kika ki to yanzu wa gari ya waya ke mana,,duk layi anata yi dake yayanki sun lalace ita kuma sai yabonta ake,,wannan yabon shi zamusa ya koma aibatawa,,yanda shikansa ammar din sai ya kyamace ta,,tabbas kawata kin kawo shawara me kyau gobe da sassafe zan shirya in biyo ta gidanki sai muje gurinshi,,yauwa ko kefa ki maidata abin kwatance,,ki dauki fansar abinda ammar ya miki dan na tabbatar sai yafi kowa shiga kunci idan ya ganta ,,,ai fa nagode lami nida duk banyi wannan tunananin ba,,,har kofar gida ta rakota suna kara tattaunawa akan muguntar da zasu ma baiwar allah da bata rikesu a zuciya ba...
Da daddare jiddah na zaune kofar daki itama inna asabe suna zaune ita da yayanta firar su suke cikin kwanciyar hankali,,sai dai kawai taji suna shewa,,kadaici ne duk ya isheta ina ma tana da iyaye da rayuwar ta bazata zama haka,,wani yaro karami ne ya shigo gidan,yace ana kiran jiddah a waje,,ba wanda ya tanka a cikinsu itace tace kace gani nan zuwa dan tasan ammar ne,,hijab kawai tasa tafita a tsaye ta same shi a kofar gidan,,gaeshe shi tayi ya amsa cike da kulawa,,shiru ne ya biyo baya kafin ya fara magana cikin sanyin murya kamar ba ammar ba,,,jiddah ya kira sunanta da sauri ta dago ta kalleshi domin kuwa yanda ya kira sunan nata ne ya sanyaya mata jiki,,ce mata yayi ga wannan amsa kawai tayi ba tareda ta duba ko meye ba,,shine yace atm carda dina ne sannan ga waya nan itama ya miko mata..amsa kawai tayi tana jiran karin bayani,,,jiddah zanyi tafiya mai tsawo abbana ya sama min makaranta a noida university india,,da sauri ta dago ta kalleshi domin kuwa maganar ta bugeta tuni har ta fara hawaye,,shima dakewa kawai yakeyi amma da ba abinda zai hana shi yin kuka amma bayaso ya karya mata zuciya,,,kuka ta fashe dashi da karfi domin ji take in ammar ya tafi kamar wani abu zai faru,kiyi hakuri jiddah ai zan rinka zuwa hutu akai akai,,,ita dai bata saurare shi ba kukanta kawai takey..jin kukan yake har cikin ransa,,,shima dan dai ba yadda zeyi ne abbansa ya matsa masa amma da ba wanda ya isa yasa shi zuwa wata kasa karatu,,dakyar ya samu ya lallabata har tayi shiru amma fa a zuciyarta ji take kamar ta mutu saboda bakin cikin tafiyar ammar,,,da kyar ya lallaba ta har ta shige gida,,shima ya tafi
a wannan daren ba wanda ya runtsa a cikinsu ,,,dan jiddah kwana tayi tana kuka...shi kuwa tinana shi wani hali zata shiga bayan tafiyar shi...
Ur's Princess Deejerh💝
[16/01, 18:47] khadija ahmad dija Marubuciya Barauniya ce Frien Din Hassn: ✨✨BA DON SHIBA✨✨
By Princess Deejerh
New Writer
Page 3⃣1⃣ to 3⃣5⃣
Haka jiddah ta raya wannan dare tana kuka..da ta tashi da safe kuwa fuskar nan tayi jajirr abinka ga farar mace,,idanuwan nan sunyi luhu luhu..a sanyaye take komai dan har yanzu zuciyarta bata dena mata zafi na tafiyar ammar ba...
Zaune yake a gaban abban shi fuskar nan a daure..sai ya dawo sak ammar din dana sani mara son wasa,,domin kuwa yayi tinanin abban shi zai goya mishi baya daya ce baya son tafiyar,,,abban ne ya fara magana cike da fushi...ammar kenan kai bakaji kunyar tunkara ta da wannan maganar ba kalleka fa shekara 22 sai yanzu ka gama scondry skul sa'annin ka duk tun yaushe suka gama saboda kai bakason cigaba kome?to wannan karon babu fashi gobe jirgin ku zai tashi da yamma ka gama duk wani shirinka dole ka tafi,,kai kafi so ka zaunj a gari kana yawo da abokan banza ana maka gata amma kai baka gani baza ka gane gata ake maka ba tukun sai nan gaba idan kayi hankali,,,tafiya kam ba gudu ba ja da baya na gama maka komai...ka tashi kaje ka cigaba da shiri,,,tun da ya fara fadan kanshi na sunkuye amma fa ji yake kamar zuciyar shi zata fashe saboda takaicin tafiyar shi,,,tashi suka yi duka kowa yayi dakin shi,,,da sauri umma dake labe tana jin duk yanda suka yi itama ta shige dakinta,,,waya ta dauka ta kira laraba ringing biyu ta dauka cikin farin ciki umma ta fara fesa mata duk halin da ake ciki,,dariya itama kwashe dashi sannan tace,ai na fada miki idan har kika yi haka dole yabar gidan tunda abbansa yana son yaga yayi karatu kafin nan da 5yrs din ai mun gama abinda zamuyi mun kara gaba,,,aikuwa dai laraba akwai ki da basira,,,kin mantani kenan umma wai dan ma nayi sanyi kenan,,,,to shknn jibi kizo da sassafe akwai magana tunda shi abban nasa ba zama zaiyiba,,,to shikenan...
Inna asabe da lami zaune a gaban na bakin rafi..lami ce zata fara fada mashi abinda ke tafe dasu,,,da sauri bokan yace mun riga mun sani tun shigowar ku dajin nan,,,yar mijinki ke baki matsala me kike so a mata a haukata ta ko a kashe ta,,,da sauri lami tace aa boka so mike a lalata rayuwarta ta koma kaman karya yanda al'umma zasu kyamace ta ta koma abin kyama,,,,katseta bokan yayi tare fadin ba yanzu ba,,,domin kuwa yanzu ba aljanin da zai iya zuwa ya rabeta dan tana ibada kuma ko yaushe cikin karatun qur'ani take duk aljanin da yaje kusa da ita kuwa yanzu to lalle sai ya kone,,,,inna asabe ji tayi kamar ta kurma ihu dan takaici taga samu taga rashi,,da sauri tace to yanzu boka ya zamu yi,,,,,cikin daga murya yace zan baki wani magani kullum ki zuba mata a cikin abinci indai tana ci to a hankali zata fara daina ibada zai saka mata kasala to a wannan lokacin ne zamu aiwatar da shirin mu a kanta,,,,amsa lami tayi tare da fadin mun gode boka,,kudi inna asabe ta ciro ta ajiyemai a gabanshi,,sannan suka fita....tafiya ce me nisa sosai tsakanin gurin da bakin titi,,inna asabe ke cewa lami,,to yaya zan bata maganin tunda kullum ne,,,mtsw lami taja tsaki kafin tace ta inda aka hau ai tanan ake sauka...nuna mata zakiyi komai ya wuce ta yafe miki ke inta kama har kuka kiyi ta yanda zata yarda kinyi nadama to ke kuma kinga kin samu hanyar yi mata komai tunda zata yarda dake,,,,tabbas shawarar ki tayi lami muje gidan dae....
atm card din daya bata ne a hannun ta ga kuma wayar a gefe..duk wannan basu take bukata ba tafi bukatar shi a kansu lokaci daya haka kwatsam...kuka ta kara fashewa da shi tana mai fadin allah ka kawomin dauki a rayuwata,,sallamar inna asabe ce ta katse mata kukan da takeyi...abin ya bata mamaki inna asabe da sallama bata kara jin mamaki ba sai da taga inna asabe ta leko tana fadin sannu jiddah ya gida,,da sauri ta mike ta fito waje dan kuwa har yanzu bata gama gyara gidan ba,,,kuma tana kara mamakin inna asabe,,zo nan jiddah taji ance daga bayanta cikin tattausan lafazi,,juyawa tayi ta nufi kofar dakin indainna take a tsaye,,,jiddah''da sauri ta dago kanta ido ta zare ganin inna asabe ido jajirr da alamu tasha kuka,,cikin muryar kuka ta fara magana jiddah ki yafemin na zalunce ki na cuceki tun kina karamar ki,zubewa tayi bisa gwiwarta tana mai kara fadin ki hakuri jiddah ki yafemin ko zanji salama a raina ina cikin kunci kada in mutu da hakkin ki a kaina ki yafemin dan allah jiddah tare da fashewa da kuka mai ban tausayi,,,,da sauri jiddah ta dago ta tana fadin inna kefah uwata ce bai kamata ki tsugunna a gabana ba wallahi na yafe miki,,,ngd jiddah cewar inna asabe allah ya miki albarka yata ta kaina,,bakomai inna komai ya wuce,,to jiddah jeki kwanta ki huta kema zatayi musu inna asabe tace lallaifa saidai ta kwanta,,ba yanda zatayi ta juya ta shige dakinta tana mamakin abinda ya faru ayau,,,inna asabe kuwa dariyar mugunta tayi kafinta tace yaro bai san wuta ba sai ya taka.....
yanzu aka fara
masoya novel dina kuyi hakuri da jina shiri kwana2 hakan ya faru ne saboda wasu dalilai amma yanzu zaku rinka ganin shi akai akai kamar yadda muka fara
Ur's princes deejerh💝
[16/01, 18:47] khadija ahmad dija Marubuciya Barauniya ce Frien Din Hassn: ✨✨BA DON SHIBA✨✨
By Princes Deejerh
New Writer
wannan shafin sadaukarwa ne ga ku masoya novel dina ina jin dadin yadda kuke bibiyar novel dina da kuma numa min kaunar da kukeyi,nima ina kaunar ku irin totallay dinnan😍😍
Masu cewa a kara yawan page kuma bana typing kullum kuyi hakuri ayyuka ne suka shamin kai amma insha allah very soon zaku fara jina kullum luv u oll😘
Page 3⃣6⃣ to 4⃣0⃣
Haka washegari ma data tashi abin mamaki baya karewa,,inna asabe da su rabi ne wai ke aikin gida😨karasa wa tayi gurin da suke kafin tace inna kawo wanke wanken in miki,,,da sauri inna asabe tace haba jiddah ai yanzu lokacin hutunki ne ki bari kawai muyi kinji yata ga abincin ki can a dakina ki dauka kije kici