Showing 1 words to 3000 words out of 20453 words

Chapter 1 - MUTUWARE GIDAN GAWA Complete By Mrs Sadauki .txt

10 Jan 2025

3870

[31/10 à 11:05] MRS SADAUKI 💫: *MUTUWARE ...*🧟‍♀️
GIDAN GAWA🧞‍♀️🌬️


Love
and
Horror story


```MRS SADAUKI💫✍🏻```


Dedicted to Ameera Adam




FCWA ☀️


_________________________




Ƙirƙiraren labari ne,ban yi shi don cin mutumci kowa ba.Duk wanda ya zo daidai da rayuwarsa to akasi aka samu.




1




#ƘASAR COTE D'IVOIRE
#Babbar asibitin Abengourou


A tsorace nake ƙara tushe kunnuwana ko zan samu sa'ar toshe ma'adanar sautina da ke zuƙo min wata murya mai cike da tashin hankali.Sai dai yaudarar kaina nake,domin kuwa toshe kunnen da na yi hakan bai canza zane ba .Na kai hannu da niyyar ɗaukar pilow ko shi Allah zai sa na dace,hasken ɗakin ne ya ɗauke ɗif wanda ya yi sanadiyar tsayawar na'urar da ke kore zafi.
Ƙaiƙayi na fara ji yayin da sauro da zafi suka ce salama alaikum,shegiyar muryar nan mai shegen naci sai ƙara ƙaimi take wurin roƙon abin da ban san mi take so ba “ku cece ni ! Ku cece ni don Allah babu kowa ne?”
Na ja tsuki bisanin na lalubo wayata na kunna fitila,duk abokan aikina baccinsu kawai suke a gajiye.Na miƙe tare da nufar ƙofa,na murɗa handle na fito ,ga mamakina ko ina na asibitin akwai hasken wuta sai ɗakinmu da kuma wani ɗakin da ke can gabashi wanda akwai ƴar tazara tsakani.
Haka kawai na ji zuciyata na tunzura ni kan na je na duba tako ɗaya ,biyu,ina daɗa matsawa ina kuma daɗa jin sautin muryar nan mai neman taimako har na isa bakin ƙofar daidai nan hasken ɗakin ya dawo.Na kutsa kai,sai na tarar da nurse biyu da wani Dr a tsaye kan wata matashiyar budurwa ,gefe kuma wata jemamiyar tsohuwa ce zaune ta na kaɗa ƙafa.
Duk kallonsu ya dawo kaina,ni ma su nake kallo ɗin.
“Ayodele mi kike yi a nan? Babu aiki ne ɓangaren ku?” Dr ya tambaye ni,na buɗa baki da niyyar yin magana na tsinkayo wata murya kuma na ce min “Ayodele please ki taimaka min ban mutu ba!”
Inda sautin ya fito na duba,sai yanzu na lura da idon budurwar rufe suke ruf kamar mai yin bacci.Da mamaki nake tambayar kaina ‘dama mai bacci ya na iya yin magana?’
“Ta rasu ne! Ƙoƙarin cire duk abubuwan da ke jikinta ne muke amma sun ƙi fita” Dr ya katse min tunani.
“Amma yanzun nan fa ta min magana akan na taimaketa ba ta mutu ba” na faɗa .
Duk kallon mamaki suka bi ni da shi,hakan yasa na ci gaba da cewa “tun ɗazu fa ita ta hana ni bacci kururuwar ta ce ta tashe ni”
“Ayodeleee?” Dr ya kira ni da wani sauti,bisanin ya tambayi nurse ɗin “ku tun ɗazu da muke nan kun ji kururuwar ne?” duk kai suka girgiza alamun a'a.
Sai ya maido kallonsa gare ni “to kin ji ta yiyu kunnuwanki ne ba su jiye miki daidai ba”
“Mi sunanta?” ita ce tambayar da na yi,“Emeka” ɗaya daga cikin nurse ɗin ta ban amsa.
A hankali na fara taka ƙafata sai dai kafin na isa ga Emekar tsohuwar nan ta taso tare da tsaya wa a gabana “ina za ki je? Mi za ki yi?” ta jero min tambayoyi haɗi da jifata da wani mugun kallo mai ratsa ɓargo da tsoka don sam bai da daɗi.
Dakyar na fizgo numfashi tare da jarumtar kallonta cikin tsakiyar ido ,kawai sai na ga mugun razani a nata idon tare kuma da saurin ja ta bani wuri ba tare da na san dalilin yin haka ba.
Kai ga Emeka na yi tsaye bisanin na kai hannu kan fuskarta na ce “Emeka ?”
“Ayodele ta fa mutu,ya kike yi wa matatta magana kamar zautatta?” Dr ya tari numfashina.Ba tare da na dube shi ba na ce “ba ta mutu ba Dr ! Doguwar suma aka sa ta”
“Wa ya sa ta doguwar suma? Nan fa asibiti ce kuma mun san aikinmu ”
“Dr ita wacce ta saka ta suman ta san kan ta! Ina iyayenta suke?” na tambaya.
“Daga ita sai Kakarta suka zo,kuma ga ta can ta fita” cewar nurse.
Na ɗago kaina sai na ga tuni tsohuwar nan ba ta nan,wato abin da na fahimta ita ce Kakar Emeka.






“Ayodele ki taimaka ki damƙa ni ga iyayena Kakata ba ta sona shi ne take son kashe ni,ta ɓoye ruhina cikin asusun ƙarfe ta lashi takobi ba za ta fiddo shi ba har abada” shiru na yi ina sauraren esprit ɗin Emeka da ke yi min magana ba tare da ni kaina na san shi ne ba.
“Dr yanzu ma ba ga shi ta na yin magana ba?”


“Mtsw! Ayodele fita! Fita na ce !” Dr ya yi min wata muguwar tsawa.
Tako ɗaya na yi na tsaya,cikin fushi ya kuma cewa “kenan ba za ki fita ɗin ba?”
Murya a raunane na ce “ba ka ga ta riƙe min hannu ba ne?”
Duk ido suka waro Dr har da ɗora hannu a kai ya ce “wai Ayodele haukata ni kike son yi? Ku kun ga ta riƙe ta?” ya tambayi nurse suka girgiza kai.


Da mamaki nake kallonsu bisanin na mayar da dubana ga Emeka wacce ta riƙe ni gam ta na girgiza kai idonta na shatatar da hawaye.
“Ke kaɗai ke jin abin da nake cewa da kuma ganin abin da nake don Allah kar ki biye su” cewar Emeka .
Cikin jin haushi Dr ya fizgo hannuna da niyyar fitar da ni da ƙarfin tsiya sai dai sam ya kasa sakamakon ɗayan hannun da ke riƙe da Emeka .
“Dr ni fa na fara jin tsoro! Ina ga fa gaskiya ne! Dubi yadda hannunta ke jone kamar a rinƙe shi ɗin kuma ....kuma gadon kamar ya na motsa wa” nurse ta faɗa.


Dr ya sake min hannu,ya ce “ba zan yi mamaki ba don Abeno cike take da ƴaƴan matsafa da Mayu....” bai rufe bakinsa ba Emeka ta fara shaƙuwa,da sauri duk suka nufeta tare da saita na'urar aiki a kanta.




Ni kuwa ganin numfashinta ya dawo kawai sai na sulale na koma can ɓangaren mu.Kasa bacci na yi sai zaune da na yi na rabka uban tagumi ina tunanin abin da ya faru.Gadon bayana ne ya fara yin ƙaiƙayi,tare kuma da wata irin tsira wa tamkar ana nitsa wasu abubuwa gefe da gefen kafaɗuna.
Dishi-dishi idona ya fara,ban san ya aka yi ba na tsinci kaina a wata duniya wacce na fi kyautata zaton ta mafarki ce.




Wani ƙaton gida mai ɗauke da ɗakuna kashi-kashi,ruhina ya sallama.Babu wanda ya amsa min haka ba wanda ya ɗago ya dube ni sai tsohuwa wacce tun farkon shigowata na ji yaran gidan na ambaton sunanta da “Yaba”


Mugun kallon nan mai cike da hassada,ƙyashi haɗi da baƙin ciki ta jefo min bisanin ta miƙe tsaye ta zo gare ni.“Mi kike so kuma yanzu?”
“Abin da kika ɓoye!” na bata amsa.
“Maganar ahali ce wannan bai shafe ki ba,kin dai yi naki ikon don haka ki....” ban bari ta dire ba na tari numfashinta da “ki bani cikin lumana ko kuma na ƙwata ta ƙarfin tsiya! Yin haka kuma babba asara ce gare ki domin duk abin da kika ɓoye zan fito da su ne”
Tsoro ne na gani shimfiɗe ƙarara a fuskar Yaba,bisanin ta yi gaba ni kuma na take mata baya har cikin ɗakinta na laka wanda aka yi ma rufin kara.
Ƙarƙashin gado ta duƙa ta fito da wani asusun ƙarfe tare da miƙo min shi,ban ɗauki lokaci ba wurin buɗe shi.Baƙin hayaƙi ya fito kamar fitar iska ya tashi sama,guntun ƙyallen atamfa na gani sai na ɗauke shi bisanin na aje asusun na fito.




Daidai nan kuma na farka daga baccina,na dafe gefen goshina da yake sara min bisanin na buɗe idona taram .Da sauri na tashi ganin Emeka a tsaye ta na min murmushi.
“Na gode sosai Ayodele,kin ceci rayuwata!” ta faɗa tare da ƙoƙarin karɓa wani abu daga hannuna da nake jin na jimƙe ba tare da na san mine ne ba sai da na kai dubana sai na ga ƙiren atamfar da na yi mafarki ne.
Emeka ta ci gaba da cewa “wannan zanen ankon bikina ce,Inna Yaba ta yi amfani da shi don kashe ni saboda kawai zan auri bare wanda ba cikin danginmu ba.Na gode!” ta na gama faɗar haka ta fice ta bar ni sake da baki ina tunanin kar dai ace mafarkin da na yi gaskiya ne? ??????












MRS SADAUKI ce🌬️
[31/10 à 11:05] MRS SADAUKI 💫: *MUTUWARE ...*🧟‍♀️
GIDAN GAWA🧞‍♀️🌬️


Love
and
Horror story


```MRS SADAUKI💫✍🏻```


Dedicted to Ameera Adam




FCWA ☀️


_________________________






3




Cike da tashin hankali na fara jijiga Momah haɗi da kiran sunanta sai dai ko motsi ba ta yi ba.Idona tuni sun fara zubar da hawaye,na ruga a guje na nufi hanyar fita sai mu ka yi kiciɓis ni da A'ishah.Ita ta fara yin magana ta na cewa “Ayodele yarinyar nan fa an wuce da ita asibiti sai wani shure-shure take ta na kiran sunan ki”
“Momah na ciki ta kasa tashi mu je ki taimaka min” na faɗa ina goge fuska da bayan hannu.Ciki mu ka koma , A'ishah ce ta yi azancin zuba wa Momah ruwan tulu masu masifar sanyi.Momoh ta ja ajiyar zuciya,idonta a rufe take yin wani Yare wanda ba Hausa ba haka ba French ba ne.
Mu ka kalli juna ni da A'ishah,ban sani ba ko ita ma tunaninmu ya zo ɗaya wato Momah ko aljanu gare ta? Ciwon kai mai tsanani da ya fara farmakata ya addabe ni a lokaci guda na nemi wurin da zan kwanta don idona tuni sun fara lumshewa.
A'isha ta riƙe ni ta na cewa “ina kuma za ki je alhalin mahaifiyar ki na cikin wannan hali?” ban bata amsa ba kawai da na janye hannuna tare da samun wuri na kwanta kan tabarma.




Momah ta dawo daidai, A'ishah ta ce “ya jikin?”
“Alhamdullah! Kin ga abin da ƙawar ki ta jindilo mini ko? Wancan baccin da take Allah kawai yasa masifar da zai haifar ” ba tare da A'isha ta san taƙamaimai abin da Momah ke nufi ba ta kalli inda Ayodele ke kwance har wani girgiza take ta na motsa baki kamar mai yin magana.Ba don ta so ba haka ta yi wa Momah sallama ta yi tafiyarta.




Kwanta wa ta ke da wuya,wani hazo ya rufen ido.Tsofi huɗu na yi tozali da su ,dukkansu na san su zan iya shaida su duk da ban san gidajensu ba amma ina ganinsu a unguwa.


“Mu za ki tona wa asiri? ”
“Mine ne ruwan ki da mu?”
“Ita Zeinab ɗin ƙanwar uwar ki ce?”
“Ya kuke ɓata lokaci wurin tambayarta? Kawai mu shaƙe shegiya mu kashe ta”


Kowacce daga cikin ta faɗa,ta ƙarshen abin da na lura ta na da zafi kuma tsafin maitarta ya fi na kowa ƙarfi shi yasa har take tunanin za ta iya ja da ni.
“Ban zo nan don na haɗu da ku ba ku dinga kawo min shirme,ruhin Zeinab nake so ku saki cikin salama kafin na ƙwata ta ƙarfi.Dukkanin ku babu wacce ban san sirrin maitar ta ba,in kuka cika ni zan rusar daular ku” na faɗa cikin kakkausar murya,duk sai suka sheƙe da dariya.
“Ke kuwa baiwar Allah miye na gudun ƴan uwanki Mayu?”
“Hhhh! To wai mine yasa kika karɓi maita in kin san ba mugunta ne burin ki ba?”
“Sannu mai son taimako al'umma,mu je mu yi farauta ke kuma ki zo ki karɓe.Kin san tun yaushe muke son naman Zeinab ? Tun ta na cikin tsumman goyo muke haƙonta sai yanzu da za mu sha romo za ki hana?”






Idona ne suka fara yin zafi,a take na ji wani abu na cika su.Na zube su kan tsofin Mayun nan,duk sai na ga sun razana a take su ma suka faɗi wani ɗalasiman tsafi nan take suka rikiɗa suka zama macizai.
Ko kaɗan ban son kashe rai,sai dai ɗaya daga cikinsu ta ja masu mutuwar kasko sakamakon shammata ta da ta yi ta cije ni a hannu.Bakina na buɗe na saki ihun azaba yayin da kuma idona ya fitar da wani tartatsin wuta duk sukama wuta su na ihu.




Na ja wani dogon numfashi ina mai buɗe idona taram kan Momah wacce ke ta ƙoƙarin ɗaure min hannu da ƙyalle jini sai zuba yake.
Mafarkin da na yi ne a yanzu ya dawo min tarau a kwanya,abin da na fahimta kawai ba irin sauran mafarkai ba ne da duk ƴan Adam ke yi nawa ya sha banban.
“Tashi mu je na kai ki asibiti,jinin nan ba zai tsaya ba” cewar Momah ,ban tambaye ta komai ba na tashi.Takalmi kawai na saka a ƙafata muka fito waje,unguwar cike take da jama'a kowa mamaki shimfiɗe kan fuskarsa yayin da yake kallon makiran tsofin nan huɗu su na birgima a ƙasa tare da tona ma kansu asiri.Duk wanda suka taɓa kamawa sai da suka faɗa hatta Zeinab.






Da sauri Momah ta ja hannuna muka bar wurin,taxi muka tara sai asibiti.“Mine ne ya same ta ?” cewar likita ,da mamaki na dubi Momah jin ta ce “sarar maciji ne”
‘To ta ya aka yi ta sani?’ na tambayi kaina a zuci.
Allura yayi min tare da bani wasu magunguna , Momah ta biyasa bisanin mu fito.


Tafiyar ƙasa kawai muke ta yi,sam ban ga alamun Momah na da niyyar tarar mana da abun hawa ba ga shi kuma na gaji.
“Hum!” ta yi tare da dubana,na dube ta kawai.Sai kuma ta ja ta tsaya,bisanin ta ja ni zuwa gefe “zauna” ta faɗa tare da nuna min dakali.Na bi umarninta,wata tambaya ta jefo min da ban fahimce ta ba “mine ne haɗin ki da tsofin unguwa uhum? Duk yadda nake son liƙe ƙofofin nan sai da kika bi duk kika buɗe su ko? Ayodele rayuwar da kike so mu yi kenan kullum cikin sauya unguwa da ƙasashe?”


“Momah ban fahimce ki ba...” ko rufe bakina ban yi ba ta zuba min yatsunta biyar bisanin ta yi zaman ƴan bori a ƙasa ta fashe da kuka.Na rumtse ido don sam ban son ganin zubar hawayenta ko ba komai ita ce gatana,ban san kowa ba daga ahalina sai ita kaɗai.
Furucinta ya saka na ware idona kanta,“Ayodele ina roƙon ki daga yau kar ki sake shiga sabgar wani maye ko mayya,babu ruwan ki da su.Ki barsu su yi rayuwarsu,abu ɗaya na sani har abada babu wani daga cikinsu da zai samu zarrar kashe ki wannan ma da aka yi cikin rashin sanin ke wace ce suka yi miki illa”


Bakina na samu da tambayarta “Momah wace ce ni ?”
Ta min wani kallo bisanin ta miƙe ta kakaɓe jikinta,“tashi mu tafi ” ta umarce ni a doli na tashi ɗin.Sai a lokacin ta nema mana abun hawa muka isa gida,da labarin mutuwar tsofin nan huɗu muka ci karo yayin da Zeinab kuwa tuni ta samu lafiya ta dawo ras.




A ranar nan ko abincin dare kasa ci na yi,magani kawai na kora da farau-farau sannan na kwanta bacci.Nan na yi mafarkin wani farin tsoho jawur da shi ya bayyana gare ni,bandejin da aka laulaya min a hannu ya warware bisanin ya saka min wasu ruwa masu masifar sanyi sai kuma yayi tafiyarsa.


Washegari ko da na tashi hannuna ya warke kamar ma ban taɓa jin ciwo ba,cike da mamaki na fara ƙwala kiran sunan Momah ina mai fitowa waje “Momah dubi hannuna ya warke ” maimakon ta yi murna akasin haka na gani.Cikin tashin hankali take cewa “shikenan ashe su na biye da mu”
“Su wa?” na jefo mata tambaya,“je ki yi wanka lokacin zuwa aiki ya kusa”
Na turo baki cike da jin haushi,na cika bokiti na je na yi wanka.Bayan na shirya ne na lumshe idona,na fara yi wa abun bauta godiya kan lafiyar da ya bani bisanin na fito hannuna ɗauke da jaka.
“Momah na tafi sai na dawo”
“A dawo lafiya” shi ne abin da ta ce min.
Sai da ina cikin taxi ne na fara duba wayata ,nan na ci karo da miss call ɗin A'isha da Fatima .Na saki murmushi,har cikin zuciyata nake son ƙawayena.




A bakin asibiti na ci karo da su kamar kullum,Fatima na da babur ita ke ɗauko A'ishah tun da kusan unguwarsu ɗaya.
Gaisa wa muka yi, A'ishah ta so yi min zancen abin da ya faru jiya sai dai ban bata fuska ba.
Ta sauka daga mashin muka ƙarasa ciki,uwanda suka kwana nan suka sauka mu kuma mu ka hau aiki bayan mun ci abinci.


Lokacin hutu mu na zaune ana hira A'ishah ta ce “Mansur ya matsa akan lalle aurenmu nan da 2weeks yake son shi,da Mama ta so masa bayanin kan lokacin ba ta gama haɗa min kayan ɗaki ba ya ce babu damuwa duk shi zai yi burinsa kawai a aura masa ni ”
“Wayyo! Kin ji daɗin ki wallahi ina ma ace ni ce .Ya kamata mu je mu fitar da anko gobe in mun sauka daga aiki” cewar Fatimah.
“Eh dama hakan na raina” hira sosai suke su biyu kamar sun manta da ni,don ko kaɗan ni ban da bakina ba saboda haka kawai na ji na tsani lamarin auren nan da ace ina da iko da babu shakka na hana shi.


“Kin yi shiru tun ɗazu halan masoyin ɓoye ake tunani?” A'ishah ta tambaye ni cikin zolaya,na ɗan taɓe baki bisanin na miƙe na ce “ku dai tashi mu koma saura minti biyar” duk suka miƙe,nan mu ka ƙara hawa aiki sai lokacin sallah kawai suke tsayawa su yi ni kuwa da ban san taƙamaimai Addinina ba sai dai na zauna.




Zuwa ƙarfe takwas na dare duk mun gaji saboda aikin likitanci sai jajirtace.Ɗakin baccinmu duk muka nufa,mu ka bar stagiaire irin sabbin likitocin da ake kawo wa asibitoci don koyon aiki sai in matsala ta yi tsanani ne sosai suke tayar da mu.


A gajiya duk muka ɓingire bacci,babu ma kamar ni da nake jin kamar an min shegen duka.
Ƙyalƙyal! Haka nake jin sautin dariya na ƙara yawaita,y wasu muryoyi ke tashi sama yayin da kuma shashekar kuka ke ƙara ƙaimi.
Ba tare da na buɗe idona ba na tashi zaune,bisanin kuma na sauko daga bed.Ban buɗe ƙofa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login