Showing 3001 words to 6000 words out of 20453 words
Chapter 2 - MUTUWARE GIDAN GAWA Complete By Mrs Sadauki .txt
ba ita ta buɗe da kanta,wani haske ke yi min jagora ni kuma ina biye da shi kamar raƙumi da akala har na isa wani ɗaki.
Tsit suka yi,sai wata murya da ke tambayar “wane ne? Ba za ka yi magana ba? Ka bar haske mu ” daidai nan hasken da ke min jagora ya ɓace hakan ya basu damar ganina mu ka yi gaba da gaba.
“Kayiii! Mace a wannan lokacin? ” tako ɗaya na ƙara duk suka ja baya tare da ɓoye wa ƙarƙashin gadajen maras lafiya aka bar mai yi min magana.
Abu guda na yi nasarar gane wa,shi a siffar mutum yake yayin da sauran kuma innuwarsu kawai ake gani.
“Su wane ne ka gayyato mana a nan ana zaman lafiya?” na jefo masa tambayar .
Muryarsa na ɗan rawa ya ce “abokaina ne! Umm.Sun zo ganina ne”
Sai a yanzu na ƙare masa kallo,hannunsa na ɗauke da tiyon da ake yi wa mutum ƙarin ruwa.
“Don sun zo ganin ka shi ne za su hana mutane bacci? Ce maku aka yi nan gidan caca ne? ” na sake faɗa cikin tsawa.
Shiru ya ɗan yi bisanin ya ce “madam ke ɗaya ce kawai kika ji mu,amma normal mutum basa ji ”
“Ka sallame su maza kar na sake ganinsu a nan har lokacin da za ka bar asibitin nan in kuma ba haka ba zan yi mugun saɓa maku” ko gama rufe baki ban yi ba ya ce “an gama ranki ya daɗe!”
Har na juya zan koma sai kuma na tsaya tare da jefo masa tambaya “shashekar kukan wa nake ji a ɗazu?”
Kame-kame ya fara,can cikin ikon Allah idona ya sauka kan wani ɗan yaro da ke kwance kan gado.Esprit ɗinsa na gani a ɗaure ana tsoratar da shi haka kawai,“wane ne yayi masa haka?” na yi tambayar tare da shaƙe mutumen wanda aƙalla zai kai shekar sittin .
Cikin magagin wahala ya ce “abokina ne! Wallahi sai da na hana shi amma ya ƙiya”
Yadda yake magana zan iya hangen wani koren abu daga cikin bakinsa,ban san da me na yi amfani ba na ciro shi daga bakinsa bisanin na je na saki yaron nan da suke cutar wa sai kuma na koma ɗaki.
Ina kwanciya kan bed sai na ji nutsuwata ta dawo daidai saɓanin a ɗazu da nake jin kamar mu biyu ne a cikin gangar jikina.
Washegari
Da na tashi na yi zaton mafarki ne na yi wannan yasa ban bai wa abun muhimmanci ba.Ɗakunan maras lafiya mu ka fara shiga mu na duba su,na zo daidai gadon wannan mutumen na jiya da dare na ji muryarsa ya na cewa “madam don Allah ki taimaka ki bani kambuna”
Da mugun mamaki na dube shi na ce “mi kake magana a kai? Ko wani abu yake ma ciwo ne?”
Ya waro ido ya ce “kambun maitata da kika karɓe a daren jiya ”
Ras gabana ya faɗi,a fili na furta “kenan ba mafarki ne na yi ba?”
“Ki ban abina don Allah na yi miki alƙawari har na fita daga nan ba zan ƙara cutar da kowa ba” ya sake faɗa a karo na biyu,wani baƙin ciki ne ya turnuƙe ni nan take.“Wato ka ma taɓa cutar da wasu kenan?”
Muryarsa na ɗan rawa ya ce “wallahi yara biyu ne kawai na shanye ma jini bayan su babu wanda na cutar”
Na lumshe ido,nan take abun da yake kira da kambun maita ya bayyana gare ni daga nan inda nake zan iya hango shi cikin jakata wacce ke can ɗakin baccinmu.
‘Duk wanda ya kashe shi ma a kashe shi,don haka kai ma dole ka bi su’ na faɗa a zuci ina mai juya wa zan fita hargaginsa ya tsayar da ni na juyo.
Duk hankalin kowa ya koma kansa,nishi kawai yake ya na zarar ido.
A'isha ta nufe shi ta fara dubasa,kafin wani lokaci ya ce ga garinku nan ya mutu.
Wani kallo na ga ta na jifata da shi na tuhuma,sai kuma ta fita babu jima wa suka shigo ita da Dr . Rubuce-rubuce aka yi bisanin a sanar da ƴan uwansa suka fita da shi.
Har muka sauka daga aiki A'ishah ba ta bar min kallon nan ba,tuni na tsargu.Ko da na je gida hankalina kasa kwanciya yayi,haka na wuni sukuku Momah ta yi tambayar duniya amma na ce da ita babu komai.
Da dare bayan duniya ta yi tsit na buɗe jakata na ciro kambun maitar nan,wata ƴar ƙaramar halitta ce mai rai sai motsi take.Sai da na ƙura idona da kyau sannan na fahimci Kunkuru ne,hannuna na rawa na ɗauko shi nan take ya ɗauki wani irin haske kamar an kunna ƙwan lantarki.
Muryar Momah na ji daga sama ta na mai cewa “kambun wane ne?” na juyo a razane ina kallon ta,sai dai abin da ya fi ɗaga min hankali shi ne iya muryar ce kawai ke ta Momah amma fuskarta ta canza .....
[31/10 à 11:05] MRS SADAUKI 💫: *MUTUWARE ...*🧟♀️
GIDAN GAWA🧞♀️🌬️
Love
and
Horror story
```MRS SADAUKI💫✍🏻```
Dedicted to Ameera Adam
FCWA ☀️
_________________________
2
Har aka fara kiran asallatu ban rumtsa ba,ina ta saƙa da warwara don gano ainahin abin da ke faruwa da ni sai dai ga banza wai an tsikari kakkausa.
Ƙarfe biyar na asubahi abokan aikina suka tashi don gabatar da sallah.Har suka ida ina nan zaune ina reto da ƙafafuna, A'ishah ta dube ni cike da kulawa ta ce “Ayodele lafiyar ki kuwa?”
“Ƙalau nake!” na bata amsa.
“Mi ya samu fuskar ki duk ta yi ja?” ta sake tambayata,ban bata amsa ba sai wata nauyayyar ajiyar zuciya da na sauke.
Fatima da ke jan casbi kusa da ita ta ce “ƙila mafarkin da ta saba yi ne yau ma ya sake zuwar mata”
Na ɗan harareta na ce “don ban da aikin yi sai mafarkin ɓoyayyen masoyi ko?” duk suka yi dariya bisanin A'ishah ta ce “Ya kamata dai ki tashi ki wanke fuskar ki tun da ba sallah za ki yi ba”
Na dube ta na ce “lokacin da nake tawa ibadar ki na ina ne?”
Ta taɓe baki ta ce “ibadar da kike yi marar alƙibila? Ke fa kan ki ba ki san wane ne kike bauta ma ba”
“Ubangiji nake bauta! Kuma na yi imani da shi,kamar yadda kuke bautar naku da ba ku taɓa gani ba” na bata amsa.
Fatima ta ce “don Allah ku bar zancen Addini! Mu je mu ida aikinmu mu kama gabanmu”
Hakan kuwa aka yi,bayan na wanke fuskata mu ka shiga fara duba maras lafiya ƙarfe tara na buga wa duk mu ka sauka daga aiki.
Kasancewar banda abun hawa yasa na zo bakin titi,dakyar na samu taxi ita ma wata tsohuwa ce.Gidan baya na zauna,mutum uku na taras a ciki hakan yasa duk mu ka matse.
“Mtsw ! ” ta kusa da ni ta ja tsaki a karo na uku,na kasa haƙuri na ce “ya dai?”
Kamar jira take in tanka ta ce “ah toh! Gari yanzu ya lalace ko ina ka je sai ka ji ana zancen Mayu ! Abun baƙin ciki har da yara ƙanana suke kama wa”
Ni kuwa na ce “kuma wallahi in kika bincika kaso casa'in na Mayun garin nan tsofi ne....” ban rufe baki ba motar ta yi wani ƙuuu! Ta tsaya.
“To shikenan kun yi sara da mutum sama sai ku fito!” shi ne abin da mai taxi ɗin ya faɗa ya na mai jan tsuki,sai kuma ya fita.
Ƴan dube-dube ya yi bisanin ya umarci kowa ya fito,duk mu ka sauka sai wani tsoho da ke gaba mai cin goro bakinsa duk yayi ja.
“Ka yi haƙuri ba su san da kai ciki ba ne shi yasa har suka tsokane ka” mai taxi ya faɗa cikin wata irin murya mai rauni.
Kamar wani sarki tsohon nan ya fito tare da tsirtar da yawu abun mamaki sai suka zuba ga jikina da kuma na matar da muke hirar.
Dariyar shaƙiyanci ya fara bisanin ya ce “halan ku baƙi ne a Abengourou? Na ce ku baƙi ne?” kamar wasu ƴaƴansa haka yake mana ihu,tuni wannan matar ta zube ƙasa ta na basa haƙuri.
Raina ne na ji ya ƙara ɓaci,zuciyata ta kawo min wuya.Ban san mi ya shiga kaina ba kawai dai na samu bakina da furta “dara ta ci gida !” sai tsohon ya ɗago da ƙarfi ya na kallona,jikinsa har rawa yake wurin ƙetara wa bakin kwalta ya karɓo ruwan leda ya zo ya fara wanke daidai inda ya tsirta min yawunsa masu ɗauke da jan goro.
Na lumshe ido ina jin zuciyata na ɗan doka wa tare da ƙoƙarin yaƙarta akan tafarfasa da take.
Cikin taxi mu ka koma don kuwa ta tashi,fafur tsohon nan ya ƙi shiga direba sai magiya yake.
Har za mu tafi na ce “ita kuma wannan da ka riƙe?”
Jikinsa na rawa ya ɓallo goro ya bata,na dubeta na yi mata alama da ta karɓa hannunta na rawa ta amsa tare da kai goron baki,mai taxi yayi mata key.
Mun ɗan tafi kaɗan matar ta fara aman baƙin wani abu kamar ranta zai fita,a dole duk mu ka sauka daga taxi ɗin na tari wata sai gida.
“Washhh! Na gaji” shi ne abin da na furta ina mai zube wa kan tabarmar kaba wacce Momah ke zaune ta na gyaran wake.
Wani kallo take bi na da shi wanda yasa na tsargu na ce “Momah ya dai ?”
Sai ta ja wata doguwar ajiyar zuciya ta ce “wa kika tsokana a saman hanya?”
“Da aka yi mi fa?” na tambayeta.
“Idon ki na ga sun canza launi” ta ban amsa.
Na yi ƴar dariya tare da canza zancen “babu ruwan ƙanƙara masu sanyi?”
“Babu sai dai ki sha na tulu,ɗiyar Asabe ta rasu duk can aka saye ƙanƙarar ”
“Wace daga ciki?”
“Zeinab mana! Ai kin san dama ta jima babu lafiya”
Na dafe ƙirji na ce “tun yaushe a ba ta da lafiya? Ban sani ba”
“Eh to ba a fi sati ba! Don a gida aka yi jinyar ta ba kowa ya san da rashin lafiyar ba”
Jiki babu ƙwari na miƙe don sosai mutuwar ta dake ni a kaf faɗin unguwarmu gidansu kawai nake shiga.Ina tafiya sai na ji kamar ana take min baya na waigo sai dai ban ga kowa ba.Ɗaki na shiga na cire kaya,ɗaurin ƙirji na yi na fito na yi wanka.
Bayan na gama na zuba kunu a roba na fara sha kenan wayata ta ɗau ringing,na ɗauka ban kai ga magana ba na ji muryar A'ishah na ce min “Albishirin ki?An kawo kuɗin aurena yanzu haka har an tsayar da ranar buki?” cike da murna na shiga tambayarta “da gaske? A'isha kar fa a ce ƙarya kike min”
“Allah gaske ne! Ki zo Please ”
Na ja dogon numfashi na ce “sai dai zuwa gobe tun da yau akwai inda zan je”
“Ke dalla wacce magana kuma kike? Ko ma ina za ki je ki jingine tafiyar kawai ki zo nan kin ga fa Fatimah nan”
Jin haka yasa na ce “ok gani nan zuwa!” sai ta kashe ,ni kuma na miƙe na je na saka kaya ko mai ban shafa ba na fito na sanar da Momah.
“Masha Allah! Ki dai dawo da wuri kin ga zan shiga gidan mutuwa zuwa biyar na marice”
“To Momah!” na amsa tare da fitowa waje.Cak na tsaya ina kallon yadda unguwar ta ɗauki wani duhu har wani hayaƙi ke tashi.Cike da mamaki sai na ga na ƙofar gidansu Zeinab ya fi yawa,a fili na furta “to! Mi kuma ke faruwa?” kiran A'ishah da ya shigo shi yasa na watsar na nufi bakin titi na samu abun hawa sai gidansu.
Ai kuwa gaskiya ne an kawo lefen ,ina shiga na ta gani mutane masu zuwa yin barka.Bayan na gaishe da Mamarta na wuce ɗakinta,nan mu ka ta yin ihun murna tare da tsara yadda bikin zai kasance.Bayan mun ci abinci ne na yi tambaya “ A'isha wai wane ne za ki aura?”
“Cousin ɗina ne! Dama kin san tun farko ya nuna ya na sona sai kuma abun ya watse tun da ya tafi Lagos to ya dawo shi ne fa aka kawo lefe” ta ban amsa cike da murna.
“Aikin mi yake na ga lefen Masha Allah kamar matar gwamna” cewar Fatimah,na karɓe zancen da “ai kuwa dai! Ko bra da pant kawai abun kallo ne uwa uba sarƙoƙin da na gani har da na zinare”
“Na faɗa maku Lagos ya je wurin diga ya samo kuɗi sosai yanzu haka ya fara kasuwanci!” A'ishah ta faɗa .
“Fatimah saura ke! Ki cewa Nasir ya fito kawai mu sha biki!” na faɗa cikin zolaya,ta kai min dundu a baya ta ce “ Allah kiyaye min ni Dr nake so”
Duk muka fiddo ido waje , A'ishah ta ce “wannan masifaffen? Tabbb! Ayodele kin san kuwa ɗazu da na wuce ta gaban su na ji ya na bai wa Dr Jameela labarin ki wai kin ceci wata su sun yi zaton ta mutu”
Wani irin ras na ji,yayin da kaina ya sara kamar zai tsage.Ba don ace na yi ƙarya ba da zan iya cewa har mahudanar jinina ta sauya tsarin gudu.
Dakyar na iya cewa “bacci ma nake ji bari na kwanta kafin a jima na tafi gida”
“Munafuka yanzu da kika ga lokacin sallah yayi ko?”
Na dubi Fatimah da idona da nake jin tamkar ana yi min masanye bisanin na lumshe su ba tare da na bata amsa ba.Ina jin lokacin da ta ci gaba da cewa “ A'isha ni kuwa lamarin Ayodele na ban tsoro idonta wani sa'in sai su koma kamar na damusa ”
Duniyar da na lula wacce take kusan zahiri ba mafarki ba yasa ban sake jin hirarsu ba.
Ranar da Momah ta zo min da zancen za mu tashi daga unguwar da muke zuwa wannan da muke ciki,ba zan manta a ranar da mu ka dira sai da na kwana da ciwo ƙafa mai tsanani.Maƙociyarmu Asabe ce take shaida mana unguwar Mayu sun yawaita duk da har yanzu ba a san su wane ne ba amma mu tashi tsaye wurin addu'o'i.Na sha daga bisanin na warke,abu guda da kuma ba zan manta ba kusan tsofin unguwarmu ba na shiri da su.
A cikin baccin nan na ja wata ajiyar zuciya ganin Zeinab ta nufo ni idonta shaɓe-shaɓe da hawaye,bayanta kuma tsofin unguwarmu ne ke biye da ita ko wacce daga cikinsu da wuƙa a hannunta.
“Ayodele? Ayodele? Lafiyar ki?” na ji muryar A'ishah wacce ta tashe ni daga bacci,na buɗe ido dakyar bisanin na lumshe su Zeinab ta sake bayyana gare ni sai dai nacin A'ishah ya saka na tashi daga baccin ba don na so ba.
“Haba sai ki tsora mutum! Haka kike bacci dama? Ninshari ne wannan kamar kururuwar damusa a cikin daji” ta faɗi haka ta na mai kallona.
“Ina Fatimah ?” shi ne abin da na tambaye ta.
“Ta tafi gida mana,tashi mu je don Allah ki yi min rakiya daga can sai mu wuce gidan ku” .
Toilet na shiga na wanke fuskata sannan muka wuce gun tela,bayan sun gama tattauna komai muka samu taxi zuwa gidanmu.
Rana tsaka ne wantsar,duk an yi gudu ba za a wuce ƙarfe uku ba.
“Ayodele sallar gawa ce ake yi wai ” cewar A'isha don ta riga ni fita daga taxi,na ziro ƙafata kenan idona yayi tozali da gawar Zeinab wacce maza suka sa a gaba su na sallata.
Gadan-gadan na nufe wurin, A'ishah ta riƙe hannuna daga baya ta na cewa “ina za ki kuma?” na fizge hannuna na je na yi tsaye kusa da makara ina mai ɗaga hannu na ce “ku dakata! Ba ta mutu ba ga ta a zaune ta na faman kuka”
Farin likafanin da aka rufeta na yaye daidai fuskarta,ni kaina ban san mine ne na faɗa ba ko kuma na yi sai Zeinab ta tashi zaune daram da ƙugunta “Allahu Akbar! Allahu Akbar! Allahu Akbar!” maza suka fara yin kabbara kafin wani lokaci har labari ya kai cikin gida.
Sam ban ga tawowar Momah ba sai ganinta na yi a gabana cikin ɓacin rai ta fizgo ni mu ka fito dandazon jama'a,ƙiiii take ja na zuwa gidanmu har mu ka shiga.
Daidai tsakiyar gida ta wani tura ni na faɗi ƙasa,cikin ɓacin rai take cewa “wannan wace irin masifa ce? Gadon tsiya,gadon jaraba! Ayodeleeee!” sai kuma ta yi shiru ta na mai dafe saitin zuciyarta,da azama na miƙe ina mai tare ta don kar ta faɗi sai inaaaa tuni Momah ta rinjaye ni ta faɗi ƙasa warwas....
[31/10 à 11:05] MRS SADAUKI 💫: *MUTUWARE ...*🧟♀️
GIDAN GAWA🧞♀️🌬️
Love
and
Horror story
```MRS SADAUKI💫✍🏻```
Dedicted to Ameera Adam
FCWA ☀️
_________________________
*Na ji wasu na ta tambaya wai free book ne? To paid ne! Sannan wannan ba gajeren labari ba ne irin su BOKANYA,MACIJIN CIKI da sauransu da nake yi iya page 20 .Duk wacce ke ra'ayin book ɗin MUTUWARE za ta iya yi min magana kai tsaye ta WhatsApp domin biyan kuɗin karatunta* +22795045822
Page 4
Fuskar Momah sak ta tsohuwa irin uwanda sun ga jiya da yau.Tuni tsoro yayi min dabaibayi ya ɗaure min zuciya,cikin wata irin murya wacce ba tata ba take shaida min “wannan halittar da ke hannunki ta na da matuƙar haɗari ki yi gaggawa mayar masu ita kayar su.Kin san kuwa mi ake kira da Kambun Kunkuru? Maita ce mai shegen naci masu ita za ki ga ko mutuwa suka yi sun dinga yin fatalwa kenan domin son duniya ba zai taɓa gushe wa ba daga zuciyarsa” Momah na gama faɗar haka kamar ƙyaftawar ido ainahin fuskarta ta dawo normal.
Wani numfashi na ga ta ja ta na mai kafe ni da ido,da sauri na mayar da Kunkurun cikin jaka ina mai cewa “Momah ke ce?”
Maimakon ta ban amsa sai kawai ta fashe da kuka,hankalina ya ƙara tashi na shiga tambayarta can ta tsagaita da kukan tare da yi min umarni na je na kwanta.
Ban musa ba na kwanta sai dai fa ko kaɗan babu ɗigon bacci a idona.Tunani kawai nake,zuwa yanzu na fahimci akwai wani ƁOYAYYEN SIRRI(MRS SADAUKI)