Showing 18001 words to 20453 words out of 20453 words

Chapter 7 - MUTUWARE GIDAN GAWA Complete By Mrs Sadauki .txt

10 Jan 2025

6249

buɗe idonsa ya zuba mata su ,iya kallon da watsa mata kaɗai sai da gabanta ya faɗi.
“Mine ne?”
“Wanka za min ”
“Can a gidanku wa ke yi miki?”
Ras gaban A'isha ya faɗi jin furucinsa sun yi hannun riga da wanda ya sha faɗa mata satin aurensu.
Dakyar ta ƙoƙarta ta je ta yi wanka ta zo ta gabatar da sallah.Ta na nan zauna har Mansur ya tashi daga bacci,direct wurin drower ya wuce ya fitar da kaya masu kyau ya saka.
“Ka manta ba ka yi wanka ba fa ” ta faɗa ganin bilhaƙi yake shirin,“uban waye ya faɗa miki manta wa na yi?” Mansur ya faɗa a zafafe ya na kallonta.
“Ka yi haƙuri ”shi ne kawai abin da ta iya furta wa.
“Ki tashi ki ɗora min breakfast!” ya faɗa ya na mai fesa turare.
“To” ta amsa tare da tashi.Tsabar takaici sai da ta zubar da hawaye ,amma a haka ta haɗa masa frite da gasashen kifi don ta ga kusan akwai komai.


Kan table ɗin cin abinci ta ajiye bisanin ta wuce bedroom,waya ta tarar da shi ya na yi sai magana yake cikin ladabi.Da ace mahaifinsa na da rai da to babu shakka za ta ce da shi ne yake waya.
Bayan ya gama ne ya zo ya rungume ta tare da cewa “har kin gama?” kai ta jinjina masa,“ok mu je”
Falo suka koma a tare suka ci abincin, Mansur na yi mata hirar soyayya hakan ya kuma ƙulle mata kai.




“Zan tafi wurin aiki,tun ɗazu shugaba ke jirana” ya faɗa tare da miƙe wa tsaye.
“Aiki kuma? A cikin satin aurenmu?”
“To sai aka yi mi? Kin ga ban so sakarci sai na dawo” ya na gama faɗa ya fice. A'isha ta zube kan salon ta na jin wata irin damuwa na dabaibaye ta,tun kafin aje ko ina auren Mansur ya fice mata a rai.“Babu wankan janaba ballantana a yi maganar sallah anya kuwa na auru? Mine ne ma ya hana shi ko fuska da baki ya wanke?” ta furta hawayen takaici na zubo mata bisanin ta ɓingire bacci.




Hayaniyar ƙawayenta ce ta tashe ta,sosai ta yi murnar zuwan su.Sauran kazar jiya ta ɗauko masu kafin a hau hira da girke-girke cike da nishaɗin ƙawarsu ta auri mai kuɗi kowacce ta sasaɓe zane ta ci abubuwa na kayan daɗi ta ƙoshi da za a tafi gida kuwa har da yin tsaraba.








AYODELE




Tun da muka dawo sabon gida Momah ke fushi da ni mai tsanani ,duk uban haƙuri da magiyar da na ta yi mata kanzil ba ta ce min ba.Hakan ya jefa raunatacen ruhina a cakwakiyar matsala,na bar cin abinci kan ƙa'ida,na kashe wayata aiki ma sam na bar zuwa.Amma hakan bai sa Momah ta tausaya min ba.
Kamar kullum wuraren ƙarfe takwas na dare na fito ƙofar gida na yi zaune,unguwar tsit take ko tsuntsu babu.
Wani mutum na ga ya bi ya wuce ta gaban ya nufi wani ɗan gangare,na bi bayansa da kallo kawai ina mamakinsa don yau kusan sau uku kenan da ina ganinsa.
Zuciyata ce ta raya min na bi bayansa,kamar aikaka haka na miƙe har da haɗa wa da gudu na take masa baya.Mun yi tafiya mai ƴar nisa bisanin na tsaya,domin ya kai wurin da ke da tsananin duhu ba zan iya shiga ba.
Idona ne ya sauka ga allon sanarwa mai ɗauke da sunan MAƘABARTA,gabana ya bada ras! ‘Ko shakka babu irin mutanen nan ne masu haƙo kabari don yi aikin asiri ko tsafi’ na faɗa a zuci ina mai ƙara ɗan yin gaba ina ɗigirgire ko Allah ya sa na hango wani abu.Daga bayana na ji an dafa kafaɗa,da mugun sauri na juyo muka haɗa ido a take hanjin cikina suka hautsana......










Ban jin daɗin jikina ina barar addu'ar ku🙏🏻
[31/10 à 11:05] MRS SADAUKI 💫: *MUTUWARE ...*🧟‍♀️
GIDAN GAWA🧞‍♀️🌬️


Love
and
Horror story


```MRS SADAUKI💫✍🏻```


Dedicted to Ameera Adam




FCWA ☀️


_________________________




To alhamdullah wannan ce page ɗin ƙarshe ta kyauta,don haka duk mai son ci gaba da karatu zai biya kuɗinsa na karatu 500 ta wannan account 2670215530
ZULFAU YAHAYA Ecobank kafin na saka shi group sai a turo shaidar biya ta WhatsApp +22795045822






Last free page 10






A'isha na nan zaune cikin halin ƙaƙanikayi Momy ta fito Mansur na bayanta.Kan salon ta hakimce ta sune ta tare da cewa “ A'isha ruwan gidan ma ba za a bani ba sai na roƙa ko kuwa ban isa ba ne?”
“Haba Momy ya za ki ce haka? Ai ko ban auren Mansur ke ɗin uwa ce gare ni domin ciki guda kuka fito ke da Mamana ” cewar A'isha ta na mai tashi da sauri har jikinta ke yin rawa ta nufi kitchen.
Drinks da abinci ta haɗo mata,ta dire su a gaban Momy sai bayan ta zuba mata komai ne ta tashi ta shige bedroom.Matsanacin kuka ya kubce mata,ta faɗa kan gado ta rusa shi cincin ƙarfinta.
Mansur ya shigo,“ A'isha?” ya faɗa cikin sanyin murya kamar ba shi ne ya ga ma yi mata tsawa ba.
Ba ta daina kukan ba ballantana ta kula shi,ya isa gare ta ya na mai jawo ta jikinsa ya shiga aikin rarrashi amma ta ƙi yin shiru .Sai da Mansur ya kai ruwa rana sannan ya shawo kanta,ashe shi ma da walakin wai goro a miya.Buƙatarsa ce ta kawo shi,kuma ko da ya samu abin da yake so ya bar ta nan.
Cike da baƙin ciki A'ishah ta isa toilet,abu ya tare mata goma da gomiya tara.
Kamar wata zararriya ta shiga dukan ruwa ta na cewa “da me zan ji? Wace rayuwa na tsoma kaina ni A'isha? Wayyo Allahna!” sai ta ƙanƙame dukkan jikinta jin tamkar ana kallonta .
Ƙoƙarin fita daga bawon wankan ta fara,sai dai tamkar wacce aka jone fatar jikinta da bawon haka ta ji ta liƙe gam.Cincin ƙarfinta ta buga wani uban ihu wanda ya karaɗe duka gidan,sai dai ko motsin wucewar ɓera ba ta ji ba ballantana Mansur ko Momy su kawo mata agaji.
Dakyar ta ci nasarar fiddo ƙafafunta waje,sai ta ga su yin wani ja ƙau jawur babu kyawun gani kamar jan nama.Hankalin A'isha bai ida tashi ba sai lokacin da Allah ya bata iko ta tashi kan ƙafafuwanta.Kaf shap ɗinta ya zube kamar an zuba sukari a ruwa,jikinta ne ya ɗauki wani irin rawa ganin ƙugunta kamar muciya saɓanin da can farko da take turbakallah.
Towel ta saka ta fito da mugun sauri,bayan Momy ta gani ta na mai fita daga ɗakinta ba tare da ta san mi ya kawo ta ba.
Bakin ƙaton madubi ta tsaya ta na kallon kanta,sai kuma ta ganta normal ba ta san lokacin da ta saki ajiyar zuciya ba.“Ashe gizau ne ban canza ba” ta furta cikin murna bisanin ta shafa mai da turare,ta saka kaya sai kuma ta fito falo.
Turus ta yi ta na kallon Momy na yayafa ruwa a duk wata kusurwa ɗaki,ba abin da ya fi bata mamaki irin sunanta da na Mansur da ta ji ta na ambato.
“In kin gama gulmar sai ki je ki yi abin da za ki yi” cewar Mamy ba tare da ta juyo ba.


‘Ko ya aka yi ta san na fito?’ A'isha ta tambayi kanta bisanin ta wuce kitchen.Girki ta ɗora ,bisanin ta dawo falo ta ɗauki wayarta.Fatimah ta kira,cikin sa'a ta same ta tamkar rariya haka A'isha ta buɗe baki ta na ba Fatimah labarin abin da ya faru da wanda ma ke kan faruwa ba tare da ta san babban kuskure ta aikata ba.




Da dare Mansur na dawo wa ya shiga ɗakin Momy,bayan ya gaisheta ne take ce masa “ɗazu matarka ta kira wata mai suna Fatimah ban san ya suke ba,amma kaf sirrin gidanka ta sanar da ita na mu'amalar ka da ita .Hum! Ni kuwa cewa ta yi jarababiyar tsohuwa ko amarci ba ku gama ci ba na zo na tare muku a gida”
Ran Mansur ne yayi bala'in ɓaci ,ya tashi da sauri ya fita.Ya na shiga ɗakin ya tarar da A'isha ta zanzare ta ci uban ado,tuni ya manta abin da ma ya kawo shi ya je ya rungumeta.
Gabanta ne ya faɗi lokacin da Mansur ke ƙoƙarin yi mata kiss saboda wani uban wari da bakinsa ke yi,warin hammatarsa kuwa ko bunsuru albarka .Amma a haka ta daure suka raya sunnah,cike da kula wa ya dube ta ya ce “daga yau kar na sake jin kin fitar da sirrina ,ko Momy ba ta faɗa min ba zan gane wa”
A'ishah dai ba ta ce komai ba ,zai lokacin da zai mayar da kaya ta ce masa “don Allah ka je ka yi wanka”
“Ba zan yi ba” ya bata amsa a takaice.
“Ko brush ka yi”
Mansur yayi saurin juyo wa ya na ƙare mata kallo cikin ido,‘ko dai maganin da na bata har ya karye ne da har ta ke iya faɗa min magana kai tsaye babu ɗigon tsoro?’ ya yi wa kansa tambayar a zuci.
“Ka yi haƙuri don Allah ” ta faɗa a ɗan daburce bisanin ta shiga toilet ta yi wanka.




Ɓangaren Momy kuwa shiru har yanzu ba ta ji ihun A'ishah ba ,ta yi zaton shegen duka Mansur zai lakaɗa mata.Ganin haƙar ta ba ta cimma ruwa ba yasa ta tashi ta rufe ƙofa da key,kayan jikinta ta cire ta ɗaura wani jan ƙyalle a ƙugu.
A cikin jakkar kayanta ta fiddo wata ƙaramar tukunyar laka mai ɗauke da layu da sauran abubuwan shirka sai kuma wani bokitin roba fari mai ɗauke da korayen ruwa,nan ta fara yin surkulle a nan take hayaƙi ya turniƙe ɗakin ba ka jin komai sai hucin narkeken kwaɗo da kukansa.
Ta ɗauki lokaci da dama bisanin ta tsaya,murmushin mugunta ɗauke a fuskarta ta ce “ A'isha tun da ki ka yi sanadin shigar ɗana ƙungiyar asiri wallahi ke ma sai na gulala miki,sai kin gwammaci kiɗi da rawarki.Da ni da ke shege ka fasa” ta gama faɗar haka ta buɗe bokitin nan fa kwaɗon nan ya yi tsalle ya fito kamar mai jira.
Shegun idonsa tulu-tulu sai faman juya su yake ya na ƙoto.Ba tare da jin tsoro ba Momy ta shafi kansa ta na mai cewa “na wakilta ka a matsayin mai ɗaukar fansata,ina so ka fitini A'isha cikin mafarki da kuma zahiri ka zame mata hawainiya ka na sauya kala kamar yadda aka bani Kambunka” ta na zowa daidai nan ta furta wasu surkulle a take ya ɓace bai bayyana ko ina ba sai a ɗakin A'isha.




Ta na zaune kan gado kunnenta maƙale da waya ta na cewa “wallahi Fatimah in faɗa miki har yanzu ma Mansur ya ƙi yin wanka,ban san dalili ba in kuma na yi magana ya yi fushi”
Can ɓangaren Fatimah ta ce “to ke kamar ba mace ba,ki rasa dubarar da za ta sa yayi wankan? Kawai ki bari sai ya na kwance ki cika bokiti da ruwa ki zuba masa ai doli ya yi wankan ”
“Katifata ta jiƙe?”
“Ai ta na da leda”
“Ok to zan jarraba na gani” sun yi hira sosai bisanin ta kashe kiran, lokacin ƙarfe takwas na dare bai gota ba.
A'isha ta sauko ƙafarta ƙasa da niyyar zuwa toilet sai ta ji wani bala'in sanyi tamkar ƙanƙara,“innalillahi!” ta fusrta da mugun sauri a take kuma ta ji normal .
Toilet ta shiga ,ta hau WC kenan ta fara jin kukan kwaɗo ta saki ihu ta fito a guje sai kuma ta ci karo da Mansur ya shigo.
Ko tambayarta bai yi ba lafiya take ihu ya zube kan bed,saboda ya gaji sosai ya sha yawo a gari ko zai samu ƴan mata huɗun da aka buƙata sai dai ko guda bai samu ba.




Baccin da ya fara da ninshari ya saka A'isha da ke can takure saurin dubansa,shawarar Fatimah ce ta zo mata a kai.Da mugun sauri ta fita waje ta ciko bokiti da ruwa ta malala masa a jiki.Hargowar da ya yi ya saka A'isha sakin bokitin ta na mai dafe ƙirji.










★AYODELE




Duk yadda na so in danne muradina akan sanin tarihina kasa wa na yi.Bayan mun gama cin abincin dare na ce “Momah wai mine ne sunan Abbana? Na ga ko lokacin da na yi makaranta Ayodele kawai ake kira na” shirun da ta yi ya saka ni ci gaba da cewa “ko dai shegiya ce ni banda uba?”
“Da ubanki Ayodele! Jarumi mai zubar da maza ko a fagen yaƙin wasa.Ke ɗin sauraniya ce ɗaya tamkar dubu,a kaf cikin ƴaƴansa maza da mata,manya da ƙanana ke ce ƴar baiwa” Momah ta faɗa wanda a ƙarshe sai da ta saki murmushi.
“To ya na ina? Mi yasa ba mu rayu a tare ba?”
“Don na tseratar da ke daga uƙubar da ababen bauta ke shirin tsoma ki yasa na gudo” ta bani amsa ta na mai kallon cikin idona, ta ci gaba da cewa “ko da na ji kin ambaci sunan Lassey na fahimci lokaci ya yi da za ki san tarihin ki,sai dai fa ba komai zan sanar da ke a yau ba sauran sai ranar birthday ɗin ki”
Cike da jin daɗi na matso, Momah ta saki murmushi wanda a cikinsa ina iya hango tsantsar farin ciki wanda ban san mi ya wanzar da shi ba sai dai na fi alaƙanta shi ƙila ta na son mahaifina irin sosai ɗin nan.


Sai da ta jawo ni jikinta kamar wata ƙaramar yarinyar,kaina na kan cinyarta hannunta kuma na shafa ƙananun kitson da ta yi min.
Momah ta ce “kamar yadda na shaida miki ke sarauniya ce to mahaifin ki shi ne Sarkin Victoria Falls inda ya gaji sarautar ne a hannun Yayarsa na manta sunanta ”
Da mugun sauri na ce “ Déborah ” ambaton sunan ya saka ƙwan lantarkin ɗakinmu fashe wa ji kake ɗuuuu.
Momah ta zabura ta miƙe tsaye,“wa ya faɗa miki sunanta? Wa ya ce miki ana ambaton sunanta a ko ina? Da na ce miki na manta a tunanin ki gaske manta war na yi?” Momah ke faɗa cikin wata irin murya wacce ba ita na santa da ita ba,idonta kuwa wani irin haske suke fitar wa kamar an kunna glov har wani canza kala suke.
Jikina ne ya ɗauki rawa ainun, musamman da ƙofofin gidanmu suka fara yin wata irin buga wa su rufe kansu su buɗe ji kake faaa-faaa!
Rufin ɗakinmu kuwa kamar zai kware har ɗaga wa sama yake,wata da ban manta inda na ɗora ta ba na lalubo tare da ƙoƙarin kunna fitila ita ma ta yi bindiga ta fashe har ɗiyan hanjinta da garin batirinta na ji a hannuna.
Tashin hankali,gobarar gemu Momah ta canza Yare ta shiga suratai.In ba gizau idona ke min ba wasu fararen siffofi ne ke faman shigo wa ɗakinmu tamkar duniyar fatale.........








A nan kawo ƙarshen free page,duk wacce ke so ta biya 500 ta akwatin nan 2670215530
ZULFAU YAHAYA Ecobank sai ki tura shaidar biya ta WhatsApp +22795045822






MRS SADAUKI NIJAR 🇳🇪

5
6
7

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login