Showing 6001 words to 9000 words out of 21779 words

Chapter 3 - BAKIN SHAFI Book 1 Free By Oum Yasmeen.txt

Advertisement

Unknown   

20 Jan 2025

3802

kinsan mu suwa ye to Kannan ango ne..,


Maryam ce ta, ta tashi tace


'' Allah ya saka uwar sa ce taya za ku shigo mana ba sallama ko wayanne irin gidadawa ne..?,


chingum ɗin bakin ta , A'isha ta tofar tace


'' ke har awa kike wannan maganar to wallahi idan yau muka ga dama sai kun yi kwanan cell kinga ko abin da nake umma ta fahimta ta toshe kunnen ta dangin matsiyata ga kayan ɗakin nata zo mu tafi..,


ta ina zata gane aminci ya rufe mata ido cewar aunty lubna


jan hannunta A'isha tayi suka fita sai jin karar tashin motar su sukai fitowa rufaida tayi tace


'' gwara da kukai musu haka yan iskan karya wallahi sai na gyarawa kowa zaman ta..,


dariya suka saka da shewa




POV ALTAB....




Dan rainin hankali ko ka gama zumu ɗin ne kamar baka son barin gidan nan tun ɗazu nake ce maka an kawo ta ka haɗa kayan ka zuwa sallar isha sai mu kai ka amma kayi buruss


Cewar RUFA'I


dan murmushi yayi shi kaɗai yasan me yake ji a jikin sa ba daban biyayyar mahaifiya ba da son kaucewa zaɓen tumin daren da yake neman ya yiwa kansa ba zai iya auren rufaida ba duk da ba abin da ta rasa ilimin addini aiki da shi tsoron Allah ya khalil ne ya shigo a birkice zama yayi ya na sauke gauran numfashi..


Zuciyar ta kasa aminta da abin da idanuwansa suka gani zancen ta yake so ya gaskata amma me ya ga fa takai bakin ta innalillahi wa'inna ilaihir raji'un Allah ya yaye mai wannan baƙin shafin da ya lulluɓe kwakwalwar sa wannan wacce irin ƙaddara ce


kallon sa altab yayi ya taɓe baki wani irin haushi sa yake ji tashi yayi yace


'' malam lafiya ka shigo min ba ko sallama..?,


idanuwansa ne suka ƙada sukai ja haka idanuwan altab akwai abin da yake hangowa a idanuwan altab amma tunanin da hangen nesan sa sun kasa hasaso mai mene wanne abu ne kamar yadda idon altab yayi ja haka na Khalil kallon ido cikin ido sukewa junan su cikin jin zafin abin da altab ya aikata khalil yace




'' Wallahi Allah altab ka bani mamaki yan zu da ka nuna musu wacce riba ka samu ni nasan wace ce nasreen na Fika sanin ta..,


Cikin ƙaraji altab yace '' wallahi karya kake yarinyar da na raina da hannuna yarinyar da tun tana cikin jini aka danƙa min ita a hannu na..,


tashi khalil yayi tamkar zai shiga jikin altab yace


'' wannan duk abanza tunda baƙa kokarin sakata farin ciki baka kokarin gushe mata damuwa ni nayi rawar gani akan nasreen dan nayi mata maganin damuwar ta na haɗa wata mata da Allah akan ta zama mahaifiyar nasreen ta nuna mata so tamkar mahaifiyar ta ta jawota a jiki sai dai kash tun kafin a je ko ina matar ta gajiya...nasreen bata cancanci tsana daga gurin ka ba har da zaka tun zura baffa yanzu dan an hanani aurenta sai me idan har nasreen mata ta ce zan aure ta...,


Karya kake idan har ina numfashi a doron duniya baza ka taɓa auren ta ba


da sauri RUFA'I ya shiga tsakaninsu yace


'' haba khalil me kuke yi haka kun tashi tare komai naku tare kuna yara ba kuyi faɗa ba sai yanzu yau fa ranar farin ciki ce a gare ku..,


Ni wallahi ba ranar farin ciki bace rana mafi muni a guri na kasan irin halin da ya jefa baiwar Allah nan kasan a halin da na barta shi ya zo yana rayuwa kamar ba shi ya saka ta ba bara kaji RUFA'I idan aka bawa ALTAB bindiga ya harbe nasreen tsab zai iya harɓe ta domin baya kaunar ganin ta a doron duniya


A'uzubilla me kake faɗa ne haka..?,


Cewar rufa'i yana riƙe altab da yake kokarin kai wa khalil duka
Ja da baya khalil yayi yace


''sake shi RUFA'I ce mai akai shi ka dai ne me zuciya...,


Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un wai me ya shiga kan ku ne ina raba ku , kuna ƙoƙarin yin faɗa da hankalin ku da tunanin ku me maƙon ku kuyi wa wani faɗa kune yau da kan ku kuke yi kar ku manta fa lokacin muna makaranta mahaifiyata Allah ya jikanta da rahama har kwatance take mun da ku amma yanzu kune kuke neman illata junan ku


Rufa'i ya faɗa ya share hawaye jikin su ne yayi sanyi musamman Khalil juyawa yayi zai fita sai kuma wayar sa tayi ringing ashe akan kujera ya ajiye ta komawa yayi ya ɗauka ganin baƙuwar number ya ɗaga tare da akarawa a kunne sallama yayi ba tare da wanda ya bugo ba ya amsa sallamar sa ya zarce da cewa kai ne khalil...?,


Cikin sauri yace '' eh nine me ta faru..,


zan turo maka address kazo asibiti yar uwarka tayi hatsari ana buƙatar ku


ehyi me kace kit ya kashe wayar kallon sa rufa'i yayi yace


'' me ya faru..?,


nima wallahi na rasa gane wa me ke faruwa wai zai turo min address yar uwata tayi hatsari


ko nasreen ce


nima haka nake tunani domin na barta a wani hali sai da na tawo nayi dana sanin tawowa amma bara na ƙara kiran shi danna kira yayi message ya shigo wayar sa da sauri ya bude a fili ya shiga karanta wa yace


Unique Care Al-Haramain Hospital
Plot 297 Jido Layout, Danladi Nasidi Housing Estate Mariri


da sauri rufa'i ya karɓi wayar karantawa yayi ka be ƙarasa ba ya karɓi wayarsa ya daka a aljihu ya fita cikin sauri ya ke komai mantawa da yayi mukulli baya jikinsa tsaki ya ja ya koma part dinsa ya dauko key ya fito bude mota yayi ya shiga


yayi mata key ya kusan buge me bawa shukoki ruwa sai kaucewa yayi ganin a yadda yake Sahara gudu a cikin gidan ya bawa ma'aikatan gidan tsoro sudai sunsan baya shaye shaye buɗe mai get me gadi yayi dai-dai sako hancin motar su lubna sai dai sune suka kauce mai amma shi kamar ma be gansu ba


ko da ya hau titi sharara gudi ya dinga yi har ya isa asbitin parking yayi a waje domin ba zai tsaya jira ba har a ba shi katin shiga da mita ayi checking ta ƙaramar kofa ya shiga wayar sa ya fito da ita daga aljihu kiran mutumin ya shiga yi amma ba ɗauka ƙara kira yayi sai a na biyar sannan ya ɗaga kai tsaye yace mai kana kina gani nan a cikin asibitin...?,


Faɗama masa yayi nan da nan ya mai da wayar aljihu ko tsayawa kashe wayar be ba ya shiga reception hannun sa na dama ya shiga akwai hanya miƙe hanyar yayi har emergency room wuru wuru ya fara can ya hango mutumin yana zurga zurga cikin sauri ya ƙarasa yace


'' tana wanne daki ne..?,


kai hakuri yanzu likitoci na kanta ta bugo ne akai nima wucewa na zo yi na ganta na kaita wasu asiti saboda rashin dan sanda ba a karɓeta ba shi ne na kawo ta nan da ita saboda abin yayi yawa zato suke ba hatsari bane


jingina da bango khalil yayi ko me ya faru da nasreen da sa hannun altab shi ne sanadin komai da ya faru da ita kasa cewa yayi sallar magariba aka kirawo dole ta saka ya tafi yayi salla bayan ya idar ya tsaya yayi mata addu'a sannan ya dawo lokacin wani likita ya fito yana share zufa da sauri khalil ya ƙarasa gunsa yace


'' yaya take kun shawo kan matsalar...?,


dafa shi baturen yayi yace


''don't worry everything will be fine..,


kai khalil ya gyaɗa yace


''I can go in and see her..,


yanzu za a fito da ita a Kaita wani dakin zaka iya shiga amma kafin nan ina son ganin wanda ya kawo ta


sai a lokacin khalil ya lura da mutumin nan baya nan yace


'' kawo ta yayi nine dan uwanta shi temaka mata yayi..,


Okay biyo ni office binsa yayi har office dinsa zama yayi sannan yace


'' a'a ga guri ka zauna mana...,


zama yayi zuciyarsa na tsananin bugu buɗe laptop likitan yayi sannan yace


'' yar uwar ka ta kamu da cutar ciwon zuciya me tsanani i am sorry to say


da sauri khalil ya ɗago yana hango baƙar fuskar altab duk shi ya sakata a cikin wannan hali ci gaba da cewa likitan yayi idan ba ayi taka tsantsan ba ko wanne lokacin zuciyar ta zata iya bugawa sannan ta kamu da cutar mental processing disorder amma wannan ba wata matsala bace hankali ana tafiyar fa ita yadda take so zata war ware
idan har kun lura za ku ga akwai abubuwan da take selecting idan kunyi kokarin da raba da shi ciwon zai ci gaba har ya girma ya zame mata matsala


Rubutu yayi a takarda ya miƙo amsa yayi yayi mai godiya magani zai siyo sannan ya biya duk wani kuɗi da aka ka she mata wayar sa ce ta fara ringing cirowa yayi sunan mamy ya gani raɗa raɗa akan screen din wayar sa yasan yanzu za su iya samin labari wata kila saboda haka ta kirawo shi ɗan haka be ɗauka ba...


A yanzu nasreen bata da wani gata da ya wuce nasa insha Allahu ba zai taɓa barin ta tayi kuka ba fita yayi yaci ka ciɓis da mutumin da kawo ta hannu ya miƙa mai yace


'' bawan Allah kai hakuri a dazu bana cikin kwanciyar hankali nagode nagode Allah ya saka da alkairi ya baka abin da kake nema duniya da lahira...,


Ba komai ai yiwa kaina wallahu nayi maka wannan uzurin kallo ɗaya za ai maka a san baka cikin kwanciyar hankali ya me jiki


aa nine da godiya me jiki alhmdllh komai ya zo da sauki


kai masha Allah motar ta tana gurina zo muje na nuna maka inda take...


KU HANZARTA PAYMENT DIN KU BAZAN DADE INA FREE PAGE BA DOMIN SHIGA PAID GROUP ZAKU BIYA


500


Amina Muhammad Alhasan opay 8141785374


Ku turo da sheda ta wannan number 09061890481


ƁAƘIN SHAFI


EPISODE 4


A'a bara na haɗa ka da bakanike ni a kwai inda zani tunda kacs motar ta samu matsala sai ya tafi da ita ya gyara ta


gaskiya ta samu matsala ga ban motar duk ya lotsai ba damuwa kira shi sai na je da shi ya dauki motar


waya ya khalil ya ciro a aljihunsa yace '' to sai dai ban san sunan ka ba..,


dariya yayi yace


'' nima ban san sunan ka ba ni dai sunana HAFIZ JIBRIL MAI DAWA...,


ƙara waya yayi a kunne yana cewa '' KHALIL HAMZA HUSSAIN MAI TANGARAN..,


to nayi saving number ka kai ma sai kayi tawa insha'Allah zan ƙara kawo muku ziyara na ga jikin ta wallahi na tsorata da ganin halin da ta shiga a lokacin da na kawota jini jiƙa min rigata yayi


Okay ba damuwa mun gode sosai wallahi sauke wayar yayi yana cewa kaga be ɗauki kiran ba rana na ƙara yi mai ko Allah zai saka ya ɗaga kaga dare na ƙara yi


Haka ne wallahi


cikin sa'a ya ɗaga karawa yayi a kunne ya danna matsa gefe ci gaba da danna wayar sa Hafiz ke yi har ya gama wayar ya dawo yace


'' ga shinan zuwa ni zan tafi phamarcy na siyo magani..,


okay Allah ya kawo shi lafiya sai ka dawo


amin ya Allah ya ce yana fita da ga gurin ba ƙaramin bill sukai mai ba haka ya dawo hannun sa riƙe da ledar magani daidai karasowar makanike dan haka juyawa yayi yana cewa


ka ganshi ya kirawo ni yana waje zo muje sai ku tafi


wayar sa hafiz ya mayar aljihu suka fara tafiya har wajen musabaha sukai da me gyaran mota sannan ya juyo ya barsu tare da man ya riga da ya gama yi mai bayani


kai tsaye dakin da aka kwantar da nasreen ya shiga tana kwance ban da na'urar da aka saka mata ke motsi alamar tana da rai ba abin da ke motsi a jikinta kanta an nannade mata shi da bandeji ga oxygen da aka saka mata limshe ido yayi ya jingina da bango a lokacin wayar sa ta ƙara ringing wannan karon adda asma ce


ɗagawa yayi cikin tashin hankali tace mai har yanzu fa nasreen bata dawo gida ba ko zaka bincika kaga inda take


kallo yabi gadon da take kwance yace


'' tayi hatsari yanzu haka ina asibitin da aka kwantar da ita amma da sauƙi...,


ajiye Sultan tayi da yake hannunta gaban ta ya yanke ya wadi tace


'' innalillahi ya akai haka ta faru...?,


adda asma ina zan sanu nima kirawo ni akai aka ce ga halin da take ci wallahi kin ganni nan jikina duk ba dadi ga ta nan ko motsi ba tayi sai na'urar da aka saka mata ita ke motsi amma baya ga haka ba abin da ke motsi a jikin ta


innalillahi wainna ilaihir raji'un Allah ya bata lafiya bara na sanar da su


cikin sauri ya dakatar da ita ta hanyar cewa adda asma kin manta dazu me ya faru...? Kinga wanda ya damu da ya neme ta ko yasan halin da take ciki wallahi abar tausayi ce NASREEN farin ciki muka kasa bata shi ya saka take tare da mutanen da take tare da su tafi jin dadin zama da su fiye da kowa


wallahi tun ba yau ba ma fahimci haka ɗebe mata kewa suke shi ya saka take zama da su amma Allah yaye wannan baƙin shafin da ya lulluɓe zuciyar mu da idanuwan mu Amin ya Allah


zan dai sanarwa da daddy Sultan idan zai faɗa musu ya faɗa muku


cewar adda asma


Okay hakan yayi sai an jima


turo min address din gobe zan zo Insha Allah


tu zan turo miki ya faɗa yana kashe wayar


zama adda asma tayi ta zuba ta gumi kasa motsi tayi har sai da uncle Yusuf ya shigo firgigit ta ɗago kanta, ta kallesa tace


'' sannu da zuwa...,


zama yayi ya kalleta yace


'' tunanin me kike..?,


Nasreen tayi hatsari yanzu haka an kwantar da ita a gadon asibiti


cikin halin ko in kula yace


'' wannan shine abin damuwa..har ya sakaki tunani..?,


runtsai idanuwanta tayi tace


'' nidai alfarma ɗaya na ke nema gobe insha Allahu zanje gurin ta idan na dubata naga halin da take ciki...,


ba a gaban ki baffa yayi magana ba wato ke zaki fara karya mai dokarsa ko ma me ya sameta ba ita ta waja kanta ba to wallahi ba ruwana idan kika je dana nan kiyi gidan ku sai na neme ki


da sauri ta ɗago sai dai ƙasa magana tayi ganin har ya fara hawa kan staircase


kwantar da kanta tayi a kan kujera rasa wanne tunani za tayi ko wanne ta kamo sai taga be mata ba...


______________⁠❥




ALTAB ya kamata fa mun binciki khalil ka gansa shiru har ƙarfe tara kai kuma baka da alamun tashi mu raka ka wasu daga cikin abokanan mu har sun tafi


Za fafe altab yace


''Rufa'i yau kai ko maye ne sai ka kyale ni dan wallahi bazan ciwu ba tun ɗazu nake faɗa maka ba inda zani ana dole ne...,


Ƙawayen amarya fa na jiranka suma suna so su tafi gida


karma su tafi su kwana anan banu da issue da shi


cewar altab yana gyara kwanciya tab abin na altab yau a zemin ne cewar wazir


zama rufa'i yayi yace


'' baƙara mi ba ni ta taɓa jin wannan abu na rasa gane inda ya dosa ya zame min bai bai wannan wanne irin baƙin shafi ne ya lulluɓe tunanin sa ..,


wayar sa ce ta ƙara ringing ɗauka yayi ya ja tsaki yayi rejecting din kiran ya saka wayar sa a playmode


can kuwa a marya ta gaji da haɗuwa sai zabga kamshi take amma zuwa yanzu ciyar ta ta ci gaba da bugun da take ko wacce sa'ar a gogo da zuciyar ta yake bugawa barin yanzu da taka 10:58 na dare karfa altab so yake ya kunya'ta ta a cikin ƙawayenta baya dauƙin ta kamar ba sabon aure sukai ba..


Sarah ce tace


'' rufaida dare fa yana yi ba ango ba dalilinsa..?,


daurin kanta ta cire ta ɗora a kan gado tace


'' sara gaskiya ina tunanin lafiya ba na kirashi amma ba ai picking..,


cije lips din tayi ba tare da tace komai ba maryam ce ta shigo tace


'' sweet kinga ba ango ba dalilin sa ni wallahi abba na ke tsoro kinsan halinsa yau mukai da shi zan dawo wannan ma zaman bikin nan fa da nayi ce wa nayi na tafi gidan kaka shi ya saka nake sharafi na...,


wallahi Maryam maganar da muke da sara kenan ko zuwa za kuyi ku bincika


rufaida ta faɗa idonta na ƙawo ruwa ba ƙaramin ado ta canca ɗaba amma duk fuskarta ta caɓe kamar ba a AC take ba da yake tana da oil face


da sauri Sara tace


'' haba rufy yawa wata mara gata da galihu taya za ayi mu tafi neman ango ranar daren farkon sa me mene sunan mu ke baki da mahimmancin da zai yi zumuɗi a kan ki komai..,


dafe kanta tayi tace


'' ko su lubna sun fada mai abin da ya faru ne kinsan shi da son yan uwansa...,


ba mamaki amma taya zai tuzarta ki ta wannan hanyar bayan ya san tare kike da kawayen ki gaskiya kune mo wani dalilin ba wannan ba cewar Maryam


Maryam nima abin da na gani kenan rufy ta faɗa tana kwanciya a gado yawa wacce kwai ya fashewa a ciki


tab tun yanzu kin fara gamuwa da shika shikan rashin mutuncin na miji ina kuma da zama yayi nisa gun gogu da juna


Cewar sara ta faɗa tana taɓe baki


ai ga irin ta nan sai da nace miki kada kiyi aure kina waje mene bakya samu ina cewa ma sai dai ki kunsawa matan auren takaici amma tunda kika kyalla ido kika ga ALTAB kika ce kefa sai shi tun yana basar dake har ya zo yana yata taki..


maryam ta faɗa tana rayata mayafi


jin sallamar sa da sauri ta fito tana cewa ganin yadda ya kalleta ta haɗiye zancen ta kallon gefen

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login