Showing 21001 words to 21779 words out of 21779 words
jazz shi kansa wandon sa yawa an kwato shi daga bakin kura ga wani Ban zan aski sai kace kan abarba kai ya jin jina ya wuce a yau zai zartar da hukunci ko ya yiwa kowa dad'i ko karya yiwa amma dole ya ɗauki mataki akan yarinyar nan tun kafin ta fara ajiye musu shegu a gida..
idan na waje yaƙi zama da ita dole ya tursasa wanda yake ganin ko bayan ransa ba zai iya hufuntar da ita ba wanda zai tsaya tsayin daka gurin tarbiyyar ta ta dawo yadda take a baya kafin ta haɗu da shedanun mutane wayar sa ciro bugu ɗaya aka dauka cikin girmamawa alhaji Usman yake kokarin gaishe shi katsai shi yayi yace
'' ka buwa yan uwanka su duk inda suke suzo ina son ganin ku...,
yana kaiwa wannan be jira me zai ce ba ya katsai wayar kafin kace mai kowa ya hallara gyara zama yayi sannan ya karato addu'ar buɗe taro yace
'' ba komai ne yasa ka na tara ku ba sai akan dalili Babba na lura ina gab da shiga cikin wani yanayi da al'ummar gari zasu fara zagina na gama hukunta masu laifi amma me laifi dake rayuwa a cikin gidana na kasa wani ɗaukan mataki akan abin da ke faruwa bayan dogon nazari da nayi yau kuma idanuwana sun gane min abin da ya kamata tun farko na yiwa tubkar hanci duk masu gadin gidan nan da security din dake cikin gidan nan da raina da lafiya ta a matsayina na babban alkali wanda ya rike mukamai da dama ni za a dinga tara yan iska a cikin gida to yau zan zartar da hukunci duk wanda yaga an mai rashin adalci ba haka naso ba amma ba yarda zanyi da nayi fushi sai kuma na gane hannunka baya taɓa rubewa ka yanke ka yar
gyatsuna fuska Hajiya tayi duk wannan kwana kwanar ya fito fili ya fada musu me ke faruwa amma sai zance yake cikin zance kallon ta mamy tayi tayi ƙasa da murya tace
'' yaya me kika fahimta a cikin wannan zancen na tsoho..?,
kallon ta tayi ta take mata kafa tace '' sai an lura damu koma mene ai zai fada...,
dan jim baffa yayi ya kalli altab yace
'' jeka ka kirawo min wannan yarinyar Khadijah..,
tashi altab yayi da sauri ya fita har yanzu tana inda take kallon ta yayi yace
'' baffa yace ki zo...,
fitowa tayi daga motar jazz tana cewa hukuma tayi kira muyi magana ta waya
okay ni yanzu akwai inda zani komin dare dai ki bar wayar ki a kunne
Okay ba damuwa ta faɗa tana bin bayan altab har suka isa parlour cire takalminta tayi ta shiga zama tayi ba tare da ta kalli kowa ba tace
'' baffa gani..,
wani kallo yayi mata sannan yace
'' KHADIJATOU ABDULRASHEED HUSSAIN MAI TANGARAN.. wannan sunan shi kike amsa wa ko..?,
kai ta ɗaga mai mayafinta ya cire yar stair din dake huyanta ya gani ta tattoo ya girgiza kai yace
'' dabi'un ki da halayyar ki sunyi kama da ta musulmin kwarai..,
da sauri ta kallesa baza ta iya ci gaba da kallon cikin idanuwansa ba maida kallon tayi kan hannayen ta da jiya taje ta cire farcen hannunta tattoo ne kawai a jikinta kasa magana tayi,
murmushi takaici yayi tace
'' ke kanki kinsa gaskiya jibi wuyan ki kamar ba yar musulma ba kai Khalil..,
da sauri yace
'' na'am baffa..,
Na baka nasreen a yau zan daura muku aure ka amince
kai khalil ya ɗaga alamar eh
da sauri ta ɗago altab ya dago zuciyar sa na tafasa Abba kuwa yace
'' gaskiya baffa ban amince ba wata kila ba za a rasa ta da cutar kanjamau ba haka kurum na rasa ɗana altab ne ya ɗago be yi zaton haka daga gurin Abba ba ya buda baki yace.....
turƙashi me hakan ke nufi me altab zai ce tab da sauran rina akaba wacce nasreen wane zai aure ta saboda duk mazan da yayi yunkurin aurenta sai a fasa wai shin ina mahaifinta
ɓangaren mazan gidan har guda uku ko wannensu akwai kudirin sa akan ta shin idan altab yace shi yaji ya gani rufaida fa ita zata ji ta gani yanzu auren ma kuwa zai yiwu...?,
domin jin wannan amsosin wa'yannan tambayar ku biyo ni a littafi na gama book 2,3,4,5
duk akan farashi me sauki 500
Idan na gama ya zama 1000
Alhamdulilah Allah nayi maka godiya da ka bani ikon gaba book 1 lafiya kamar yadda na gama lafiya Allah ka bani ikon gamawa sauran lafiya.
ni fatahiyya Muhammad yakasai (oumyasmeen) nake cewa ku huta lafiya
kar ku manta masu son a tallata musu hajojin su kofa a buɗe take muyi magana ta wannan number 09061890481