Showing 42001 words to 45000 words out of 61919 words

Chapter 15 - RUMANA BOOK COMPLETE BY MAMAN KHADY.txt

20 Jan 2025

8546

kuka,Aiko yanajina amma yai biris saima murmushi dayasaki danya lura rigimace kawai irinta masu yaronciki.
[4/2, 3:09 PM] Re@l💍 K@usy🌹: Rumana 47






Tallabeni jikinshi yayi yana sakin k'aramin kuka betaba tunanin cikina biyu bane domin kusan so hudu yanamin scanning amma saidai yaga guda daya amma k'ato.


Hawayen wahala keta ziraromin ga wancan yaron nata son fara kuka gakuma na jikina yaki fitowa duk kokarin da yakeyi.


Muryarshi na rawa yace daure Ruma kadda ya mutu rikeni sosai kiyi nishi me karfi zai fito saiki huta kinji.
Cikin muryar kuka nace "bazan iyaba haidar mutuwa zanyi"


Da sauri ya sakeni yakoma cikin kayan da yake ajewa sabida tsaron lalura irin Wannan saigashi da allura,Acinya yaimin ita kamin wani lokaci nai wani mugun nishi daya fiddo ragowar babyn,.


Wani irin barcin wahalane yai gaba dani kokuma sumewa nayi oho dai nidai bankuma sanin inda kaina yaiba tunda nasamu wannan azababban ciwon ya sakeni.


Jikinshi babu inda be rawa sabida tsabar rudewa sai shafa yaran yakeyi gasu zabga zabga kamar haihuwar daya daya,Saima kokarin kuka da sukeyi.
Dakyar ya jawoma kanshi dauriya ya goge yaran dayake dama kayan haihuwar ashirye suke saida ya gama gyarasu tsaf sannan yaima hasan din sheda sabida kwata kwata babu abinda ya banbantasu.
Kuma saka hannunshi ahancina yayi yaji ina numfashi sannan ya kwashe yaran bayan yasakamusu riguna ya nanndesu cikin bargunansu masu taushi,Addu'a yaimusu sannan ya koma wajena lokacin tuni barcina yai nisa.


Ruwa me zafi yafara hadamin sannan yatasheni,Wani kuka nasakamishi ina kwace hannuna"Nika kyaleni inyi barci"


Cikin lallashi yace "To aidama barcin zakiyi zo ki gyara jikinki yanda zakiji dadin barcin ko?


Saida yaimin allura sannan yaimin wankan da kanshi hatta jinin saida ya rageminshi sannan na idasa gyara jikina nafito. Shikuma ya tsaya wanke bayin Dan na zubar da jini sosai.


Riga da zani nasa na daura kallabina sannan na lallaba kusa da yaran na kwanta wata irin azaba nakeji gabana nayi Wanda dacan banjishi sai yanzu.


Idona biyu har yagama gyaran ko ina ya wanke kayan dana bata da nashi danshima mugu mugu yayi saikace shima haihuwar yayi.
Saida yasa turare sosai bayan ya lullube har fuskar yaran sabida zai iya yimusu karfi,Sannan yadawo kusa dani ya zauna yana sauke numfashi.


" Hannunshi nakamo na rike gam ina hawaye.
"Hannun nawa yacigaba da mirzawa cikin lallashi yace" Kiyi hakuri kindan k'arune shiyasa kikejin ciwo bari in inyimiki dinki yanzu saimuyi barci kinji ko?
Nidai ba baka sai kunne.


Saida yaimin allurai har biyu sannan yaimin dinkin banwaniji zafiba sannan ga allurar hadda ta barci danhaka bankuma sanin me akecikiba.


Ajiyar zuciya yaita saukewa akai akai kamar Wanda yaga halaka ya kufce sai kallon yaran yakeyi wa inda keta barci har hawayen dadi yayi tsabar farinciki jiyake kamar canzashi akayi.


Wanka yakumayi sannan ya dauro alwala yafara nafilfili yana godiya ga Allah dayaimishi wannan kyauta lokacinda beyi zatoba sannan kyautar da babu wani mahaluki daya isa yaimaka irinta.


Saida yai sallar asbahi sannan yasamu ya tsallaka can karshe ya kwanta yaran na tsakiya saidai su motsa su koma.






*** ***




Umman haidar ko zaki leka yarancan ne nifa bansan inji shiru banji motsinsuba kinsan bawani hankali garesuba ko?
Farfesun dake gabanta ta ture kamin tace "Alhaji kadaisan halin haidar da shiririta yaufa lahadi tunda yasan ba aiki zashiba aidama da wuya sutashi yanzu"


"Uhumm kofa sallar asuba bejeba kidaije ki lek'a kokuma ni inje.


Tashi tayi tana " Kai alhaji ko bari inje tunkamin katashi kai gaba,Cikin nan dai ko kai za ahaifar mawa iyakarta kenan!!! Ficewa tayi tana dariya yayinda shima yabita da kallo yana dariya.




Tajima tsaye tana bugun kofar amma shiru babu wani bayani,Da sauri ta juya Dan dauko key din dake wajanta Dan lokaci guda zuciyarta tafara gayamata ba daidaiba.


Ganin tashiga amatukar rude yasashi biyota data dauko key din,Ko ina lif babu haske duk da cewa Tara na safe yama wuce.
Tsaye sukai tsakiyar falon suna sallama nan ma shiru.
"Bafa tsayawa zakiyiba binta shiga zakiyi kiga ko lafiya nikuma zanjira nan.


Dakin datasan munfi amfani dashi ta nufa zuciyarta inbanda matsanancin bugu babu abinda takeyi,Fatanta daga alkhairi ba sharri ba.

Innalillahi wa inna ilaihirraji'un Alhaji zokagani Dan Allah.
Lokaci guda salatinta ya karade gidan,jikin Abban har rawa yake wajan afkawa cikin dakin wani irin burki yaja lokacinda ya fahimci metake nunamishi.


Nice ta farko sai yaran kudundune atsakiya saikuma haidar din Wanda ke daf da yaran yo ai dole ai ramuwar barci wannan artabu da akasha cikin dare.


Duka umman ta bugama haidar Wanda yasashi tashi agigice yana lalubar yaran Dan karma ya kasance mafarki yai duk wannan wahalar dayasha.


Jikinsu har rawa yakeyi wajan daukar yaran wayyo murna Abba hadawa yayi da Umma da yaran ya rungume yana godema Allah tare da jeramishi kirari.
Lamo haidar din yayi yana sakin murmushin farinciki dama yasan burin iyayeshi kenan suja jininshi yau gashi Allah yabashi har guda biyu.


Hannu Abban ya mikama haidar din Wanda yaketa kallonsu yana murmushi tare da share kwallar farinciki,Tashi yai yashige jikin mahaifinshi suka rungume juna,Itama umman hadasu tai ta rungume fuskarta jage jage da hawaye.


Saida suka natsa sannan tace "Hardar ita uwar lafiyarta lau ko?


" Lafiya lau Umma amma saida naimata dinki.


"Allah sarki baiwar Allah ai dole wa innan yara haka manya manya gashi ta fari Allah yabata lafiya bari mukoma falo kadda atasheta,Tasamu ta huta sosai ,Ammadai tai wanka ko?


Kai ya dagamata yana lumshe ido wani irin barci yakeji shima.


Komawa falon sukai suka zubama yaran idanu kowa sai sakin murmushi yakeyi ko magana sunkasa yima juna tsabar farincikin da suke ciki.
" Ammadai haidar yaso yai wauta meyasa be kirakiba kin temakamishi?


"Uhumm Aiko gashinan shima duk ya zube dare daya kawai daga gani kwana sukai Abu daya,Mudai ai anyi barka tunda anrabu lafiya"


"Hakanekam Allah shine abun godiya Allah yaimata albarka ai tayi kokari sosai wallahi yarinyar akwai ta da dauriya,Cewar Abban bakinshi har keya,Sai faman liliyar hannun yaron dake hannunshi yake.






Zubamin manyan idanunshi yayi ganin yanda fuskata tadan tasa sabida gumurzun jiya lallai ba k'aramar juriya nayiba,Wani murmushine ya kufcemishi lokacinda ya tuno da fitsarin daya saki lallai yayi abin kunya Allah ma ya rufamai asiri lokacin ban cikin hayyacina lallai dayayi abinda zanta tsokanarshi dashi.


Fuskata ya dinga shafawa har saida na bude idanuna nai wata doguwar mika gwanin dadi na juya yanda raina keso,Ai bansan lokacinda na rungumoshi jikinaba cike da farinciki" Shikenan yanzu nima zandinga barci yanda raina keso"


Murmushi yayi tare da sumbatar kuncina"Allah yaimiki Albarka matata Allah ya farantamiki Ruma Allah ya jikan iyayenki yai musu rahma,Ina rokon Allah yabani iko da damar farantamiki har karshen numfashina nagode sosai Allah yabarmu tare.


Cikin sanyi jiki na amsa da Amin ya haidar nima nagode da kyautatawarka gareni.


Wani murmushin kauna yabini dashi kamin yace muje in nunamiki yanda zaki gasa jikinki saiki karya nasan dai akwai yunwa cikinki tunda kinfitar da wa incan basawan,Kamin kuma sufara Neman abincinsu.


Kusan wankan ma da kanshi yaimin duk da irin shagwabar da nake zubamishi,Umma shigowarta biyu amma bamu fitoba saidai tanajin maganarmu,"Kai yaran zamani sai abarsu.


Abba na rungume da yaran gaba daya sai kiran waya yakeyi yana fadi yayinda umma keta shige da ficen ganin ta kammala abinda zan karya dashi ga yaran harsun fara Neman abincinsu.


Saida nafara shafa mai sannan shima yashiga wankan,Mamaki nakeyi wai yara biyu na Haifa duk maza lallai Allah shine mabuwayi gagara misali.
Riga da zani na sa wa inda rabon da insasu harna manta sabida girman ciki,Amma gashi yanzu sun shige tsaf sai kirjina dayacika sosai.


Saida tagama shiryamin abinda zanci sannan taima yaran wanka ta shiryasu cikin wasu kaya masu matukar kyau da Tsada saidai kalarsu daban sabida babu Wanda yai tunanin biyu zan haifa duk da mutane da yawa na fadin gaskiya da wuya idan dayane Sabida girman da cikin yayi.


Lokacinda shadaya na safe yayi ai tuni gidan yafara dinkewa da 'yan barka.
Falona cike yake da dangin umma sabida itace 'yar gari kamin dangina su iso duk da dai duk Wanda yakirani sai inji yace sai suna zaizo amma innata kam tace tana nan tafe yau dinnan kuma sai anyi suna sannan zata koma.



Niyyar kwanciya nake sabida har kaina yafara ciwo sabida hayaniya saigashi ya shigo da yaran daga bangaren Abba yake sabida abokanshi dana Abban daketa zuwa ganinsu.


Duk kuka suke yanata jijjiga da lallashi saikace sunsan abinda yakeyi.
Hararata yayi kamin yace anya kinada kai kuwa?Ya za ai ki hana yaran abincinsu tun jiya haba Dan Allah"


Cikin marairaicewa nace kayi hakuri Allah da umma ta kawosu dazu bansan yanda zanyibane kuma sainaga sunkoma barcin saina kyalesu.


Zee din rigata yaja kamin yace to ai saikiyi magana anunamiki amma yara sai kuka sukeyi rike ki gani.
Yai maganar yana mikemin daya sannan ya kwantar da dayan acinyarshi ,Da kanshi ya zaro nonon yana tambayata kin gogo da nace ki goge?


Kaina na dagamishi tare da tayashi gyara yaron.


Wani k'aramin ihu nasaki lokacinda yaron ya damki nonon,Bansan lokacinda na dafe hannun haidar dinba ina hawaye.
Cike da tausayawa yake cewa"Sannu kinji ahankali zai bari sannu kadda ki ciremishi kinga sosai yakeja yunwa yakeji.


Ummace ta shigo da sallama,Tana kallonmu "Sannu Ruma zafi ko? Kiyi hakuri zai bari bari inje indawo dama bakine sukazo.


" Dan Allah kabarshi hakanan yafa koshi!!!


Hararata yayi kamin yace gidanwa ya koshi kina gani saisha yakeyi.


Saida yaron ya saki Dan kanshi sannan ya amsheshi ya dorashi akan kafadarshi yabani dayan,"Yauwa bashi wannan yanda kikaima wannan din dasun koshi saikiyi barcinki kinji 'yar albarka.
Yana zaune duk saida yaga suncika cikinsu sannan yace in kwanta shikuma ya fice da yaran.


Sonake inyi barci kamin inna ta iso musha hira.
[4/2, 3:09 PM] Re@l💍 K@usy🌹: Rumana 46




Sallamar Abba yasani kokarin gyara zamana,Amma saiya kalleni cike da tausayawa "A a yi zamanki rumana sannu kinji Allah yarabaku lafiya yabada masu albarka"
Sadda kaina k'asa nayi Sabida kunya inason tsohonnan wallahi sosai yake kaunata.
Naman dake hannunshi ya ajiye gabana yana fadin ga sakonki da zafinshi sosai.


Godiya naimishi sannan najawo ledar na bude bayan barinshi falon.


Haule itace yarinyar da Umma tasamu tanadan tayata aikace aikace idan tadawo makaranta,Yarinyar tanada kokari sosai diyar malam habu megadi ce dayake babu nisa tsakanimmu dasu.


Shigowa tayi da kular tuwo ta gaisheni sannan ta ajiye gabana, Kallonta nayi sainaga Sam yarinyar kamar bata da gaskiya hakanan dai na ja kular ina dibarmata naman dake gabana nace kice angode.


Zamatai nan cikin falon tana kallo saidai duk dagowar da zanyi saimun hada ido,Gaza hakuri nayi nace haulatu lafiya kuwa?
Akunyace ta mike kamin tace lafiya lau Aunty cikinki kawai nake kallo naga kullun kuma girma yakeyi.


Murmushi nayi kamin nace to ai dole yai girma tunda kullun kwanaki yake kumawa.
Takai bakin kofa zata fice saiga haidar zai shigo danhaka saita koma baya saida yashigo ta gaidashi sannan tafice tana waiwayenshi.


Zama yai kusa dani saida ya sumbaci katon cikina sannan ya gyara zamanshi tare da jawo ledar gabana yafara cin naman yanabani labarin daga wajan harun yake.


"Tashi muje mu kwanta"


"A a kajira Umma tafito mana nifa bammajin barci wallahi.



** ** **




Rayuwa ta kasance yanda muke bukata sosai nakejin dadin rayuwata, Ahalin yanzu zuwan inna uku Sabida tsufan da cikina yayi komai wahalar yimin yakeyi Sabida nauyi nazama wata abar tausayi.
Bangaren Umma nake yini ita kemin komai bata taba nuna gajiyawartaba akaina abinda nakeso shi takemin danace washhh zasu rude Sabida fargaba.




Zaune nake natasa uban cikina ina kallon yanda yakemin buruntu kamar me niyyar fasa cikin yayo waje,Kai anya cikinnan yaro dayane kuwa kamar yadda ya haidar din yagayamin?
To gaskiya ina mamakin nauyin cikinnan inko yafara motsi jinake kamar zan mutu wallahi.


Zama yai gefena tare da riko hannuwana yana kallon idanuna," Rumana tunanin me kikeyi?


Ajiyar zuciya na sauke kamin ince babu komai jinake dai kamar bazan iya fita tattakinnanba wallahi"
"A a zaki iya ruma banso kisha wahala wajan haihuwa gara kidinga yawo gabobinki nakuma budewa ai insha Allah ankusa ban tunanin zaki kuma kai sati daya dashi tunda kinga edd dinki ya cika Tashi insamiki wannan doguwar rigar gidan harun zamuje mukuma ganin amarya.


Marairaicewa nayi kamin nace haba ya haidar akwai nisafa!!


" Nasani ammadai daurewa zakiyi kinji ko?


Shiya temakamin nasaka doguwar Riga me fadi tawani yadi sannan yasakamin hijab ko hoda babu fuskata Sabida hasken danayi saidai man lebe dayasamin kadan.
Wayoyinmu ya dauka sannan ya kamamin hannu muka fita ahankali nake takawa hannuna tallabe da cikina Dan idan ina tafiya nakanji kamar zai fado k'asa ne.


Umma mukaima sallama sannan muka fita,Kasancewar yammacine sai fitar taimin dadi sosai Ahankali muke tafiya yanda bazan galabaitaba babu ruwanshi da idanun mutane danagaji zai tallafeni harna huta sannan mutafi,Mutane da yawa sai kallonmu sukeyi,Anan mukaci karo da haulatu da kanwarta antasosu daga islamiyya Wani irin mayen kallo tabi haidar dashi bayan sungaidamu.
Kasa hakuri nayi harna furta lafiyarki kuwa?


Cikin alamun jin kunya tace babu komai saikun dawo.


Harararshi nayi ganin bece komaiba saima murmushi da yake saki.
"Ruma kincika nemo rikici wallahi kwanakin baya ai nacemiki wannan yarinyar akwai wata manufa aranta kikace bawaninan saima laifin da kikai kokarin maidawa kaina aigashinan yanzu kingani da idanunki ko? Shiyasa ko tuwon nace adaina kawo na gidansu gara na dinga amso miki wajan hajiyar harun kullun,So gara ki dinga kula.


K'afata na fisge wacce ya duk'a yana gyaramin takalmin kamin ince to tunda ka gane nufinta ai saika takamata birki tun wuri ko?


Shidai hannuna kawai ya rike mukaci gaba da tafiya har gidan harun,Sabida anyi bikinshi wata daya daya wuce.


Da farinciki suka taremu mayarshi mesuna Humaira tanada mutunci sosai zuwanta biyu wajena.
Harunne ya kalleshi bayan mun huta yace" Aliyu mekaima uwar biyune naga tanata hura hanci haka?


Dariya yayi kamin ya ajiye kofin lemondake hannunshi,"Aikasan yanzu rigima wajanta hadda ta saidawa waifa dannayi kasuwa shine takemin Bakin ciki,Wato wata zukekiyar yarinyace ta ganni tanaso shine taketa kunburinnna kasan ita takoma cus babu Wanda zai dauketa ahaka.


Kuka nasaka Sabida takaici,Dan dama yanzu kuka bawai wahala yakeminba.
Gaggawar rungumeni yayi yana lallashi yayinda idanun Humaira sukacika da kwalla itafa mamakin yanda akai nake iya tafiya da cikinnan takeyi, Amma shine Dan iskanci hadda tsonakanata sukeyi ahaka,Tasan itama datasamu haka zasuyimata.


Saida mukai magriba sannan muka baro gidan marata ta daure gama Sabida gajiyar tafiyar munyi hutu yakai goma kamin mu k'arasa gida, Umma da Abba tsaye muka taddasu harabar gidan da alama jiranmu sukeyi.


Kujera Umma tabani na zauna ina sauke numfashi kamin ta mikomin ruwa,Abbane keta hararar haidar din kamin yace "waikai Dan gidanku bance kadaina janta waje da nisaba kai meyasa bakada tausayi haidar?

Keyarshi ya shafa kamin yace kayi hakuri Abba gidan harun kadaifa mukaje kuma Ahankali muke tafiya.


Tsaki yaja kamin yabar wajan yana sababi.
Shidai haidar komawa yayi domin yin sallar isha'i nikuma bayan nagama hutawa Umma ta rakani bangarena na zauna jinake kamar indora hannu aka inta kurma ihu wallahi, komai yadainamin dadi jinake kamar nikadaice nake cikin wannan damuwa.






******






Mungama duk shirin kwanciya amma Sam banjin dadin jikina marata saiwani daurewa yakeyi tana warwarewa Sam banbari ya lura da hakanba dannasan kilama ya yayibeni muyi asbt.
Jikina yake tausamin ina lumshe ido kamin ya Dora hannunshi akan cikina yanajin yanda cikin yaketa wutsul wutsul gwanin ban tausayi,Kallon idona yayi kamin yace Sannu rumana ko zakici wani abune naji cikin yaki nabba'a?
Kwanciyata na gyara kamin ince nakoshi wallahi yau nayi lodi da yawa ai,Kyaleshi danayi barci shikenan.


Abuk'ace yake sosai dani

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login