Showing 18001 words to 21000 words out of 61919 words
mana yanzu.''
"To akwai matsala babba ba k'arama ba domin kuwa alhaji na nan yana shirin yiwa Haidar aure wanda bamu san wace kala yarinyar zai auro mishi ba.''
Duk cikinsu babu wacce maganar bata doketaba amma da yake 'yan duniya ne babu wacce ta nuna, Saima hajiya Saude ce da tayi murmushi tace.
''Lallai daga gani makwad'ait ne idan ba haka ba waye zai ba mahaukaci d'iyarshi? kai bama haka ba anya ansan ya Haidar d'in yake kuwa da zasu bashi auran 'yarsu? kodai rufa-rufa aka yiwa iyayenta?''
Nanfa sukai shiru bayan sun tsayar da magana d'aya cewar duk wacce ta samu dama to lallai ta bugi cikin alhajin har sai ya fad'i gidan su yarinyar ta yanda zasuje su kashe maganar domin suna so su tona abinda shi alhajin ya rufe kowa yasan babu wani me hankali da zai d'auki d'iyar shi ya dankawa mahaukaci ita, kai ina bama zai yiwu ba.
*****
Bayan sati d'aya. A ranar muka dawo BAKORI bayan na gama zagaye dangina na uwa dana uba sunata nanata min sai sunzo biki insha Allah. Ni dai iyakata ido da murmushi domin gani nake yi kamar labari ne na kanzon kurege.
Aranar da muka dawo aranar alhaji Yahaya yazo gidan mu ya kuma ce wajena kawai yazo yana son magana dani. Rashin sabo tsakanin mu yasa duk hankalina ya tashi inna da kanta takai mishi tabarma har zaure sannan ta dawo gida bayan sun gaisa. Ban yarda na kalleshi ba a haka muka gaisa dashi sabida kunya inda ya fara da ce min.
"To Alhamdulillah *RUMANA* na san cewa babu wanda ya tuntub'e ki domin jin ta bakinki akan kina son auran Haidar ko bakya son shi, sabida ana ganin an isa dake. Toh nima ba tambayarki zanyi ba Rumana sai dai nayi miki godiya da amincewar da kika yi domin yin wannan jihadi, insha Allahu nasan zuwa gaba zakiji dad'i sannan zaki yi alfahari da hakan ina fatan Allah yai mana jagora kuma ya shigemana gaba a cikin wannan lamarin.''
Kaina a kasa na amsa da 'amin' ba tare dana bari ya jiba.
"Ga wannan waya ce Yusufa yace a baki ko zaku dinga gaisawa tsakaninku dashi, sannan dan Allah kadda kidamu da rashin ganin mijinki a yanzu domin sainan da watanni biyar zai dawo, ke kuma kinga yanzu saura satittika ya rage ayi bikin ku, zan turo miki Usman na wajena ai na san kin sanshi, to abokin shi Haidar d'in ne saiku dinga aiwatar da komai dashi na hidimar bikin kinji ko? Koda kina bukatar wani abun shi zakiwa magana kin fahimceni ko?''
Kaina a kasa nace ''Ehh nagode Allah ya saka da alkhairi.''
Komawa nayi cikin gida jikina duk ya gama yin sanyi, jinai kawai hankalina be kwanta da wanda zan aura din ba to inba haka ba shi ace zamu gaisa din dashi mana amma sai ace da mahaifinsa zamu yi, gaskiya nifa dama can bana kaunar na auri wanda baya sona sabida idan namiji baya sonka wallahi komai zai iyayi dan ganin ya wulakantaka, bare shi wannan daga yanda naga labarinshi kudi sun gama bud'e mishi idanu, wai tsaya ma wani kalane shi mijin da zan aura..? Tambayar da bata da amsa a yanzu kenan.
******
''Alhaji kayi hakuri kamar yadda na gaya maka a wancan lokacin kaki yadda to yauma daka dawo maganar zan nanata maka, yaronka kwakwalwar shi lafiya lau take, sannan bashi da wata lalura mai alama da tabin hankali, kawai dai an kauce hanya ne aka had'ashi da mugayen aljanu wad'anda suke zuwa suna bidirinsu ajikin shi wani lokacin, shine zakaga ya koma kamar mahaukaci amma sam ba mahaukaci bane. A tun lokacin da nayi maka wannan bayanin idan da ka amince inaga da yanzu Allah ya bashi lafiya domin Allah zamu rok'a kuma shine zai yi maganin komai, Amma lokacin saika nuna kai a'a ba zai yiwu ba sabida kana tunanin baka nufin kowa da sharri dan haka babu wanda zai nufeka dashi ko? To yanzu ba k'aramin kuskure bane, dan wanima bakasan shi ba amma yana nan yana neman hanyar da zai cutar dakai balle kuma wanda kasani kuma yake jikinka, Bawai ina nufin wani naka bane yaiwa yaronka wannan sharrin a'a kawai dai inaso in nuna maka cewa k'addarar Allah yawa ne da ita sannan zakaga komai yana da sila da sanadi yanzu dai fatan mu Allah ya shige mana gaba ya kawowa yaron nan sauki.''
Muskutawa yayi kafin yace. ''Amin ya Allah, nagode malam to yanzu wane mataki ya kamata afara bi?''
''Yauwa to maganar danake son ji kenan daga bakin ka, yanzu abinda ya kamata anan shine da farko dai za'a fara da almajirai yara ayi sauka ta alkur'ani sau d'aya, sannan za'a bawa mabuk'ata sadaka, Sai a fara bashi rubutu na sha da shafawa insha Allah wata rana sai labari. Sannan bayanin dakai min na auran da zaka yi mishi shima wannan naji dad'i kuma nayi farin ciki domin indai ita matar tashi ta fahimci lalurar tashi to lallai ko maganin zaifi tafiya yanda ya kamata ajikin shi, Amma ka daina maganar sha'awarshi eh gaskiya ne yana da yawan bukatar mace kuma koda bakin shi yasha gaya maka amman yanzu ma da lalaurar ta kamashi su aljanun basu tab'a mishi wannan b'angaren sha'awar tashi ba shi yasa take tashi lokaci zuwa lokaci amma dan Allah kadda kaba da kofar da zai kusanci yarinyar mutane alhalin baya cikin hayyacin shi dan lallai za'a iya samin matsala wacce bama fata.''
Kuma numfasawa alhaji Yusuf yayi jiyake jikin shi kamar anyi mshi duka sabida tashin hankali shi kam duk wanda ya yiwa Haidar haka bazai tab'a yafe mishi ba idan kuwa zai ganshi kila sai ya zama ajalin shi. Sallama yayi akan sai ya dawo sai a fara abinda ya dace ammafa har lokacin tunani yake anya kuwa gaske ne wani ne zai kauce hanya domin ya cutar da d'an uwansa musulmi?
Jiki a sanyaye ya koma gida ko b'angaren shi bai nufa ba sai dai ya fara nufar na Haidai d'in. Kwance yake yana bacci, shi kuma Mudi na saman kanshi yana ragemai sumar kanshi a hankali gudun kadda ya tashi yayi ta borin daya saba.
Zama yayi ragwaf tare da d'agawa Mudi hannu wanda yake gaidashi, Lumshe idanunshi yayi yana tunani wanda yanzu ya zame mishi jiki.
Yana zaune yana kallon Mudi har k'umba sai da ya rage mishi sannan ya gyara mishi sajen shi nan da nan fuskarshi tai wani fayau kai baka ce yana da wata lalurar ba.
"Mudi aure zan yiwa Haidar.'' Cewar alhaji Yusuf yana kallon yanayin Mudin, cikin washe baki yace.
''Kai alhamdulillah alhaji hakan yayi kyau wallahi Allah ya bashi ta gari wacce zata kula dashi tsakaninta da Allah.''
Bayan sati shida.Zuwa wannan lokacin gidanmu ya kacame da hidima sabida karatowar biki. Zaune nake inna tana ta lailayemin jikina da lalle dagani sai wata bak'ar bes a jikina, inna da kanta ta siyota a kasuwa sabida wannan aikin da take mim. Kirjina na kalla wanda yayi wani cirko-cirko kasancewa babu bra a jikina, har kirjin nawama be tsira ba tunda bani takeyi tace na shafa idan tagama.
Fatata ta canza sosai wani uban laushi da santsi takeyi sannan ga kamshi domin akwai wata madarar turare da ake zubawa cikin kwabin lallan yanzu wajan wata daya kenan dafara yi min wannan gyaran ammafa na canza nayi kyau ta yadda daka ganni zaka san cewar ni din amarya ce.
"Dan Allah duk gyaran nan da nake miki ki daure idan anyi auran nan kiciga ba da yi domin wallahi ba k'aramin temakawa jiki yake yiba, kune dai yaran zamani da sai kuce ku dole sai kayan shafe-shafe shi yasa da an kwana biyu sai jiki ya jeme ya lalace.'' Ban kalleta ba nace.
''Toh inna.''
Shigowar dije da wasu k'awayenmu yasa inna barin d'akin mukuma mukaci gaba da shirya yanda za'a yi duk da dai ni ina zaune iya kaci na dasu kallo.
Usman shine wanda yayi ruwa yayi tsaki wajan ganin komai ya tafi dai-dai an shirya walima kadai kamar yadda mahaifin ango ya tsara sannan aka bani wadatattun kud'i koda zan buk'ata lefena kwananshi hudu da kawowa babu abinda babu akwatina shida masu shegen kyau da tsada sannan ga uwa uba kayan da aka zuba a ciki.
K'awayena sunata tayani murna tare da nanata suma Allah ya mai dasu kamar ni, Ni kam jinsu kawai nake yi domin ina cikin wani yanayi wanda ni kaina bazan ce ga kalarshi ba......
*MAMAN KHADY.*🙇🏻♀
[4/2, 11:15 AM] Re@l💍 K@usy🌹: Rumana 16
Zaune nake ina tilawar alkur'ani me girma shikuma yana gefena yai zugudun saikace mai tunanin wani abu.
Inuwa kawai nagani saman kaina,Kusan atsorace na dako kaina aiko wata mace nagani tsaye saman kaina tana taunar cingam tare da wani girgije girgije saikace karuwa agefen titi.
"Wani miyau na hadiye kamin ince sannu da zuwa ki zauna mana.
Wani kallon banza taimin kamin tace" Ke dallah dakata kekuma awa da zakice in zauna ko kina tunanin wani matsayi gareki?
Da mamaki nake kallonta,Kamin ince ikon Allah to Dan Allah kadda ki zauna kiyita tsayuwa.
Sabida raina tuni yafara baci dama wani lokacin fadane dani balle wannan ko sallama bataiminba kuma Dan iskanci naimata tayin wajan zama zata nunamin itama wata shegiyace.
Hannun haidar nakama na kaishi daki sannan nai zamana acan Dan banga amfanin dawowata falon ba.
Bansan ya akaiba saidai naji banbamin masifa natashi acikin falon,Mamaki da tsoro ya hanani ko motsin kirki Saida naji ana kwalamin kira da cewa ke matar mahaukaci kina ina fito.
Hijab dina na d'auka nasa sannan nafita.
Uwargidan Abba ce tsaye da wannan me zubin 'yan duniyar.
Duk'awa nai tare da cewa hajiya ina yini?
Wata shegiyar harara ta sakarmin kamin tace"Dallah can matsa bani guri algunguma kawai ubanme k'anwata taimiki kika zageta?
Idona waje na furta zagi kuma?Wallahi hajiya ban zagetaba itacema tashigo ko sallama bataima tana gayamin maganganu shine sai nikuma natashi nabata wuri dama ko zama bataiba.
"Mitsw aikin banza to Dallah dama ancemiki zama tazo to bari kiji wannan itace nafeesa wadda haidar zai aura kamin yazama mahaukaci kuma koyau ya warke itace matarshi nasan kedai kozai mutu bazai zauna dakeba domin yafi karfinki garama ki kama kanki ankawokine domin ki wahalamishi kamin yaji sauki ya sallameki wawuya kawai,Kenan har wata mace ce?
Hawaye share share idanuna nakebata hakuri yayinda zuciyata nakejin kamar zatayo waje tsabar tafarfasar da takeyi.
Saida tagama masifarta ta zagemin iyaye tas tare da kirana da kwadayayya sannan sukabar falon.
Kuka nacigaba dayi sosai hadda sheshsheka saiga Harun ya shigo.
" Subhanillahi Amarya meya faru?
Muryata ashake nace wallahi wannan hajiyarce tazo da kanwarta wai wacce zata auri ya haidar shine suka zagemin iyaye wa inda basusan me akeyiba.
"Kanshi ya dafe kamin yace ammadai kinban haushi wallahi shine kika tsaya kina kuka bakici uban shegu ba?Toma tsaya idan ita hajiyar kin ragamata shikenan sai itama wannan Mara kunyar ki kyaleta?
To bari kiji wallahi kinji na rantse matukar kuka zaki dinga musu to ki tabbata kwanan nan hawan jini zaikamaki domin ta dinga shigomiki kenan tunda dama takanzo idan sunyi hutun makaranta kuma tana dadewa danhaka ki kankaroma kanki mutunci tunkamin dare yaimiki.
Ina mutumin nawa? Yaya kike ganin jikin nashi?
" Alhamdulillahi da sauki sosai gaskiya domin komai yafara sauki.
"To Alhamdulillahi ai haka akeso yanzu abinda yai saura shine kiyi k'okarin ganin umma ta dawo k'asar nan kema hankalinki nasan saiyafi kwanciya.
Haidar ne ya fito da cup ahannu da kallo duk mukabishi Sabida ganin abinda zaiyi.
Yana zuwa saitina ya wurgomin shi da sauri na cabe ina ihun tsoro dannariga na sadakar saiya rushemin kai.
Da sauri na mike naje na hadomishi tea saida ya koshi sannan ya kwanta jikina yacigaba da sauke numfashi.
Haidar yace" Lallai kina kokari amarya lallai jiki yafara kyau kenan yanzu yafara sanin yunwar cikinshi kenan ko?
Dan murmurshi nayi kamin nace eh hakane kam anasamin cigaba sosai.
Da farinciki ya furta Allah yak'ara afuwa ammafa yakamata ki dinga lura kina kiyayewa kadda yadinga raunataki kwanakima Abba yacemin har yankarki yayi da wuka ko?
"Eh wallahi nashiga zanyi girki Ashe yabini saidai kawai naji sukar wuka ahannuna Ashe harya dauki wukar bansaniba.
" To Allah ya kiyaye gaba Sabida zai iyacigaba da faruwa tunda bawai tunanin daidaine akanshiba yanzu duk abinda yaga dama zakiga shizai aikata,Bari intashi in wuce insha Allah danadawo tafiyarnan zanfara nemamiki gurbin karatu tunda naji haka Abban yakeso ammadai ni nafiso umma ta dawo tukunna Sabida abubuwan suyimiki sauki.
Godiya naimishi sannan yaimana sallama yatafi.
Gaskiya Harun yanada kirki sosai shine ke kula dani matukar Abba benan kuma betaba nuna alamun gajiyawaba nikuma saina daukeshi amatsayin yayana kawai tunda bani da kowa ahalin yanzu.
Aunty nifa gaskiya hankalina atashe yake kinsan dai inason haidar sosai amma kalli yanda kikabari aka tsauna dukiya wajancan kuma ji matarshi ainasan ko warkewa yayi bazai kalleniba tunda ga wadda ta kula dashi shiyasa nacemiki na amince aimana auren zan zauna yanda yake kikace a a.
"Mitsw lallai sai yanzu nasan baki da hankali uban waye yacemiki zai warke?Ke yanzu da ajinki da komai amma saiki yadda ki zauna da mahaukaci? To bari kiji haidar ba warkewa zaiyiba wannan ciwon nashi mutu ka rabane itama matar tashi 'yar gidan matsiyatane shiyasa sukabada auranta garesu kuma inbanda aikin bauta metakeyi agidan ko kina tunanin akwai wani Abu bayan wannan?
Itadai nafeesa ba haka tasoba shiyasama ta tunzuro bakinta gaba domin ita tanason haidar sannan akwaita da bakin kwadayin tsiya domin inda an biyemata ma da ahakan ta aureshi,Musamman yau data shiga taga irin dukiyar da alhajin yabata ma wajan.
Misalin bakwai na magriba na lalubi wayata muryar umma kawai nakeson ji kwana biyu bata kiraniba bansan meyasaba haka kawai naji matar taimin ina tsananin sonta duk da bantaba ganintaba.
Yanke kiran tayi sannan ta kirani.
" Ummu Rumana ya kuke?
"Lafiya lau umma munyi kewarki Dan Allah ki dawo wallahi ina cikin kadaici da kewa.
Murmushin farinciki tayi kamin tace Rumana kenan karki damu zandawo insha Allah.
Cikin shagwaba wacce bansan lokacinda nafarataba nace haba umma Dan Allah kullun fa haka kike cewa amma har yanzu kinki dawowa ko incema Abba ya kawomu?
Dariya tayi me sauti kamin tace lallai ma kuruciya na damunki kema basaikunzo zanzo insha Allah.
Bansoba amma haka mukai sallama bayan takuma bani shawarwari tare da yimin fatan Alkhairi.
Saida yagama duk abinda ya kaishi harma ya turo da kayan Nigeria sannan ya nufi India cike da kwarin guiwa domin tuni yagama duk binciken daya dace kai daidai da gidan da umman take zaune saida yasani lokacin fita aikinta lokacin dawowarta kai da duk ma sauran shige da ficenta.
Kwalliya yasha kamar zashi zawarci sai bula kamshi yakeyi saidai tuni zuciyarshi ta dade da hautsinewa musamman da yake tunanin wace kalar tarba zai samu sannan ya zaiganta.
Numfashi ya sauke me karfi lokacinda yaganshi tsaye kofar gidan,So wajan biyar yana kai hannu zai kwankwasa sai yaji tsoro ya kamashi,Saida yaga hankalin masu wucewa yafara yowa kanshi sannan yai shahada ya kwankwasa.
Jin motsin taba kofar za abude yasa kirjinshi yai wani irin mummunan bugawa Wanda har saida yakai hannunshi yadafe.
Ido biyu sukai da ita lokacinda ta bude kofar,Kallon juna suka tsaya yi kallo irinna tsantsar mamaki.
[4/2, 11:15 AM] Re@l💍 K@usy🌹: Rumana 15
Alokacinda garin
Allah ya waye har kosawa nayi inji kiran malam liman musamman danaga har rana tafito.
Kudi nabada aka shiryamana kayan kari me kyau musamman Harun Wanda besa da wa innan gargajiyan ba tunda anaji da gayu ga dukiya Allah ya hore.
Saida nagama shiryawa tsaf sannan kiran malam liman ya iso gareni.
Jikina har rawa yake tsabar sauri,Zama nai gefenshi na gaidashi kamin inbude kunnuwa domin jin yanda zance zai kasance.
Yajima cikin yin shirukamin yace"Alhamdulillahi dukkan godiya ta tabbata ga Allah insha Allah komai yazo da sauki ummu ruman domin Allah ya gwadamin komai yanzu ga magunguna nasa anhadomiki Wanda zakije dasu wa'incan jarkunan kuma duk rubutune nida su saminu mukayi shi jiya domin ban kwantaba har saida naga komai yamin daidai,Yanzu bin komai za ayi ahankali kadda ayi gareje domin tabbas akwai sharrin jinni cikin hidimar ga sihiri Wanda tuni aka kaudamishi da tunani Wanda wannan shine za adan dauki lokaci kamin ya warware amma sauran matsalar inshaAllahu kamin wa innan magungunan sukau Allah yayi maganinta.
Wannan nakine sha zaki dingayi kullun in zaki kwanta sannan ki dage da addua kinji ko?
Wannan aruwan wanka zaki dinga sawa kadan aimai wankan har kanshi ma'ana ko ina da ina, sai wannan kidinga fesamishi idan zai barci komi kokwawarshi kadda ki barshi insha Allah duk zasu gudu su barshi.
Babu ke babu sauraren kade kade da wake wake domin yin hakan shine zaisa kosun tafi su dinga kokarin dawowa,Wannan kuma rubutunne yakasance ruwan shanshi,Kicigaba da hakuri insha Allah wataran sai labari sannan kibar wannan maganar amatsayin sirri lallai kadda ki yadda wani yasan maganar nan balle taje kunnen iyayenki na dangin babanki kinji ko?
Kaina akasa na amsa da to insha Allah zan kiyaye Allah yasaka da alkhairi ga wannan Dan Allah sai adinga mana sadaka lokaci zuwa lokaci wannan kuma sai asallami su yaya saminun domin samun lada da warwarewar matsalar.
Saminu Dan yayan mama ne kuma shima masanine sosai afannin addini shike temakama malam liman da wasu abubuwa sabida hali na tsufa.
Wayar Harun na kira nace yashigo dakin malam inaciki sabida in nanata maganin agabanshi kadda sainaje gida kuma in manta.
Ina cikin mishi bayani sai kawai muka tsinci muryar IYA tana rafka sallama.
Da sauri malam yace zuba wa innan aljihunka Haruna zansa akaimuku sauran mota,Wannan tsohuwar yanzu saitai tunanin wani Abu daban.
Da