Showing 15001 words to 18000 words out of 61919 words
hakura lokacin tsarabata tagama zuwa ko ina.
Sai wajan Tara na dare sannan nasami halin ganawa da malam liman domin anan akayima harun masauki ma.
Yaji dadin ganina sosai saidai tunkamin yace wani Abu na sakamishi kuka domin ina tunanin duk duniya babu tsohon da yakejin matsanancin tausayina kamarshi domin damacan yafi kulawa dani akan kakannina na wajan uba.
Rungumeni yayi ajikinshi kamin yace" Rumana kiyi shiru kadda ki tayarmin da hankali kindaisan ba cikakkar lafiyace daniba gayamin menene ko akwai matsala ne?
"Kuma shigewa nai jikinshi kamin inbashi labarin duk halin da haidar yake ciki tare da Wanda nake niyyar shiga yanzu.
Bakinshi ahangame yacika dajin tsoron Allah kamin yai karfin halin cewa iko sai lillahi Ashe hakan abun yake?
To ki kwantar da hankalinki insha Allah komai yazo karshe zanyi bincike me zurfi da izinin Allah ayau da darennan duk abinda ALLAH ya gwadamin idan yaso sai musan ta inda zamu kamo bakin zaren ai kinyi wauta Ummu da tuni kin kawomin labarinnan,Amma ba komai ko yanzu dinma babu abinda zai gagara insha Allah,Yanzu kije ki kwanta kome kenan zan ganki da safe kamin lokacin tafiyarku,Amma kinaganin babu matsala dazaki kwana nan kindaisan halin iya da mita ko?
Cikin shagwaba nace nidai nan nakeso kyaleta taita mitar ta aidama ita babu me iyamata.
Cikin kwanciyar hankali nai kwanciyata sai fatan inwayi gari lafiya.
Saidai me wani tunanin ya haidar ne yaimin kiki kaka acikin zuciya musamman yanda yake yanzu nasan Abba nacan yana fama,Duk da dai munyi waya da abban dazu yacemin babu matsala nasan kila yadai fadane kawai.
Safiya ta gari.
[4/2, 11:15 AM] Re@lπ K@usyπΉ: πππ *RUMANA* πππ
Na
*MAMAN KHADY*ππ»ββ
(Mk)
*HASKE WRITER'S ASSOCIATION*π‘
(Home of expert and perfect writer's)
Page 7
A can bangaren alhaji Yusuf muea ya tada wani lafiyayyan gini abimka ga masu naira, Sosai ya tsauna dukiya a wajen, abinda ya kuma tashin hankalin matan gidan musamman da suka ga ya fita hanyarsu shi dai abinda ke gaban shi kawai yake yi.
Falo ne d'an madaidaici wanda aka k'awatashi da wasu manyan kujeru masu matukar ban sha'awa sune wad'anda sukaiwa falon kawanya, Sannan sai k'ofar kicin daga gefe sai kofar store ajere sannan ta toilet daga gefe.
Sai kofofin bedroom da akai har guda hudu kuma kowan ne d'aki akwai gurin ajiye kaya da gado da madubi da sauran abun bukata na bedroom, an akawata wajen da wasu manyan labulaye masu shegen kyau kai dolema idan ka tsinci kanka a wajan kaji ka cikin nishad'i da son kasancewa a wajan.
Sai da ya shirya har kayan Haidar d'in sababbi da kuma wasu nashi na da sannan yaji hankalinshi ya kwanta, ana gobe d'aurin auren ya cika musu store d'in su da duk wani nau'in abu naci.
Hankalinshi ba a kwance yake ba sabida gajaniya tayi mishi yawa gashi yaki yadda da kowa wanda zai taimaka mishi da wani abun..
****
Gida ya kacame da hidima musamman wayewar garin yau, domin yaune aketa hada hadar sallamar masu d'aurin aure. Misalin biyu da rabi na ranar asabar aka d'aura aurena akan sadaki dubu hamsin anan garin bakori aka d'aura sabida yiwa mijin innan halarci tunda dai shine yake rikona a yanzu.
Tunda aka ce an d'aura wani mugun zazzabi ya rufeni dama ina d'akin inna hayaniya ta isheni, nan da nan jikina ya kuma dumewa duk yanda abokan ango suka so su ganni abin sai ya gagara domin kwance nake sosai.
Nayi mamaki da akace abokan ango na nemana ashe mahaifin Haidar duk ya sanar dasu wajan ya cika da matasa masu aji sannan ga manyan mutane wa'inda suka zowa alhaji Yusuf d'in dan yi masa kara.
Kowa yasan akwai tazara tsakanin bakori da katsina dan haka uku nayi zuwa da wasu mintina aka ce a fito da amarya a wuce da ita gidan ta. Tunda wannan kalma ta doki kunnena sai hankali na ya kuma tashi na fara kuka ina rike inna itama rikeni tayi tana hawaye. Yau wace rana inna na kukan tausayi a kainaπ° har sai da mukabawa kowa tausayi a wajan nan. Nida dije k'awata ne a motar sai kuma gwaggo Hauwa da inna Sa'ade wato dangina na uwa d'aya na uba d'aya.
Tunda mukabar bakori nake kuka har zuwa cikin katsina domin jinake yi kamar makasata za'a kaini, tun suna lallashina har suka gaji suka kyaleni. Mun sami mutane sosai ashe dangin mahaifiyar Haidar d'in sunzo gidan sai dai sun tare a b'angaren alhajin amma cikin matan gidan babu wacce tai musu kallon tsiyama balle su sakaran na arzikin.
Alhajin yaji dad'in ganin su musamman da yaga harda wasu daga cikin matan abokan shi amma wa'inda suke abota da ita mahaifiyar Haidar d'in.
A hannunsu aka mikani nidai na kasance kamar bindi domin sai inda aka jani lokacin har muryata ta dishe sabida kukan dana sha.
Ba k'aramin k'ok'ari Alhajin yayi ba domin sai da ya tsaya-tsayin daka wajan ganin komai ya tafi yanda ya tsara sannan ba tare da an sami wata matsala ba, kuma alhamdulillahi domin zuwa daren wayewar gari gidan babu kowa duk an watse an barni dagani sai halina shine ma yake ta shige da fice a b'angaren namu sai kace shine angon sabida tsabar yanda yake zirga-zirga.
Shigowar shi ta karshe itace daya shigo yi min sallama sai da na duka na kuma gaida shi duk da dai yau ban san iyakar gaisuwar da nayi mishi ba. Zama yai yana sauke numfashi kafin yace.
''Sannu Ruma ki duba ko'ina da ina inda baki gane ba saiki tambayeni jeki ina nan ina jiranki.''
Jikina a sanyaye na mike duk da cewa d'azu sai da na leka ko'ina. Yana nan zaune na dawo yace min.
"Akwai matsala?'' Muryata tayi laushin dole sabida kuka nace.
''Eh akwai kayan da ban san yanda zanyi amfani dasu ba a kitchen d'in.'' Mikewa yayi tare da cewa.
''Muje ki dai yi hakuri Haidar beda uwa ne agidan na san da itace zata zama madadina, to kinga bata nan dole nine zan tsaya miki ko gobe kadda kijira a kawo miki abinci kiyi abinki da kanki akwai komai na buk'ata sannan koda wata ta kawo miki abinci ban yarda kici ba kinji ko? kome kikeso ni zaki nema insha Allah zuwa jibi kingama hutawa zamu yi wata muhimmiyar magana dake.''
Kaina nakuma sunkuyarwa kasa ba tare da nayi magana ba.
"Kidinga min magana Ruma ki d'auke ni amatsayin mahaifinki kinji ba siriki ba domin nima matsayin d'iya na d'aukeki kinji?" Cikin jin kunya nace.
''Toh.'' Yafe min.
"Yauwa ki dinga kirana da Abba sabida mijin kima haka yake ce min kinji ko?''
"To.'' Itace kalmar dana kuma amsawa da ita, gabaki d'aya wata irin soyayyar dattijon ce ta kamani domin gaskiya yana da kirki sosai ga kamala.
Da kanshi ya nuna min komai harma sai da yasa na gwada had'a tea sannan ya ajiye min ledar dake hannunshi ya kunna min TV sannan yayi min sai da safe ya tafi.
Wani tsalle nayi na antaya kan gadon ina murna bayan na cika cikina da naman kazar daya ajiye min.
''Oh ikon Allah wai yau nice cikin wannan daular?''
Sai da na shiga bedrooms d'innan duka wai zab'en wanda zan kwana a ciki, duk shegen tsoron da nakeji haka nayi kwanciyata bayan nayi sallar godiya ga Allah tare da tarin addu'a wadda har sai da narasa mema zance.
*****
Zaku yi matukar mamakin yanda na tashi domin sai mutum ya rantse bani bace jiya aka kawo ina ta koke-koke ba. Tunda nayi sallah da asuba ban koma ba to dama ban saba komawa d'inba, saina d'ora da karatun alkur'ani mai girma har sai da gari ya waye sannan na jiye tare da nad'e sallayar da hijab din jikina na gyare d'akin tsab na saka turaren da nagani birjik a saman madubi sannan na koma parlour, nan ma sai da na share na kakkabe na goge sannan na shiga kitchen ina tunanin mai zan dafa musamman dana lek'a store d'in na ganshi shake da kayan cima kala-kala ammafa duk na 'yan gayu ne.
Ruwan tea na dafa sai kwai dana soya saina d'auki biredi na koma can wani d'an keb'antaccen waje da aka malaleshi da wani kafet mai kyawun gaske dama an tanaji wajen ne domin cin abinci kamar yadda Abba ya gaya min jiya.
Shigewa bedroom nayi, wanka nsyi sannan na gyara jikina hoda kawai na shafa amma ko kwalli ban saba, danni dama kwalliya bawai damuna tayi ba.
Karfe goma da wasu mintina na gama karyawa sai lokacin naji an kwankwasamin kofa. Mayafi na d'ora saman doguwar rigar dake jikina na nufi k'ofar. Kallon sama da kasa tayi min kafin tace.
"Kece amaryar?''
A kunyace na d'aga kaina ba tare dana bari mun kuma had'a ido ba, domin ban san wacece ita ba sannan na lura daga ganin kallon da take yi min inaga banyi mita ba.
Zama tayi bayan na gaisheta taci gaba da karewa falon kallo tana yatsina fuska. Lallaikam alhaji ashe uban kud'i ya kashema wajennan shi yasa ya hanamu mu shigo ko gani muyi lallai ma.
"Sunana hajiya Saude nice uwar gidan Alhaji ina yi miki barka da shigowa wannan gidan, sannan ina yi miki jaje na auran mahaukaci da kika yi.''
Binta nayi da kallo yayin da zuciyata taci gaba da wani irin bugu ban san lokacin da ta karasa ficewaba, sabida tunanin da yasha kaina. Ina nan jigum dani duk wani karfin gwiwa ta ya gudu, saiga Abba ya shigo bansan lokacin da na mike na nufeshi ba sabida fargaba.
Ganin yanda na taso cike da damuwa yasa shi jin jikinshi yayi sanyi domin ba haka yaso ba, yaso ya taddani cikin walwala. Zama yayi ni kuma na zauna wajan k'afafunshi ina gaida shi tun kafin ya gama amsawa na d'ora da tambayarshi.
''Abba wai mahaukaci nake aure?'' Idanunshi ya rantse kamin ya kalleni.
"Ki kwantar da hankalinki Rumana yanzu zan baki labarin komai, amma ina so dan Allah kiyi min uzuri tare dajin tausayina kadda kiyi fishi sannan kadda kik'i yadda da kaddara kinji ko?''
Idona harya cika da hawaye na san shikenan tawa ta kare daga yanda yake maganar nan na san cewa gaskiya matar nan ta fad'a.
"Kamar yadda kika sani sunana Alhaji Yusuf ni haifaffen garin bakori ne amma bayan na gama karatuna saina koma garin katsina na cigaba da aiki. Nafara aiki da shekara biyu mahaifina ya rasu dama kuma mun dad'e da rasa mahaifiyarmu domin ta rasu ne tun bani da wayau. Dagani sai yayana Alhaji Yahaya iyayen mu suka haifa amma muna da dangi sosai babu laifi. Bayan rasuwar baban mu sai yayana ya tilastamin yin aure sabida yace shi dai hankalin shi be kwantaba da in zauna jiran sai nayi gidana na kaina, nufinshi na kawota nan bakori kamin na mallaki muhalli a nan katsinan. Saudatu itace matata ta farko kanwar wani abokina ce da mukayi karatu tare, na aureta tun bata gama mallakar hankalin kantaba, sai dai tunda na aureta ko b'atan wata bata tab'a yi ba, tsawon shekara shida sai yayana yace na kuma yin wani auren,
''Saina nemi auran Saratu nan da nan aka bani domin alokacin ina da muhallina a cikin katsina sannan ina da kudina danni ban yarda da aikin gwamnatiba kawai, ina had'awa da kasuwancina. Itama Saratu duk hakan take domin shekara hudu itama shiru ba haihuwa sai hankalina ya fara tashi sabida tuni na fara tunanin matsalar daga jikina take kila nine bana haihuwar gashi zullumi ya hanani zuwa ganin likita sabida ina jin tsoron abinda za'a ce min,
''Ban hakura ba saina auri Bilkisu itama dai shiru, banyi niyyar yin wani auren ba daga mata uku din nan sai dai a ranar danaga Fatima naji idan ban aure ta ba har mutuwa zan iyayi, Nasha wahala sosai kafin na samu iyayenta subani ita domin sunce baza suba me mata har uku 'yarsu ba haka kawai aje a nakasa musu yarinya tunda yanzu ba wani tsoron Allah ake jiba. Amma na jajirce na like har sai da suka gamsu da kalar son da nake mata sannan suka amince min na aureta. Matana sun nuna b'acin ransu sosai da wannan auran musamman da suka ganta yarinya ce sosai kuma a lokacin duk ta fisu ilmin addini dana boko.''
Numfasawa yayi kafin yaci gaba, nima zamana na gyara tare da kuma bud'e kunnuwana domin na fahimce sosai yaci gaba da cewa.
"Ina son Fatima sosai domin tana da matukar tarbiyya a zaman da muka yi bazan ce ga ranar da ta sab'a min ba, saima nine wani lokacin idan aka kawo zugarta tai kaza zanyi mata fad'a koda batai laifin ba. Kwatsam sai Fatima ta fara laulayi bayan watanni takwas da auren mu. Babu wanda ya kawo mata cewa ciki ne domin ni a lokacin na riga na saddak'ar da cewa lallai bana haihuwa. Tsabar sa ido na hajiya Saude yasa ta fahimci akwai matsala domin ni dai ban sani ba wata rana ina kwance cikin d'akina sai gata ta shigo, zama tayi kusa dani tace.
''Alhaji wai kakai matar ka asibiti kuwa?'' Ba tare da na bata wata kulawa ba nace.
''Ban kai taba amma tace min ita taje.''
"To katashi kaje ka bincika idan ba haka ba kakusa d'aukar shege a hannunka tunda kowa yasan baka haihuwa ita kuma ai laulayi take yi.''
Ban san lokacin da nakai d'akin Fatima ba a lokacin, aikuwa saina tarar da ita tana ta amai duk ta galabaita, ban yadda cewa Fatima zata iya cin amanata ba domin koda na aureta budurwa na sameta sannan suna da duki ya dai-dai bakin gwargwado bare nace kwadayi zaisa tayi min haka. Da kaina na taya ta tagyra jikinta sannan nace muje asibiti. Likita ne ya tabbatar min da cewa ciki ne da ita na wata uku.
A wannan lokacin rasa abinda zanyi nayi shin farin ciki zanyi ko kuwa bakin ciki. Yayinda ita Fatiman naji ta saka ihu harda birgima ita wallahi ba ta son cikin ya za'ai ace duk cikin matana babu wacce naiwa ciki sai ita, ita wallahi sai dai azubar dashi. Na shiga tashin hankalin jin kalamanta wanda yasani fallamata mari sai dai kuma tana kukan najawota jikina na rungume sabida tunanin da gaskiyarta fa kuma dole ta shiga damuwa.
Bayani naima likitan tun daga farko har karshe yayi min tambayoyi sannan yace zai min awo. Gado aka bata domin ta huta nikuma a lokacin naga likita, sai dai iyakar binciken su sun gaya min cewa iyakar kwan haihuwata guda d'aya ne kacal kuma na fitar dashi akan Fatima.
Kusan ban yadda da maganar su ba saina shirya mana tafiya nida Fatima a wannan lokacin zuwa India, nanma maganar d'aya ce domin har cikin Fatima sai da suka bincika min cewar lallai cikin nawa ne kumama namiji ne jinana ne. Saudiyya muka wuce nan ma saida suka gama binciken su amma duk maganar d'aya ce dan haka anan na zauna nayi addu'a-nayi addu'a tare da nuna godiya ta ga Allah. A lokacin jinake babu abinda nake kauna sama da Fatima da abinda ke cikinta.
Matana sune suka fara sheganta min yaro sabida suna ganin aisu basu haihu ba sun manta cewa Allah shine mai tsara komai kuma a sanda yaso. Sai da mukai masifa dasu harma nayiwa Bilkisu saki d'aya sannan suka saduda suka bari alokacin ne nayi musu bayanin duk abinda ke faruwa tare da musu bayanan da likita yayi min a lokacinma harna basu zabi cewa duk wacce ke bukatar haihuwa to tayi min magana na sallameta sabida kadda na shiga hakkin su. Amma sai suka nuna zasu ci gaba da zama dani.
A lokacin da aka haifi Haidar kowa sai ya kara tabbatarwa da cewa lallai yaron jinina ne domin beyi kama da maman shi ba dani yayi kama kamar nayi kaki sai dai ya dauko farar fatar mamarshi domin tafini fari nesa ba kusa ba. Nasami haihuwa Ruma a lokacin da na fidda rai da samu shi yasa nayi shagali iyakar shagali sannan na saki kudi sosai aka yi taron suna.
To nidai bazance ga abinda ya dinga faruwa ba a tasowar Haidar sai dai dole tasa na kai Fatima wani gidana sabida a lokacin tace in dai ban raba musu gida ba to wallahi gidan su zata tafi, gashi nayi-nayi ta gaya min menene matsalar amma taki, dole na kaita wani k'aramin gidana. A nan Haidar ya taso ba sai nace komai ba akan kulawar da yake samu sabida ban had'a sonshi da komai ba. Shekaran shi goma na fitar dashi waje karatu, sai dai dawowar shi ne mummunar kaddarar nan ta afku.''
*MAMAN KHADY*ππ»ββ
[4/2, 11:15 AM] Re@lπ K@usyπΉ: πππ *RUMANA* πππ
Na
*MAMAN KHADY*ππ»ββ
(Mk)
*HASKE WRITER'S ASSOCIATION*π‘
(Home of expert and perfect writer's)
Page 6
Kai tsaye b'angaren sauran abokan zamanta ta nufa hankali a tashe, razana tayi sosai lokacin da taga babu kowa a babban falon. Wayarta ta jawo ta danna musu kira d'aya bayan d'aya akan gatanan a babba falo tana jiransu. Mata ne mugayen mata suna da tsananin kishi tsakanin su amma sai suka had'ewa mahaifiyar Haidar kai, har sai da sukai yanda suka yi suka rabata da gidan bayan sun nakasa mata yaro.
Sunayin tarayya wajan ganin sun ruguza shi Haidar d'in gaba d'aya wannan dalilin ne yasa lokuta da dama suke danne kishin su, ammafa ko wacce cikin zuciyarta akwai wani mugun nufi dake makale wanda inda ko wacce zata samu dama tofa sai inda karfinta ya kare, amma a haka bazaka tab'a ganewaba domin ko wacce ta iya takunta.
D'aya bayan d'aya suka dinga shigowa cikin parlourn ko wacce taci gayunta sai kamshi ke tashi kai baka ce akwai wani mugun nufi a cikin zukatan suba. Hajiya bilkisu ta dai-daita nutsuwarta hanci a sama tace.
''Kun kuwa san meke shirin faruwa cikin a gidan nan?'' Hajiya saratu ta yatsina fuska tare da cewa.
"Babu abinda muka sani Bilki sai dai idan ke zaki gaya