Showing 1 words to 3000 words out of 24634 words
*JALLI JOGA*
NA
MAMAN AFRAH
FCW
Page 1️⃣➡️2️⃣
Inna da Lami ne suka fito daga ɗaki cikin sanɗa, kallon ƙofar Yaya Lado suka yi wacce take hanyar ƙofar gida ganin ya ɗan karo ta saboda sanyin ruwan saman da aka wuni ana yi, dan yana dawo wa daga masallacin ishsha'i ya shige ɗaki. Hakan ya basu ƙwarin gwiwar yin bayan gidan dan ba zai yi wu su bi ta ƙofar gida ba kasancewar ɗakin Yaya Ladon a hanyar fita daga gidan yake.
Lami ta taka duron da suka kifa ta haura katangar, ta dira wajen santsi na barazanar warɓar da ita ta daddage bata faɗi ba, Inna ma cikin ƙarfin hali ta taka ta hau duron tana damƙe baki da haƙoranta ƙafafunta na karkarwa ta ɗane katangar, tare da maƙalƙale katangar wacce take a jiƙe da ruwan sama, tamkar wutar lantarki ta kama mutum haka Inna da damƙe katangar hannayenta da ƙirjinta suna kan katangar ƙafafunta da fa miƙa waje za ta dira sai reto suke basu dira ƙasa ba. Hannu Lami ta sanya ta riƙo cikin Inna daga bayanta ta taimakawa Innar ta sakko. Babu batun jira wai an ɗaurawa karya zani haka suka fara surfa sauri tamkar za su ci da ka, duk da caɓalin ruwan amma a haka suke bi suna kewaye caɓali.
Tun da suka fara tafiya Inna take sufa a laka, dan daga ta ga Lami ta tsallake waje sai ita ma ta ce fafur ta wajen za ta bi dan haka kuwa sai su shiga kokawa da caɓalin laka, ƴar tafiyar da suka yi a hanyar faɗuwar Inna a laka ta yi bakwai jikin nan nata sharkaf yake da ruwa da laka sai tsiyaya take tamkar yaro ya saki fitsari a tsaye. Dan wani wuri da ya yi caɓali da yawa tana taka wa takalminta silifas ya ce bai ga ta fitowa ba haka Inna ta shiga jan katanar takalmin amma babu yadda ta iya ta sille su ta barsu a wajen Lami tana mata dariya dan ta ce ba za ta tsaya ciro takalmi ba su ɓata lokaci.
A haka suka ƙaraso wani gida mai ƙatuwar kwata, wanda yake kusa da gidan Malam Ashiru daga hagu. Lami ta daddage ta tsallake kwalbatin Inna tana zuwa sai da ta ɗora ƙafarta ta dama za ta tsallaka ya zamana ƙafafun duk sun tale kwatar na tsakanin ƙafafun Inna Uwani, tana son tsallakawa ta yi taga-taga aikuwa santsi ya ja ƙafar Inna da babu takalmi ta tafi suuuuuu ji kake tunjum Inna ta kamo kifi. Dariya ce ta ƙwacewa Lami da ta waiwayo dan har ta yi gaba, ganin Inna kwance cikin ruwan saman da ya cika kwatar maƙil, sa kan kake hangowa tana ƙifƙifta idanun tana tamkar wacce kishiya ta kama ta da satar kwanan ɗakin miji, duka uban jikin ya lume sai kan kawai kake hangowa tana rangaɗa shi tamkar tsohon najadu ya ji kalangu.
Dakyar Lami ta taimaka wa Inna ta fito, kayan nan sun yi jargwaf sai rawar ɗari take kasancewar kishi kumollan mata sai Inna bata damu da jiƙewar ba haka Lami ta cigaba da tafiya cikin sassarfa, Inna kuwa sai take tafiya a hankali.
"Haba Inna maimakon kike gudu-gudu sauri-sauri tafiyar larabawa amma kin tsaya a baya kina tafiyar kamar ƙwai ya fashe miki a ciki"
"Haba Lami ya kike so in yi da raina ne, wannan sauri da kike ina dalili ina ɗan mafari duk ƙwaurina ya gaji, kina gani tafiya kaɗan sai santsi ya niƙa ni da ƙasa, ga jikin tsufa amma sai daɗa saurin muke sai kace wanda za mu tashi sama"
"To shikenan ki yi ta tafiya a hankali, wanda bai ji bari ba ai ya ji hoho! Ke da za a kaiwa amarya yanzu, amma duk ƙoƙarin da nake miki bakya gani"
"Yi haƙuri ƴar jikallena Lamisa, na sani amma tun da kina ganin bana sauri bari in ɗaga ƙafa... Kafin Inna ta kai ƙarshen maganar santsin lakar ruwa ya ɗauketa sai da ta yi gaba ta dawo baya ji kake timmm ta rafku da ƙasa, wani ƙara ta saki a wahalce ta ce
"Wayyo kwankwasona, duk faɗuwar nan da nake ji nake tamkar an sa inji za a murɗe mini kwankwaso, haka kawai in je in karye a banza Malam ya ji daɗin cin amarcin a...
Bata ƙarasa ba Lami ta katse ta da jaraba
"Wai Inna so kike Malam ya shiga ɗakin Duduwa, kin ga idan ya shiga sai mu koma gida kin ga mun zo a sadaka za mu koma a alakoro, bayan kin san ke da kika yi yaji wajen sati uku bakya nan babu wanda ya yi bikonki na taimake ki zan mayar da ke ɗakin ki na miki alƙawarin kazar amarcin da Malam zai kai wa Duduwa ke za ki cinye amma kike sanya tafiya kaɗan sai ki zube a cikin laka tamkar tsohon ginin da ruwa ya duka to ƙur'anin Allah ba a bori da sanyin jiki" Tana gama faɗar haka ta cigaba da tafiya. Haka Inna ta daure ta tashi ta bi bayan Lami duk da ta lura yarinyar tana sauri ga wani uban duhu dan ma da hasken farin wata sai dai wani lokacin yana shiga cikin gajimare amma haka suka ƙaraso, gidan Malam Ashiru mai almajirai suka nufa inda nan ne gidan Innar shi ne ta yi yaji dan Malam zai auri ƙawarta Duduwa daga can bayan gidan suka tsaya.
"Inna kalli dangan karan da aka sake sabo dal taɓɗi lallai sai kin yi da gaske in ba haka ba sunanki soriye ba ma sore (Sorry) Ba a gidan nan" Cewar Lami tana ƙarewa sabon dangan kallo ta farin wata. Wata ajiyar zuciya Inna ta sauke tana jin zuciyarta na suya, ga faɗuwar da ta yi har lokacin kwankwasonta kamar ba a jikinta ba yake, hannu ta sanya ta goge hawayen kishin da ya gangaro mata tare da jan hanci ta ce
"Ɓalle shege mu wuce ai wallahi Ashirulle ya ɗakko ruwan tafasa kansa"
"Inna sabon dangan karan za a ɓalle?"
"I mana ai dama ƙarsheb tika tiki tik"
Lami bata yi wata -wata ba ta saka wani murɗigegen icce ta shiga buga dangan, sai da ta musu kofa (Ƙofar ficewa) Sannan ta shige, duk tana karcewa da karan amma dan kudura sai da ta shige.
"Duƙa Inna, ki shigo a hankali, yi dibara kar ki je ki buge ƙoƙon baya" Ta faɗa cikin raɗa.
Haka Inna ta daddage ta kutso ta cikin karan amma tana zuwa saitin ƙugunta ya maƙale. Haka Lami ta kama hannayen Inna ta shiga janyota tamkar ta samu gugan rizabuwa. Inna kwa faɗi take
"Haba Lamisa jani sannu a hankali mana tsautsayin gaban auren Malam kar in mutu in bar Malam, yo kar ki girgiɗe mini kwankwaso bikiji ba idan kika fisgi hannun nan nawa tamkar birin da aka ɗaure a ƙugu har wani garrrr nake ji wallahi ba dai azaba ba...
Wata irin fisga da Lami ta yi wa Inna hakan ya sanya Inna damƙe bakinta dan tana buɗe bakin ihu ne zai fito asirinsu ya tonu.
"Lami kwarankwatsa dubu mazaunai na za su huje a banza" Cewar Inna tana sakin kuka.
"Wai Inna mene ne hakan? " Lami ta faɗa cikin tsiwa.
"Lamisa wallahi wata zarɓeɓiyar ƙaya ce ta shige mini ɓarin ɗuwawuna na dama, kuma ki duba har ɗankwalina ma ya maƙale haɗe da beɗon kitsona (Jelar kitso)"
Da sauri Lami ta duba ta cire ɗankwalin kitson kuwa dakyar ya ciro Inna tana kukan azaba marar sauti dan kar a ji su.Ƙayar ma dakyar ta fita dan Inna har wani ƙara ta saki jin tamkar za a cire gefen ɗuwawun.
Kafin Innar ta dawo hayyacinta Lami ta samu nasarar fisgota daga tsakiyar dangan karan sai gata kwacar yashe a gefe guda tana maida numfashin wahala.
"Wannan wadaƙa da kwankwasona yake sha yau Allah dai ya sa kaffara ce amma na ga ta kaina ni na ga jalala auren karuwa ba sadaki" Inna ta faɗa tana mirginawa ta tashi zaune tana riƙe da ƙugunta da hannu biyu sai murza wajen ƙayar take tamkar wacce likita ya yi wa allura ya ya ce ta murza. Ganin Lami ta yi adungure da shala sai gata tsaye daram a kan ƙafafunta dan da ta janyo Innar faɗuwa ƙasa ta yi, hakan ya sanya Inna tuntsurewa da dariya ƙasa-ƙasa amma kuma wata wawiyar guɗa da wata tsohuwa ta rangaɗa ɗaya daga cikin ƙawayen amarya ita ce ta sanya ƙirjin Inna ya bada wani dammmm wata uwar harara ta aikawa yankin da take jiyo tashin ƙaran guɗar.
"Inna a duƙe fa za mu tafi kar a ganmu kuma kar ki tsaya tsegumi ki ce za ki hango ɗakin amaryar ko ƴan kawo amaryar aje a ganmu"
"Haba Lami yo ni ina ma na ga nutsuwar kallonsu ina ta kaina ai ni burina bai wuce in ga Ashirulle a ɗakina ba ya kawo kazar nan da rabona da in ci tun ta amarci shekara saba,in ina ga har da ɗoriya"
"Inna wai yau ba Malam ɗin ba Malam Ashirun sai Ashirulle kamar wata atamfa"
"Ke rabu da ni namiji ɗan jakar uba n, ba ɗan goyo bane in da sunan shantu ma zan kirawo shi ƙyaleni, ke Allah ko da sunan garken dabobi na kira shi aradu sunan ya dace da shi"
A haka suka shiga tafiya a dudduƙe tamkar masu ƙusumbi a baya. Har suka isa kewayen Inna da ke can ƙarshen gidan.
Babu mukulli dan haka suka rasa yadda za su yi.
"Lami shiga ta taga(Window) Ki ɗakko mukullin a cikin samirar da nake ajiyewa kin san da na tashi tafiya yaji ban tafi da mukulli ba shine shi kuma mai gidan ya kulle wato ma ko lissafin dawowata ba ya yi wai shi nan mai amarya" Lami bata tanka wa Inna ba haka ta kama windown ta haye har tana karcewa da langa-langan jiki haka ta dira ta ɗakko mukullin ta buɗe suka shige cikin ɗaki. Da sauri Lami ta kunce harshen zaninta ta ɗakko wani ɗan magani a ƙulle, kwanon sha ta ɗakko ta ɗauki wani allo mai rubutu a jiki ta zuba ruwa ta wanke allon maganin ta zuba a ciki ta gwauraya, ta juye a ƙaramin kofi. Inna tana kallonta bata ce mata komai ba dan ta san hatsabibancin Lami babu wanda ta bari kuma ta san duk abin da ta saka gaba sai ta ga bayansa dan haka Inna bata taka mata birki domin ita ma tana taimakonta.
Ficewa ta yi riƙe da kofin da ta zuba rubutun ɓangaren amaryar ta nufa mata tsofaffi suna ta hayaniya. Wata tsohuwa da ke carara guɗa ta ɗan yafito gyalenta ta ce
"Wai ga wannan rubutun in ji Malam a bawa amaryarsa, na taryar ango ne ta sha" Karɓa tsohuwar ta yi ta shige ɗakin ta kaiwa amarya Duduwa a take aka ba amarya sai da Lami ta tabbatar sun ba amarya Duduwa dan ƴar tsohuwa ta kwankwaɗe magani wata tana a bincika a tabbatar Malam ɗin ne ya aiko aka gwasileta ana cewa waye zai iya aikin Malamai.
Bayan ƴan kawo amarya sun watse aka bar amarya zaune a bakin gado, dan tun kan su tafi take jin jikinta duk ya saki babu ƙarfi duk idanunta sun mata nauyi. Iya Duduwa ta hangame baki tana wata doguwar hamma Lami da ke laɓe a gefen window tana kallonta a take ta fara gyangyaɗi tun tana yin a zaunen har ta dawo tana yin wanda dai ta gyangyaɗa goshinta ya kusa kaiwa kan cinyarta, a haka gwaggwaron nata na ɗankwalin kanta ya ɓingire daga kan baka hango komai a kan sai kitson zanen hausa wanda har da ɗan gaba aka mata an saka tsakiya(beat) Gyangyaɗin da take sai kusa tuntsurawa sai ta dawo ta zauna har dai ta tuntsuro daga kan gadon timmm ta faɗo ƙasan ɗakin amma cikin bacci mai nauyi bata san ma ta yi ba, a ƙasan ta kwanta ta yi ɗai-ɗai ta shiga sakin munshari tamkar an shaƙewa rago wuya.
Lami hannu ta shiga ɗaga wa Inna da ke can tsaye tana jiran umarni daga Lami, cikin sauri ta taho dan lokacin har ta saka wasu kayan ta shafa turare dan Malam ya tabbatar amaryarsa ce Dududuwa Inna tana zuwa suka shiga ɗakin amarya Duduwa, Lami ta kama haƙarƙarin Duduwa ta ɗagota ta kama hannayenta daga baya, baki sake take kallon Inna da ke bin ɗakin da kallo tana taɓe baki.
"Allah suturu buƙui in ji kishiyar mai doro, kuma haka tara dai in ji kishiyar mai mageduwa" Cewar Inna tana hararar an kayan da aka jera wa amarya wanda tsofaffi ne kuma dama Innar ta san su a gidan mijin Duduwar na baya dan su suka jera mata, dan tun kayanta ne na auren fari, kafin mijin ya mutu yanzu shekaru bakwai. Wata uwar harara da Lamin ta dokawa Inna ita ta ankarar da Innar da sauri ta kama ƙafafun Duduwa bayan ta sakar mata mugun ranƙwashi a wannan kan fa makitsiyar ta gama taltale shi sai ƙyalli yake Duduwa da ke bacci magashiyan ta saki jiki tamkar gawa, Lami ma hannu ta saka ta dungurewa Duduwar rantalelen goshinta haka suka cicciɓota suka fito da ita daga ɗakin, Inna da ke riƙe da ƙafaffun duduwa sai faman doka mata harara take haka suka ƙarasa ɗakin Innar Inna ta saki ƙafafun Duduwa ji kake jaɓak ta zube kamar kayan wanki, sannan Inna ta zaune Dududuwa.
"Maciya amana da kika aure mini mijina, daga ke har shi kun ci amana wallahi, ai Ashirullen ya fi kowa ya ɗauki fuska kamar ta tsulan biri" Cewar Inna tana tashi daga kan Duduwar ta ƙara zaunawa jaɓar sai da ta yi haka sau uku ta saka hannu ta sakar mata wani uban ɗaɗe a mazaunai. Lami banda dariya babu abin da take.
"Kishi kumallon mata Inna, yanzu mai mazaunanta suka miki?"
"Ke rabu da ni yo wa ya sani ma ko mazaunan nata ya gani ya ƙyasa, ke baki san namiji ba kina dai ganin mazaunan nan nata masu kama da fantalo to wallahi sai ya ɗauki hankalinsa ai wallahi Ashiru ya ci amanata" Inna ta faɗa tana share hawayen takaici.
" Yo Inna ta yaya zai gani shi da ba gani yake ba Rabu da su Inna daga shi har ita sai mun gasa musu aya a hannu
"Haba Inna kar fa Malam ya shigo ya same mu ki kama ta mana daman ke da za ki kamata kika je kika saka ledoji kika ƙulle hannaye kamar wanda za ki kama wani mushen arne"
"Yo ba gwara mushen arne ba Lami kar ki manta fa jikin kishiya zan kama haka kawai in je in kama jaraba, a hakan ma sai faman harararta da nake idanuna har ciwo suke saboda zarosun da nake"
"Wa ya ga ban san ana yi ba kunu a maƙota ita da take bacci, kuma ma kr dai aminiyarki duk garin nan waye bai san ki da Duduwa ba, ku zauna a ɗakin nan naki kuke hira kuna tafa wa abinku amma yau har kike ƙyanƙyamin taɓa jikinta sai ka ce wata mai cutar kuturta"
"Humm Lamisa ai da kika ce to tun da tsoho bai ji kuyar hawa jaki ba ai jaki ba zai ji kunyar kayar da shi ba, yanzu ai dole in ji ƙyanƙyaminta tun da yanzu turaka ɗaya za mu ke shiga ni da ita, yo kama-kama za muke yi da ita (Sharing ɗin miji) Inna ta faɗa tana kauda kai gefe.
Haka dai suka kama ta ƙiiii rabin jikin da mazaunanta suna janƙasa, ƙasan gado suka ɗaɗɗauke fantekoki suka samu buhun hatsi suka saka amaryar Malam a ciki kai kaɗai suka bari a wajen buhun suka tura ta ƙasan gado. Ɗakin Innar suka mayar suka kulle kamar ma ba a buɗe ba.
Ɗakin amarya suka koma Inna ta zauna a bakin gado, tamkar ita ce amaryar.
"Sai Innata, ai indai ina raye ba za ki yi maraici ba, kuma ba za ki yi kuja va dole na share miki hawaye" Lami ta faɗa tana dafa kafaɗar Inna da murmushi ya kasa barin fuskarta.
"Na sani Lami ai shi ya sa nake alfahri da ke, ga shi yanzu kin share min hawayena, mun saka sabuwar amarya a buhun hatsi ni kuma na maye gurbinta dama duk wanda ya ce tukunyar wani ba za ta tafasa ba tashi ko zafi ba za ta yi ba, yanzu saura kazar amarci"
"Ita ma ke za ki ci"
Malam Ashiru suna tsaye da abokinsa Malam Liman suna ɗan taɓa hira amma Malam Ashiru kunnensa yana ƙofar gidansa yana so ƴan kai amarya su watse ya je gun Duduwarsa masoyiyarsa, duk da ba gani yake ba amma kuma yana ankare.
"Kai Malam Ashiru wannan kazar amaryar da ƙamshi take wallahi ƙamshinta duk ya cika mini hanci da cikina"
"Aikuwa Malam Liman haka za ka ɗau na annabawa kake haɗiyar miyau dan kazar nan ko ƙafa ba zan iya baka ba, ka san dai ta amarya ce ni ma rabona da cin gashin kaza tun ta amarcina da Uwani wannan ma kuɗin larabar da nake karɓa wajen almajiraina, na tara na laraba takwas shi ne na siyo mu yi Allah kaimu"
Allah kaimu kuma?"
"Allah kaimu mana, ina nufin Allah kaimu lokacin da zan kuma yin wata amaryar in siyo kazar a ci da ni"
*JALLI JOGA*
NA
MAMAN AFRAH
FCW
Page 3️⃣➡️4️⃣
"Taɓ gaskiya dai Malam Ashiru kana taro aradu da ka, yanzu a nan gaba har kana ganin za ka iya ƙaro wata matar? Bayan yanzu wutar da za ta kunnu gidanka baka tanadi ruwan kashe ta ba, ka aurowa Uwani ƙawarta Dududuwa aikuwa ka ɗakko ruwan dafa kan ka, ka san dai dukansu ba kanwar lasa bane"
Wata dariya Malam Ashiru ya yi ya ce
"Malam Liman ai da kake ganin mata kawai ka barsu, ni yanzu dai gabaɗaya hankalina yana kan kazar nan da kuma