Showing 12001 words to 15000 words out of 24634 words
yanzu za ki mana adungure bakwai kafin ki tafi" Ya faɗa yana sauka daga bayan Innar.
Wani irin sagewa bayan Inna ya yi har ƙara ta ji ƙashin bayanta ya yi.
"An gama indai adungure ce amma a caɓalin nan zan yi?"
"To ko na kwanta ki yi a kaina?"
"Ni shegiya Uwani wace ni, ƙaryata ta sha ƙarya" Ta faɗa tana wani bashi girma. Bai ce komai ba dan har lokacin ma ya kasa tsayuwa da ƙafafunsa dan kayan mayen basu saka shi ba.
"Tashi ki duddungura"
"Yanzu kwa" Ta faɗa tana tashi tsaye duk ƙafafunta a sage suke, tashin da ta yi ganin saurayin tsaye a gabanta sai ƙirjinta ya cigaba da lugude dan babu yadda za ta yi amma da tuni ta ari na kare(Ta gudu) Amma sanin duk gudun da bil adama zai yi ba zai tserewa aljani ba sai ta daure ta tsaya duk da ita ma tsayuwar tata bata da banbanci da tsayuwar saurayin domin kuwa ita ma tangal-tangal ɗin take saboda karkarwar tsoro da ƙafafunta suke yi, ga zaninta da je barazanar kuncewa sai ɗaurawa take amma sai kuncewa yake yaa neman sumɓulewa daga tsantsar tata amma saboda gudun yin tsirara gaban aljannu sai ta kama zanin daga tsantsa ta ƙanƙame.
"Tsohuwa za ki iya fara wa"
"To,to,to, ta ina zan fara?"
"Tambayata ma kike?"
"Ni kaza, ba haka nake nufi ba ina nufi daga kaina zan fara adunguren ko kuma da mazaunaina zai zan fara"
Wata dariya saurayin ya saki jin abinda ta faɗa dan har ya hango yadda za ta yi adungure ta mazaunai.
"Ki yi daga mazaunan, amma ba wai a nan za ki tsaya ba kuna dungurawa kina tafiya daga kin yi bakwa sau ki tashi ki tafi da ƙafafunki kuma ko da wasa kar ki kuskura ki ce za ki waiwayo"
"An gama ranka shi daɗe na gode" Ta faɗa tana koma wa ta zauna tana tunanin ta inda za ta fara adungure fa mazaunan bata ma san dalilin da ya sa ta tambaya ko daga mazaunai za ta yi ba sai dai ta san hakan bai rasa nasaba da tsoron da kuma gudun yin ba dai dai ba dan duk a ruɗe take. Haka ta fara dungurawa amma dakyar ta yi ɗaya saboda wahala amma ya za ta yi a haka ta cigaba da tafiya shi kuma yana tsaye yana kallonta, tana ta dungurawa tamkar kunkuru haka Inna ta koma sai da ya ga ta yi biyar ya fashe da wata dariya da ta sa Inna ta fara dungura wa kafin ta ɗago ta sake juya mazaunan ta dungura ba ƙaramar wahala take sha ba da a ce ba a ce ba aljannu bane suka saka ta ba da babu yadda za a yi ta iya yin ko sau ɗaya ne. Yana gama dariyar ya fara waiwayen wajen kogon kukar jin wani ɗan motsi daga wajen cikin hanzari ya bar wajen dan shi ma a tsorace yake da wajen kuma rass yake ba wai a buge yake ba kawai tantiranci ne dan ya tsorata tsohuwar dan ya san dai babu wani abin kirki da zai sa ta fito tsakiyar daren nan ba. Shi ma daga yawo yake suka je wani ƙauye kallon wasa da samari ke gabatarwa shi ne da suka dawo abokin nasa ya ajiye shi a hanya ya tafi a machine ɗin dan dare ya yi yana shirin yin hanyar gidansu ya hango Inna tana tahowa tana waƙa shi ne ya fara maganar ƴan shaye-shaye.
Inna kuwa tana ta dungurawa har ta yi bakwai amma saboda tsabagen ruɗewa bata ma san ta yi bakwai ɗin ba, dan haka bata dakata da adunguren mazaunan ba har sai da ta yi goma sha uku lokacin ta gama jigata dan haka sai kawai ta kwanta a tsakiyar hanyar dan ƙarfinta ya ƙare. Amma tsoro da fargabar kar aljannu su biyota su mata aure da jinsin su, su kaita birnin sin haka ta tashi zaune ta cigaba da jan ɗuwawu a ƙasa har Allah ya kaita gidan Yaya Lado amma kasancewar ba da saninsa suka fita ba dan in ya sani ma sai ya musu faɗa hakan ya sa ba za ta bi ta ƙofar gidan ba wajen shiga cikin gidan bare ma ƙofar a rufe take da sakata daga ciki.
Lallaɓawa ta yi ta je inda suka hauro ɗazu ta katanga dan dama an ce ta inda aka hau ta nan ake sauka ha Inna ta kama katangar nan tana ƙi-ƙi-ƙiƙitun hawa amma cikin rashin sa'a ta kasa hawa da yake a hayowa ma sai da suka taka duro bare ɓa sai da Lami ta taimka mata ta samu ta sakko dan haka yanzu kuwa babu duro kuma babu Lami bare ta ciccigata.
"Yauwa na ga ta kaina, kaza garen tone-tonenta ta tono wuƙar yankanta, yanzu ni Uwani ina zan saka kaina babu kowa a hanyar nan hallaw idan mutanen ɓoyen nan suka biyo ta hanyar nan haka za su ci mutuncina in banda tambaɗa ma kai da ɗuwawunka a ce ba za ka yi tusa ba sai abu ya zama jidali, haka kawai Allah ya halasta yin abu amma su haramta yin tusa haka kawai a ce wai za a toshe mini ƙofar fitowar kashi wannan jalala da na gani yau ai tafi gaban wasa, ga shi ban san lokacin zuwan lami ba bare ta taimaka mini tana can suna artabu da Malam ko ya aka ƙare" Ta kai ƙarshen maganar tana sakin dariyar mugunta tunowa da ta yi da yadda bakin Malam ya koma suntumeme. Sai da dariyar ta tsagaita sannan ta tashi ta shiga riƙetun hawa katangar dan ta san muddin aljannun nan suka kamata a wajen nan in har suka dawo suka tarar da ita to kashinta ya bushe.
Katangar ta kama da hannun biyu ta ɗare sai dai ƙafafunta da take son hayowa da su daga ta ɗare su jikin katangar suke zamewa saboda ruwan da ya jiƙata. Amma dan ƙarfin hali ɓarawo da sallama Inna bata daina yunƙurin hawa ba dan ta san bata da mafitar da ta wuce wannan. Tana cikin hakan ta kusa hawar da ƙafar tata kawai sai inda ta kama ƙasar jikin katangar ta ɓantale gabaɗaya Inna ta iyo baya idanunta duka biyu a zare tamkar za su faɗo sai ga Inna kwacar a ƙasa hannunta duka biyu riƙe da ƙasar da ta guntule daga jikin katangar saboda ruwan da aka yi katangar ta jiƙu sosai in da har wani ɓangare na katangar duk ya zagwanye.
"Wayyo ni Uwani matar Malam Ashiru kakar Lamisa, ya Allah ka raba bawa da wahala wai gwauro a teburin mai shayi" Ta faɗa tana jin tamkar ta yi ta rasgar kuka da ƙarfinta yadda jama'a za su ji su kawo mata ɗauki. Sai dai kash babu damar hakan domin kuwa sakin kukanta da ƙarfi tamkar tonuwar asirinta ne dan ta tabbata muddun maganar abinda suka yi wa Malam da Duduwa ya koma kunnen Malam to tamkar ta saka kuɗinta ne ta sayi takardar sakinta da domin ta san dai babu fashi wai tusar asubar fari ga gauro dan farilla ne tusa a masallaci sai Malam ya yanke igiyar da ke tsakaninsu in ma bai yanke duka ukun ba ita kwa ina za ta kai wannan abin kunyar dan ta san har jikokin Lami ba za su tsallake gorin abinda suka yi ba idan har asirinsu ya tonu to ta shigegen dan lafinta za a gani tun da Lami yarinya ce.
"Inna! Mai kike yi a nan har yanzu baki shiga gida ba?" Cewar Lami tana kama hannun Inna ta ɗaga ta daga kwancen da take tana kallonta cike da mamakin ganin duk ta fita hayyacinta ga kayan jikinta jargaf da ruwa da ƙasa.
"Ke dai bari Lami labarin mai mugun tsawo ne ke dai tun da kika tarar da ni da rai kawai mu yi mu bar wajen nan dan idan aka zo aka ganmu zai zama mun yi tufka da warwara kuma abin da muka yi zai zama fallasa auren bashi" Cewar Inna tana kallon Lami da take haƙi da alama ita ma gudu ta yi kodai mugun sauri.
Haka Lami ta kama Inna ta ciccigata tana cewa
"Wallahi Inna ki riƙe gagam kuɓa kar ki saki nauyinki domin katangar nan ta jiƙu da ruwa sosai karki je ki zuba mata nauyinki ta je ta faɗi ta rufta da ke in shiga uku"
"Ai ban bata nauyi ba Lami na riƙe kayana, ke dai taimako ki cicciɓani in dira wannan abin da kike jihadi ne"
Haka aka cicciga Inna ta haye ta taka duron da yake wurin dan dama a wajen suka barshi sai da ta ganta tsaye a kan ƙafafunta duk da gwiwoyinta na mata raɗaɗi saboda duk sun ɗan sassale a rarrafen da ta yi na yi wa saurayin nan doki.
"Kula maza Lami mace mai kamar maza kwarin ne babu an buga an barki Lami jikar Uwani bada kanki a sare ki je gida ki ce ya faɗi" Ta faɗa tana kallon Lami da ta yi wa katangar Yaya Lado hawan ƙawara dan ita ko da ta hayo bata hau kan duro ɗin ba ta dira a ƙasa. Tana wani hura hanci ita ala dole kirarin da Inna ta mata ya shigeta.
Sai da suka gyara duron kamar yadda yake sannan cikin sanɗa suka lallaɓa suka shige ɗakin nasu bayan sun ƙarewa ɗakin Yaya Lado kallo suka ga yana nan yadda yake alamar bacci ya yi masa kamun kazar kuku dan babu alamar ma ya fito daga ɗakin har suka dawo. Ɗakin rufo suna shiga Inna ta kunna fitila tana kunna wa suka shiga taka rawa suna kwaso shoki na cikar burinsu da suka yi wa kazar amarcin Duduwa kankat.
*JALLI JOGA*
NA
MAMAN AFRAH
FCW
Page1️⃣3️⃣➡️1️⃣4️⃣
"Inna wai kuwa kin ga yadda Malam duk ya diririce har da shiga akurkin talo-talo kin san Allah Inna sai na ga ya saje da su sosai na gan shi kamar jimina" Lami ta faɗa tana dariya har da riƙe ciki itama Innar dariyar take cike da mugunta. Sai da Lami ta bata karkaf yanda komai ya wakana har yadda ta fito ta yi dibara ta rufe kafar dangan ya koma tamkar ba a huda shi ba.
"Ai kin min dai dai Lami kuma kin haifu aradun Allah ai maganin ɓeran daji sai ɓeran birni, kuma Duduwa ya kamata ta ƙara rabbatarwa duk wanda ya ci tuwo da Uwani to alal haƙiƙa miya ya sha, miyar ma miyar kuka tsalala marar kauri wacce ita kanta kukar kaɗin bata ishi miyar ba. Da in banda ɗan adam ma butulu ina Duduwa ina auren mijina a tunanina ko wata Duduwa ta ga za ta ci amanata ta hana ashe dai gaskiyar ƴan magana da suka ce makashinka yana tare da kai, kuma Allah ya bayyana mini Duduwa baƙar fura ce ana gama ta mai gida na mutuwa, yo banda ma duniya ba amana da gaskiya ai aradu Duduwa ta mayar da ni ƙaramar danga mai daɗin tsallaka, amma ba komai mu je zuwa wai mahaukaci ya hau kura" Inna ta faɗa cike da takaicin abinda Duduwar ta mata dn tana ganin ma ko me ta yi wa Duduwa bata huce ba dan gani take duk abinda ta mata bata rama ba.
"Barta Inna ai za ta gane shayi ruwa ne , dan dama duj wanda kika ga ya yaga rigarsa to tabbas ya san inda zare ke tsada! Dan sai ta ɗanɗani kuɗarta a gidan nan daga ita har wanda ta kawo ta gidan, yanzu dai suna can ƙasan gado ko ya wasan zai kaya Allahu a'alamu, ai alƙur'an karambanin akuya ya sa ta leƙa ɗakin kura" Cewar Lami suna tuntsurewa da dariya har da yafawa abinsu.
"Ah Lamisa yau na tari aradu da ka, ai yau na ga bin umarni waiwayen makaho, ni na ga balbalalin bala'i muraran wai ganin kama ruwan siriki!
wai ni Uwani ni ce na ɗauki aljani a bayan nan nawa ni da tun da uwata Laure ta haifeni ko gamo ban taɓa yi ba amma sai gashi yau aljani ya buɗe mini ido, abin takaicin ma bai wuce da yake cewa wai ni ce mai akori kura dan ya rainani wai ni za a toshewa mafitar kashi, kuma ko in yi yaya, wai har da cewa za a ɗaura mini aure yo da ubansa za a ɗau...
Hannun da Lami ta saka ta rufe mata baki shi ne dalilin da ya hana fitowar ragowar maganar tata. Lami kuwa sai wani kallon saman ɗakin take tana wani kallon ko ina na ɗakin tamkar wacce ta yi wa sarki ƙarya aka kama ta.
"Ke dalla ja can, rabu da ni in faɗi son raina meye na rufe mini baki kamar wanda zan faɗi saɓo" Inna da ta saka hannu ta fincike hannun Lami daga bakinta ta faɗa tana hararar Lami dan so Inna take Lami ta barta ta kai ayar labarin da take bata.
'Inna, labarin aljannu fa kike, kin manta su suke ganinmu ba mu muke ganinsu ba, da kike wannan maganar to idan kika ga yanzu ya tsago bangon ɗakin nan ya shigo fa ya za ki yi d...
Ai Inna bata bar Lami ta ƙarasa maganar ba ta shiga zazzare idanu dan sai a lokacin ma ta lura da ɓaran-ɓaramar da ta yi nan take ta ja bargo ta lafta a jikinta ta rufa har kanta tana karanto ayatul kutsiyyu. Lami dariya take wa Inna ganin harta tsorata tabbas Inna kura ce ga tsoro ga ban tsoro.
Lami dai ta samu cire kayanta ta canja Inna kuwa ko motsi ta kasa bare a yi zancen tashi a canja kaya, juyin duniyar nan Lami ta yi da ita a kan ta tashi ta cire kayan amma Inna fafur ta ƙi ta kwanta da jiƙaƙƙen kayan tana ta faman karanto ƙulaƙuzai har bacci ya yi awon gaba da ita.
*MALAM*
Tun da ya shige ƙasan gadon nan ko motsi ba ya yi saboda yadda ya tsorata, a haka yake tamkar wani matacce shi dai ba bacci yake ba amma fa banda numfashi babu abin da yake aiki a jikinsa, numfashin ma kaɗan-kaɗan yake yi gudun jar ya saki numfashin duka aljannu su ce ta yi laifi.
*DUDUWA*
Ita dai bata san ma wainar da ake toyawa ba, saboda baccin nan da aka sakata na dolen doliya sai da gari ya yi haske shaaaa sannan ta ɗan fara motsi Malam da ke ƙasan gadon jin ƙusur-ƙusur sai ya ƙara shiga tashin hankali wanda ƴan magana suke yi wa kirari da wanda ba a sa masa rana. Haka ya daddage yana addu'a har wani yawu yana zubowa daga bakin saboda ba ya iya rufe bakin dan wani lokacin ma ta baki yake ƙarasa numfshinsa. Duduwa da ta ɗan fara falkawa sai ta ji ta a ƙudundune hakan ba ƙaramin ɗaga mata hankali ba ya yi ba.
"Allahu akbar kabiran, Allah ka sa na zo a sa'a Allah ka rabani da macijan kabari wayyo ni Duduwa ai da na san ma sa'ina ya yi da ban yi auren cin amana ba ashe ma kwanakina sun zo gargara ban sani ba gashi ko amarcin ban ci ba mala'ikan mutuwa ya ɗakko raina, shikenan na barwa Uwani Malam ɗinta wayyo ni Allah" Cewar Duduwa a zuciyarta jin ƙafafunta da uban jikinta ƙunshe cikin buhun hatsi duk a tunaninta mutuwa ta yi aka saka ta cikin likafaninta. Amma kuma abinda ya bata mamaki bai wuce yadda take jin hucin numfashinta ba yana fita da yake kuma ƙasan gadon da ɗan duhu duk da gari ya fara waye wa sai bata ganin hasken a ƙasan gadon. Idanunta ta buɗe warai sai ta ga suna juyawa har ma tana ɗan hango alamar haske daga ɗan nesa da ita. Motsawa ta shiga yi sai kuma ta ji kasarsar ɗin buhun da take ciki ko kusa bai yi kama da laushin likafani ba gashi dai har hannayenta a ciki suke cikin ɗaurewar kai ta shiga kiciniyar fitowa da hannayenta har dai ta fito da su har lokacin tana mamaki ƙafafunta ta fitar tana daga kwancen ta yunƙura za ta tashi zaune amma sai ta ji ƙum ta buge kai da yake ƙasan gadon ba zai isa ta tashi zaune ba.
Malam kuwa tun sanda ya ji motsi a kusa da shi sai ya yi saranda yana daga kwancen nan rubda ciki ya cigaba da jin motsin nan a kusa da shi kusan ma dab da shi dan haka sai tsoro ya ƙara cika shi dan zatonsa aljannun nan ne dai suka dawo duk da ya san zuwa lokacin gari ya fara wayewa duk da ba gani yake ba dan a kan kunnensa ladanin masallacin kusa da gidansa ya rangaɗa kiran sallah, kuma yana jin lokacin da abokinsa Malam Liman ya ja sallar, shi da kullum shi ne a sahun farko wataran ma shi yake yin ladanci amma yau ga shi ko alwala bai samu yi ba bare sallah kai jikinsa ma ba a tsarkake yake ba, banda uban fitsarin da ya sha jabgawa wani kan wani dan ko a ƙasan gadon ma yadda ƙirjinsa ke bugawa haka fitsari ke ƙwace masa yana fita da kaɗan-kaɗan dan bashi da ƙarfin hana fitsarin fitowa dan ya yi fitsarin a ƙasan gadon ma sama da sau bakwai har mamaki yake yi yadda yake fitsarin tamkar wanda ya haɗiyi famfo amma hakan bai bashi ƙarfin gwiwar daina jin tsoro ba dan shi ba gani yake ba idan aljannun ne a kusa da shi.
Sai da ta lura sosai sai ta ga alamar mutum a kusa da ita ƙafa ta miƙa ta ɗan shureshi. Malam da ke tsaka mai wuya yana cikin halin ƙaƙanikayi jin an zungureshi sai ya yi zaton aljannun nan ne dan haka sai jikinsa ya ɗauki wata irin karkarwa a take haƙoransa suka shiga haɗuwa kafkafkaf. Duduwa ma ganin hakan sai tsoro ya dirar mata dan ta