Showing 6001 words to 9000 words out of 24634 words
a nata bakin. Ƙafafu ya shiga haurawa tamkar wanda yake gangarar mutuwa.
Bakinta da abin yajin naman da ta ci dan haka abin sai ya haɗe wa Malam biyu wai shege da hauka. Tun da ta damƙi laɓɓan Malam take ta faman tsotsa ta ƙi saka wa Malam wani raɗaɗi da zugi ne suka ratsa bakinsa har ƙwaƙwalwarsa yake ji dan haka ya shiga tura Inna amma Inna ta yi ƙememe ta ƙi sakinsa dan haka sai ya shiga zullo yana haura ƙafa tamkar wanda ake cire wa rai dan shi kaɗai ya san azabar da yake sha. Inna da take masa abin da mugunta musamman da ya ce wai Duduwa cw mace su sauran suna mata ne bayan ita kaɗai ce matarsa tun auren saurayi da budurwa tun kan Allah ya saukar masa da makantar da ya samu daga ciwon ido, soyayya da kula wa kai har da alƙawarin ba zai mata kishiya ba amma sai yanzu tsofai-tsofai da su zai auro mata ƙawarta aminiyarta Duduwa, Duduwar da cacakurukuci cikon banci ce amma har yake ikirarin ita ce mace. Kishi ya saka Inna ta ƙara damƙe laɓɓan har da ɗan gatsawa da haƙori. Azaba ta saka Malam sakin fitsarin wuya sai da Inna ta tabbatar ya wahaltu tare da jigata sannan ta saki laɓɓan aikuwa Lami ta taƙarƙare cikin muryar Duduwa ta ce
"I lobiyu wujiga-wujiga Malam"
Malam da bai gama jin raɗaɗin ba wani irin haushin amaryar tashi ya ji dan shi dai bai ga kyan wuri a kunnen jaki ba dan ko kusa wannan abin da aka masa bai yi kama da soyayyya ba soyayyar ma wujiga-wujiga.
Amma gudun kar ran amarya ya ɓaci tun da an ce amarya bata laifi ko ta kashe ɗan masu gida dan haka ya mayar da ƙwallarsa ya ce
"Na gani Dududuwa, nikwa na ga ƙauna muraran gata kina nuna mini" Ya faɗa amma cikin ƙarfin hali dan shi kaɗai ya san abin da ya ji a kiss ɗin da ta masa.
Inna kuwa kallon bakin Malam ta yi sai ta ga ya ƙara tsini a kan da kumburin ya ƙaru tamkar an hura balo wata dariya ce ta kusa ƙwace mata amma sai ta danne Lami ce ta kashe murya cikin kwaikwayon muryar Duduwa ta ce
"Bari in ƙara maka na san ka ji daɗin abin dan da ganinka har ka shiga yanayi irin yanayin da angwaye suke shiga ranar da suka tare da amarensu na shauƙin ƙauna" Lami na gama faɗar haka Inna ta ƙara miƙa hannu ta cafko wuyan Malam, ai Inna bata ankara ba sai ganin Malam ta yi zumɓur ya miƙe tsaye kamar an tsikare shi.
"Lafiya angona ina za ka je kai da muke tsaka a filin soyayya kafin mu tsunduma kogin ƙaunayya"
Sai lokacin ma Malam ya gane wautar da ya yi ta tashin tsaye, dan haka cikin wayancewa ya koma ya zauna yana sakin wani murmushin yaƙe wanda ya fi kuka ciwo ya ce
"Ni dai ba sai kin sake mini irin wannan ba bakya ganin yadda bakina ya koma kamar na zomo kar gobe almajiraina suke kallon bakin suna mini dariya kin san yara da sheƙiyanci bare kuma ni ba gani nake ba" Kallon bakin nasa Inna ta yi aikuwa ta ga ya koma kamar na zomon dan har ya fi na zomon ma tsawo.
"To mu ci naman" Lami ta faɗa cikin muryar Duduwa.
'To ya ce dan shi kwata-kwata ma ba ya gane cewar wacce ke kusa da shi ba ita ce ke magana ba duk da ita ma Lamin a kusa take da su amma sanin daga shi sai amarya a gidan kuma bai taɓa tunanin ko a mafarki Inna da Lami za su masa wannan ƙanƙanci ba.
Haka yake zaune zugum kamar an ajiye turmi dan naman ma sai ƙaran taunar Inna yake ji dan shi babu halin ci ga yawunsa banda tsinkewa da taruwa a bakinsa babu abinda yake sai dai ya haɗiye dan babu yadda zai yi naman kazar da tun ba yau ba yake saƙa yadda zai masa cin wulaƙanci dan a yau tun koko da ya sha da safe shi ma dakyar ya sha kokon dan tun da ya fara kissima ɗanɗanon kazar a bakinsa yana tunano yadda zai ji zauzau a bakinsa to fa duk wani abu da zai sa a bakinsa sai ya ji lami shataɓ amma kuma ga shi yanzu babu yadda zai yi ya ci naman cikinsa sai kira ciroma yake dan babu komai a ciki sai yunwa.
"Kai angona amma ɗan garki mai nama ya iya gashi, kazar nan dan daɗi kamar kunne na zai tsinke" Ya ji muryar Lami a matsayin ta Duduwa ta daki majiyar sautinsa wani takaici ne ya baibaye shi, dan shi ina zai adar da baccin makaho tun da ba cin naman ya yi ba, banda guda ɗayan nan da ya danna zai masa cin mun daɗe bamu haɗu ba amma abu ya ƙi da daɗi sai fito da shi ya yi wanda shi bai san ma inda ya faɗi ba dan yana riƙe a hannunsa amma azabar da ta ziyarce shi lokacin da Inna ta yi wa laɓansa kamun gugan mai janyo ruwa a rijiya hakan ya saka bai ma san ya jefar da shi ba.
Inna kuwa abinsu bajau ita da jikarta, idan ta ɗau naman ɗaya sai ta miƙa wa Lami ɗaya, a haka suka ci suka ƙoshi dan kazar ƙatuwa ce dan haka sun ci nama sun more abinsu ai da suka cinye tas Inna ta zuba ƙasusuwan a cikin ledar.
"Amarya idan kin ci ki ɗaure sauran ki bani ledar in saka a fanteka zuwa tsakiyar dare idan na falka in bakin nawa ya sassauta mini sai in ji dan baki ji yadda cikina ke kiran ciroma ba sai ƙara dake ƙululu-ƙuluuuuu, idan kuma bai sace ba da safe sai in ci dan jinsa nake ya yi wani luhuhu kamar an busa balan-balan" Malam da duk takaicin yadda taunar Inna fa cika masa kunne ya faɗa dan kar ta je ta yi wa naman cin mugunta ta rage masa kaɗan.
"Allahu akbar kabiran, Allah sarki angona, na Duduwa bada kanka a sare ka je gida ka ce ya faɗi, ai ni da na ga bakinka a kumbure na ɗauka ba za ka iya ci ba dan gabaɗaya na gama yi wa naman nan aiki sai dai idan ka siyo mana na gobe idan kana da rabo bakin ya sace sai ka ci...
"Duduwa! Kika ce kin cinye naman duka ina nan zaune gaho kika cinye sai ka ce wanda kike zuba wa buhu ba a ciki ba, to wa ya ce miki naman kaza koko da ƙosai ne da za ki tunanin gobe ma kawo wa zan yi yo idan dai ba fara zan sa almajirai su kamo miki ba idan sun je gona yin ciyawa su kawo ki silala a siyo ko majan murtala (20) Ki soya da lan manda(Gishiri) Ki maida yawun bakinki ina na ga wani kuɗin kaza kin san rabon da na ci naman gashashshiyar kaza to aradu tun ranar da aka kawo Uwani gidan nan tun ta amarci shekaru saba'in da ɗori" Cewar Malam da ya harzuƙa wani takaici da haushin amaryar tasa ya turnuƙe shi jin wai ta cinye naman har tana ikirarin gobe zai samo bayan wannan ma kuɗin larabar da yake karɓa a wajen almajirai ne yake tarawa ya suyo naman da shi.
*JALLI JOGA*
NA
MAMAN AFRAH
FCW
Page7️⃣➡️8️⃣
"Fara fa ka ce Malam?"
"Haka na ce"
"Ikon Allah na zaune ya faɗi, yanzu amaryar taka ce sai ka ce wata amaryar alade za ka ce a kamo mini fara, farar ma wai in soya da manjan murtala (20) Kuka ba ma in saka yaji ba sai ka ce wai in sa manda(Gishiri) Sai ka ce wata tsohuwar mayya"
"Yo da ban, matar da kike hallaka kazar amarci a lokaci ƙanƙani ki ƴar kunyar nan ta amare babu da yanga da suke yi sai kawai ki cinye" Ya faɗa a ransa a fili kuma sai ya ce
"Yo ai kin san yanzu rayuwarce sai a hankali Duduwa, komai tsada yake in ma ba ni ba mai ƙarfin hali ɓarawo da sallama waye zai kai wa amarya kaza a wannan zamanin mulkin Tinubuyya ( Tinubu) Mulkin da ake ganin har gwara Bahariyya sau dubu, to yanzu ko saurayi ne ya auri budurwa kifi yake kai mata a matsayin kazar amarci"
"Kifi fa ka ce Malam?"
"Kifi mana, yo kifin ma ba ta samu ba ina laifi wai bikin ƙanwar kishiya ka bada jaka guda (200) To wajan masu tuyar kifi angwaye ke zuwa su bada kuɗi a naɗe musu kifi sadin tanƙwashe biyu,sai su siyo gurasa ta sha ƙuli-ƙuli da albasa to idan suka riƙo ledar ƙawayen amarya ba za su ji ƙarnin kifi ba bare su yi wa ƙawarsu amarya gorin ba a kaoo kaza va dan ƙamshin ƙaragon gurasar nan sai su ji tamkar ƙamshin kaza, idan suka tafi sai ango ya buɗe su ci kayansu babu wanda ya sani sai ya ce bakinta alekum ko ƙawaye sun zo neman sauran kazar amarci ta ce mage ta ɗauke"
"Taɓ" Lamu ta faɗa da muryar Duduwa.
Hannu ya miƙa ya warto ledar hannun Inna ya shiga buɗawa yana lalume aikuwa banda ƙasusuwa babu abin da ya ci karo da su a cikin ledar dan ƙasusuwan ma duk yawu ne a jiki alamar an gama tsotse su.
Haka ya saki ledar ta faɗo daga kan gadon yana jin wani takaici da haushi kamar ya yi kuka, yana tunano yadda ya yi ta saka rai a naman amma ga shi ko tsoka ɗaya bai haɗiya ba, ya tuno yadda abokinsa Malam Liman ya yi ta haɗiyar yawu saboda ƙamshin kazar amma ya hana shi ashe dai shi ma ba zai ci ba.
"Wallahi sai na yi Allah kaimu" Ya faɗa yana sakkowa daga kan gadon ya shiga lalumen ƙasa. Inna da Lami da ido suka bi shi suna son ganin abin d yake so ya yi. Aikuwa haƙarsa ta cimma ruwa domin kuwa ya yi nasarar ɗora tafin hannunsa a kan ƙatuwar tsokar da ta faɗi a hannunsa wacce ya saka a baki taƙi ciyiwa. Haka ya ɗakkota yana ta faman faɗin.
"Allah na gode maka ashe dai da rabona ai dama rabon kwaɗo ba ya hawa sama" Ya faɗa yana tasowa riƙe da naman ya zauna a kan gadon ya ce
"Riƙe mini nan amarya idan na kwanta ki miƙo mini dan yau ko ana ha maza ha mata sai na ci naman nan" Ya faɗa yana miƙa wa Inna ta karɓa. Inna da Lami sai ganin suka yi ya kwanta a kan gadon ya yi reran ya miƙo hannu ya ce amarya ta bashi naman Inna ta bashi aikuwa ya shiga cira tsokar nan sai da ya cira ta gida uku yana daga kwancen. Ɗaya bayan ɗaya ya shiga jefa wa cikin hanga-mamman bakinsa da ya buɗe duk da yana jin raɗaɗi amma ya sha alwashin sai ya ci naman. Haka ya dinga saka wa cikin dibara yana cinyewa dan wani ma idan ya jefa haɗiye wa yake ba tare da ya tauna ba. Sai da ya cinye duka ya tashi zaune yana lamushe baki yana suɗe kumburarran bakinsa da yaji ya ɗan taɓa. Sai lokacin ya ji ɗan dama-dama a ransa amma da ransa ƙuna yake na rashin cin naman duk da kaɗan ya ci ba haka aka so ba ƙanin miji ya fi mijin kyau amma dai wanda za shi sama ya taka leda haƙiƙa ya ci ƙarfin tafiya.
Bayan ya ya tashi daga zaunen da yake, ya miƙe tsaye yana wani baza babbar rigarsa, aka cire huta tare da rigar gabaɗaya kusa da Inna ya matsa yana rattabo mata kalaman soyayya duk zatonsa Duduwarsa ce amaryarsa.
Lami ganin haka sai ta fice daga ɗakin, Malam Ashiru haka ya shiga gabatar da sunna da Inna sai da ya ci amarcinsa son ransa. Haka suka fito da shi da Inna za su je bayi yin wanka sai yabon Duduwa yake yana kushe Inna Uwani bai san cewa da Innar yake tare ba dama ƴan magana sun ce rashin sani ta fi dare duhu.
Dama Inna da Lami sun gama shirya yadda komai zai kasance dan Lami ta ce Inna za ta tafi gida ita kuma za ta yi muryar da za ta tsorata Malam dan Lami babu muryar da bata iya yi. Dan haka sai ta cewa Inna ta tafi ita za ta biyo bayanta idan ta gama abin da za ta yi. Malam suna fitowa sai Inna ta sakar masa sandarsa da ta ɗauki wani takalminta ɗan madina a ƙofar ɗakinta ta lallaɓa ta fita ta kafar da suka shigo sai dai wannan karon bata sha wuya wajen fita ba.
"Amaryata ina kika yi wai, ai yau take sallah gaskiya na ji daɗi da kika aure ni Duduwalleta" Ya faɗa yana wani washe baki har kunne amma kuma sai ya ji shiru can sai ya ji wata murya mai abin tsoro ta ce
"Mu ne mutanen ɓoye mun ɗauke amaryarka mun tafi da ita kogon aljannu" Lami da ta maida muryarta ta ƙaton namiji ta faɗa tana daga can gefe idanunta a kan Malam.
Malam sakin sandar hannunsa ya yi, a take jikinda ya ɗauki karkarwa, ƙafafunsa suke neman kasa ɗaukan gangar jikinsa wani fitsari da ya matse shi yana so idan sun je bayin zai yi a take ya shiga bin ƙafafunsa lokaci ɗaya ya yi jargaf da shi dan dama ya cire wancan wandon da ya yi fitsari a ciki yanzu ma wannan ɗin ya jiƙe kamar an sheƙa masa ruwa.
Hannu ya fara bazawa alamar lalume tun da ba gani yake ba kuma ya saki sandar tasa da ta kasance ƴa jagorarsa, gabas ya yi sai ya dawo ya yi yamma, hallaw ya yi arewa ya rasa ma ina zai yi duk ya ruɗe.
"Muna so ka fito da jelar biri a mazaunanka dan mun ga kamarku ɗaya da gwaggwon biri in ba haka ba yanzu za ka ji ka yi sama kana tashi kamar tattabara" Muryar nan mai ban tsoro ta katse Malam. Tsabar ruɗanin da ya shiga sai kawai ya shiga zagaya inda yake tsaye tamkar dai yadda ake ɗawafi.
"Ya Allah ka fito mini da jela jela zankaɗeɗiya" Faɗa yake cikin muryar kuka dan shi gabaɗaya ma ya sare tun da an ce an ɗauke Duduwa kuma shi kaɗai ne a gidan yau ai sai ta Allah.
"Dakata!" Aka katse shi da muguwar tsawa, ita kanta Lamin sai ta danne dariyarta ganin irin halin da Malam ɗin ya shiga. Malam kuwa da sauri ya ƙame a waje ɗaya tamkar soja haka ya dakata da abin da yake yi cikin bin umarni dan yadda yake jin muryar a kusa da shi ya san komai zai iya faruwa da shi.
"Tun da baka fito da jele ba ka fito da cikin wata tara a jikinka"
Da hanzari Malam ya saka hannu biyu ya dafe cikinsa, yana jin wani iri a ransa in har aka ce ya fitar da cikin wata tara a jikinsa aikuwa an tashe shi tsaye domin kuwa shi dama tsigi tsila ne babu ko ƙibar kirki a jikinsa bare a yi zancen timbi har ta kai ga samun cikin wata tara, shi da ko tafiya yake tamkar iska za ta kwashe shi ta watsar haka yake.
"Fiddo ciki ko ƙusumbi"
"Hasbunallahu wa ni'imal wakil ni Ashiru na ga ta kaina yau, Allag gamu gareka ɓarawo a hannun mata" Cewar Malam yana karkarwa dan maganar cikin nan da ta ƙusumbi ba ƙaramin dulmiyar da tunanin Malam ya yi ba a take ya ɗauke hannayensa daga kan cikinsa ya miƙa ƙeyarsa ya taɓo bayansa inda ƙusumbi yake fitowa nan take ya hango shi a idanun zuciyarsa yadda zai koma kamar aljani matsawar aka fito masa da ƙusumbi ya san ba ƙaramin aikin aljani bane ya fitar masa da ƙusumbin.
Da sauri ya zube gwiyoyinsa a cikin caɓalin ruwan nan na sama ya haɗe hannuwa ya fara roƙo da ban haƙuri. Lami kuwa a hankali ta matsa kusa da Malam ta miƙa hannu ta dafa bayansa saitin inda ƙusumbi ke fitowa mutum. Wani irin ɗauke wuta Malam ya yi cike da bala'in tsoro a take ya ji ya fara kokawa da numfashinsa dan ji ya yi tamkar za a ɗauki ransa ne.
"Yau na ga ikon Allah ɓatan nono a ƙirjin budurwa ni Ashiru ni ne yau a daren amarcina da Duduwa durƙushe a ƙasa cikin ruwa aljani yana dafe da bayana ya Allah ka sanya kar ya fitar mini da ƙusumbi jama'ar gari suke guduna" Ya faɗa a ransa hawaye suna ambaliya a fuskarsa.
"Za mu sanya maka sharaɗi"
"To, to, to, ku faɗa ko mene ne zan muku amma kar ku mini cikin wata tata ko ƙusumbi ku taimake ni k...
"Ba ma son yawan magana"
Ɗiff Malam ya yi yana danne kukan da ya taho masa.
"Ko da wasa idan amaryarka ta faɗa maka magana dangane da daren yau ka ce to dan za ta iya iyuwa ba da ita kuka zauna ba da ɗata daga cikin jinsinmu ne dan ita mun ɗauketa kar fa ta nuna maka bata san da wani zance ba ka yi musu" Lami ta faɗa cikin muryar da take tsorata Malam ɗin da yake tunanin aljannu ne a tsakiyar daren nan, dan ta yi hakan ne dan kar Duduwa ta ce ba ita ta ci nama ba ya zargi wani abu duk da ta san tunaninsa ba zai taɓa bashi su ne suka zo suka masa wannan ƙanƙanci ba.
"An gama" Ya faɗa yana wani gyaɗa kai da sauri da sauri.
"Za mu barka amma da cewa na yi zan fito maka da ciki na wata tata da ƙusumbi lokaci guda in barka a haka sai kuma in motse kan ka ya koma kamar na ƴan ruwa in mayar maka da ƙafafu kamar zabirar wanzan, kan ka kuwa sulsul zwi dawo wa ya ga sulluwaye"
"A mini rai tuba nake"
"Ka tashi ka kama gabanka" Lami ta faɗa da muryar tana ɗauke hannunta daga bayansa sai kuma