Showing 9001 words to 12000 words out of 24634 words

Chapter 4 - JALLI JOGA FREE Book Complete by Maman Afra .txt

23 Jan 2025

4306

ta saka ƙafa ta dungure shi. Ai a gigice Malam ya tashi yana karanto salatin annabi kafin ya kai sai ya kamo alamnashrah duk ya duburburce sai miƙa hannu yake yana lalume abinka da makaho ba gani yake aba. Caɓal-caɓal kake ji Malam yana faɗa wa cikin guntayen ruwan da yake tsakar gidan tsabar gigicewa hanyar kijin talo-talonsa da yake kiwo ya nufa wanda tun la'asar ɗin fari ya sa aka rufe su duk dan riɗin zuwan amarya bayan ba a rufe su sai da magariba.


Yana zuwa bum-bum kake ji yana ta gwaruwa da jikin langa-langan kejin can dai ya samu ya ɗora hannunsa a kan ƙofar kejin, duk tunaninsa ƙofar ɗaki ce amma bai san wane ɗaki bane dan shi tunaninsa ko wane ɗaki ne ma ya je burinsa kawai ya ceci ransa daga aljannun nan kar su masa cikin wata tara ko su fito masa da ƙusumbi.




Ga sun ce za su mayar masa da kansa irin na ƴan ruwa ya san kuwa kan ƴan ruwa tamkar ƙwarya ko tulu haka yake, bare ma sun ce kan nasa taltal za su masa ai kawai aljani sak dan ya san idan suka mayar da shi haka to daga ranar sai dai ya tashi daga suna Malam Ashiru ya koma Malam Ifritu. Lami tana can gefe tana dariya har da riƙe ciki har wani sunkuya wa take saboda yadda dariyar ke cin ƙarfinta amma marar sauti take yi.


"Hahahahhhhahh" Ta saki wata ƙatuwar dariyar da ta saka Malam tsabar ruɗewa har amsa kuwwa ya ji tana masa. A take ya ja ƙofar kejin wacce tana da ɗan faɗi dama kasancewar talo-talon na da ɗan girma. Yana cin nasarar buɗewa sai kawai ya afka cikin kejin ji kake burum ya shige ciki amma kuma rabin uban jikin ne ya shige kasancewar cikin babu wani space sosai. Yana shige talo-talon suka tsorata a take suka fara karo da juna suna neman wurin gudu dan duk ya hargitsasu. Fat,fat,fat kake ji ƙaran gwaruwar junansu.


Malam kuwa yana jin yadda suke gwaruwa shi da ba gani yake ba sai ya ƙara tsorata kasancewar an ce dabbobi suna ganin aljannu sai ya yi tunanin aljannu ne suka biyo shi, shi ya sa da suka gan su suka tsorata, wannan ya sa ya ƙara tsorata dan ya san tabbas abinda ya tsorata dabba to ina kuma ga mutum.
*JALLI JOGA*


NA


MAMAN AFRAH


FCW

*JALLI JOGA*


NA


MAMAN AFRAH


FCW
Page9️⃣➡️🔟


Ƙara kaimi Malam ya yi wajen totsuwa dan so yake ya ji shi ya shige cikin ayarin talo-talon ko ba komai ai ya yi ɓadda kama a cikinsu idan aljannun sun ƙaraso ya samu rangwame. Totsuwar da ya fara yi wani cikin kijin yana so ya shige duka jikinsa aikuwa wani talo-talo ya cako bakin Malam wani zafi Malam ya ji a bakin nasa da yake a kumbure har lokacin kafin ya gama jin raɗaɗin wani talo-talon ma ya cako hancinsa sai kawai Malam ta saki kukan takaici kuka mai sauti ma kuwa saboda yana tunano wai shi Malam Ashiru mai almajirai da mutane suke girmama wa almajirai suna jiran ya bada umarni su aiwatar wai shi ne yau a cikin kejin talo-talo har talo-talon suna cakon bakinsa da hancinsa. Kukan da ya saki hakan ya yi dai dai fa zuwan Lami wajen aikuwa ta daddage ta ɗaga hannu ta daki jikin langa-langan.


"Wayyo ni Malam Ashiru na ga ta kaina, wbin ya mini yawa shege da hauka ashe dai kejin talo-talon da na shigo a zatona ɗaki ne, kuma da na gane keji ne tunanina na tsira ashe dai akwai ya babu ne kakar wajen uba, an yi ba a yi ba juyin fatar fara" Ya faɗa a zuciyarsa yana sakin kukan takaici yana jin ina ma dai zai ɓace ɓat domin ya tsira daga tsoron aljannun nan da ya cika masa zuciya. Ƙara buga kejin Lami ta yi ai sai kawai Malam ya iyo baya ya fito daga kejin dan ya gane babu mafita gwara ya nemi wata mafakar. Yana fitowa ya yi taga-taga zai faɗi bugun da Lami ta yi wanda ya fi na farko shi ne ya saka Malam ya bazama da ɗan gudu-gudu cikin sa'a sai ya faɗa kewayen Inna Uwani lalamen ƙofa ya fara aikuwa ya ji ta rufe da ɗan kwaɗo. Sai lokacin ma ya tuno ashe fa Innar bata nan dan haka sai ya shiga lalamen windown cikin ikon Allah ya samu dama takalmansa tuni ya warɓar da su wajen gudun famfalaƙin ceton ransa daga aljannu .


Yana jin ya ɗora hannunsa a windown sai ya fara kiciniyar hawa aikuwa ya ɗane ya maƙalƙale buuuummmmm ɗin da ya ji na ƙaran kejin da Lami ta taɓa dan so take ya samu mafaka dan gidan Yaya Lado take so ta tafi ta ba Inna labari. Ƙaran nan ya sanya Malam hayewa windown bai ti wata-wata ba ya hantsila aikuwa da ka ya je, yana faɗawa da ka sai ya kwanta lifet a inda ya faɗa ya yi rubda ciki cikin faɗuwar da gabansa yake dufdufduf ya fara magana


"Innahu min sulaimana, wa innahu bismillahir rahmarnir rahiiiim, Alamnashra lakasadarak, tabbat yada abilahabin watabbu, maaa agnee anhu maluhu wama kasab, wadduhee, wal laili iza saje, inna a'a ɗaina kalkausar" Haka Malam ya shiga rattabowa idan ya fara wata kafin ya ƙarasa sai ya sake ta ya kama wata surar idan ya yi aya ɗaya, biyu sai ya saketa yana cikin wannan halin na rayuwa ko mutuwa Lami ta zo ta buga ƙofar Innar dan ta san dole zai nemi mafaka, kuma dai mafakar ta san ba za ta wuce ƙasan gado ba dama kuma so take ya je wajen amaryarsa Duduwa da ke ƙasan gadon a cikin buhu idan ta falka sai ya yi tunanin aljannu ne suka kaita ƙasan gadon tun da dai ya san shi ma ta window ya shiga ɗakin domin ƙofar a rufe take bare ya yi wani tunanin da ban duk da ta san ko wace irin ƙwaƙwalwa gareshi ba zai taɓa gano abin da suka shirya ba sai dai in su suka faɗa da bakinsu.


Malam cikin ƙarfin hali da rashin ƙarfin jiki dan duk jikinsa ya mutu saboda tsoro haka ya ƙuƙuta ya fara jan ciki yana tafiya da baya da baya, a haka ya ƙarasa wajen gadon na Inna sai wani nishi yake sakarwa tamkar wanda aka shaƙewa maƙoshi. Ƙafafun ya miƙa ƙasan gadon sai ya shige yana ta faman faɗar .


"Lahaula wala ƙuwwata" A haka ya shige har kansa lifet ya kwanta tamkar babu rai a jikinsa yana ji a ransa bai taɓa shiga tashin hankali wanda ya gigitashi sama da na yau ba.


*INNA UWANI*


Tun da ta fito daga kafar karan dangan gidan Malam take jin ta a sama sai wani shauƙi take tana ta saka wa Lami albarka irin yadda ta ringa faɗi tashi har burinta ya cika dan tana ganin dai ga shi ta shiga gidan Malam salin alin ta fito ta kuma ci naman kazar amarcin Duduwa sannan kuma ta murƙushe amaryar a cikin buhun hatsi.


"Allah ka yafe mini ai wallahi na yi hakan ne saboda auren cin amanar da aka yi mini tana aminiyata ta san sirrina amma ta aure mini miji, shi ma kuma dan rashin ta ido yana so ya nuna mini iyakata da kuma halinsu na maza ya manta da babina ina can na yi yaji sati ɗai-ɗai har uku amma ko ta kaina bai bi ba yana nan zai kwashi ganimar amarci da Duduwa, aikuwa baka kwashi amarci da sabuwar amaryarka Duduwa ba ka kwashi ganimar amarci da matarka Uwani" Inna ta faɗa tana sakin wata bazawarar dariya haɗe da wata gyatsa da take jin gabaɗaya cikinta a cike yake dam-dam.


Tana cikin tafiya ta ji ta yi wata uwar sufa a cikin laka tagar-tagar ta yi za ta faɗi dakar ta yi nasarar tsayawa a kan ƙafafunta eata ajiyar zuciya ta sauke ganin bata kai ƙasa ba. Ƙafafunta ta zare daga cikin takalman nata da suka maƙale a cikin lakar ta saka hannu ta saka ta ɗauki takalman tana yin gaba abinta dan ita yanzu jinta take warai babu wata damuwa sai annashuwa.


Cigaba ta yi da tafiya ko tsoro bata ji sai ma waƙar soriye da take rerawa har wani ɗan rausaya wa take yi, dan har tsaya wa take tana rawar ittigi a hanya idan ta yi, ta ƙara yi sai kuma ta cigaba da tafiya abin ta dan wani nishaɗi take ji wanda bashi da misali.


"Mai akori kura tsaya a nan in hau ka kaini gida" Wani matashi da ya shawo kwanar da Inna take yana tafiya yana haɗa hanya ya faɗa cikin muryarsa da ya sha ya bugu. Inna kuwa tsaya wa ta yi ganin ya sha gabanta ta shiga waiwaye ko za ta ga akori kurar amma sai ta ga wayam babu kowa sai su kaɗai daga ita sai shi dan farin watan da ya haske duniya daga sararin samaniya shi ne hasken da suke amfani da shi wajen ganin juna dan daga ita har shi babu mai fitila dan basu ɗakko ba ita da Lami suna sauri a haka suka taho. Ƙoƙarin kewaye shi ta shiga yi dan ta tafi abinta fan ta ga babu mutane kar ya je ya libga mata shegen duka a zo ana A'i ina indo. Shi ma cikin rashin kuzarinsa ya ƙara tare gefen da Innar ta yi za ta wuce.


"Haba kai kuwa jikana bani hanya mana in wuce in tafi ka tare ni a tsohon daren nan"


"Ke!Tsohuwa waye jikan naki, kuma da kike batun tarewa ai ni cewa na yi ki tsaya in hau akori kurar ki kaini gida"
Galala baki sake Inna take kallonsa wai jin ita ce za ta ɗauke shi a akori kurar sai dai kuma a take ta kawar da tunanin hakan duba da yadda yake a buge ta san kuwa shaye-shaye babu abinda ba zai saka ba tun da ba a hayyacinsa yake ba to dole ƙwaƙwalwarsa ,a ta nuna masa ƙarya.


"Ni fa a ƙafata nake tafiya ko gare-garen wasan yara babu a hannuna bare wata akori kura"


"Billahil lazi huwar rahmanu tsohuwa sai kin ɗauke ni, a kan me ga abin hawa zan tafi a ƙafa"


"Oh ni Uwani na dawo in ji ɗan yawon duniya ni ce abin hawan? TO ƙur'ani ni kaɗai ce singil fakitin buɗe magananka da kyau ɗan nan, ko dai ka yi makuwa ne?"


"Kin manta makau na yi ba makuwa ba, to yasin babu mai rabani da ke yanzun nan zan miki filla-filla yankan naman layya, ko in miki sala-sala"


"A'ubillahi haba kai kuwa ɗan nan sala-sala sai ka ce wata lemon fata"


"Kin ɗauki abin wasa, to ba wai duka zan miki ba aradu kalacin dare zan yi da ke dan wallahi yanzun nan zan kwaɓe in yi zigidir a nan in gurji amarci...


"La'ilaha ilallahu, muhammadur rasulullahi, S.A.W yanzu ɗan nan dan ka kwashe kayanka daga gaban ma'aiki tsofai -tsofai da ni za ka gurjeni sai ka ce wata rigar da ta yi dauɗa?"


"To shikenan kar ki sunkuya in hau bayanki bari ki ga aiki da cikawa" Ya faɗa cikin muryar buguwa yana kama wando. Ai da sauri Inna ta saki takalman hannunta ta zube a ƙasa gwiwa bibiyu ta duƙa irin yadda yara ke yin wasan doki, aikuwa saurayin nan bai yi wata-wata ba ya ɗaga ƙafa ya haye bayan Inna. Inna da ta ji tamkar an ɗora mata dakon tirela ta danne kukan da yake son fito mata.


"Ja mu je, bari in sa giya" Ya faɗa yana karkaɗa ƙafafunsa a jikin Inna irin yadda masu hawa jaki suke kaɗa wa jaki ƙafafu idan suna tafiya a kansa, giyar kwa da ya ce zai saka sai da ya daidaici kunnenta ya kama ya murɗa tare da lanƙwasa wa har sai da ta saki ɗan ƙaran azaba aikuwa Inna jin azabar da ake gana mata sai ta fara jan ƙafafun tana rarrafa wa dakyar saboda nauyin saurayin.




A haka suke tafiya shi kwa sai ƴar waƙa yake ya yi wa Inna sandan-dan a baya.


"Da wane shegen ya fito da ke a tsohon daren nan?"


"Daga gidana nake ɗiyata ce aka ce tana naƙuda ni kuma gozoma ce shi ne zan je can" Ta samu kanta da sharara masan ƙarya dan ta san muddun ta faɗi abin da ya fito da ita to tabbas zai iya mata tonon silili. Shiru ya yi bai ce komai ba a haka take tafiya dakyar ga santsin laka da yake jan gwiwarta da tafin hannunta ga nauyinsa a haka take bi ta cikin lan sauran ruwan da suke taru a hanya duk da zuwa lokacin ma ruwan duk ya janye ya shanye. Bai tanka mata ba sai dai ya cigaba da buga ƙafafun har wani is-is-is yake cewa irin yadda ake kiran tattabaru.


Sai da suka yi tafiya mai ɗan nisa ya kalli wata bishiyar kuka da k gefen hanya ya ce


"Ga gidana can a can za ki ajiye ni"


"Ina ne?"


"Gashi can ai logon kukar can nan ne ƙofar shiga gidana"

Wani sautin ƙululuuuuu cikin Inna ya bada a take jikinta ya shiga karkarwa lokaci guda kuma ta fara fitar da wata iskar tusa a jere a jere tamkar wata bodara. Dan ta san dai babu wani wanda zai ce gidansa a kogon kuka in ba aljani ba, a nan take ta fara tunanin kenan aljani ne a bayanta, amma haka ta daure ba ta ce komai ba amma har wata gudawa ta ji tana neman ƙwace mata.


Ɓuuwwwt sautin tusar Inna ya daki kunnen saurayin.


'Mene ne haka tusa kuma?"


"A yi haƙuri yallaɓai mai gidan kogo wallahi ba da sanina na yi ba suɓuce mini ya yi ban san lokacin da ta sufce mini ba"


"Duk kin sa dakarun rundunar aljannun da suke biye da mu a kan ababen hawansu suna buɗe baki za su haɗiye ki saboda kin ɓata ransu"

Ɓiiiɓiɓiiiit Wata tusar ta samu nasarar fitowa wata kan wata. Ga kuka marar sauti da Inna take gabaɗaya sai ta ji duniyar ta mata ƙunci tana da na sanin fitowa daga gidan Yayanta da tana can babu abin da zai da ta ɗauki aljani a gadon bayanta har rundunar aljannu suke binsu a baya. Sai ta ji dama bata je gidan mijin nata ba ta yi haƙuri ta jure.


"Ki riƙe tusarki kar ki ƙara yi wa mutane tusa a nan in ba haka ba za ki ga kin ɓace ɓat ko kuma a rufe miki ɗuwawu babu ke babu wata tusa bare kuma kashi sai dai ki ga ana yi" Ya faɗa cikin muryar ƴan shaye-shaye dan har lokacin a buge yake.




*JALLI JOGA*


NA


MAMAN AFRAH
FCW

Page 1️⃣1️⃣➡️1️⃣2️⃣


Jin ya ce za a rufe mata ɗuwawu ta daina tusar ma bare wani kashi, da sauri ta ɗauke hannunta ɗaya daga dafe ƙasa da ta yi. Miƙa hannun ta yi bayanta daitin ƙofar da tusar ke fitowa ta saka tafin hannun nata ta toshe ƙofar dan ta san idan har aka ce ta daina tusa da kashi ai babu lafiya yo ina za ta saka ranta a ce ka daina tusa da kashi ai ta san to kuwa akwai gagarumar matsala bare kuma a ce aljannu ne za su toshe maka ɗuwawu to a ina ma za a gansu bare a ce su buɗe to tabbas dole ta yi iya yinta dan ganin ta yi yaƙi da usjar tusar da take fitowa tana ƙoƙarin mata shamaki da yin kashi ma gabaɗaya wanda ta san ko likitoci ba lallai su iya ɓarke toshiyar da aljannun za su yi sai dai ta haƙura da yin tusa da kashi, idan kuwa haka ta kasance to tabbas ko abinci sai dai ta haƙura da ci tun da babu inda za a kasayar da shi.


" Yallaɓsi ai ita tusar da kanta ta yi kaɗan ta ci ƙarya ta kwana da yunwa ta ƙara ƙetara umarninka tajawarka lafiya ai na done kafar da tusar takw fitowa babu yadda ma za a yi ta kufce ta fito.


"Da dai ya fi tsohuwa mai rangwangwan, ga ki da tsoron jinsin aljannu kamar farar kura amma kuma kina fitowa tsakiyar dare lokacun da rundunar mu suke fitowa dan zuwa gidan biki da zuwa kasuwa ku kuma lokacin bil adama duk kuna bacci amma saboda kankanba kika fito, to yanzu da ke za mu shiga kogon kukar nan a yi shagalin bikin ɗan ƙundalo da ke"


Ɓiriɓiiiiiit Ƙaran wata tusar da iskarta ta zarce a kan hannun da Inna ta toshe ta fito abinta sariri dan ƙaran har ya fi na sauran tusosin da ta ɓurɓurka ɗazu.


"Hasbunallahu wa ni'imal wakil, amma ke kuwa tusa mai ya kai ki wannan ɗanyan aiki an ce ki daina fitowa su yallaɓai basa son jinki amma kika fito gaba yo ai sai ki bari idan na koma gidan Yaya Lado na shiga ɗaki sai ki yi ta keto hazo kina fitowa haba amma dan jan jafa'i za ki...


"Ai kin zo kenan a nan za a sama miji a haɗa shagalin bikinki da na ɗan ƙundalo a kai ki can birnin sin"


"Wallahi matar aure ce ni, Uwani ce matar Malam Ashiru mai almajirai na unguwar tudun tsira" Cewar Inna tana sakin kuka mai sauti.


"Yanzu kuma za ki samu cigaba ki auri Sarkin aljannu kin ga kin tashi daga matar bil adama Malam za ki koma matar mutanen ɓoye a mutanen ɓoyen ma.


" Wayyo Allah ni Uwani yau cuta ta ɗakko cuta akuya ta ɗakko akwatin miciji, dan Allah ku mini rai ku barni a jinsina wallahi ina da jikata marainiya bata da uwa bata da uba Lami ni kaɗai take da ni"




"To kin ci sa'a amma

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login