Showing 30001 words to 33000 words out of 60654 words

Chapter 11 - FEERYAL BOOK COMPLETE DOCUMENT by RASHEEDAT S DIRECTOR.txt

07 Feb 2025

6785

ta bayan kofar ya sa hanu ya d'au wata doguwar karfe, kana a hankali yashiga takawa cikin d'aki, yana rarraba ido cikin d'akin.
lungu da sako ya dudduba baiga komai ba.
kasancewar ba wani tarkace bane cikin d'akin. daga
makeken bed and bedside sai wardrobe manne a bango guda TV fridge sai doguwar kujera.
har cikin bathroom ya duba babu komai.
ya dawo cikin d'akin gaban gado ya tsaya, a hankali ya kai hannu ya d'auki pant d'in Feeryal, daya gani tsakiyar gadon,
wan daya tub'e mata ranar.
da alama dai tun bayan korar sa da akayi babu wanda ya shigo d'akin,
ko ma'aikata masu gyaran side d'in su ma basu shigo bedroom d'in sa ba.


Ya d'ago pant d'in yana kare masa kallo, sai kuma da sauri ya mannashi a fuskarsa yana wani irin shinshinarsa, yana wani lullumshe ido.
Ajeemal da shigowar sa kenan zai wuce bedroom d'in sa, ya hango kofar Zaraddin a bud'e, ya karaso bakin kofar.
can ya hangosa tsaye da abin da yake yi.


Da mamaki Ajeemal ke kallon sa, har ya karaso cikin d'akin Zaraddin bai san ya shigo ba, ya shagala da abun da yake yi.
"Zaraddin."
Ajeemal yakira sunan sa.
da sauri ya ware idanunsa tare da cire pant d'in a fuskarsa ya yi baya da hanun sa ya b'oye shi ta bayan sa.


"Kace baka cire mata pant ba, ta ya akayi wannan yazo nan?."
Ajeemal ya yi maganar yana kamo hannunsa daya b'oye ta bayansa.
da karfi Zaraddin ya fisge hannusa yana hararar sa
"Sai kuma aka ce maka nata ne wannan d'in, to sayowa nayi."
kai Ajeemal ya girgiza sannan ya ce
"Sabo da ka koma mace shiyasa ka siyo pant dan ka rika sakawa ba, Zaraddin kabi a sannu dai."
"Anki a bi a sannun idan nabi da gudun ma me ya dame ka."
kafad'a Ajeemal ya d'aga
"Babu ruwa na life d'in ka ne, amma abun bakin cikin dole a danganta ka da mu."
"To ku san yadda zakuyi ku goge hakan mana."


"Rabu dashi Ajeemal zo mu tafi ga Faisal can a mota mu yake jira, badai ka mance 9:30 zamu shiga class ba."
cewar Shamsuddin yana karasowa bakin kofar bedroom d'in.
yaci gaba da fad'in
"Duk wanda ya yi na gari ai don kansa duniya ce ai gashi ga ita, ta ishe sa riga da wando,
ba sai ya siyo pant d'in sawa ba, zo mu tafi kar muyi latti."
Shamsuddin ya juya Ajeemal yabi bayansa.


Zaraddin yabi bayansu da harara tare da jan tsaki
"Mttss munafukan banza kawai."


Ya fito parlour ya samo laida ya kulle pant d'in ciki yaje ya jefa sa cikin dosbin.
kana ya koma bedroom d'in sa ya wuce bathroom domin yin wanka.


Tun da Aunty ta sami labarin dawowar Zaraddin takuma tsananta tsaro wa Feeryal.
ko da aka gama hutu suka koma makaranta, duk safiyar Allah idan lokacin tafiya makaranta ya yi ita ke fita ta kaita mota da kanta, sai ta tabbatar da sun bar gidan kafin ta koma,
lokacin dawowar su nayi kuwa zata fito ta tsaya har sai taga shigowar su ta kama d'iyarta su shige ciki.




Wannan ke nan.


A can cikin fadar sarkin aljanu.
sarki aljani Matip ne hakimce a kan karagarsa,
ya yin da fadawarsa ke zagaye da shi.
wasu kyawawan yara mata ne guda biyu ke zaune a gefe da gefen sa,
kan wasu kujeru masu tsananin walkiya.
waziri Kutup ya d'ago da dubansa daga kan wani makeken madubi dake ta juyayi kamar ruwa.
ya dubi sarki Matip yana fad'in
"Ya shugaba na, ga dukkan alamu tana cikin koshin lafiya, da kulawar daya dace, babu wani abin cutarwar da yake dumfarota a yanzu."
kai sarki aljani Matip ya jijjiga sannan ya ce
"Akwai kalubale a gaba mai tarin yawa cikin rayuwar ta lokaci baiyi ba tukun,
amma sai dai bayan mu akwai wani wanda zai bayyana zata kuma sami kariyar daya dace feye da wanda muke bata."
kasa waziri Kutub ya yi da kansa ya ce
"Ya shugaba na shin akwai wani wanda zai bayyana ya bata kariyar kwatankwacin irin wanda muke bata."
sarki aljani Matip ya jijjiga kai
"Kwaraikuwa akwai shi zai yayyana."
"A jinsinmu ko a jinsin bil'adama?."
yakuma jefo masa tambayar.
sarki aljani Matip ya gyara zaman sa sannan ya ce
"A jinsin bil'adama zai bayyana, shi babban kariya ne a gare ta."


Wasiri Kutub ya jinjina kai yana mai makikin girman isa irin na wannan bil'adama da har zai fisu bata kariya wanda su duk motsinta tamkar a kan idanunsu yake.
ya ce
"Wani hukunci ne za'ayi wa yaron da ya nimi cutar da ita."
sarki aljani Matip ya ce
"Sa'ar sa guda da ya yi amfani da duhu ba a haske ba, da yayi kokarin cimma burinsa a haske ne da mun makantar da shi, a barshi a iya tsoratarwar da akayi masa, gaba idan bai kiyaye ba zamu waiwaye sa,
a kirawo Tarmuzu yanzun nan."


Nan take waziri Kutub ya murza wata kambu, cikin dakika 1 aljani Tarmuzu ya bayyana, a gabansu ya zube bisa gwuiwowinsa yana fad'in
"Na amsa kira ya shugaba na."
sarki aljani Matip ya dube sa tare da cewa
"Daga yau aikin ku ya kare Chuchu da Chulu ne zasu cigaba daga inda kuka tsaya."
rusunar da kai ya yi yana cewa
"Mun d'auki tabbaci ya shugaba."
ya zaro wata kambun dake d'aure a hannunsa ya aje shi gaban shugaban nasu.
sannan ya mike ya koma cikin fadawan nan ya zauna.
sarki Matip ya dubi yara mata biyun nan dake gefen sa sannan ya ce
"Chuchu Chulu, kuje ku bayyana gare ta."
ai ko nan take suka b'ace.






Yau asabar babu makaranta, Feeryal tasha baccinta har wajen karfe goma kafin ta farka.
ta mike zaune tana mussuke idanunta tare da yin hamma.
fuska ta kwab'e zuwa yanzu tana jin yunwa.
cikin tsiririyar muryarta mai kama da na shagwab'a ta ce
"Ammie yunwa."
jin bataji motsin Ammien nata cikin d'akin ba, sai ta kuma ware idanunta sosai tana kokarin zamowa bakin gado.


Da d'an fuskar mamaki take kallon yara guda biyu tsaye cikin d'akin girmansu dai-dai da ita tsawonsu ma d'aya.
suma kuma ita suke kallo suna yi mata murmushi.
itama murmushin tayi musu, tana fad'in
"Laa ku suwaye ne ya sunan ku,
kunzo da Ammie'n ku ne, ina take tana gurin Ammie na, zaku kwana a gidan mu?."
ta joro musu tambayar tana washe baki.


Baki suka had'a wajen fad'in
"Mu kawayen ki ne, sunan mu Chuchu da Chulu,
bamuzo da Ammie'n mu ba mu kad'ai mukazo, idan kina so sai mu kwana a gidan ku idan kuma kince mu tafi zamu tafi, zakiyi wasa da mu?."
kai ta gyad'a tana cewa
"Har da Miemie ma zamuyi wasan, ku jirani Ammie na tayi min wanka nayi breakfast, zakuga Miemie ma tazo.


"Ke Feeryal da wa kike magana ko mafarki kike?."
cewar Aunty data sako kanta cikin d'akin, hab'a ta rike tana kallon Feeryal data rike kugu tana magana tana lankwasa gefe da gefe irin yaro yana jin dad'in abin da yake ko ya gani na burgewa.
"Ke Feeryal wai dama ba mafarki kike ba, da wa kika tsaya kina ta zuba uban zance haka, ko mirror kike wa magana?
ni da nake ta jiranki ki tashi kiyi wanka, taho maza muje kiyi wanka ki samu kiyi breakfast."
ta janyo hannunta suka nufi bayi.


Kafa tashiga bubbugawa tana fad'in
"Kar ku tafi ku jira ni bari Ammie na ta min wanka,
Ammie kiyi min da sauri zamuyi wasa ne."


Cak Aunty taja ta tsaya tare da waigowa tana bin cikin d'akin da kallo, bayan kayan dake cikin sa babu wani halitta mai numfashi ciki sai ita da Feeryal d'in.
"Ammie kiyi sauri ki min kinga sunzo da kayan wasa da yawa."
tayi maganar tana jijjiga hannun Aunty.
cikin yanayin soma shiga fargaba Aunty ta ce
"Feeryal babu kowa fa a nan sai ni da ke, a ina kika ga wasu har da kayan wasan?."


Baki ta cuno tana jan hannun Aunty ba tare da ta bata amsar tambayar ta ba, sai cewar da tayi.
"Ammie yi sauri kuma yunwa nake ji."


Aunty bata kuma kawo komai a ranta ba, sai tunanin shiririta ne kawai irin na yaro.


Tana gama mata wanka ita tariga Aunty fita a bayin, wanda kafin yau idan tayi mata wanka haka zata langwab'e sai ta d'auko ta ta fito da ita,
ta share mata jiki ta shafa mata mai takuma samata kaya.
dube-dube tashiga yi tana niman ta in da sabbin kawayen nata suke amma bata gansu cikin d'akin ba.
tana shirin fita parlour taje ta duba su ko suna can, Aunty ta fito ta ce
tazo ta sa mata kaya.


Aunty na gama shiryata tayi parlour da sauri, ganin basa nan ma sai ta b'ata fuska tare da cuno d'an karamin bakin ta gaba.
Aunty ta karaso in da take tana fad'in
"Zo muje dinning kiyi breakfast."
"Ammie sun tafi gidan su ne yau she zasu kuma zuwa?."
tayi maganar tana d'ago kanta sama tana duban Aunty.
"Wai su waye ne kam Feeryal?
babu fa wanda suka zo gidan nan, Miemie ma bata zo ba tukun, a ta ina kika gansu mebi mafarki kikayi, taho muje kici abinci."
ta janyo ta suka haura dinning.


Tana cikin yin breakfast d'in Miemie ta shigo da babyn wasan ta,
tana gamawa kuwa sukayi d'akin Feeryal d'in dan suyi wasa a can.
wannan d'akin sunan nata ne kawai amma bata kwana ciki da rana ne kad'ai yake da amfani da dare kuma guduwa take gun Ammie'n ta a can bedroom d'in Aunty take kwana.


Suna shiga bedroom d'in Feeryal ta waro ido tana fad'in
"Laaa dama nan kuka zo, shine baku jirani a bedroom d'in Ammie na nayi wanka ba,
ga Miemie tazo muyi wasa."
dariya duk sukayi mata.
d'aya daga cikin su ta ce
"Ai bazamu tafi ba tun da bamu sallame ki ba, idan kika ce mutafi sai mu tafi, mun jiraki a nan ne kizo muyi wasa."


Murmushi tayi tana jin dad'i tayi sabbin kawaye 'yan wasa.
ta dubi Miemie ta ce
"Miemie zauna muyi wasa da su a gwada girma da babyn mu da nasu wanne yafi girma."


Zama Miemie tayi bawai dan ta fahimci inda batun nata ya dosa ba, suka cigaba da wasa Feeryal tana yi tana magana da bada amsa ita kad'ai.
Miemie kam data gaji
ta mike ta d'au babynta ta kama hanyar fita daga d'akin tana fad'in
"Feeryal ni kam zanje garden nayi wasa ta a can ki zo mu je."
da sauri Feeryal ta mike tabi bayanta tana cewa
"Zo ki basu babyn shine zaki kwace a hannunsu, suna mata kitso."
Miemie kam tuni tayi waje daga d'akin dan bata fahimci abin da Feeryal d'in take nufi ba.
"Miemie ki tsaya ki basu aro ai idan suka gama wasan zasu baki."
tayi maganar tana rike babyn Miemie.


Aunty da ke zaune cikin parlour ta ce
" 'yan'matan Ammie rigima ko, ina naki babyn je ki d'auko mana, gobe zansa diraiba yakai Baba Rabi taje tayi miki shopping ta siyo miki wata tun da bakya son wancan d'in, babbama wanda tafi wannan;
zo abinki 'yammatan Ammie, zo mu zauna a nan."


Kafad'a ta make tare da cuno baki gaba ta ce
"Ammie kawaye na ne fa suke wasa da babyn ta shine ta kwace."


Ido Aunty ta zuba mata Miemie kam tayi waje abinta.


Gwuiwa a d'an sanyaye Aunty ta ce
"Wasu kawayen naki Feeryal?."
"Ba gasu can a d'aki ba shine Miemie ta hanasu abin wasa."
tayi narai-narai na ido zatayi kuka.
Aunty ta mike ta na fad'in
"Yaushe suka zo suna ta ina ko tare da Miemie suka zo."
kai ta girgiza tayi gaba Aunty ta bita a baya.


Daga bakin kofa Aunty ta tsaya tana raba ido cikin d'akin babu kowa, numfashi ta sauke ta ce
"Ina kawayen naki Feeryal ni banga kowa cikin d'akin nan ba."
"Ammie gasu nan baki gansu bane."
jiki a sanyaye Aunty ta girgiza kai tana fad'in
"Ban gansu ba Feeryal, ni banga kowa ba."


Juyowa tayi in da kayan wasan ta suke ta ce
"Ammie na wai bata ganku ba, ai bazata sa Baba Rabi ta siyo muku babban baby ba, Ammie ki ware idonki da yawa zaki gansu gasu nan."
ta yi nuni da hannunta.
sai kuma ta waro ido tana fad'in
"Ammie wai ke bakya ganin su inji wannan?."
takuma yin nuni da hannunta.


Zuwa yanzu jikin Aunty ya fara yin la'asar kai ta gyad'a
"Eh ni banga kowa ba, Feeryal ki dai na wasa babu kowa a nan taho mu tafi."


Aunty tayi waje da sauri zuciyar ta na d'an harbawa.


Daga inda take tsaye cikin parlour tana jiyo sautin maganar Feeryal, wanda yake nuni da tabbas akwai wanda ita take gani harkuma suke magana sakaninsu, wanda ita Aunty bata iya ji ko ganin su.........!












Mommyn Twince ce






🌺🌺 *FEERYAL* 🌺🌺




*NA*
*RASHEEDAT S DIRECTOR*




( _Book 1_)




*~Free page~*






*_Littafin na kud'i ne 500 account no 3170524141 Rashida Salihu first bank ka-ki tura shaidar biya ta WhatsApp number ta 08034690723_*


*____________________________________*


*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation




*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻


https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association


*____________________________________*










🅿️10














Kamar wasa Feeryal ta b'ata tsawon lokaci cikin d'aki, Aunty na zaune a parlour tana jiyo ta tana ta surutu can anjima kuma ta kwashe da dariya.
shiru Aunty tayi da tunani fal cikin ranta.
"Anya Feeryal bata sami matsala ba kuwa?."
tayi wa kanta da kanta tambayar.
me yake kuma shirin faruwa ne bayan lokaci mai tsayo da aka d'auka bata kara ganin wani sauyi tare da ita ba sai yanzu?.
wani b'ari na zuciyar ta ya shiga karanto mata.


"Kar dai ace sai da ta barki kika sakankance da ita kafin ta ke son nuna miki asalinta."


Da sauri tayi kokarin kawar da wad'annan tunanin ta mike ta nufi kichin, tana sawa ranta kawai wasa ce da shiririta irin na yaro.
ta sami Baba Rabi suka cigaba da aiki.




Wasa gaske Feeryal ta share awanni uku tana wasa.
lokaci zuwa lokaci Aunty take zuwa ta leka ko zataga 'yan wasan nata,
amma wayam bata ganin kowa.
yoghurt da cake kad'ai ta fitowa ta d'auka ta ce wa Aunty zasuje suci su sha da kawayenta.
ita dai Aunty to kawai ta bita da shi.
ganin batada niyyar barin abin da takeyi bare ma harta fito ta ni mi abinci, Aunty ta tako bakin kofar ta leko tana fad'in
"Feeryal ya isa haka wasan taso kizo kiyi wanka ki ci abinci lokacin wanka ya yi."


Fuska ta b'ata ta cuno baki gaba
"Ammie wasa fa mukeyi."
kai Aunty ta dafe
"Oh Allah
ki ce da kawayen naki suma suje suyi wanka, kuma kar su dawo,
sai gobe, maza taso kizo muje."


Feeryal ta juya tana kallon wani gefe sannan ta ce
"Kuma kuje ayi muku wanka nima Ammie na zatayi min."
murmushi ta sake sai kuma ta d'aga hannu tana bye-bye.
sai da ta daina ganin su kafin ta sauke hannunta.


Aunty na tsaye tana kallon ikon Allah.
"To taso muje."
ta fad'a ganin ta sauke hannun nata, ta ruko ta sukayi waje.


Washegari da safe Aunty na kichin tabar Feeryal tana bacci.
tana gama abinda take ta dawo d'aki taga bata nan.
bathroom ta shige tana kiran sunan ta,
tsayuwa tayi ganin bata ciki, sai ta juya tanufi kofa tana cigaba da kiran ta.
bata parlour bata kuma cikin bedroom d'inta in da take wasa ciki.


Daddy dake zaune cikin parlourn ya dube ta yana fad'in
"Ko tana toilet ne kin duba can."
"Babu in da ban duba ba Daddy."
batare daya d'ago daga kallon labaren safe da ake a TV ba ya ce
"Zata fito ai tashige wani gurin ne."


Bata kuma magana ba dan ita kam lungu da sako duk ta duba bata nan.
da d'an mamaki ta tsaya cikin parlour da tunanin to ina taje.
"To ina taje? kar dai ace taje gurin Miemie ce."
tayi maganar tana nufar kofar fita daga parlour'n, da sauri.


Tana fita farfajiyar waje, cikin hanzari ta nufi bakin get d'in side d'in ta.
har tarike karamar kofa zata bud'e, taji yo dariyar ta ta can baya ta cikin garden.
da sauri ta waigo tare da soma nufar gurin da take jin sautin dariyar nata.
da mamaki take kallon ta kan lilo ita kad'ai, lilon na lilata sai b'arkewa da dariya ta ke tana kuma fad'in
"Ku kara yi min sau biyar ni ma zan muku."


Hannu Aunty ta d'aura a kirjinta tana son dai-dai nutsuwarta, cikin karfin hali daga in da take takira sunan ta.
"Feeryal."
da sauri ta kalli gurin da Aunty take sai kuma ta ce
"Kutsai da ni ga Ammie na zanje gurin ta, zan dawo na rama muku."
ta diro a kan lilon da gudu ta taho in da Aunty take, ta ruko hannunta tana d'an bubbuga kafa cike da shagwab'a take fad'in.
"Ammie yunwa nake ji."


Aunty ta had'iye tsoro mai had'e da fargaban da yake taso mata ta dube ta a hankali ta ce
"Shine kika tsaya anan kina kuma jin yunwa iye Feeryal? to muje kiyi wanka sai kici."
sun kusa isa bakin kofar parlour Feeryal ta juyo tana fad'in
"Kuma zakuje Ammie na tayi muku wankan kuci abinci ne?."
da sauri Aunty ta waigo, bataga kowa ba sai ji da ta kuma tana fad'in
"Ammie suma zakiyi musu wankan ko?."


Bata iya yin magana ba har suka shige cikin parlour.


Daddy na ganin su ya ce
"A'ina kika samo ta, Feeryal ina kkje da safiyar nan?."
Zamewa tayi a hannun Aunty ta koma jikin sa tana fad'in
"Daddy wasa muke yi da kawaye na."
"Wasa kuma Feeryal da safen nan, baki ji ana sanyi ba,
ko kayan sanyi fa babu a jikin ki, sanyi zai kamaki je maza Ammie'n ki ta sa miki rigar sanyi."
ta ce to. ta mike ta dawo gurin Aunty da ke tsaye.
Aunty ta kad'a keyarta ta ce
"Je maza ki jira ni a bathroom ina zuwa, kice da kawayen naki kar su biyo ki."
kai ta gyad'a da gudu tayi cikin bedroom.


Fuska Aunty ta kwab'e tana kallon gefen da Daddy ya ke.
murmushi mai sauti ya yi, kana ya miko mata hannu ya na fad'in
"Taho muji ya akayi ne, kefa wani lokacin rikicin ki yafi na d'iyarki Feeryal."


Hannu tamika masa ya janyo ta tazauna gefen sa.
sosai ya maida hankalin sa gare ta,
"Mene ne ko angaji da zaman gida ne, nayi mana bukin zuwa London."
kai ta girgisa sannan ta ce
"Yanzu ina fad'a sai kace gizo ne, kai bakaji Feeryal ta ce maka taje wasa ne da kawayenta ba, sai tayi ta magana ita kad'ai fa tun jiya,
kamar da wasu take magana, kuma har nuni tayi min ta ce ga wad'an da take maganar da su,
nikuma banga kowa ba."
murmushi ya yi, ya ce
"Gimbiyata ban isa in fad'i ba yanzu kam, dan naji da kunnena ta fad'a,
magana kuma a gun yaro shi kad'ai, ba yana nufin da wani agun bane,
yaro shi komai nashi na wasa ne."
baki ta tsuke bata kuma cewa komai ba, dan tasan duk yadda tayi da shi bazai tab'a fahimta ba.
ta zame jiki tayi d'aki.



Tana shiga bathroom ta isketa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login