Showing 60001 words to 60654 words out of 60654 words

Chapter 21 - FEERYAL BOOK COMPLETE DOCUMENT by RASHEEDAT S DIRECTOR.txt

07 Feb 2025

6786

wata babba dudu 15 yeah gare ta, in zaka shekara kana mata magana kan wani na son ta bazata ce maka komai ba,
FEERYAL ba irin sauran yaran da ka sani ba ne,
a yanzu yarinya mai shekarun ta tasan ciki da wajen soyayya,
amma ban da FEERYAL har yanzu da sauran ta,
so duk wan da ya biyo ta hannu na kan yana son ta, bana matsa mata kan dole sai ta so shi,
sa boda har yanzu bata da wayon yin soyayya,
bana son kuma na tauye mata hakkin ta,
nafi so da kanta taji tana so, ba tare da an matsalta mata ba,
bare kuma yanzu ne ma zata fara karatu, ai da sauran ta tukun, duk suyi hakuri, su jira."
"To mun aje kokon baranmu a layi kar kuma a zo a wuce kanmu."


Tana shirin bashi amsa taji kamar ana magana sama-sama.
shiru tayi tare da kasa kunne tana jiyo maganar can kasa.
da sauri ta zabura tamike, da sauri ta masa jikin window ta zuge labule ta leka.
kirji ta dafe da karfi ta ce
"Mun shiga uku!."
Nasir da keta magana tun d'azu bata bashi amsa ba ya ce
"Yaya dai lafiya Maryam me ya faru?."
"Nasir kamar b'arayi ne suka shigo mana gida, ga mutane a bakin get da bindigogi kuma ina jin magana a parlour, da muryar su Abba."
da sauri Nasir ya ce
"B'arayi kuma anya kuwa Maryam ko dai ma'aikata kika gansu, kinfa san yanzu dare tayi biyu saura yanzu."
Tass karar harbi yasashi had'iye ragowar maganar sa, Maryam ta saki kara tana toshe bakin ta.


A parlour kuwa Abba da Hajja Umma ne shinfid'e a kasan carpet in da b'ayin suka sasu kwanciya plat hannayen su a bayan ke yarsu.
d'aya daga cikin b'arayin da yake hakimce a kan kujera, ya d'aura kafa d'aya kan d'aya yana busa sigari.
ga dukkan alamu dai shine babban su ya ce
"Ku shiga ku fito da sauran mutanen akwai saura a ciki."
da sauri Abba ya ce
"Ku kyale su dan Allah ko ma meye mu kare da ku anan,
in dai kud'i ne akwai ko nawa kuke so zan baku,
wad'ancan yara ne dan Allah ku rabu da su.


Bakin bindiga ogan nasu ya d'aura masa a kai ya ce
"To ai d'aukar amarya muka zo, idan muka tsaya daga nan me mukayi ke na, ku tsaya a nan ku zaku mana rakiya."
ido Abba ya rumtse da karfi jin yadda yake dannan bakin bindigar a kansa da karfi.


A razane Maryam ta sake wayar ya fad'i kasa jin an banko kofa.
jiki na rawa tashiga ja da baya.
su biyu suka shigo d'akin, dukkanin su rike da manyan bindiga.
d'aya ya yi kan FEERYAL dake bacci ya fisge blanket d'in da take dukunkune ciki, ya fizgota kasa ya dire ta kan kafafun ta.
kara ta sake a gigice san da ta ware idanunta masu d'auke da bacci a kan su,
tuni ta nimi baccin ta rasa, tuni jikin ta ya d'auki kyarma.
gashin kanta ya rike ya turo ta waje, d'ayan ma ya janyo Maryam.
suna zuwa tsakiyar parlour'n ya angiza ta ta zube kasa.
kara ta sake tana rike kafarta data fad'i a kai.
kallo d'aya Maryam tayi masa ta gane shi, shine wan da yasha gaban su d'azu da yamma a hanya har Feeryal ta razana da tukin ita ta dawo da su gida.


Ogan b'arayin ya mike da sauri ya sunkuyo gabanta tare da rike kafar da take rike da shi,
wan da tuni hawaye yashiga zarya kan kyakkyawar fuskarta.
yad'aga kai ya dubi wan da ya wurgotan ya ce
"Kai baka da hankali, idan ka b'alla kafar amaryar da wani kafa zata tafi ke nan,
wannan kyakkyawan furen a hankali zakayi mata karta tsinke."
ya saka yatsarsa a kan fuskar ta ya lakato hawayen ta ya ce
"Wayyo Allah me yasa ka firgitata baka taso ta cikin ruwan sanyi ba,
da nasan bazaku iya ba da da kaina naje, na taso ta,
yi shiru lu'u-lu'u ki dai na kuka."
sai kuma ya yi zaman dirshem
ya nad'e kafafun sa a gabanta yasa annu biyu ya dafe kumatun sa yana kallon fuskarta,
sai kuma da sauri ya........!










Mommyn Twins ce

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login