Showing 3001 words to 6000 words out of 60654 words

Chapter 2 - FEERYAL BOOK COMPLETE DOCUMENT by RASHEEDAT S DIRECTOR.txt

07 Feb 2025

6769

alla-alla ta yuya ta ce
"Daddy wai kazo inji Hajiya."
tana gama fad'i ta juya da sauri.
gudu ta saka bata tsaya ko ina ba sai side d'in Hajiya Halima mahaifiyarta kuma uwargida ga Alhaji Abubakar Fiya.
a parlour ta tadda uwar tata, da kuma Hajiya Karima mata ta biyu ga Alhaji Abubakar, da y'ay'an su duka.
kamar zata zube kasa cikin haki take fad'in
"Mommy Aunty ta haihu."
cikin rashin fahimta Hajiya Halima wato Mommy ta ce "Ke wata Aunty? kin shigo a razane duk kin razana mutane."
murya na rawa cike da tsugudidi ta ce
"Aunty Fatima wlh yanzu nan naganta tana baiwa jariri nono, Daddy na zaune a gurin."


Ido Hajiya Karima ta gwalalo tare dare da fad'in
"Zancen banza kai yaushe akayi cikin da za'a yi haihuwar har kowa ya kasa sani, ai wannan sai dai taga haihuwa a tsuliyar wani badai a nata ba."
"Wlh Umma Karima naganta da idona tana bawa yaro nono."
kirji Hajiya Karima ta buga har suna had'a baki da Mommy wajen fad'in
"Yaushe tayi ciki har ta haihu bamu sani ba."
"Wlh ni dai na ganta dama Hajiya ce ta aike ni kiran Daddy tun jiya take ta kiransa a waya baya d'auka,
shine tace naje na kirawo mata shi dan tasan yana can makale wajen kinibabbiyar matar nan tasa, bari ma naje na sanar mata sabon labari."
tafice da gudu tanufi sashin Hajiya wato kakar su.


Tun daga bakin kofa take fad'in "Hajiya Hajiya Hajiya."
wata dattijuwar mata dake zaune a wani kayataccen parlour tana sanye da gilashi a idanunta, hutu da kwanciyar hankali sun bayyana a kijinta, wanda ya b'oye tsufarta, zaka iya mata kallon daya gaza shekarunta sabar hutu.


"Ke wani irin shashancin kira ne wannan, sai naci mutuncinki Farida, ina tun d'azu na aike ki sai yanzu kikaga damar dawowa ko."
cikin rad'a da iya gulma ta ce
"Hajiya wlh Aunty ta haihu Daddy yana can."
baki Hajiya ta karkace ta ce
"Ke Farida Fatima ce ta haihu cewa akayi miki haihuwar wasa ce, shekara nawa tana zaune sai dai taci taje ta juye a shadda, ko b'atan wata bata tab'a yi ba,
wannan da ita yafara aura nasan bazata tab'a barinsa ya kara aure ba, da ni da ganin jikokina ta gefen sa kuwa har abada, sai dai in cikin abinci tayi ta haifa a shadda, bari naje na ganewa idona."
"Wlh Hajiya kije kigani da gaske ne."


Hajiya ta mike tanufi kofa tana fad'in
"Yanzu ma kuwa, dan rashin daraja Fatima tafi masa ni, tun jiya baizo ya gaishe ni ba yana makale a gurin ta."


A b'angaren su Mommy kuwa bakaramin girgiza sukayi da jin lamarin ba, dukkanin su suka nufi sashin Aunty dan gane wa idon su abin da ke faruwa.
a kusan tare suka iso da Hajiya dan ita direban ta tasa ya kaita side d'in Aunty'n dan tafiyar tafi yi mata sauki.
suna shiga parlour'n kowa yatsaya cike da d'in bin mamakin ganin jaririya a hannun Aunty tana shayar da ita.
hankali tashe Mommy da Umma Karima suke kallon-kallo, kowa da irin abun da yake sakawa a ransa.
hajiya ta rafka wani uban salati tare da tafa hanu tana fad'in
"Ikon Allah Abubakar ina cikin gidan ayi haihuwa ban sani ba, kamar yadda bansan da cikin ba, Eh lallai ta wanke ta baka kasha, ka mance da uwar da ta haife ka."


Da sauri Daddy ya mike yana fad'in
"Sannu da zuwa Hajiya yanzu nake shirin zuwa gaishe ki, bismilla ga guri zauna."
hannu ta d'aga masa tana fad'in
"Ba zama ne ya kawo ni ba, na ce yaushe ta haihu ban sani ba!."
kai ya sunkuyar kana ya d'ago ya dubi mahaifiyar tasa kana ya ce..........!












Mommyn Twins ce








🌺🌺 *FEERYAL* 🌺🌺




*NA*
*RASHEEDAT S DIRECTOR*




( _Book 1_)




*~Free page~*






*_Littafin na kud'i ne 500 account no 3170524141 Rashida Salihu first bank ka-ki tura shaidar biya ta WhatsApp number ta 08034690723_*


*____________________________________*


*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation




*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻


https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association


*____________________________________*






Bismillahirrahmanurrahim






🅿️2








"Da ma Hajiya zanzo muyi magana, amma tun da har kinzo ki zauna kiji yadda akayi zata haihu ne baki sani ba."
"Ba gashi kuwa sai zuwa nayi naga d'a a hannu ba, ai baka d'auke ni da mahimmanci ba, narasa me ke damunka Abubakar akan Fatima duk ka susuce kazama wani iri, tun jiya nake kiran ka a waya sabo da kuna nakudar munafurci kaki d'aga wayar ma, bare har kazo in da nake,
Allah yasa kafin ta haihu dubunta sun haihu,
ko wani munafurcin ne na b'oye cikin da haihuwar oho."
wani irin mummunar fad'uwar gaba Umma Karima ta ji.
yanzu bawai haihuwar ce ke firgitata ba, duk da tabbacin da take da shi kan cewa bazata tab'a haihuwa ba har abada, ga kuma akasin hakan ta gani.
fatan ta d'aya kada a ce namiji ta haifa.
a b'angaren Mommy ma haka abun yake.
mita ta shiga yi tana dad'a ingiza Hajiya
"Yanzu har rashin muhimmancin mu yakai ta haihu a cikin gidan nan bamu saniba, idan an b'oye ciki sai a b'o haihuwa, haba Alhaji me ka mai da mu haka."
Hajiya ta cab'i zancen da fad'in
"Marasa mutunci mana haka ya mai da kowa, to ka zauna da matarka kucigaba da munafurcin ku, kada ka sake kazo in da nake."


Ta juya tana kokarin fita da sauri ya tare ta
"Hajiya kiyi hakuri ki saurare ni,
bafa haihuwa Fatima tayi ba, sai kuma tayi ciki har ta haihu ki gaza sani, abun da ake fatan samu idan aka samu ai kowa sai ya sani,
bana gida ba har da na waje, kowa za'a sanar masa yataya mu farinci,
jiya a hanyarmu ta dawowa muka tsinci jaririyar a cikin ruwa, da alama had'ari iyayen ta sukayi tana bukatar taimako,
shine muka d'auke ta, likita ya shaida mana bazata iya rayuwa ba sai da nonon uwa shiyasa aka samarwa Fad'imatu ruwan nono domin ta ceto rayuwar ta."


Wani irin zabura dukkanin su sukayi.
Hajiya ta bigi kirji ta tuma tsalle ta zube kasa ta saka hannu a ka tana fad'in
"Wayyo Allah Abubakar da Fatima zasu kashe ni, tsintar ta kukayi kuma a cikin ruwa, anya Abubakar
kanka d'aya kuwa ko aljanu sun shafe ka ne,
ku tsinci 'yar kuma acikin ruwa ma har ka lamunci matarka ta shayar da ita,
sabo da karasa 'ya'ya ne ko me?
idan ita juya ce bata haihuwa ai kai da 'ya'yan ka ta ganka tafe da kafafun su,
duk basu ishekaba har sai kanimi kari da 'ya'yan aljanu."


Tamaso ta leka fuskar Feeryal dake rungume a hannun Aunty, data rungume ta tsam kamar za'a kwatar mata ita.
Hajiya takuma zabura tare da mustsuke idonta tana fad'in
"Lahaula maganin baki wasayyahuuuuu ya tsaya a kanki Fatima!
Abubakar d'iyar aljanu kuka d'auko kuka kawo mana gida,
wlh ko shakka babu wannan d'iyar aljanu ce, tun da nake ban tab'a ganin mutum irin wannan ba,
ko a fina-finan masu jajayen kunnuwan da nake gani ana haskosu a TV,
dubi kalarta dubi kalar kwayar idanun ta, sam basuyi kalar na mutane ba,
kwayar ido kamar na magen mayu wlh ba mutum bace;
maza-maza kuyi gaggawar d'aukar 'yar su ku mayar musu in da kuka d'auko musu ita,
tun kafin bala'i ya sauka a gidan nan,
dan bazamu iya da fad'an aljanu ba,
dan babu kaura cikin dangin mu,
wani bala'in kuke son d'auko mana, zaku d'auko aljanar ruwa ku kawo mana ita gida."


Mommy da Umma Karima har suna rige-rigen zuwa leka fuskar yarinyar, bakaramin firgici suka shiga da ganin halittar 'yar ba,
'ya'yansu ma kowa sai da yaje yagano fuskar ta.
Mommy tashiga zabga salati da tafa hannu tana fad'in
"Wlh aljana ce Hajiya dakur'ani bazamu zauna da aljanar ruwa a gidan nan ba, ko a fita da ita ko mu mufita da 'ya'yan mu, dan ambaliyar ruwa bazataci da mu ba ehe."


Umma Karima ta karkata baki cike da rashin mutunci tana aikawa Aunty kallon banza ta ce
"An dai yi asara rashin haihuwa nason bud'a miki kai shine har zaki d'auko aljana ki kawo mana ita cikin gida,
to wlh ba a gidan nan ba, idan haihuwar abin banza ne ki haifa mana,
sai kinje kin d'auko aljanar ruwa kin kawo mana damuwa."


Rumtse ido Aunty tayi tana jin yanda maganganun su ke mata yawo cikin kwakwalwa.
da sauri Daddy yataro Hajiya ganin yadda take shiga bata nan take fita ba.
ya ce
"Hajiya kiyi hakuri amma ba aljana ba ce mutum ce, ina kyautata zaton watakila badaga yankin kasarmu take ba,
shi yasa kamanninta ya bambanta amma mutum ce ita irin mu."
"Inji uban wa tun da kake katab'a gani mutum kyakkyawa irin wannan?
kana kallon aljana kiri-kiri kace mutum,
dama ance aljanun ruwa kyawawa ne gashinan kiri-kiri ina gani kace ba haka ba,
kai Ajimi kirawo min Sulaiman da Tukur yau zan bar gidan nan dan bazan zauna da aljana ba."


Ajeemal ya juya yana jan kwafa, sam baya son fitinar kakar nan tasu.


Hajiya ta cigaba da fad'a har tana kumfar baki, su Mommy na tayata.
batare da b'ata lokaci ba Alhaji Sulaiman da Alhaji Tukur suka amsa kiran mahaifiyar tasu.
Hajiya na ganin su takawo kuka ta saka tana sharb'e hanci da fad'in
"Zamata yakare a gidan nan Abubakar ya zab'a ko ni ko aljanar ruwa da matarsa."
da sauri suka karaso in da take sukashiga bata hakuri, Alhaji Sulaiman ya ce
"Hajiya dan Allah kiyi hakuri zo muje sashin ki muyi magana."
da kyar suka janye ta zuwa sashin nata.


Numfashi Daddy ya sauke ganin fitarsu kana ya maida dubansa kan Mommy da Umma Karima ya ce
"Duk wacce bazata iya zamaba ta kama gabanta."
yana kaiwa nan yajuya yabi bayan su Hajiya.


Mugun kallo suka wasawa Aunty Umma Karima ta ce
"Bokanki yafad'a miki karya sai dai ke kibar gidan nan ba dai mu masu 'ya'ya ba."
Mommy kuwa kwafa tayi tare da kuma wasa mata harara tajuya takad'a keyar 'ya'yan ta tana fad'in
"Maza kubar nan kada aljana tashiga jikinku."
Murmushin takaici Aunty tayi tare da bin bayansu da kallo, tana mai dad'a rungume Feeryal ajikinta.


A can sashin Hajiya kuwa sosai ta tubure ita ala dole sai dai Daddy ya zab'i ko ita ko aljanar ruwa,
dan bazata zauna da aljana a gida d'aya ba, bare ta shafe ta ta shafi jikokinta.
da kyar suka shawo kanta da alkawarin za'a mai da yarinyar inda aka d'auko ta.


Ko da suka fito daga sashin nata Alhaji Sulaiman wato Abbieh da Alhaji Tukur Dad suka dubi d'an uwan nasu.
Dad ya ce
"Yaya ina ganin a d'auki yarinyar nan a mayar da ita in da aka sameta ina ganin shine kad'ai samin masalaha,
Hajiya tayi fushi sosai."


Kai Daddy ya girgiza sannan ya ce
"Adai canza mata wani gurin dai-dai ta huce, ta ya za'a ce a maida ta cikin ruwa kisan kai ke nan zamuyi,
yarinyar nan ba aljana ba ce mutum ce, imma aljanar ce iyayen ta suzo su d'auke ta anan ba sai an kaiga cutar da rayuwarta ba,
sannan idan aka rabata da Fad'imatu itama an cutar da rayuwarta,
dan yanzu tamkar mai sabuwar jego take."
"Yaya to kayi wani abu dan Allah dan gujewa fushin hajiya."
cewar Abbieh, kai Daddy ya girgiza kana ya ce
"Insha'allah."




Aunty na zaune tayi jigum Daddy ya shigo, ya zauna gefen ta.
da sauri ta dube shi jiki a sanyaye ta ce
"Hajiya bata hakura ba ko?
dan Allah Daddy kar a rabani da Feeryal wlh ina son ta."
takarashe maganar da damke hannunsa murya a marairaice tamkar zata zubda kwalla.


Hannunta yakuma rikewa cikin nashi kana ya ce
"Insha'allahu baza'a rabaku ba nayi miki alkawari."
wasu hawaye ta share ta ce
"Nagode Daddy." murmushi mai sauti ya yi tare da jan hancinta
"Ammie'n Feeryal a kwantar da hankali haka a daina damuwa da yawa."
kai ta girgiza tana mai da masa murmushin.




A sashin Hajiya bayan fitar su Daddy da d'an jimawa, Hajiya ta cewa Farida taje ta duba mata aljanar tana nan har yanzu ko an tafi da ita.
ko da Farida taje sashin Aunty'n a kulle yake tadawo ta shaidawa Hajiya.
Hajiya tayi kwafa dan a zaton ta sun tafi mai da jaririyar in da suka d'auko ta ne.
ta gyara zama ta soma cin abincin da kulu mai aikin ta takawo mata yanzu,
tana fad'in
"Iya shegen banza da raina da lafiya ta ina gidan wai sai abin da Fatima ke so za'a yi,
rashin haihuwa hauka ce, da zata fara bin teku tana d'iban 'ya'yan aljanu tana kawo mana cikin gida;
wan nan badun daga gidan arziki tafito ba sai na ce wani muguntar take son kitsawa,
takawo aljanu su kwashe mana dukiya su kai mata gidan iyayenta."


"Hajiya wai ashe aljana Hajiya Fatima ta kawo wlh kar kiga yadda na razana aljana kuma a cikin gidan nan, to ita meye gamin ta da aljanu kuma."
cewar Kulu tana zama kan kujera d'an nesa da Hajiya.
Hajiya takai loman katon nama baki tana fad'in
"Niman jaraba mana da niman ganin bayan mutum, to ni nafi karfinta da jikokina,
sai dai taje can ta karata da aljanun, ba dai a gidan nan ba kam, je ki kawo min lemon gorar nan mai d'an sanyi."
Kulu ta tafi tana rike hab'a da mamakin lamarin.


Kwanan Feeryal uku a gidan batare da kowa yasan tana nan ba, dan kowa ya yi zaton da hajiya ta tada bori an mai da ta in da aka d'auko ta.
itama Hajiyar sam batasan tana nan ba.


Umma Karima ce cikin Bedroom in Daddy, shigowarta kenan bayan komawar ta part inta da asuba, data kwana a sashin nasa,
anje anyi wanka an cab'a kwalliya, an shafo wasu turaruka masu tsayawa a kuwa.
ganin baya side d'in gaba d'aya, ta koma side d'in ta,
ta tura babbar 'yarta Saddiqa taje ta duba mata Daddyn su yana part d'in Aunty'n su.


A bakin get in shiga side in Aunty suka had'u da Ajeemal zai wuce side d'in Hajiya.
yana ganin ta ya sai da ta.
"Ina zakije?."
ta ce "Umma ce ta ce naje na duba Daddy a side in Aunty."
ya ce "Wuce ki koma kice baya nan."
baki ta zumb'uro, tana ganin wucewar sa da gudu tayi cikin side d'in.
tana shiga parlour'n Aunty kai tsaye ta wuce cikin bedroom inta babu ko knocking bare sallama.
Aunty na zaune bakin gado tana shirya Feeryal data yi mata wanka,
jin an turo kofa yasata d'agowa tana duban mai shigowar.
ganin Saddiqa ce, ta girgiza kai tana fad'in
"Saddiqa bana ce in zaku shigo kurika yin knocking da sallama ba, ba kyau shigowa d'aki kai tsaye batare da yin sallama ko niman izini ba,
to ya akayi?."
Aunty tayi tambayar tana mai da hankalinta kan shirin da take yiwa Feeryal.
Saddiqa ta juya ta fita bare da ta ce komai ba, kai takuma girgiza wa ta cigaba da abin da ta ke.


Da sauri ta koma side d'in su, tun kan takaraso in da Umma Karima ta ke tashiga fad'in
"Umma Umma Umma wlh Aunty tadawo da aljanar nan, naganta tana sa mata kaya."
huf Umma Karima ta mike ta ce "Ke wai da gaske kinga yarinyar nan a sashinta, eh lallai Fatima anyi bakar munafuka wato boye 'yar tayi,
ko komawa tayi takuma d'auko ta, to wlh sai ta bar gidan nan."
tayi waje fuuu sai sashin Hajiya.


Kirji Hajiya ta buga da jin abun da Umma Karima tazo dashi.
Hajiya ta mikawa Umma Karima waya tana fad'in
"Lalub'o min lambar Abubakar yanzu-yanzun nan, wai ni Abubakar zai maida mutumiyar banza, yazab'i tsintacciyar aljana a kai na."


Daddy na d'aga wayar Hajiya tafashe da kuka tana fad'in
"Ni zakayiwa haka Abubakar wlh yau babu abin da zai zaunar da ni a gidan ka, yanzu-yanzun nan zan bar maka gidan ka,
kacigaba da zama da matarka da bakason b'acin ranta da aljanar da ta tsinto."
Hajiya ta kashe wayar tana sharb'ar hanci, tamike ta nufi bedroom d'in ta tana fad'in
"Ina zan iya zama da annoba a gida d'aya, gara natattara inawa-inawa na koma Yalwa yafi min kwanciyar hankali."


Umma Karima ta saki murmushi akasan ranta tana fad'in
"Fatima ke karamar makira ce."
tamike tafice takoma part d'inta.




Cikin hanzari Daddy yashigo side d'in Hajiya, yana shiga parlour'n ta,
Hajiya nafitowa janye da akwati.
da sauri ya isa inda take yana fad'in
"Dan Allah Hajiya kiyi hakuri kada ki tafi."
"Bani guri da alla! in zauna inmaka me?, ni da bani da mutunci agurin ka,
gara nabaka guri kacigaba da zama da wad'an da kake ganin su da kima,
ina dalili ina mafari zama da aljana guri guda, ina bil adam, kai da kazabi haka sai kayi ta zama da ita,
amma kasani idan jikokina suka sami wata matsala bazan yafe maka ba!."


Da sauri Daddy yarike akwatin ganin tana kokarin tafiyar da gaske ya ce
"Hajiya dan Allah kiyi hakuri ki gafatarce ni, kada ki tafi, za'a maida ita inda aka d'auko ta dan Allah kiyi zamanki."
"Ni Abubakar ai ka gwada min iyakata aljanar ruwa tafiye maka ni,
ni uwar da na haife ka naci kashinka, ni Abubakar ni."
Hajiya tasaki kuka tana sharb'e hanci da bakim mayafinta.
akwatin ya karb'a a hannunta yana
"Yi hakuri dai Hajiya yanzu za'a fita da ita."
yaja akwatin ya maida shi ciki bedroom, yafito ya isketa zaune a parlour.
hakuri yacigaba da bata sai da yaga ta d'an sauko kafin yafita.




A b'angare Aunty lokacin da Hajiya ta kira Daddy shigowar sa side d'in ta kenan, ko zama baiyi ba yafita zuwa kiran Hajiya.


Kuma jin motsi yasa Aunty fitowa, ganin Daddy ne ta karaso in da yake jiki ba kwari.
murmushi ya yi mata domin karfafa ta, fuska ta dan marairaice ta ce
"Hajiya bata hakura ba ko?."
zama ya yi a bakin gado yana fad'in
"Zanji da ita zaki rayu da Feeryal insha'allah, nayi miki alkawari."
zama tayi gefen sa kana ta ruko hannunsa tana jaddada godiyar ta a gare sa.
tana mai alfaharin kasantuwar sa a matsayin abokin rayuwarta,
dan bai tab'a rageta da wani abu ba, duk abin da ta nima a gurin sa tana samu; hakan kuma baya rasa nasaba da so da kauna da kuma yardar da yake yimata.


Wanda itako take saka masa ta hanyar nuna masa tsantsar kulawa mai had'e da zallar soyayya da nuna damuwa kan abin da ka damu da shi.


Hakan yasa abokan zaman ta suke ganin tagama mallakesa ta hanyar asiri, wan da sam abun ba haka yake ba, Hajiya Fatima babu abin da ta tsana take kyamatar sa sama da bin bokaye da malamam tsubbu.


Hajiya Fatima mata ce mai hakuri da juriya gami da kawaici, tana da matukar hakuri ga ladabi da biyayya; tsafta iya girki iya kwalliya, iya tafiyar da miji yadda ya kamata, uwa uba ruko da addini.
shiyasa tazamo lamba d'aya a gurin maigidan nata wato Alhaji Abubakar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login